Muddin Nahiyar Afirka Ta Farka Ba Za A Iya Raina Ta Ba
Published: 12th, March 2025 GMT
Hakika yadda kasar Amurka ta dakatar da tallafi a wannan karo ya nuna ra’ayin shugaba Donald Trump dangane da kasashen Afirka. Wanda za a iya fahimta bisa ganin yadda ya bayyana kasar Lesotho a matsayin “kasar da ba a san ta ba”, wacce ba ta cancanci tallafin da ake ba ta ba, a kwanakin baya, yayin da yake magana da ‘yan majalisun kasar Amurka.
A daura da haka, ana iya ganin fahimtar matsayin kasashen Afirka mai dacewa, a cikin maganar da ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya fada a kwanan baya, yayin da yake amsa tambayar da wakiliyar kafar yada labaru ta Najeriya NAN ta gabatar masa. Inda ya bayyana nahiyar Afrika a matsayin wuri mai muhimmanci a karni na 21, wanda samun kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arzikinsa ya shafi makomar bai daya ta daukacin dan Adam. Sa’an nan, bayan da ya yi bayani kan kokarin da kasar Sin ta yi wajen haifar da takamaiman ci gaba a kasashen Afirka, jami’in na Sin ya ce, “Nahiyar Afirka na cikin wani sabon mataki na farkawa. Kamata ya yi a mara musu baya, don su iya dogaro da kai wajen tafiya a kan sabuwar turbarsu ta raya kasa.” (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Musulmi ya buƙaci gwamnonin Arewa suke saurarar ƙorafin jama’a
Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya shawarci gwamnonin jihohin Arewa 19 su riƙa sauraron masu sukarsu tare da amfani da shawarwarin da ake ba su domin inganta salon mulkinsu.
Ya bayar da wannan shawara ne a ranar Litinin, yayin taron haɗin gwiwar Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya a Kaduna.
’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 13 da ɓacewarsu a Borno ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa masu ibada a KogiSarkin Musulmi, ya ce bai kamata shugabanni su yi biris da ƙorafin jama’a ba, musamman a wannan lokaci da Arewa ke fama da matsalolin rashin tsaro, talauci da matsin tattalin arziƙi.
A cewarsa, babu wani gwamna ko shugaban ƙasa da zai nemi ƙuri’un jama’a sannan bayan ya hau mulki ya juya musu baya.
Ya nuna damuwa cewa mutane da dama na zargin gwamnonin da rashin yin aiki, alhali suna fuskantar matsin lamba.
Sarkin ya shawarce su da su rika karɓar ƙorafe-ƙorafe masu amfani tare da gyara inda ya dace, domin hakan na taimakawa wajen yanke shawara mai kyau.
Haka kuma, ya yi kira da a ƙara samun haɗin kai a tsakanin gwamnonin, inda ya ce hakan ne zai taimaka wajen inganta Arewa da daidaita ƙasa baki ɗaya.
Sarkin Musulmi ya tabbatar wa gwamnonin cewa sarakunan gargajiya na tare da su, kuma a shirye suke ba su goyon baya a kowane lokaci.
Ya kuma bayar da shawarar cewa ya kamata gwamnoni da sarakunan gargajiya su riƙa gudanar da taruka akai-akai domin tattauna matsaloli da yanke shawara tare.
A ƙarshe, ya ce sarakunan gargajiya za su ci gaba da bayar da gudummawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa da Najeriya gaba baki ɗaya.