An yi cikakken zama na uku na taron shekara shekara na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin da safiyar yau Lahadi a babban dakin taron al’umma dake birnin Beijing, inda zaunannen memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar, wanda kuma shi ne shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin, Wang Huning ya halarci taron, kana, membobin majalisar guda 14 ne suka gabatar da jawabai.

A jawabinta, mambar majalisar Ge Huijun ta ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi a wajen babban taron murnar cika shekaru 75 da kafa majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar, jawabin da ya kafa alkabila da samar da babban tushe ga ci gaban harkokin majalisar. Ta ce ya dace membobin majalisar su kara gogewa wajen sauke nauyin aiki, da kara kwarewa a fannonin da suka shafi bada jagoranci ta fuskar siyasa, da bada shawarwari game da ayyukan zamanantar da kasa, da kara tuntuba gami da hidimtawa jama’a, tare kuma da kokarin raya kasa da farfado da al’ummomin kasar. (Murtala Zhang)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Kaduna Ta Amince da Dokar Kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani

Daga Shamsuddeen Mannir Atiku 

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokar kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani ta Jihar Kaduna, wacce za ta taimaka wajen ƙarfafa tsarin fasaha na jihar da inganta gasa a fannin tattalin arziki.

Dokar mai taken “Kaduna State Information Technology and Digital Economy Agency and for Related Matters, 2025” ta samu amincewa bayan karatu na uku a zaman majalisar na ranar Talata.

Shugaban majalisar, Hon. Yusuf Dahiru Liman, wanda ya jagoranci zaman, ya bayyana muhimmancin dokar, yana mai cewa kafa hukumar zai faɗaɗa damar tattalin arziki tare da bai wa jihar Kaduna damar cin moriyar cigaban fasahar zamani a duniya.

Ya ce hukumar za ta ƙarfafa kirkire-kirkire, bunƙasa ƙwarewar dijital, da daidaita jihar da sauye-sauyen fasaha da tattalin arzikin dijital a duniya.

Tun da farko, shugaban kwamitin haɗin gwiwa kan Yada Labarai, Kungiyoyi Masu Zaman Kansu da Abokan Cigaba, Mr. Henry Marah Zakariah, ya gabatar da rahoton kwamitin.

Ya bayyana cewa an yi nazari mai zurfi kan dokar, kuma an tabbatar da cewa mataki ne mai muhimmanci wajen ƙara damar samun ayyukan yi da sauƙaƙa wa al’umma samun ilimin fasahar zamani.

Mr. Henry Zakariah ya kuma jaddada cewa kafa hukumar za ta bunƙasa tattalin arzikin jihar da samar da kudaden shiga, inda ya bayyana cewa za a kafa cibiyoyin fasahar zamanin a yankunan karkara domin bai wa kowa damar cin gajiyar ayyukan Hukumar.

Daga karshe majalisar ta amince da dokar baki ɗaya, bayan Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Birnin Zaria, Barr. Mahmood Lawal Sama’ila ya gabatar da kudirin amincewa inda ya samu goyon baya daga Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Makarfi, Isiyaku Ibrahim ya goyi bayan shi.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Lebanon
  • An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo
  • Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya
  • Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu
  • Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 
  • Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 
  • Za A Gudanar Da Taron Masana Harkokin Yada Labarai Karo Na 2 A Kano
  • Majalisar Kaduna Ta Amince da Dokar Kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani
  • Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar
  • ’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu