ECOWAS ta kaddamar da rundunarta mai dakaru 5,000 don yakar ta’addanci
Published: 13th, March 2025 GMT
Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta kaddamar da wata rundinarta mai manufar yaki da ayyukan ta’addanci da miyagun laifuffuka a yankin.
Ministan tsaron Nijeriya, Mohammed Badaru Abubakar ne ya sanar da hakan a yayin taron Kolin ECOWAS na hafsoshin tsaro karo na 43 a babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja a ranar Talata.
Badaru ya ce taron ya jaddada kudurinsu na magance matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
“Kaddamar da wannan runduna yana kara jaddada kudurinmu na tunkarar ta’addancin da ya shafi tsaron yankin,’’ in ji shi.
Taron ya samu halartar manyan hafsan hafsoshin tsaro na kasashen kungiyar ECOWAS, banda kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar wadanda suka raba gari da kungiyar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Pakistan Ta Zargi Kasashen Afghanistan Da India Da Hannu A Garkuwa Da Jirgin Kasa Na Sojoji
Gwamnatin kasar Pakistan ta ce da akwai hannuwan Afghanistan da kuma India a garkuwa da jirgin kasa na soja da aka yi a cikin kasar a ranar 13 ga watan Maris,wanda ya jefa mutanen kasar cikin damuwa akan batun tsaro.
Mahukuntan kasar ta Pakistan sun kuma ce; Binciken farko ya tabbatar da cewa wasu masu dauke da makamai ne su ka yi garkuwa da jirgin kasar, da sun shigo ne daga iyakar Pakistan sai kuma wani dan India wanda ya shiya yadda za a yi.
Gwamnatin kasar ta Pakistan ta sanar da tsananta matakan tsaro domin kame wadanda su ka yi garkuwa da jirgin da kuma daukar matakan hana, irin haka faruwa a nan gaba.
Ya zuwa yanzu babu wata kungiyar da ta fito fili ta dauki alhakin abinda ya faru.
Gwamnatin kasar ta Pakistan ta ce, da akwai masu dauke makamai da sun kai 50 da suke garkuwa da jirgin kasan. Ya zuwa yanzu dai mutane 31 ne su ka rasa rayukansu da usn kunshi jami’an tsaro da kuma fararen hula.
A cikin shekarun bayan nan alaka a tsakanin Pakistan da Afghanistan ta kara kamari.