Za a ci gaba da sayar da ɗanyen mai a farashin Naira — Gwamnati
Published: 9th, April 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sayar da ɗanyen mai da man da aka tace farashin Naira, maimakon amfani da dalar Amurka.
Wannan mataki na daga cikin manufofin gwamnati na bunƙasa tattalin arziƙin cikin gida, rage matsin lamba kan kasuwar musayar kuɗi, da kuma bunƙasa makamashi.
’Yan bindiga sun mamaye garuruwa 64 a Filato — Gwamna Mutfwang ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a SakkwatoMa’aikatar Kuɗi ta bayyana hakan ne a shafinta na X, inda ta ce wannan ba mataki ne na wucin-gadi ba, sai dai tsari ne da ake son ya ɗore wanda Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, ta aminta da shi.
“Wannan manufa za ta taimaka wajen bunƙasa tace mai a gida, rage dogaro da dala, da kuma inganta tsaro a fannin makamashi a Najeriya,” in ji Ma’aikatar.
“Wani muhimmin ɓangare ne na shirin gwamnati don kare makomar tattalin arziƙin ƙasa.”
A ranar Talata ne manyan jami’an Ma’aikatar Kuɗi, NNPCL, FIRS, CBN, da wasu manyan hukumomi suka gana domin duba yadda aikin ke tafiya da kuma magance matsalolin da ka iya tasowa a tsawon lokacin aiwatar da shirin.
“Mun fahimci cewa sauye-sauye irin wannan suna zuwa da ƙalubale,” in ji wani jami’i daga cikin mahalarta taron.
“Amma dukkanin hukumomin da ke da hannu a cikin shirin sun ƙudiri aniyar ganin an cimma nasara.”
A baya-bayan nan NNPCL ya daina sayar wa matatar Dangote ɗanyen mai a farashin Naira bayan ƙarewar yarjejeniyar da suka ƙulla.
Hakan ya haifar da tashin farashin man fetur a gidajen mai a faɗin ƙasar nan, lamarin da masana suka ce hakan zai sake shafar tattalin arziƙin Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dalar Amurka ɗanyen mai farashi Ma aikatar Kuɗi Naira
এছাড়াও পড়ুন:
Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta ci gaba da shirin gudanar da babban taronta wanda za a yi a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan da ke Jihar Oyo.
Tun da farko, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta hana jam’iyyar gudanar da taron, inda ta ce PDP ta karya dokokinta na cikin gida.
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDPMai shari’a James Omotosho, wanda ya jagoranci shari’ar, ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da kada ta karɓi ko ta wallafa sakamakon taron har sai PDP ta cika dukkanin sharuɗan da doka ta tanada.
Sai dai a cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar da yammacin ranar Juma’a, kakakinta na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce jam’iyyar ba za ta dakatar da shirin gudanar da taron ba.
Ya bayyana hukuncin kotun a matsayin tauye haƙƙin dimokuraɗiyya a Najeriya.
Ologunagba, ya ce hukuncin ba zai hana PDP ci gaba da shirye-shiryenta na zaɓen sabbin shugabanni da za su jagoranci jam’iyyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa ba.
Ya yi nuni da cewa Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa jam’iyyu na da ’yancin tafiyar da harkokinsu na cikin gida.
“PDP na kira ga mambobinta da shugabanni a faɗin ƙasar nan da su kuma ci gaba da shirye-shiryen babban taron jam’iyyar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar mai bin doka ce, kuma ta umarci lauyoyinta da su ɗaukaka ƙara game da hukuncin kotun.