Aminiya:
2025-11-03@10:10:59 GMT

Majalisar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara

Published: 17th, March 2025 GMT

Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Similanayi Fubara daga muƙaminsa.

Hakan na ƙunshe cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai cike da ƙorafi da majalisar ta fitar, inda take shirin tsige Gwamnan tare da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu.

Trump zai tuntuɓi Putin kan yaƙin Ukraine Madalla da hutu ga ’yan makaranta domin azumi

A cikin wasiƙar wadda take kafa hujja ta tanadin da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya yi, ’yan majalisar sun zargin Gwamna Fubara da kashe kuɗaɗen jama’a ba bisa ƙa’ida ba.

Haka kuma, wasiƙar ta ce Gwamna Fubara ya hana majalisar gudanar da aikinta, da kuma naɗa mutane a muƙaman gwamnati ba tare da tantancewa ba.

Kazalika, tana tuhumar Gwamnan da ƙin biyan albashi da wasu alawus alawus da aka ware wa majalisar ciki har da dakatar da albashin Sakataren Majalisar, Emeka Amadi.

A bayan nan ne tsohon Gwamnan Ribas kuma Ministan Abuja mai ci, Nyesom Wike, ya ce ba zai hana majalisar sauke nauyin da rataya a wuyanta ba wajen tsige Gwamna Fubara.

A wata hira da manema labarai da ya gabatar ranar Laraba a Abuja, Mista Wike ya ce ’yan majalisar ba su yi laifi ba idan suka yanke shawarar tsige Fubara, saboda ya aikata laifukan da suka cancanci a tsige shi, ciki kuwa har da riƙe musu albashi na tsawon watanni.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun bayan ’yan watanni da zama Gwamnan Ribas, aka sa zare tsakanin Fubara da Wike, inda har kawo yanzu rikicin siyasa a tsakanin ɓangarorin biyu ke daɗa ƙamari.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Majalisar Dokokin Ribas Siminalayi Fubara Gwamna Fubara tsige Gwamna

এছাড়াও পড়ুন:

Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum

Rikicin jam’iyyar PDP ya ƙara tsananta bayan sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Illiya Damagum.

Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, Anyanwu, wanda yake ɗan tsagin  Nyesom Wike, ya ce an dakatar da Damagum da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda biyar saboda zargin rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin bin hukuncin kotu.

Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike

“Mun yanke shawarar dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Ilya Damagum, saboda rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin mutunta hukuncin kotu,” in ji Anyanwu.

“An dakatar da shi na tsawon wata guda, kuma dole ne ya gurfana gaban kwamitin ladabtarwa.”

Anyanwu, ya kuma yaba da hukuncin kotu wanda ya soke babban taron jam’iyyar na ƙasa, inda ya bayyana cewa wannan nasara ce ga mambobin PDP baki ɗaya.

“Muna jinjina wa ɓangaren shari’a bisa wannan hukunci da ya nuna adawa da zalunci da rashin bin doka. Wannan nasara ce ga kowane ɗan jam’iyyar PDP,” in ji shi.

Sauran da aka dakatar sun haɗa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba; mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu, Taofeek Arapaja.

Akwai kuma sakataren kuɗi na ƙasa, Daniel Woyenguikoro; jagoran matasan jam’iyyar, Sulaiman Kadade da mataimakin sakataren jam’iyyar na ƙasa, Setonji Koshoedo.

Sanarwar Anyanwu, na zuwa ne bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da shi da wasu magoya bayan Wike, lamarin da ya ƙara ba tsananta rikicin shugabanci a jam’iyyar PDP.

Anyanwu, ya kuma sanar da naɗa Alhaji Abdulrahman Mohammed, mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa ta Tsakiya, a matsayin sabon muƙaddashin shugaban jam’iyyar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific
  • Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC
  • An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
  • Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
  • Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC
  • Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar  Christopher Musa