ECOWAS Ta Kaddamar da Dakarun Yaƙi da Ta’addanci
Published: 13th, March 2025 GMT
Ya ƙara da cewa, ECOWAS na da aniyar tunkarar matsalolin tsaro don tabbatar da zaman lafiya da wadata ga al’ummomin ƙasashen yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 2, sun ƙwato makamai a Borno
Dakarun Sojin Rundunar Operation Haɗin Kai, sun kashe ’yan ta’adda biyu a wani samame da suka kai yankin Shettimari da ke Ƙaramar Hukumar Konduga, a Jihar Borno.
Majiyoyi sun shaida cewa rundunar ta kai harin ne ƙarƙashin Operation Desert Sanity V da safiyar ranar Alhamis.
Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan bana na Turkiyya Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a BinuwaiWata majiyar soji ta ce, “Sojojin sun tare mayaƙan a kusa da inda suka ke shirin kai hari a yankin da misalin ƙarfe 1:20 na dare.”
Ya ƙara da cewa, “Sojojin sun yi nasarar daƙile ’yan ta’addan nan take, inda suka kashe biyu daga cikinsu yayin da wasu suka tsere.”
Bugu da ƙari, majiyar ta ce daga baya an gano wasu bama-bamai guda biyu da kuma wani gidan harsashi guda ɗaya mai ɗauke da harsasai 23 masu ɗangon 7.62mm x 39mm da ’yan ta’addan suka watsar yayin tserewa.
Majiyar ta ƙara da cewa, “Babu wanda ya mutu a cikin sojojin, sai dai daga baya tawagar sojojin sun ci gaba da aikinsu.”