Ukraine Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Wata Guda Da Rasha
Published: 13th, March 2025 GMT
Majiyoyi sun bayyana cewa Donald Trump na shirin tattaunawa da Vladimir Putin a cikin makon nan domin ƙara fahimtar juna dangane da wannan shiri.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, na kira ga ƙasashen Turai da su haɗa kai domin tallafa wa Ukraine wajen tabbatar da tsaron ƙasar bayan wannan tsagaita wuta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Majalisa ta amince da buƙatar Tinubu na karɓo rancen N1.15bn
Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na karɓo rancen Naira tiriliyan 1.15 domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025.
Amincewar ta biyo bayan rahoton da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamunin Cikin Gida da na Ƙasashen Waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Manu Haruna, ya gabatar.
Matasa 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana Super Falconets ta lashe gasar WAFU ta ’yan ƙasa da shekaru 20Ya bayyana cewa kasafin kuɗin 2025 na Naira tiriliyan 59.99 ya bar giɓin naira tiriliyan 1.15 wanda dole ne a cike ta hanyar nemo rancen a cikin gida.
Sanatoci sun amince cewa rancen ya zama dole domin ci gaba da aiwatar da muhimman ayyukan gwamnati da tabbatar da nasarar kasafin kuɗin 2025, musamman ɓangaren manyan ayyuka.
Sai dai sun jaddada muhimmancin yin gaskiya da bayyana bayani kan yadda za a yi amfani da kuɗin.
Wasu sanatocin sun shawarci Ma’aikatar Kuɗi da Ofishin Kula da Lamuni (DMO), da su riƙa bai wa Majalisar Dattawa rahoto lokaci-lokaci kan yadda ake kashe kuɗin da kuma yadda za a biya bashin.
Sun ce hakan zai taimaka wajen kauce wa almundahana da kuma tabbatar da ɗorewar tsarin lamuni na cikin gida.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yaba wa kwamitin kan yadda suka gudanar da aikinsu a kan lokaci.
Ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa Majalisar Dattawa za ta ci gaba da sanya idanu kan yadda za a yi amfani da rancen domin tabbatar da cewa an yi amfani da shi wajen ci gaban ƙasa.