HausaTv:
2025-05-25@05:58:07 GMT

Trump Ya Dakatar Da Taimakon Da Kasarsa Take Bai Wa Ukiraniya

Published: 4th, March 2025 GMT

Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa, shugaban kasar Donald Trump ya bayar da umarnin dakatar da duk wani taimako na soja da ake bai wa Ukirnaiya, daga ciki har da makaman da ake kai wa ta sama da jiragen ruwa da kuma wadadna  a halin yanzu sun isa kasar Poland.

Jaridar “Bloomberg” ta bayyana cewa; bayan kwanaki kadan da aka yi cacar baki a tsakanin shugaban na Amurka Donald Trump da kuma takwaransa na Ukiraniya  Volodymyr Zelensky, shugaban na kasar Amurka ya bayar da umarnin a dakatar da bai wa Ukiraniya duk wani taimako na soja.

Wani jami’i a ma’aikatar tsaron Amurka ya bayyana cewa;               “ Amurkan ta dakatar da duk wani taimako na soja da take bai wa Ukiraniya a halin yanzu, har zuwa lokacin da shugabannin kasar za su nuna cewa da gaske suna son zaman lafiya.”

Ita kuwa jaridar “Washington Post” ta nakalto cewa, jami’an gwamnatin Amurkan suna kuma nazarin yadda za su dakatar da musayar bayanai da suke yi da Ukiraniya, haka nan horon soja da ake ba su.”

A ranar juma’ar da ta gabata ne dai shugaban kasar Ukiraniya Volodymyr Zelensky ya kai ziyara Amurka, sai dai ba ta kare da dadi ba a tsakaninsa da shugaban kasar Donald Trump, saboda sabanin da su ka samu akan batun tsagaita wutar yaki da kuma yarjejeniya akan ma’adanai.

Trump ya zargi shugaban na Ukiraniya da kokarin kunna wutar yakin duniya na 3,alhali bai taki wani abu ba.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Ba Zai Yiwu Amurka Ta Kafawa Chips Kirar Kasar Sin Wani Shinge Ba

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Afrika ta Kudu ta karyata ikirarin Trump na kisan kiyashin fararen fata
  • Donal Trump Ya Kori Gomomi Daga Cikin Ma’aikata A Majalisar Tsaro Ta Kasar Amurka
  • Amurka Tana Takurawa JMI Don Biyan Bukatun HKI Na Ta Dakatar Da Shirinta Na Nukliya
  • Iran: Inda Makiya Kasar Sun San Cewa Zasu Sami Nasara A Kan Iran A Yaki Da Tuni Sunn Farmata Da Yaki
  • Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Amurka Ya Bukaci Amurka Ta Jefa Makaman Nukliya Kan Gaza
  • Ba Zai Yiwu Amurka Ta Kafawa Chips Kirar Kasar Sin Wani Shinge Ba
  • Dakarun Yemen Sun Hana Zirga-Zirgan Jiragen Sama A Filin Jirgin Saman Ben Gurion Na Isra’ila
  • Gwamnatin Afirka Ta Kudu Ta Musanta Zargin Cin Zarafin Turawa ‘Yan Kasar Fararen Fata
  • Araghchi: Iran ba za ta tattauna kan batun inganta sinadarin Uranium din ta ba
  • Kamfanonin jiragen sama sun tsawaita dakatar da zirga-zirgar zuwa Isra’ila