2025-07-09@19:37:26 GMT
إجمالي نتائج البحث: 210
«Sharuɗa»:
Wata Babbar Kotu a Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa Farfesa Ignatius Uduk hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari kan laifin sauya sakamakon zaɓe. An gurfanar da Farfesan kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da gazawa wajen aiwatar da aikinsa, sauya sakamakon zaɓe, da kuma yin rantsuwar ƙarya a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe....
Hukumar ICPC ta samu gurfanar da Mohammed Idris, wani jami’i a ƙofar shigen shiga wurin Hajji da ɗiban kaya na filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagas, kan laifin bayar da bayanan ƙarya da kuma cin da kuɗaɗen haram. A gaban Mai shari’a O.A. Fadipe na kotun laifuka ta musamman da ke Ikeja,...
Ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles ta Nijeriya da ke buga wasa a ƙungiyar Galatasaray Victor Osimhen, ya shigar da ƙarar wani ɗan jaridar Turkiya Tolga Bozduman bisa zargin ɓata masa suna. A cikin wani saƙo da wani makusancin Osimhen ya wallafa a shafinsa na X, ya ce za a fara sauraron ƙarar da...
A wannan hirar, Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatuil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi magana game da cece-ku-ce kan ɗaukar nauyin wani taron Al-Ƙur’ani da aka shirya. Da yake magana jim kaɗan bayan wata lacca ta musamman a sakatariyar JIBWIS ta ƙasa da ke Abuja a wannan makon, shugaban ya bugi...
Aston Villa na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke son ɗauko ɗan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford, ɗan wasan mai shekaru 27 bai taka leda a United ba tun lokacin da babban kocin ƙungiyar Ruben Amorim ya ajiye shi a wasan Manchester derby a ranar 12 ga watan Disamba. Amorim ya...
Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mafarauci mai shekara 55 mai suna Yusuf Garba wanda aka fi sani da Gana kan zarginsa da tona kabari tare da yanke kan mijin mahaifiyarsa. A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne a...
Aƙalla mutane 20 ne ska rasu a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a Jihar Unity da ke Sudan ta Kudu. Rahoton gidan rediyon Miraya, na tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke ƙasar, ya bayyana cewa jirgin ya yi hatsari ne jim kaɗan bayan tashinsa daga wata rijiyar mai a Unity, inda ya ɗauki...
Ɗan wasan Nijeriya kuma gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar Afrika, Ademola Lookman, ba zai buga wasan da Atalanta za ta kara da Barcelona a gasar cin kofin Zakarun Turai yau Laraba ba, sakamakon rauni da ya ji a gwiwarsa. A wata sanarwa da kulob ɗin Atalanta ya fitar, ya ce ɗan wasan mai shekaru 27 ya...
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya na da wadataccen arzikin da za ta ci gaba da ɗawainiyar duk wasu tafiye-tafiyen Shugaba Bola Tinubu zuwa ƙetare. A bayan nan dai ’yan Nijeriya na ci gaba da bayyana damuwa kan yawan tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi a kai-a kai zuwa ƙetare la’akari da...
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda...