2025-09-17@21:58:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4401
«yan wasa»:
Jihar Legas, mahaifar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta samu ayyukan gwamnati da darajarsu ta kai Naira Turkiya 3.9 a cikin shekaru biyu na gwamnatinsa. Ayyukan da gwamnatin ta ba wa Jihar Legas ya zarce jimillar abin da aka ware wa jihohin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas baki ɗaya, waɗanda suka...
Gwamnan Jihar Taraba, Dokta Agbu Kefas, ya shirya wa Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas inda ya shirya musu ƙasaitaccen biki da liyafar dare a Jalingo, a gabanin taron gwamnonin da za a gudanar yau Asabar. An gudanar da liyafar ne a daren Juma’a a babban ɗakin fadar gwamnati, inda aka nuna raye raye na al’adu...
Editan Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, ya ce zargin cin zarafi a wurin aiki da ake yi masa ba su da tushe. Lamarin ya samo asali ne bayan wata tsohuwar ma’aikaciyar BBC Hausa, Halima Umar Saleh, a yayin wata tattaunawa da tashar Arewa24 ta bayyana cewa ta fuskanci musgunawa a lokacin aikin ta,...
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya ce ’yan Najeriya sun riga sun yanke shawara kan zaɓen shekarar 2027 da ke tafe. Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar NNPP, Kwankwaso ya ce: “A yau, yawancin ’yan Najeriya na kokarin yadda za su samu abinci....
Bisa wani rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, hakan ya nuna cewa, wannan shi ne karo na farko da Asusun Anita na Nijeriya ya samu karuwa tun daga watan Disambar shekarar 2021. Kazalika, rahoton ya sanar da cewa, a watan Agusta Asusun ya ci gaba da karuwa wanda daga watan aka samu kimanin...
Dantsoho ya sanar da cewa, tun lokacin da aka yi aikin Tashoshin Jiragen Ruwa na Tin Can Island shekaru 48 da kuma aikin Tashar Jiragen Ruwa ta and Apapa 103 a shekaru da suka gabata, babu wani yunkuri da aka yi, na gyransu ko kuma kara daga darajarsu. Shugaban ya kuma koka kan yadda...
Jami’an tsaro sun halaka aƙalla ’yan ta’adda 50 a yayin wata musayar wuta a yankin Ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja. Hadin gwiwar sojoji da sauran tsaro sun aika ’yan ta’addan lahira ne a yayin wani ƙazamar arangama a yankin Kumbashi da ke Ƙaramar Hukumar. Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Neja, muka wakilin Ƙaramar...
“Zan iya tabbatar muku da cewa an kammala dukkan sharye-sherye na sauya shekan wani gwamna na PDP zuwa cikin APC. Ana ganin wannan gwamna a matsayin gwamna mai aiki tukuru da kwazo wanda yake da farin jini sosai a fagen siyasa a jiharsa. Abin da zan iya cewa a yanzu shi ne, ya kasance yana...
Shaidu sun ce jirgin cike yake da mata, maza, da yara, kafin ya kife a tsakiyar ruwa. Wasu daga cikin fasinjojin sun yi nasarar yin iyo inda suka tsira, amma har yanzu ba a gano da dama ba. Al’umma sun daɗe suna zargin irin waɗannan hatsari na faruwa ne saboda ɗauke fasinjoji fiye da ƙima,...
Tare da jagoranci da zuba jari, Nijeriya na iya samun fiye da Dala biliyan 4 a shekara a kudaden fitar da fata, kirkirar miliyoyin ayyukan yi, da kuma dawo da matsayin tarihi a matsayin babbar mai karfi a duniya a fannin fata. Misali daga Jihar Legas Jihar Legas kwanan nan ta kaddamar da...
Francesca Albanese, Jami’a mai tattara bayanai kan al-amuran Falasdinawa a MDD ta yi tir da gwamnatin kasar Jamus dangane da yadda jami’an tsaron kasar suke dirar mikiya kan masu goyon bayan Falasdinawa a birnin Berline. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Albanese tana fadar haka a yau Jumm’a ta kumamkara da cewa:...
Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta kafa kwamitin bincike mai ƙarfi na ƙwararrun jami’an tsaro tare da haɗin gwiwar rundunar ‘sojan Najeriya, domin gano abin da ya jawo aka kashe wani jami’in soja da wani sifeton ’yan sanda ya yi a jihar kwanan nan. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda (PPRO), CSP Ahmed...
Haka kuma, Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, kasar Sin tana son mutunta juna, da zaman tare cikin lumana, da kulla hadin gwiwar samun nasara ga kowane bangare tare da Amurka, bisa tabbatar da kare muradun ikon mallakar yankunan kasarta, da tsaro da kuma ci gaban kasar. Ya kara da cewa, a shirye muke...
Osuman ya koka kan yadda a kowace rana ake kashe rayukan mutane a yankin, ya kara da cewa, yara, mata, maza, tsofaffi duk sun fada cikin matsalolin ambaliyar ruwa, ta’addancin ‘yan bindiga dadi, ayyukan ‘yan ta’adda da sauran annobobi. Ya bukaci shugabannin arewa da mazauna yankin da su farka, su hada kawunansu kana su...
Shehu, a cikin littafin nasa wanda ya bai wa wakilinmu na LEADERSHIP, ya yi zargin cewa; Obasanjo ya bijiro wa Buhari da wasu bukatu a lokacin da yana shugaban kasa (Obasanjo). Ya kara da cewa, “Akwai da dama a kusa da Buhari da ke ganin cewa; abin ban mamakin da ya faru a tsakanin...
Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Jibrin Ado bisa laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita a unguwar Gerawa da ke jihar. Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne a ranar Alhamis daga wata sanarwa ta manhajar X ta wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama. Ambaliya ta raba...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki Gwamnatin Tarayya kan ƙara kuɗin fasfo. Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), ta ƙara kuɗin fasfo mai shafi 32 zuwa Naira 100,000, yayin da mai shafi 64 ya koma Naira 200,000. Ambaliya ta raba ƙauyukan Sakkwato 6 da sauran sassan...
Ambaliyar ruwar da ta biyo bayan mamakon ruwan saman da aka tafka ta raba kauyuka shida da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato da saurann yankunan jihar. Kauyukkan da ambaliyar ta shafa su ne Makuwana da Dangawo da Faru da Gumbula da ’Yan Faruna da kuma Magajin Dawaki, sannan ta lalata hanyar da...
Duk da yawan wadanda aka gano suna dauke da cutar, jami’an kiwon lafiya sun bayyana irin ci gaban da ake samu. Daraktan kula da lafiyar al’umma a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Dakta Godwin Ntadom, ya bayyana cewa; Nijeriya ta samu sanarwar bullar cutar tarin fuka mafi yawa a 2024, inda ta gano sama da mutum...
Yana mai cewa: “Da yawa yanzu an manta zaurance ko ba a yi, saboda yanayin yadda zamani yake. Amma a da, musamman ma idan ka je wajen da ka ga sun iya Hausa kuma su ba Hausawa ba ne, za ka iya juya harshe ta amfani da zaurance wajen canza yaren ba tare da wanda...
Masu shirya taron sun dauki lokacin ana shirye-shiryen garin taron ta yi armashi da kuma nasara musamman saboda gayyato baki da aka yi daga makwabciyar kasar wato jamhuriyar Nijar. Kasancewar masarautar Daura na da alaka da aka al’adun gargajiya an shirya kasaitaiccen bikin wanda ya burge mahalarta taron musamman baki. Masu shirya taron...
Ba wai muna yin jayya da sanarar da ofishin Nuhu ya samu a tsakanin wadannan watanni ba ne kuma muna sane da kokarin da yake yi, na ganin cewa, ‘yan Nijeriya na samu su kwanta su yi barcin dare, idanuwansu biyu a rufe ba tare da wata fargabar ko za a kai masu hari ba....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU:...
Har ila yau, hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa; an fara bincike kan hatsarin da jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna ya yi a garin Asham da ke Jihar Kaduna. Hukumar ta ce, binciken zai gudana ne karkashin kulawar hukumomin da abin ya shafa tare da sa ido daga ma’aikatar sufuri...
Daraktan Tsara Tafiye-tafiye na Gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya maka jaridar Daily Nigerian da mawallafinta, Jaafar Jaafar a gaban kotu, bisa zargin ɓata masa suna ta hanyar kiransa da ɓarawo. A kwanakin baya ne dai jaridar ta zargi Daraktan da karkatar da kudade har sama da Naira biliyan shida da rabi zuwa asusunshi, kodayake...
An kafa ta a cikin 1955 kuma tana da hedikwata a Tokyo, IAPH kungiya ce ta duniya mai dauke da tashoshin jiragen ruwa fiye da 190, kuma tana gudanar da kasuwanci a cikin ƙasashe 89. Mambobin kungiyar IAPH suna kula da sama da kashi 60 cikin 100 na cinikin teku da kwantena na duniya....
Ƙasar Habasha ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani reshe na Rukunin Kamfanonin Dangote na Nijeriya domin gina wata sabuwar masana’antar samar da takin zamani ta kimanin dala biliyan 2.5. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed ya wallafa a shafin X ranar Alhamis. Sanusi Mikail Sami ya zama...
Ƙasar Habasha ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani reshe na Rukunin Kamfanonin Dangote na Nijeriya domin gina wata sabuwar masana’antar samar da takin zamani na kimanin dala biliyan 2.5. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed ya wallafa a shafin X ranar Alhamis. Sanusi Mikail Sami ya zama...
Siyar da Nkunku kuma yana nufin cewa Chelsea za ta iya samun riba a kasuwar musayar yan wasa, inda ka samu kusan fam miliyan 309 wajen siyar da yan wasa yayinda ta kashe fam miliyan 277 wajen sayen yan wasa, Nkunku ya zura kwallaye 18 sannan ya taimaka aka ci biyar a wasanni 62...
Nafisa wacce ta wakilci Nijeriya a karkashin Kwalejin Tulip International ta Nijeriya, ta buge abokan karawarta fiye da 20,000 daga kasashe 69, ciki har da kasashen Turanci. Gasar ‘TeenEagle’ babbar gasa ce ta duniya wacce ke bibiyar ƙwarewar ɗalibai cikin harshen Turanci, kaifin basira, da ƙwarewa a salon magana. Daga kanmu, magana ta...
Alhaji Sanusi Mikail Sami Gomo na III ya zama sabon Sarkin Zuru. Kwamishinan Ƙananan hukumomi da masarautu, Alhaji Abubakar Garba Dutsin-Mari ne ya sanar da hakan yau Alhamis, a fadar Sarkin Zuru wanda kuma ya miƙa masa takardar naɗin da Gwamnan Kebbi, Nasir Idris ya sanya wa hannu. Ambaliya: Manoma sun yi asarar miliyoyin Naira...
Sanadiyyar ambaliyar ruwa a gonaki amfanin gona na miliyoyin Naira ne suka salwanta inda ɗaruruwan filayen noma suka shefe da ruwa a Jihar Taraba. Kodayake, ba a bayyana ko an sako ruwa daga Logdo Dam ba ne daga jamhuriyar Kamaru ba, amma kogin Benuwe da ke Taraba ya yi ta malala daga gaɓarsa wanda ya...
Dakta Abdullahi Idris, ya bukaci sabbin shugabannin da zage damtse wajen ganin an samu nasarar abinda suka sanya a gaba wajen samar da zaman lafiya da hadin kan ‘yan Arewa. Akan hakan, ya bukace su da su zama jakadu na gari a jihohinsu wajen kare martabar kungiyar da kuma lalubo hanyar da za’a kara...
“A yau (Ranar Laraba) majalisar zartaswa ta yi la’akari da batun ƙarin kuɗin fansho ga tsofaffin ma’aikatan jiharmu da suka yi ritaya, hakan ya biyo bayan ƙarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata da kuma mafi ƙarancin kuɗin fanshi na ƙasa da gwamnatin tarayya ta amince da su,” in ji shugaban ma’aikatan. Barista Sani ya ƙara...
Gwamnatin Jihar Gombe tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Rotary International sun ƙaddamar da shirin aikin jinya domin rage mace-macen mata da yara a faɗin jihar. Shirin da aka gudanar a Ƙananan hukumomi uku da suka haɗa: Gombe da Kaltungo da Yamaltu-Deba, inda aka yi wa jama’a gwaje-gwaje, jinya da wayar da kai a unguwannin Yelenguruza...
Hukumar Ƴansanda a birnin Tripoli, Libya, ta kama wasu ƴan Nijeriya biyu bisa zargin hannu a wasu jerin fashin shagunan kasuwanci da ake gudanarwa a sassan birnin. Rahotanni sun bayyana cewa an cafke mutanen ne a ranar 25 ga Agusta 2025, bayan wani bidiyon na’urar tsaro ya nuna su suna satar kaya daga wani shago....
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ta sanar da ƙarin kuɗin yin Fasfo, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2025. A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, ACI AS Akinlabi, ya fitar a ranar Alhamis, an bayyana cewa wannan sabon tsari zai shafi aikace-aikacen da ake yi ne...
Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya ta kara farashin yin fasfo daga ranar day aga watan Satumbar 2025. A cewar wata sanarwa da Kakakin hukumar, ACI AS Akinlabi ya fitar ranar Alhamis, hukumar ta ce karin ya shafi iya wadanda suka nemi fasfo din a iya cikin Najeriya ne. Ana zargin miji da...
An kai shi asibiti, inda aka kula da shi sannan aka sallame shi domin halartar jana’izar iyalan nasa. Jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA), Bello Garba, ya ce ba su samu rahoton faruwar lamarin a hukumance ba, amma sun shirya gudanar da bincike kan lamarin. An binne mamatan bisa tanadin addinin...
Aƙalla mutum uku ne sun rasu, yayin da wani ɗan sanda ya ji rauni a wani rikicin ƙungiyoyin asiri da ya auku a kasuwar Owode Onirin da ke Jihar Legas. Rundunar ’yan sandan jihar, ta bayyana cewa tana neman Abiodun Ariori, Shugaban Kamfanin Golden Venture Limited, bisa zarginsa da hannu a rikicin. HOTUNA: Tinubu ya...
Dukkan mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, in ban da Amurka, sun goyi bayan ayyana bullar yunwa mafi muni a yankin zirin Gaza ta hanyar rahoton kungiyar Integrated Food Security Phase Classification (IPC), wata kungiya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya. Kasashe 14 da daga cikin 15 da suka amince da hakan, sun...
Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu ta ADC za ta iya fito da ‘yan takara daga kowace shiyya, duk da cewa APC da PDP sun nuna cewa daga Kudu za su fito da ɗan takara a 2027. Duk da cewa wasu na ganin tasirinsa ya ragu a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa tsakaninsa da Nyesom Wike,...
Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da ɗaya daga cikin yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyar ba. Farfesa Piwuna, ya ce ASUU a koyaushe na zaɓar tattaunawa da jami’an gwamnati a matsayin mafita. Amma duk da cewa sun cimma matsaya kan batutuwa masu muhimmanci...
A lokacin ziyarar, ya gana da Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, da sauran manyan jami’an ƙasar. Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniya guda biyar da suka shafi sufurin jiragen sama, harkokin waje, kimiyya da fasaha, da kuma noma, da wasu muhimman fannoni a ci gaban Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare....
’Yan bindigar da suka sace wani mutum, matarsa da ’yarsu a Jihar Katsina, na neman Naira miliyan 600 a matsayin kuɗin fansa. Wanda aka sace sun haɗa da Anas Ahmadu mai shekara 33, matarsa Halimat, da kuma ’yarsu Jidda. Ba zan tsaya takarar kowanne irin mukami ba a 2027 – El-Rufai NAJERIYA A YAU: Matakan...
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba zai tsaya takarar kowanne irin mukami ba a zaben 2027, inda ya ce burinsa kawai ya samar wa jiharsa da Najeriya nagartattun shugabanni. Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Kaduna, lokacin da ya karbi wasu matasa karkashin jagorancin Aliyu Bello da suka sauya sheka...
Lardin Hubei shi ma ya bi sawu, inda ya bullo da nasa shirye-shiryen na raba takardun tallafin tare da mai da hankali musamman a kan bangaren da ya shafi cin abinci. Babban makasudin hakan shi ne a karfafa mutane su rika fita zuwa gidajen cin abinci. Wannan ya kara farfado da salon cin abinci...
Musiba da auka wa wani gida a Zariya da ke Jihar Kaduna, bayan da katangar wani kango da ke maƙwabtaka da su ta faɗa wa mazauna gidan suna tsaka da barci. Wakilinmu ya ruwaito cewa, ruftawar ginin wadda ta auku a safiyar wannan Larabar ta yi ajalin matar gidan, Habiba Nuhu da ’ya’yanta biyu, Hauwa’u...
Wannan na zuwa ne bayan samun labarin kama wata mai suna Maryam Hussain Abdullahi a Saudiyya da zargin fataucin miyagun ƙwayoyi a daidai lokacin da take aikin Umara. Da yake bayyana yadda aka bankaɗo harƙallar ta hanyar, wadda ke jefa mutanen da ba su ji, ba su gani ba cikin masifa, ya ce ‘yan...