Gwamnatin Yamen Ta Gargadi HKI Da Amurka Kan Cewa Tana Sa Ido A Kan Abinda Ke Faruwa Da Tsagaita Wuta A Gaza
Published: 3rd, March 2025 GMT
Kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta gargadi HKI da kuma Amurka kan cewa, tana sanya ido a kan yadda suke sabawa yarjeniyar budewa juna wuta da suka cimma da su. Musamman yadda HKI ta sabawa yarjeniyar a mashigar Rafah na barin abinci ya shiga Gaza, da kuma bukatar sake tattauna wasu al-amura a yarjeniyar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran nakalto Hazem Al-asad mamba a majalisar siyasa ta kasar Yemen, yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, kungiyar a shirye take ta sake shiga yaki da Amurka, a duk lokacinda suka yi kokarin cutar da mutanen Gaza.
Al-Asad ya gargadi gwamnatin Amurka da masu goyon bayan HKI a duk wata cutarwa da zata yiwa mutanen Gaza.
Har’ila yau, wani mamba a majalisar, Nasir-Addeen Amir ya bayyana cewa idanummu na kan abubuwan da suke faruwa a Gaza, sannan hannayenmu suna kan na’urorin bude wuta a kan dukkan abubuwan da suka shafi HKI da Amurka, don kare mutanen Gaza.
Amir ya kara da cewa dukkan makamai masu linzami na kasar Yemen su na cikin shirin komawa yaki idan HKI ko kawayenta suka sake farwa mutanen gaza.
Ya kuma kammala da cewa mayakan ansarullah za su sake budewa jiragen ruwa masu zuwa HKI wuta a tekun maliya da sauran wuraren da ta kaiwa hare-hare a baya bayan an fara yakin Octoban shekara ta 2023.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Za a fara yi wa ɗaliban jami’o’i gwajin ƙwaya — Gwamnatin Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta bayanna cewa za ta soma yi wa ɗaliban jami’o’in ƙasar nan gwajin miyagun ƙwayoyi a wani mataki na daƙile yaɗuwar ta’ammali da ƙwayoyin.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da haɗin gwiwar Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA ne za su jagoranci aikin.
Sarkin Gudi na Jihar Yobe, Isa Bunuwo Ibn Khaji ya rasu Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamaniHakan na zuwa ne bayan ganawar Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya da kuma ministan ilimin ƙasar, Olatunji Alausa a jiya Laraba.
Ɓangarorin biyu sun kuma amince da ɓullo da daftarin koyar da darasin ilimin ta’ammali da ƙwayoyi a makarantun sakandiren ƙasar.
Buba Marwa wanda ya jagoranci tawagar jagororin hukumar NDLEA ya bayyana cewa gwajin ƙwayar zai shafi duk ɗaliban jami’o’in da sabbin da za su shiga.
Yayin da yake jawabi a wajen ganawar, Buba Marwa ya ce za su mayar da hankali ne kan makarantun ƙasar, waɗanda ya ce akwai miliyoyin yara da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimin ƙasar.
Buba Marwa ya ce rashin daƙile ta’ammali da miyagun ƙwayoyi daga wajen ƙananan yara ya taimaka wajen jefa matasan ƙasar cikin ayyukan ta’addanci da fashin daji da sauran miyagun laifuka.
Ya bayyana mummunan tasirin shan miyagun ƙwayoyi a kan matasan ƙasar, yana mai cewa yaƙi da miyagun ƙwayoyi yaki ne don ceton rayukan matasan Nijeriya.
Marwa ya ce a yanzu hankalin hukumar zai fi karkata ne zuwa makarantu da cibiyoyin ilimi, yana mai ƙarawa da cewa akwai miliyoyin yaran Nijeriya da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi, kuma wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci.
Shugaban hukumar ta NDLEAn ya ce a dalilin goyon bayan da suka samu karkashin Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a tsawon shekaru biyu da suka gabata, hukumar ta kama mutane 40,887 da ake zargi da aikata laifuka, ta daure 8,682, kuma ta kwace tan 5,507 na miyagun ƙwayoyi.
A cewarsa, tun daga watan Janairu bara, an ƙwace ƙwayar tramadol da ta wuce ƙwaya biliyan ɗaya, wanda kudinta ya fi naira tiriliyan ɗaya.
Shugaban NDLEA ya jaddada cewa Shugaba Tinubu yana kuma tallafa wa hukumar wajen gina cibiyoyi bakwai na gyaran masu fama da shan miyagun ƙwayoyi, baya ga sauran cibiyoyi 30 da ke karkashin umarnin NDLEA a faɗin ƙasa.