2025-09-17@21:59:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4401
«yan wasa»:
Gwamnatin Tarayya ta rage farashin jinyar ciwon ƙoda daga kimanin N50,000 zuwa N12,000 a Asibitocin Tarayya — ragin da ya kai kashi 76 cikin 100. Wannan saukin farashi ya samu ne bayan amincewar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda mai ba shi shawara kan harkokin sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana a cikin...
Allah Ya yi wa Alhaji Ahmed Momohsani Ododo, mahaifin Gwamna Ahmed Usman Ododo na Jihar Kogi, rasuwa yana da shekara 83 a duniya. Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya sanar da rasuwar a yammacin ranar Litinin, 18 ga Agusta, 2025. Gwamnatin jihar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga...
Wani mutum ya soka wa budurwarsa mai suna “Ima” wuka har lahira a unguwar Okereke Street da ke garin Fatalkwal na Jihar Ribas. Mutumin, wanda ake wa lakabi da “Doctor” ya daba wa budurwar tasa mai suna “Ima” wuka ne bisa zargin tana cin amanarsa. Lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, wanda shaidu a...
Wasu masu garkuwa da mutane sun yi hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa rabon kudin fansar mutanen da suka sace a Jihar Nasarawa. Jami’an tsaro sun kwato bindigogi uku da tsabar kudi Naira miliyan 6.9 daga motar ’yan bingidar bayan hatsarin motar a yankin Garaku, daura da wani shingen bincike na Jami’an Kula da Lafiyar...
Mutum 62 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su sama da wata guda sun tsere bayan rundunar soji ta kai farmakin sama da ƙasa a maboyar ’yan ta’adda a Karamar Hukumar ƊanMusa, Jihar Katsina. Farmakin da aka kai a ranar Asabar da misalin ƙarfe 5:10 na yamma ya gudana ne bisa sahihan bayanan leƙen...
Gwamnatin Jihar Jigawa tace tana gudanar da ayyukan gyara da ginawa da kuma inganta hanyoyin mota domin cimma kudirin ta na bunkasa bangaren aikin noma. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka yayin kaddamar da aikin sanya kwalta akan hanyar Dandi da Farin Daba zuwa Gada a karamar hukumar Kazaure. Ya ce gwamnatin jihar ta...
Wani jirgin ruwa ɗauke da mutum sama da 30 da kuma babura takwas, ya nutse a garin Kojiyo da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo a Jihar Sakkwato. Wani mazaunin yankin mai suna Nasiru Goronyo, ya ce jirgin ya yi hatsari ne a kogin garin bayan ya ɗauki mutane da kaya da suka fi ƙarfinsa. Kano: NNPP...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Suna sa ido kan abubuwan da ke faruwa a Kudancin Caucasus cikin lura Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ismail Baqa’i, ya yi nuni da yadda Iran ke daukan abubuwan da ke faruwa a yankin arewa maso yammacin kasar da muhimmanci, yana mai jaddada cewa: “Suna...

Gwamnatin DR Kongo Ta Nuna Rashin Amincewarta Da Zabin Kenya Kan Wajen Da Zata Bude Karamin Ofishin Jakadancinta A Kasarta
Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta ki amincewa da nadin sabon karamin ofishin jakadancin Kenya a birnin Goma Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta sanar da kin amincewa da nadin sabon karamin ofishin jakadancin Kenya a birnin Goma da ke gabashin kasar, duba da matakin da ya saba wa ka’idojin diflomasiyya, duba da yadda Kongo ke ganin ci...
Al’ummar unguwar Jauro Jatau da ke hanyar Bypass a Ƙaramar Hukumar Akko, Jihar Gombe, sun koka kan tsawon watannin da suka shafe ba tare da wutar lantarki ba. Sun roƙi gwamnati, ’yan siyasa da masu hannu da shuni su kawo musu ɗauki cikin gaggawa. Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Zuru Adam A. Zango...
An ceto wani mutum mai shekara 50 ya yi yunƙurin kashe kansa a garin Bama na Jihar Borno. Lamarin wanda ya afku a yammacin ranar Juma’a a unguwar Hausari, inda al’ummar yankin ne suka kai masa ɗauki. Shaidu sun ce mutumin ya daɓa wa kansa wuƙa har sau uku a ciki, kafin ya yanke mazakutarsa...
Dubban mutane a birnin London sun yi cincirindo a kofar shiga sansanin sojojin sama da ke arewa maso yammcin birnin London inda suke zargin gwamnatin kasar da hannu dumu-dumu a kisan kiyashin da ke faruwa a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa jiragen yakin F-35 na kasar Burtania suna shawagi...
Al’ummar unguwar Jauro Jatau da ke kan hanyar Bypass a Ƙaramar Hukumar Akko, Jihar Gombe, sun koka kan dogon lokacin da suka shafe ba tare da samun wutar lantarki ba. Sun roƙi gwamnati, ’yan siyasa da masu hannu da shuni da su kawo musu ɗauki cikin gaggawa. Tun a watan Ramadan Al’ummar sun bayyana cewa...
Jakadan Iran a Saudiyya Alireza Enayati ya tabbatar da ci gaba da tuntubar juna tsakanin babban hafsan hafsoshin sojin Iran da ministan tsaron Saudiyya. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na IRNA Alireza Enayati ya yi nuni da cewa, Saudiyya na kallon alakar ta da Iran a matsayin alaka mai matukar muhimamnci, kamar yadda...
Jami’an tsaro sun kama manyan shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru, ciki har da shugaban ƙungiyar, Mahmud Muhammad Usman wanda aka fi sani da Abu Baraa. An daɗe ana zarginsa da kitsa hare-hare masu yawa a Najeriya. ’Yan sanda sun kama matashin da ya yi garkuwa da kansa a Ondo Majalisar dokokin Gombe ta fara...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo, ta cafke wani matashi mai suna Azeez Bello, mai shekaru 29, wanda ya kitsa garkuwa da kansa domin karɓar kuɗin fansa Naira dubu 500 daga hannun iyayensa. Kakakin rundunar, Ayanlade Olushola, ya bayyana cewa Bello, ɗan asalin garin Ipele da ke Ƙaramar Hukumar Owo, ya yi haka ne bayan mahaifinsa...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Suna godiya ga Iraki saboda karimcin da ta yi wa masu ziyarar Arba’een na Imam Husain {a.s} Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yaba da kokarin gwamnati da al’ummar Iraki wajen karbar bakwancin masu ziyarar juyayin Arba’een na Imam Husaini {a.s}. A yayin da yake...
Aƙalla mutum 164,390 ake sa ran za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar dokokin Jihar Kaduna a mazaɓar Zariya da kewaye. Sai dai yawancin masu zaɓe ba su fito ba. APC ta buƙaci a soke zaɓen cike gurbi a Kano An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 288 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama mutanen da makamai masu hatsari, ciki har da bindigogi ƙirar gida, wuƙaƙe da adduna. Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan...
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar da kama aƙalla ’yan daba 100 da ake zargi da tayar da zaune-tsaye a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Bagwai a Jihar Kano. Kwamishinan INEC na Jihar Kano, Abdu Zango, ya shaida wa manema labarai a Bagwai cewa jami’an tsaro...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa sojojin JMI a shirye suke su shiga yaki a ko dauce, amma yana ganin yiyuwar a sake shiga yaki da HKI nan kusa yana da wuya. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto Abbas Argchi yana fadar haka, a daren Ashamis da ta gabata, a...
Jami’an tsaro sun kama wani mutum da tsabar kuɗi Naira miliyan 25 da ake zargin kuɗin sayen kuri’a ne a zaɓen cike gurbin da ke gudana a Jihar Kaduna. Da misalin ƙarfe 3 na dare kafin wayewar garin safiyar Asabar da ake gudanar da zaɓen ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka...
A wasu yankunan Jihar Katsina da suka daɗe cikin fargaba da hare-haren ’yan bindiga, zaman lafiya ya fara dawowa sakamakon sulhu da al’umma suka yi da masu tayar da ƙayar baya. Wannan sulhu, wanda ba a haɗa gwamnati ba, ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu cikin daminar bana. Manoma sun fara noma cikin...
Rundunar sojan Mali ta sanar da kame wasu manyan hafsoshin sojin Mali guda biyu, dan kasar Faransa, da wasu mutane da dama da ake zargi da yunkurin tayar da zaune tsaye a kasar ta hanyar yunkurin juyin mulki, wanda kuma aka yi nasarar dakile shi. Ministan tsaron kasar Janar Daouda Aly Mohammedine ne ya bayyana...

Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa
“Mun amshe bukatun, sannan bayan hakan kwamitin yin nazari kan sake yi wa tsarin mulki garambawul wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau yake jagoranta zai tattance tare da shirya rahoto ga majalisar. “Da zarar rahoton ya kammala, majalisar dattawa tare da hadin gwiwar majalisar wakilai za su gudanar da cikakken jin ra’ayin jama’a....
Tun Farko tawagar gwamnatin ta Isa fadar hakimin Barnawa domin isar da sakon ta’aziyyar gwamnatin jihar kaduna na rashin matashi inda suka tabbatar wa da Hakimin cewa gwamnatin jihar kaduna zatayi duk Mai yiwuwa wajen ganin anyiwa matashi Abubakar adalci da kuma gano dalilin mutuwarsa. Hakazalika, tawagar gwamnan sun Kai ziyarar jaje gidan mamacin...
Daya daga cikin manyan nasarorin da Dakta Bello Matawalle ya samu shi ne kaimi da aka yi wurin yaki da ta’addanci, ta hanyar kyautata hadin gwiwa da Sojojin kasa, da Sojojin sama da sauran hukumomin tsaro. An yi rugu-rugu da matattaran ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas, wanda hakan ya yi sanadiyar raguwar hare-hare. A...
Tinubu ya kara da cewa tun bayan karbar mulkinsa, gwamnatinsa ta bayar da fifiko wajen samun damar kudi kuma ta yi alkawarin tallafa wa harkokin kasuwanci da zai habbaka samar da ayyuka da samun kwarewa da kuma masana’antu. Ya yaba wa gwamnatin Kuros Ribas kan kirkiro shirin tattaunawa da fasahar zamani a harkokin kasuwancin jihar,...
Da safiyar yau Jumma’a, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar da rahoton tattalin arzikin kasar na watan Yuli, inda ta bayyana cewa, kasar Sin ta gaggauta daidaita manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, tare da inganta dunkulewar manyan kasuwanni cikin sassan kasar, ta yadda aka tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin tsari, da kara...
Ita ma da take nata jawabin Maryam Bukar Hassan ta ce, akwai bukatar a samar da wani shiri na kawo sauyi wajen samar da zaman lafiya mai dorewa. Hakazalika Maryam ta jaddada cewa, idan har ba zaman lafiya babu yadda za a iya cimma muradun ci gaba mai dorewa (SDGs) kuma zai kasance mara amfani....
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi a garin Potiskum a daren Juma’a zuwa safiyar yau Juma’a ya haifar da ambaliya, wanda ya haifar da tashin hankali ga mazauna garin. Kamar yadda majiyar da ke garin ta shaidawa Aminiya cewa, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fara shi tun kusan tsakar...
“Sama da yara miliyan 10.1 ne ba su kai makaranta, kashi 70 masu zuwa makarantar kuma ba su da dabarun koyo, kuma fiye da kashi 60 na malaman firamare na gwamnati ba su da ilimin dijital,” in ji ta Da take yaba wa gwamnatin Koriya ta Arewa bisa tallafin da ta samu ta hannun hukumar...
Jami’an tsaro sun kuɓutar da wasu fasinjoji 10 da aka yi garkuwa da su a hanyar Itobe – zuwa Ochadamu – Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu a Jihar Kogi. Fasinjojin da aka kuɓutar an yi garkuwa da su ne a ranar 11 ga watan Agusta a ƙauyen Ugbakpedo da ke kan titin, lokacin da wata...
“Manufar ita ce a ninka adadin likitoci, ma’aikatan jinya, masu hada magunguna, kwararrun dakunan gwaje-gwaje da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya. Wannan ko shakka babu zai kara habaka harkokin kiwon lafiya a kasar,” in ji shi. Tsohon gwamnan Jihar Katsinan ya bayyana cewa, a bana, TETFund ta samu tallafinta mafi girma na Naira Tiriliyan...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja domin ziyarar aiki zuwa ƙasashen Japan da Brazil. Ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 11:15 na safiyar Juma’a, inda zai tsaya a Birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Matsalar ƙofa ta hana fasinjoji 58 hawa jirgin Abuja zuwa Landan Matsalar tsaro...
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa ƙimar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta sauka zuwa kashi 21.88% a watan Yuli 2025, daga kashi 22.22% da aka samu a watan Yuni 2025. Wannan na nuni da raguwa da kashi 0.34% idan aka kwatanta da watan da ya gabata. Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin...
Shugaban hukumar kula da wasanni ta ƙasa (NSC), Bukola Olopade, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa Super Falcons ba su samu kuɗin alawus ɗin da aka yi musu alƙawari ba, yana mai cewa an riga an biya duk ƴan wasan, sai kaɗan daga cikinsu da ke da matsalar asusun banki. Ya ce ya tabbatar da...
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce matsalar tsaro na iya hana ta gudanar da aikin rijistar masu zabe a kananan hukumomin jihar Borno guda hudu. Kananan hukumomin da lamarin zai iya shafa su ne Abadam, Guzamala, Marte da Kala-Balge. Jama’a ba sa yaba wa kokarinmu na hana aikata laifi – Babban Sufeton ’Yan Sanda...
Babban Sufeton ’Yan Sanda na Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce galibin jama’a ba sa yaba wa kokarin jami’ansu na hana aikata laifi a cikin al’umma, duk da yana daya daga cikin manyan ayyukansu. Kayode, wanda Mataimakin Babban Sufeto mai kula da sashen sayo kayayyaki na rundunar, A.A. Hamza ya wakilta, ya fadi hakan ne a...
Bugu da kari kuma, gudummawar da Nijeriya ke bayarwa ga kokarin wanzar da zaman lafiya a duniya ba za su misalta tu ba, wanda hakan ke jaddada aniyarta na inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Manufofinta na kasashen waje a al’adance suna nufin ingantawa da kuma kare muradun Nijeriya tare da tallafa wa...
Akwai wasu tsaffin ‘yan siyasa daga yankin Arewacin Najeriya,wadanda ke ci da gumin ‘yan Arewa. Wadannan tsaffin ‘yan siyasa, yanzu alkadarinsu ya riga ya karye, ba su da wani abu da ya rage illa su rungumi siyasar kabilanci da bangaranci. Ba tsaffin ‘yan siyasa kawai ba ne. Gungu-gungu ne. Wasun su, tsaffin ‘yan boko ne....
Wata kotun tarayya a kasar Kanada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon dan siyasa, Douglas Egharevba, mafaka a kasar saboda alakarsa da jam’iyyun. Jaridar Peoples Gazette ta rawaito cewa alkalin kotun, Phuong Ngo, a hukuncin da ta yanke ranar 17 ga watan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A wasu jihohin Arewacin Najeriya, masu karɓar fansho suna cikin mawuyacin hali sakamakon ƙarancin kuɗin da ake biyansu duk wata. Wasu daga cikinsu sun bayyana yadda suke karbar naira dubu 5 a kowane wata a matsayin kudin fansho bayan kwashe shekaru suna aiki. NAJERIYA A YAU: Yadda matasa...
Alkaluman sun nuna cewa, cikin wa’adin, yawan sakwannin da aka yi jigilarsu a cikin birni daya sun kai biliyan 9.26, adadin da ya karu da kaso 6.5 bisa dari a mizanin shekara, yayin da wadanda aka yi jigilarsu daga birni guda zuwa wani na daban, suka kai biliyan 100.43, karuwar da ta kai ta...
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da miƙa wa mataimakinsa, Malam Faruk Jobe, ragamar mulkin jihar, inda shi kuma zai tafi hutun mako uku domin duba lafiyarsa. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Salisu Zango, ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta bayyana cewa hutun zai fara...
A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan...
A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan...
“Kowa ya sani wadatar abinci yana ɗaya daga cikin alamun da ke nuna kyautatawar tattalin arziki na ƙasa baki ɗaya, don haka ne muka himmatu wajen ba da namu gudunmawar ta wannan fannin.” Ya kara da cewa, an kafa gidauniyar ne domin taimakawa a ɓangaren kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki wanda rabon takin na...
Shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya cancanci yabo kan daidaita tattalin arzikin ƙasar nan da yake ci gaba da yi. Okonjo-Iweala ta shaida wa manema labarai hakan ne ranar Alhamis bayan ta gana da shugaban ƙasar a Abuja. Motar tifa ta murƙushe ɗalibai biyu...
A yankin Arewa-maso-Gabas, ya ce sojojin, sun kawar da ‘yan ta’adda da dama, sun lalata sansanonin kayan aikinsu, sun kwato makamai, sun wargaza hanyoyin hada-hadarsu tare da samar da amintaccen wuri don sake tsugunar da ‘yan gudun hijira. A cewar Kangye, sojojin sun kama mutane 37 da ake zargin ‘yan ta’adda ne, tare...