HausaTv:
2025-09-18@00:42:53 GMT

ECOWAS na Shirin hada rundunar dakaru 260,000 domin yaki da ta’addanci

Published: 27th, August 2025 GMT

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta ce tana shirin kafa wata runduna ta dakaru 260,000 domin yaki da ta’addanci.

Shugaban hukumar ta ECOWAS, Omar Alieu Touray ne ya bayyana haka a taron hafsoshin tsaron kasashen Afrika na shekarar 2025 a Abuja.

Taken taron shi ne “Maganin barazana ga zaman lafiya da tsaro a Afirka a wannan zamani: muhimmancin hadaddiyar dabarun tsaro.

Touray wanda ya samu wakilcin kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na kungiyar ECOWAS, Ambasada Abdel-Fatau Musah, ya ce hakan wani bangare ne na rage tushen ta’addanci da sauran nau’ikan rashin tsaro a yankin.

Ya ce baya ga matakan yaki da ta’addanci, kungiyar tana kuma kokarin aiwatar da dabarun tsaron teku, yana mai cewa babu wani yanki na Afirka da ya tsira daga kalubalen ta’addanci, yaki da rashin ci gaba.

Ya ce kungiyar na bukatar dala biliyan 2.5 don kafa rundunar yaki da ta’addanci da za ta ba da taimakon kayan aiki da kudi ga dakarun da ke kasa a kasashen da ke fuskantar ta’addanci.

Ya ce tashe-tashen hankulan na iya kasancewa na cikin gida, amma suna bukatar mayar da martani ga nahiya, tare da kungiyar Tarayyar Afirka (AU) a matsayin jigon wannan yunkurin.

“Babu shakka cewa yammacin Afirka, musamman yankin Sahel, shi ne ya fi fuskantar matsalar ta’addanci a duniya, inda bincike ya nuna cewa yankin Sahel kadai zai kai kashi 51 cikin 100 na yawan mutuwar ta’addanci a shekarar 2024,” in ji shi.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka August 27, 2025 Syria: Adadin mutanen da suka mutu a harin Isra’ila a yankin Damascus ya kai 5 August 27, 2025 An Kammala Taron Iran Da E3 A Geneva August 26, 2025 Iran Ta ce Zata Rama Kan Korar Jakadanta Daga kasar Australia August 26, 2025 Najeriya: Jirgin Kasa tsakan Abuja da Kaduna Ya Sauka Kan Layin Dogo August 26, 2025 Iran A Shirye Take Ta Hada kai Da Pakistan Don Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci August 26, 2025 An Kashe Mutum Guda A Harin Isra’ila (HKI) A yankin Duddan Golan Na Siriya August 26, 2025 Jagora: Yahudawan Sahayoniyya Sune Mafi Kyamar Al’umma A Duniya Saboda Muggan Halayensu August 26, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Tarihi Ba Zai Yafe Jinkirin Yin Allah Wadai Da Bala’in Gaza Ba August 26, 2025 Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Tun Bayan Barkewar Yaki Da Iran Babu Wata Hulda Tsakaninta Da Amurka August 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: yaki da ta addanci

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .

Rahotanni sun bayyana cewa kasar iran ta bayyana sabbin kayayyaki guda 5 da ta kera a wajen babban taron kere-kere na kasa da kasa karo na 23,kuma dukkansu kamfanonin kasar iran ne suka yi su domin rage dogaro da kayyakin kasashen waje.

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban hukumar kula da kimiya da fasaha ta kasa da sauran shuwagabannin kamfanoni inda ya nuna irin karfin iran wajen kere-kere da kuma mayar da hankali kan kamfanoni dake filin shakatawa na pardis technology park.

Daga cikin magungunan da aka gabatar a wajen akwai Sirolimus wanda Zist takhmir company ya kera, kuma magungunan rigakafi ne da ake amfani da su wajen hana dashen gabobin jiki da kuma kula da cututtuka da ba kasafai ake samun su ba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi September 16, 2025 Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya September 16, 2025 Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya September 16, 2025 Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan   September 16, 2025 Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida September 16, 2025 Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya September 16, 2025 An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •   Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam ” Nahid 2″ Da Zai Samar Wa Yankunan Karkara Hanyar Sadarwa Ta “Internet”
  • Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila
  • Iran da Saudiyya sun bukaci hadin Musulmi game da halin da ake ci a yankin
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta.
  • Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha
  •  Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China
  • Fizishkiyan:  Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI