Aminiya:
2025-08-10@12:21:28 GMT

Kotu ta yanke wa tsohon Shugaban Peru ɗaurin shekaru 15

Published: 16th, April 2025 GMT

An yanke wa tsohon shugabar ƙasar Peru, Ollanta Humala hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari.

Wata kotu a ƙasar ce ta yanke masa hukuncin bisa samunsa da laifin halatta kuɗin haram a badaƙalar cin hanci da katafaren kamfanin gine-gine na Brazil Odebrecht ke yi don samun kwangila.

Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Juma’a da Litinin

Haka kuma, ita ma mai ɗakinsa, Nadine Heredia, an yanke mata makamancin wannan hukuncin, duk da cewa ba ta halarci zaman kotun ba, saboda haka alƙalin ya bayar da umarnin kamo ta.

Ollanta Humala, mai shekaru 62, ya kasance tsohon shugaban ƙasar Peru na biyu da aka samu da laifi, lamarin da ya sa nan take aka kai shi wani gidan yari da ke gabashin Lima, inda ake tsare da tsoffin shugabannin kasar Peru Alejandro Toledo da Pedro Castillo.

Wannan hukuncin na zuwa ne sama da shekaru uku da fara shari’ar Humala wanda ya mulki ƙasar Peru daga 2011 zuwa 2016 —amma dai lauyoyinsa sun bayanna cewa za su ɗaukaka ƙara.

Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta ce Kamfanin Odebrecht ya ba da cin hanci dala miliyan 788 a cikin shekaru goma ga gwamnatocin yankin Latin Amurka domin samun kwangilar gine-gine.

Kamfanin ya bayyana cewar ya bayar da dala miliyan 29 na cin hanci ga Peru a tsakanin 2005 da 2014.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Shekara nawa shugabanni ke bukata don cika alkawuran zabe?

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci ‘yan takara kan dauki alkawura.

Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka?

NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani?

Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi
  • Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr
  • An Maka Gwamnatin Neja Da NBC A Kotu Kan Barazanar Rufe Gidan Rediyon Badeggi FM
  • Nazari Kan Dalilin Da Ya Sa Kajin Gidan Gona Ke Samar Da Ƙananan Ƙwai 
  • Cacar Baki Ta Ɓarke Tsakanin el-Rufai Da APC Kan Tazarcen Tinubu A 2027
  • Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh
  • Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara 
  • Tsohon Shugaban PDP Audu Ogbeh Ya Rasu
  • Yadda ma’aikatan gwamnati ke gina gidaje da kuɗin sata a Abuja
  • NAJERIYA A YAU: Shekara nawa shugabanni ke bukata don cika alkawuran zabe?