Leadership News Hausa:
2025-08-12@09:31:20 GMT

Sharhi Kan Dabarun Noman Dabino A Nijeriya

Published: 14th, February 2025 GMT

Sharhi Kan Dabarun Noman Dabino A Nijeriya

Duk da cewa, ana kara samun yin nomansa da yawa, ana kuma ci gaba da samun karancinsa, musamman saboda yadda al’umma ke kara bukatarsa.

Kamar Ban Ruwa Nawa Bishiyar Dabino Ke Bukata?

Dabinon da aka shuka, bai cika bukatar a dinga yi masa ban ruwa bayan an shuka shi ba, musamman a lokacin kakar damina.

A Wane Yanayi Dabino Yake Girma?

Dabino ya fi yin girma a  yanayin zafi, haka nan kuma ya fi yin kyau a kasar noma ta kasar Amurka da ake samun rana mai zafi.

Kamar Zufin Rami Nawa Dabino Ke Bukata?

Yana girma a zurfin ramin da ya kai kafa daya zuwa kafa sha daya tare kuma da santi mita daga talatin zuwa arba’in da biyar, wannan ya danganta da irin ingancin kasar noman da aka shuka shi da kuma irin yanayin, haka nan; yana kai wa daga tsawon shekara 15 zuwa 20 kafin ya kammala girma.

 

A duk fannin duniya, Nijeriya ce kawai ke nomansa sau biyu a shekara, har Nahiyar Afirka ta Arewa da Gabas ta tsakiya, inda ake hasashen Dabinon ya samu asali, sannan ana yin nomansa ne a kakar noma daya.

Dabinon da aka shuka, na fara fitar da fure ne daga watan Janairu zuwa watan Fabirairu, inda kuma yake kammala nuna daga watan Yuni zuwa watan Oktoba.

Wanda kuma aka shuka a kakar noman damina, yana fara yin fure ne daga watan Satumba zuwa watan Oktoba, inda kuma yake kai wa munzalin a girbe shi daga watan Fabirairu zuwa watan Maris.

Batun Shuka Shi:

Ana amfani da Iri don shuka shi ko kuma a shuka Saiwarsa wacce ke girma zuwa Bishiya.

Ana kuma yanko Saiwar ce daga jikin Bishiyar da ta kai daga shekara hudu zuwa biyar, inda kuma ake fara shuka shi daga watan Juli zuwa watan Satumba, haka a kadada daya ana iya samun Bishiyar Dabino kimanin 150.

Gyaran Gona:

Ana so a gyra gonar da za a shuka Dabino kafin ruwan damina ya fara sauka, inda ake so a yi wa gonar haro; domin ta samu danshi sosai.

Zuba Taki:

An fi so a zuba masa takin gargajiya da ke dauke da sindarin ‘Nitrogen’, musamman domin ya yi saurin girma.

Ban Ruwa:

Bishiyar Dabino na jurewa kowane irin yanayi na noma, an fi so a yi masa ban ruwa, musamman a lokacin rani.

Cire Ciyawa:

Ana bukatar  manomi ya tabatar ya kiyaye  wajen yin noma, musamman don gudun kada ya kamu da cututtuka ko  harbin kwari.

Lokacin Yin Girbi:

Ana yi masa girbi ne bayan ya kammala girman baki-daya, wato daga shekara 15 zuwa shekara 20.

Adana Shi Bayan Girbi:

Sabon Dabinon da aka girbe, ana adana shi a cikin na’ura mai sanyi daga sati biyu zuwa uku, ana kuma iya adana shi har zuwa tsawon wata hudu.

Hada-hadar Kasuwancinsa:

Dabino ne yake  tallan kansa da kansa, musamman ganin cewa, jama’a na kara bukatarsa, kana ana sarrafa shi zuwa nau’ikan wasu abin sha; kamar kunun Aya da sauran makamantansu.

Daga Tsawon  Kafa Nawa Bishiyar Dabino Ke Girma?

Bishiyar Dabino na kai wa tsawon kafa 20, banda ganyensa; yana kuma kai wa tsawon shekara daga 15 zuwa 20 kafin ya kammala girman.

Har ila yau, Dabinon da ya kai tsawon shekara 100, yana iya kai wa tsawon kafa 100.

Ana Samun dimbin Riba A Noman Dabino

A shekarar 2020, Kalifoniya ta samar da tan 49,300 da aka noma kadada 12,500, inda kuma a duk kadada daya aka noma tan 3.94 da kudinsa ya kai  dala 2,320 na  kowane tan daya. An kuma kiyasta yawan amfanin Dabinon da cewa; ya kai dala miliyan 114.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Bishiyar Dabino Bishiyar da

এছাড়াও পড়ুন:

Ana Neman Daukar Karin Matakin Kawar Da Shingayen Dake Hana ‘Ya’ya Mata Zuwa Makaranta A Zamfara

Mahalarta taron masu ruwa da tsaki na yini daya don tabbatar da sakamakon bincike kan al’amuran zamantakewa da suka shafi ilimin ‘ya’ya mata a jihar Zamfara, sun bukaci iyaye, shugabannin al’umma, da gwamnati a dukkan matakai da su magance matsalolin da ke hana yara mata zuwa kammala karatun sakandare.

 

Kungiyar AGILE da ke Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar Media and Publicity Consult ta shirya taron masu ruwa da tsaki na rana daya domin tabbatar da sakamakon binciken da aka yi kan ka’idojin zamantakewa da ke kawo cikas ga ’yan mata matasa da ke hana shiga makarantun gaba da sakandare a jihar Zamfara.

 

Da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Abubakar Aliyu Liman na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya jaddada bukatar masu ruwa da tsaki su samar da yanayi mai kyau da zai karfafa gwiwar ‘ya’ya mata su ci gaba da karatu.

 

Farfesa Liman, wanda kuma shi ne babban mai ba da shawara kan aikin bincike na AGILE a Zamfara, ya bayyana cewa auren dole da rashin goyon bayan iyaye a matsayin wasu manyan matsalolin da suka shafi ilimin ‘ya’ya mata a jihar.

 

 

Wakilan Ma’aikatun Mata da Ilimi na Jihar Zamfara sun yaba da tasirin aikin AGILE a Zamfara tare da yin kira da a ci gaba da inganta ayyukan da suka hada da samar da ingantattun hanyoyin ruwa, tsaftar muhalli a makarantu.

 

Mataimakin kodinetan hukumar AGILE a jihar Zamfara, Dakta Salisu Dalhatu, ya bayyana cewa an kammala makarantu 317 daga cikin 440 da aka ware domin gyarawa a karkashin hukumar ta AGILE, yayin da sama da ‘yan mata 8,000 ke cin gajiyar shirin bayar da tallafin kudi.

 

Manajan Daraktan yada labarai da tuntuba (MPC), Malam Nasiru Usman Biyabiki, ya ce taron tabbatar da shi an yi shi ne da nufin tace sakamakon binciken don samun ingantacciyar hanyar shiga tsakani.

 

A cewarsa, gangamin wayar da kan jama’a ya taimaka wajen ganin jihar Zamfara ta kasance cikin jerin jahohi biyar da suka fi aiwatar da ayyukan AGILE a fadin kasar nan.

 

Taron wanda MPC ta kira, ya kuma yi nazari kan sakamakon da Daraktar ICT ta kungiyar, Hibban Buhari ta gabatar, wanda ya bayyana talauci, al’adu, auren dole, da rashin ingantaccen tsarin karatu a matsayin manyan abubuwan da ke kawo tarnaki ga ‘ya’ya mata da kuma rike su.

 

Binciken ya ba da shawarar yin amfani da harsunan Hausa, Fulfulde, da Larabci wajen kamfen na wayar da kan jama’a, inda rediyon ya zama cibiyar farko saboda yawan isar da sako.

AMINU DALHATU.Gusau

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sashen Masana’antun Kirar Motoci Na kasar Sin Ya Samu Gi Gaba A Watan Yuli
  • Ana Neman Daukar Karin Matakin Kawar Da Shingayen Dake Hana ‘Ya’ya Mata Zuwa Makaranta A Zamfara
  • Ma’aikatan shari’a 97 sun samu ƙarin girma a Borno
  • NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas 
  • An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi
  • NDLEA Ta Cafke Masu Baburan Da Ke Kai Saƙon Muggan Ƙwayoyi A Abuja
  • Abubuwan Da Suka Ja Hankalin Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Tsarin Noman Waken Soya
  • ASUU na shirin sake tsunduma yajin aiki
  • Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno
  • Tsohon Shugaban PDP Audu Ogbeh Ya Rasu