Mutum 1,010 Sun Mutu Sakamakon Hare-hare A Watan Fabrairu – Rahoto
Published: 12th, March 2025 GMT
Duk da raguwar hare-haren da kashi 2.19 idan aka kwatanta da Janairu, har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da zama barazana ga al’umma a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatan lantarki na shirin shiga yajin aiki a faɗin Najeriya
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ta yi barazanar dakatar da dukkan ayyukan samar da wutar lantarki a faɗin Najeriya, sakamakon harin da ta ce jami’anta sun fuskanta a Jihar Imo.
Ƙungiyar ta bayyana cewa wasu jami’an ’yan sanda ɗauke da makamai ne suka kai wa ma’aikatanta hari a Egbu 132/33kB Transmission Substation da ke Owerri, Jihar Imo, lamarin da ya janyo fargaba da tayar da hankali ga ma’aikatan da ke wurin.
Fiye da yara miliyan 400 na fama da talauci a duniya — UNICEF An gano wurin da ’yan bindiga ke tsare da ɗalibai 25 da aka sace a KebbiA wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na ƙasa ya fitar, NUEE ta ce wannan hari na nuna take haƙƙin ma’aikaci, kuma ba za a lamunta da shi ba.
NUEE ta bayyana cewa ba za ta yi shiru ba yayin da tsaro da mutuncin mambobinta ke fuskantar barazana ba.
Sanarwar ta ce, “Wannan hari da jami’an tsaro suka kai ya saɓa wa duk ka’idojin aikin yi. Jami’anmu na gudanar da aikinsu ne na yau da kullum, amma aka afka musu da duka da barazana. Mun gaji da irin wannan cin zarafi.”
Ƙungiyar ta gargaɗi gwamnati da shugabannin rundunar ’yan sanda da cewa za ta rufe dukkan tashoshin wutar lantarki a sassan ƙasar, muddin ba a ɗauki matakin hukunta masu laifin da kuma bada tabbacin tsaron ma’aikata ba.