HausaTv:
2025-08-16@16:54:35 GMT

Ukraine ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 30

Published: 12th, March 2025 GMT

Kasar Ukraine ta bayyana aniyarta ta amincewa da shawarar da Amurka ta gabatar, game da dakatar da bude wuta nan take tsakaninta da Rasha har tsawon kwanaki 30, biyowa bayan fara tattaunawa da tawagar Amurka a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.

Wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin wakilan Ukraine da na Amurka da aka fitar a jiya Talata ce ta tabbatar da hakan, bayan sassan biyu sun shafe sa’o’i suna tattaunawa.

Sanarwar ta ce akwai yiwuwar tsawaita yarjejeniyar, kuma Amurka za ta tuntubi Rasha kasancewar amincewarta zai tabbatar da cimma nasarar matakin.

Baya ga hakan, Amurka ta amince da dage matakin dakatar da musayar bayanan sirri, kuma za ta ci gaba da baiwa Ukraine tallafin tsaro, yayin da kuma sassan biyu suka tattauna kan muhimmancin aiwatar da matakan samar da tallafin jin kai, musamman a wa’adin tsagaita bude wutar.

Har ila yau, masu shiga tsakanin sun amince da samar da tawagogin da za su fara tattaunawa, da nufin cimma nasarar wanzar da zaman lafiya mai dorewa.

 A daya hannun kuma, Amurka ta jaddada aniyarta ta hawa teburin shawara da Rasha, yayin da Ukraine ta jaddada muhimmancin shigar sauran abokan hulda na Turai cikin tsarin na cimma daidaito.

Bugu da kari, jagororin Ukraine da na Amurka, sun amince da gaggauta kaiwa karshen cikakkiyar yarjejeniyar bunkasa cin gajiya daga muhimman ma’adanan Ukraine, ta yadda za a kai ga fadada tattalin arzikin kasar. 

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Akwai Bukatar Samar Da Sauyin Zaman Lafiya Mai Dorewa A Duniya — Maryam Bukar

Ita ma da take nata jawabin Maryam Bukar Hassan ta ce, akwai bukatar a samar da wani shiri na kawo sauyi wajen samar da zaman lafiya mai dorewa.

Hakazalika Maryam ta jaddada cewa, idan har ba zaman lafiya babu yadda za a iya cimma muradun ci gaba mai dorewa (SDGs) kuma zai kasance mara amfani.

“Ba maganar talauci idan zaman lafiya da adalci sun tabbata.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Putin da Trump sun tabbatar da aniyarsu ta kawo karshen rashin jituwa da warware batun Ukraine
  • Takht-Ravanchi: Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa kan hakkinta na nukiliya
  • Akwai Bukatar Samar Da Sauyin Zaman Lafiya Mai Dorewa A Duniya — Maryam Bukar
  • Ma’aikatan Sufurin Jiregen Sama Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Shirin Sayar Da Filayen Jiragen Sama
  • Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Gina Asibitin Dabbobi A Jihar Kwara
  • NLC Ta Baiwa Gwamnati Kwanaki 7 Don Magance Badaƙalar Satar Kuɗin Ma’aikata
  • An zabi sabuwar firaminista a Luthuania
  • Tsarin Samar Da Kayayyaki Na Masana’antar Lantarki Ya Ci Gaba Da Samun Karfin Juriya A Kasar Sin
  • Rashin Lantarki: Babu wanda za mu zaɓa a 2027 — Jama’ar Talasse
  • Amurka za ta sayar wa Najeriya makaman N530bn don yaƙi da ta’addanci