Aminiya:
2025-09-18@00:54:06 GMT

Saudiyya ta buɗe shafin rajistar masu Itikafi

Published: 3rd, March 2025 GMT

Mahukuntan Saudiyya sun buɗe shafi na musamman domin yin rajista ga masu sha’awar yin ibadar Itikifa a watan Ramadan da muke ciki a ƙasar.

A ranar Lahadi, 1 ga watan Ramadana ne aka sanar da buɗe shafin ga masu sha’awar yin Itikafi ’yan asalin ƙasar da kuma baƙi.

Sanarwar ta bayyana ka’idojin da masu sha’awar za su cika domin samun gudanar da ibadar a kwanaki 10 ma ƙarshen watan Ramadan a masallatan Haramin Makkah da Madina da sauransu masallatan ƙasar.

Bayanan da ake buƙata sun hada da:

Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan MDD ta taya Musulmi murnar zuwan watan Ramadan

1- Ƙasar mutum: Ta asali ko inda yake zama. Sanarwar ta bayyana cewa wajibi ne mai yin rajistar ya kasance ɗan ƙasar Saudiyya ko ya mallaki takardar iznin zama a can.

2- Wurin yin rajista: Wajibi ne mutum ya kasance a Saudiyya a lokacin da zai yi rajista, domin wanda ke wajen ƙasar ba zai iya shiga shafin ba.

3- Shekaru: Wajibi ne mai yin Itikafi ya shekarunsa su kai aƙalla 18.

4- Yanayin lafiya: An buƙatar ya kasance cikin ƙoshin lafiya ta yadda zai iya gudanar da ibada ba tare da wahala ba. Za a yi wa mutum gwajin duk wasu cututtuka masu tsanani. Idan mutum na buƙatar kulawa ta musamman, wajibi ne ya bayyana a yayin yin rajista.

5- Wa’adin Itikafi: Dole ne mutum ya bai ka’idar kwanakin da ya ɗiba na Itikafi. Lokacin ya fara ne daga ranar 20 ga watan Ramadana zuwa bayan Sallar Isha’ ta ranar jajibirin Ƙaramar Sallah.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ramadana Saudiyya yin rajista

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara

Aƙalla masallata 40 ’yan bindiga suka sace a wani masallaci da ke Gidan Turbe a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da safiyar wannan Litinin.

Majiyoyi sun ce an yi awon gaba da masallatan ne zuwa dazukan Gohori da ke yankin Tsafe.

Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas

Wannan harin dai kai tsaye masu ruwa da tsaki na kallonsa a matsayin kawo ƙarshen yarjejeniyar sulhu tsakanin ’yan bindigar da mahukuntan jihohin Zamfara da Katsina.

A baya-bayan nan ne jihohin Katsina da Zamfara suka ƙulla yarjejeniyar sulhu tsakaninsu da ’yan bindigar da suka addabi al’ummar jihohin arewa maso yammacin Najeriyar.

Yarjejeniyar sulhu da aka cimma a dajin Wurma ta samu halartan manyan ’yan bindiga irinsu Alhaji Usman Kachalla Ruga da Muhindinge da Yahaya Sani ( Hayyu ) da kuma Shu’aibu.

A ɓangaren mahukunta, akwai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi da kuma shugaban ƙaramar hukuma Babangida Abdullahi Kurfi.

’Yan bindiga sun saki wasu mutane da suke garkuwa da su a lokacin yarjejeniyar sulhun, tare da barin al’umma zuwa gonakinsu ba tare da wata fargaba ko tsangwama.

To sai dai kuma, ƙasa da wata guda bayan cimma wannan yarjejeniya, rahotanni sun ce ’yan bindiga sun kutsawa wani ƙauye a Zamfara tare da awon gaba da masallata.

Shaidun gani da ido sun ce, maharan sun yi wa masallacin ƙawanya da misalin ƙarfe 5:30 na safe, daidai lokacin da jama’a ke sallar asuba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
  • Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS
  • Majalisar Dattawa Ce Kawai Za Ta Iya Dawo Da Sanata Natasha – Magatakardar Majalisa
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
  • Sarki Sanusi II ya koka kan yawan cin bashin Najeriya