Abba ya rantsar da sabon Kwamishinan Gidaje na Kano
Published: 17th, March 2025 GMT
Gwamna Abba Kabir Yusuf a wannan Litinin ɗin ya rantsar da sabon Kwamishinan Ma’aikatar Tsarawa da Bunƙasa Gidaje ta Kano, Ibrahim Yakubu Adamu.
Wannan dai shi ne karo na huɗu cikin ƙasa da shekaru biyu ke nan da gwamnan yake faɗaɗa majalisar zartarwa jihar ta Kano.
Ana zargin wa da ƙani da yi wa almajiri yankan rago a Adamawa Majalisar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna FubaraAminiya ta ruwaito cewa gabanin wannan sabon naɗin, Ibrahim Yakubu Adamu shi ne Shugaban Hukumar Tsara Birane ta Kano KNUPDA.
Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Kano, Haruna Isah Dederi ne ya jagoranci rantsar da sabon Kwamishinan da aka gudanar a fadar Gwamnatin Kano.
Da yake jawabi, Gwamnan ya yaba wa sabon kwamishinan wanda ya ba da shaida kan ƙwazo da kuma ƙwarewa haɗi da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban birnin na Dabo.
Gwamnan ya buga misali da yadda sabon kwamishinan ya jagoranci aikin tsarawa da kuma bunƙasa rukunin gidajen nan na Kwankwasiyya da Amana da Bandirawo waɗanda aka gina a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015 a zamanin gwamnatin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Sabon kwamshinan wanda ƙwararren mai zana gine-gine ne, Gwamnan ya hikaito yadda ya taka rawar gani wajen tsarawa da kuma aiwatar da wasu muhimman ayyukan gine-gine a lokacin da yake Kwamishinan Ayyuka da Gidaje a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.
A wani labarin mai nasaba da wannan, Gwamnan ya umarci duk waɗanda suka mallaki gida a rukunin gidaje na Kwankwasiyya ko Amana ko Bandirawo da su tabbatar sun tare nan da watanni uku ko kuma su sanya ’yan haya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ibrahim Yakubu Adamu Kwamishinan Bunƙasa Gidaje da sabon Kwamishinan
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da tsaro
Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Masarautar Saudiyya sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya domin ƙarfafa dangantakar tsaro da haɗin gwiwar soja tsakanin ƙasashen biyu.
A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle kan yaɗa labarai Ahmed Dan Wudil ya fitar, ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta shafi muhimman fannoni kamar musayar bayanan leƙen asiri, horas da sojoji, haɗin gwiwa a harkar samar da kayan yaki da kuma gudanar da ayyukan tsaro tare.
Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa ’Yan jaridar Daily Trust da Trust TV sun lashe kyautar binciken ƙwaƙwaf ta Wole Soyinka ta banaMinista Matawalle ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da Dakta Khaleed H. Al-Biyari ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Masarautar Saudiyya.
Ministar ya bayyana cewa, wannan ci gaban babbar dama ce da za ta ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu da kuma taimakawa wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.
Ya ce, ma’aikatar tsaron Najeriya tana maraba da wannan ci gaba, tare da fatan hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ake fama da su a sassa daban-daban na ƙasar.