Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Kafa Sansanin Soji a Jihar Binuwai
Published: 13th, March 2025 GMT
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.কীওয়ার্ড: Binuwai
এছাড়াও পড়ুন:
Hafsan sojin ƙasa ya buƙaci sabbin dakaru su zama masu kishin ƙasa
Rundunar Sojojin Najeriya, ta yaye sabbin dakarun soji guda 3,439, bayan kammala ɗaukar horo a cibiyar horar da sojoji da ke Zariya, a Jihar Kaduna.
Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar W. Shaibu, ya yaba wa sabbin sojojin bisa jajircewa, haƙuri da ƙwazon da suka nuna tsawon watannin da suka yi suna karɓar horo.
An kashe mutum 11 da jikkata wasu 29 a bikin Yahudawa a Ostireliya Akwai fargaba kan noman ranin banaJanar Shaibu, ya bayyana hakan ne a wajen bikin yaye sojojin, inda ya ce wannan nasara na nuni da ƙoƙarin rundunar soji na ƙara yawan ma’aikata domin fuskantar matsalar tsaro a ƙasar nan.
Ya taya sabbin sojojin murna, inda ya bayyana cewa kammala horon shi ne mataki na farko na rayuwar sadaukarwa, kishin ƙasa da hidimta wa jama’a.
A cewarsa, sabbin sojojin sun shiga rundunar a lokaci mai muhimmanci, ganin yadda ƙasar ke fuskantar matsalolin tsaro da dama.
Ya buƙace su da su kasance masu gaskiya, ladabi da bin doka a duk inda aka tura su aiki.
Babban Hafsan ya ƙara da cewa horon da aka ba su ya horar da su yadda za su iya fuskantar aikin soja a zamanance tare da sauran hukumomin tsaro.
Ya kuma yaba wa Kwamandan Depot NA, Janar Ahmadu Bello Muhammad, da jami’an da kw horar da sojoji bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ganin horon ya gudana cikin nasara.
Ya ce buɗe sabbin cibiyoyin horo a Osogbo da Abakaliki zai ƙara wa rundunar ƙarfin karɓar sabbin sojoji.
Haka kuma, Janar Shaibu ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu bisa goyon bayan da yake bai wa rundunar soji, tare da jinjina wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, da al’ummar Zariya saboda kyakkyawar alaƙa da sojoji.
Ya kuma taya iyalan sabbin sojojin murna, inda ya roƙi sabbin dakarun da su ci gaba da zama masu kishin ƙasa da jajircewa wajen hidimta wa Najeriya.