Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar da shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin daƙile ayyukan miyagu da ke iya ƙoƙarin cin gajiyar yanayin a matsayin wata dama ta aikata mugun laifi ko ta’addanci.

Damuwar ƙwararru kan ƙarsashi da karfin sojoji

Wani ƙwararre kan harkokin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce illar wannan lamari ta wuce ɓarnar zahiri da kuma yiwuwar asarar rayuka.

Ya ce, “Lalacewar makamai, harsasai, da sauran muhimman kayan aikin soja a barikin babban asarar kayan aiki ne da ke iya shafar shirye-shiryen ayyukan soji kai tsaye da ma sauran ayyukan tsaro a yankin Arewa maso Gabas da kuma yankin Tafkin Chadi.”

’Yan acaba sun yi wa mai fura fyaɗe Abuja Wulaƙancin da ake mana a Kudu ya yi yawa —Hausawan Legas

Kabiru Adamu ya ƙara cewa hanyoyin samar da kayan aikin soji — waɗanda tuni suke cikin matsi saboda yanayin aiki mai wahala — za su iya samun ƙarin cikas, wanda zai sa gyarawa ya zama da wahala.

Kabiru Adamu ya kuma yi gargaɗi game da irin tasirin da lamarin zai iya yi a tunani da ƙwarin gwiwar sojoji. Ya ce, “Lamarin na iya raunana jin tsaro da kwanciyar hankalinsu, musamman tunda suna zaune ne a cikin barikin.

“Wannan na iya kawo raguwar ƙwarin gwiwa da ƙaruwar damuwa,da kuma raunana ruhin faɗa. Zai kuma iya jawo rashin amincewa da ka’idojin tsaro da kuma shugabannin da ke da alhakin tabbatar da su,” in ji shi.

Ya ƙara jaddada cewa cikas na wucin gadi da lamarin ya haifar na iya kawo tsaiko ga ayyukan rundunar Operation Hadin Kai har sai an maye gurbin kayan aiki da suka salwanta.

“Dangane da ƙoƙarin yaki da ta’addanci, wannan lamarin na iya zama koma baya. Yana iya karfafa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP su ƙara kai wa sojoji da fararen hula hare-hare. Suna iya ganin lamarin a matsayin alamar rauni ko wata dama,” in ji shi.

Kabiru Adamu ya kuma nuna haɗarin raguwar amincewar jama’a, yana mai cewa “Ga fararen hula a Maiduguri, waɗanda tuni suke fuskantar barazanar ta’addanci koyaushe, abin da ya faru a Barikin Giwa na iya kawo fargaba game da tsaro gaba ɗaya da kuma rage sakin jiki da ikon sojoji na kare su — wanda zai iya shafar bayanan sirri da ake samu daga al’ummar yankin.”

Masanin ya kuma lura da  yiwuwar amfani da lamarin wajen yada farfaganda abokan gaba.

“Ƙungiyoyi kamar Boko Haram da ISWAP na iya nuna shi — ba tare da la’akari da ainihin dalilin ba — a matsayin nasara ko kuma wani aikin ikon Allah, su yi amfani da shi don ƙarfafa ɗaukar sabbin mayaƙa, da ƙarfafa ƙwarin gwiwa, da kuma rage amincewar jama’a ga gwamnati da jami’an tsaro.”

Don haka ya ce, “Dole ne sojojin su magance sakamakon lamarin cikin gaskiya da gaggawa. Karfafa ka’idojin tsaro da samar da ingantacciyar sadarwa suna da matuƙar muhimmanci wajen dawo da amincewa. Rashin yin hakan na iya ƙarfafa matsayin ’yan ta’adda da kuma tsawaita rikicin.”

Mun ɗauka harin ’yan ta’adda ne — Mazauna

Manyan fashe-fashe da ƙarar harbe-harbe da tartsatsin wuta da kuma hayaki da ke tashi sama, sakamakon gobarar ma’aajiyar makaman sun firgita mazauna unguwannin Polo, Fori, GRA, Unimaid, da sauran wurare, inda fita kan tituna, saboda fargabar yiwuwar harin Boko Haram.

Wani mazaunin gari, Adamu Yusuf, ya ce fashewar farko ta faru ne da tsakar dare, sai kuma harbe-harbe da suka biyo baya waɗanda suka kara musu tsoro.

Ya ce, “Mun yi magana da wani tsohon soja wanda ya kira abokin aikinsa a barikin, ya tabbatar da cewa gobara ce ta tashi a ma’ajiyar makamai. Amma karar hare-haren da ya biyo baya ya sa mana shakku.”

Kyari Bulama, wani makwabcin barikin, ya ce ƙarar fashewar da habe-harben ne suka tashe shi daga barci. Ya ce, “Mun zaci harin Boko Haram ne, muka yi ta guje-guje a gidan. Abin ya fi ban tsoro da na fito fita waje. Kusan kowa sun fito kan tituna, motoci da Keke NAPEP na guje-gujen barin yankin.”

A Jami’ar Maiduguri, ɗaruruwan ɗalibai sun gudu daga ɗakunansu na kwana suka koma cikin gari don guje wa yiwuwar harin ’yan ta’adda.

Wani dalibi ya ce, “Fashewar ta yi matuƙar ƙarfi, kuma kamar tana ƙara kusantowa. Mun fito da gaggawa daga ɗakunan kwananmu, amma jami’an tsaro ba su iya gaya mana abin da ke faruwa ba. Daga ƙarshe, mun samu labarin cewa ma’ajiyar makaman sojoji ne ta yi gobara.”

Aisami Lawan, wani mazaunin unguwar Polo, ya ce lamarin ya tuno musu da wani harin da ya faru a baya.

Ya ce, “Akwai matuƙar ban tsoro. Rabon da irin haka ya faru tun lokacin harin Boko Haram a barikin a shekarar 2014.”

Ya ƙara da cewa, “Alhamdulillah, ba mu samu labarin mutuwar fararen hula ba, amma akwai ƙaruwar fargabar cewa rayuwar sojoji da waɗanda ake tsare da su a barikin na cikin haɗari sosai.”

 

Ba hari ba ne — ’Yan sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta bayyana cewa fashewar da ta faru, ba harin abokan gaba ba ne.

Kakakin rundunar, Kenneth Nahum Daso, ya ce bincike na farko ya nuna cewa fashewar ta samo asali ne daga ma’ajiyar makamai da ke cikin barikin.

Daso ya ce, “Bayan rahotannin fashewar da aka ji a Maiduguri, bincike na farko ya nuna cewa fashewar ta samo asali ne daga gobara a ma’ajiyar makamai da ke Barikin Giwa, ba harin makiya ba, kuma har yanzu ana ci gaba da tabbatar da tsaro,” in ji Daso.

Ya kara da cewa jami’an tsaro da kuma hukumar kashe gobara a halin yanzu suna wurin suna aiki don kashe gobarar da ta barke.

Gwamnatin Jihar Borno ta wata sanarwa daga Hukumar Kashe Gobara, karkashin Ma’aikatar Yada Labarai da Tsaro na Cikin Gida, ta tabbatar da cewa an shawo kan gobarar.

Sanarwar ta ce, “Gobarar ta shafi ma’ajiyar makamai a cikin barikin, kuma wasu makamai sun fashe, wanda ya haifar da kara mai karfi. Bincike na farko ya nuna cewa tsananin zafin da ake fama da shi a Maiduguri a wannan lokaci na shekara ƙila shi ne ya haifar da gobarar.”

Sanarwar ta kuma lura cewa tawagar hadin gwiwa ta masu ba da agajin gaggawa daga Hukumar Kashe Gobara ta Sojojin Najeriya, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Borno sun mayar da martani cikin gaggawa kuma sun yi nasarar kashe gobarar.

 

Tsananin zafin rana ne ya haifar da fashewar — Sojoji

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa fashewar ba harin ’yan ta’adda ba ne, sai dai sakamakon tsananin zafin rana.

Muƙaddashin Mataimakin Daraktan hulda da jama’a na rundunar HADIN KAI, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya ce, “Tsananin zafin da ake fama da shi a Maiduguri a halin yanzu ya haifar da fashewar wasu harsasai a rumbum ajiyar makamai,” amma an shawo kan lamarin cikin gaggawa ta hanyar hadin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Borno da sauran masu ba da agajin gaggawa.

Ya ce, “An tura dakaru domin tabbatar da doka da oda tare da hana miyagun mutane amfani da halin da ake ciki.”

Kovangiya ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, ya kuma ba da tabbacin cewa an dauki duk matakan da suka dace don tabbatar da tsaro da kuma hana maimaituwar hakan a nan gaba.

Harin da aka taba kaiwa Barikin Giwa

A ranar 14 ga Maris, 2014, ɗaruruwan ’yan ta’adda sun kai hari mai ƙarfin gaske a Barikin Giwa da ke Maiduguri.

Daga baya, sojojin Najeriya suka sanar cewa sun yi nasarar fatattakar maharan, inda dakarun sama da na kasa suka kashe da yawa daga cikin ’yam ta’addan.

Wani ganau ya shaida wa kungiyar Amnesty International cewa mambobin kungiyar Civilian Joint Task Force (CJTF) sun kama wasu daga cikin waɗanda ake tsare da su da suka tsere a lokacin harin.

Wannan lamarin ya bar babban tabo a zukatan mazauna da yawa, kuma fashewar da ta faru kwanan nan a ranar Alhamis ta tuno musu harin na 2014, ta kuma sake tayar da fargaba a cikin al’umma.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Barikin Sojoji na Giwa Boko Haram fararen hula fashewa ma ajiyar makamai Tsaro Hukumar Kashe Gobara ta ma ajiyar makamai cewa fashewar Barikin Giwa ya haifar da kashe gobara Jihar Borno fashewar da a ma ajiyar yan ta adda tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

An garzaya da ’yan Isra’ila 154 asibiti bayan harin Iran

Isra’ila ta tabbatar cewa an garzaya da ’yan ƙasarta aƙalla 154 asibiti bayan sabbin hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kawo mata.

Ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta ce aƙalla mutum huɗu daga cikin waɗanda aka kai asibitin suna cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, wasu biyar kuma na samun kulawa ta musamman saboda tsananin tashin hankali.

Alkaluman da ma’aikatar ta fitar sun nuna cewa mutum 130 daga cikin majinyatan sun samu raunuka marasa tsanani a sakamakon hare-haren.

Wannnan na zuwa ne a yayin da Iran ta ci gaba luguden rokoki a matsayin ramuwar gayya a sassan Isra’ila a a ranar Talata.

Isra’ila ta ce Iran ta lashe mata mutane akalla 24.

A ɗaya ɓangaren kuma Iran cewa harin tsokana da Isra’ila ta kai mata ya yi ajalin kimanin mutum 224.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Kashe ‘Yan Ta’adda 6,260, An Ceto Mutane 5,365 Acikin Shekaru Biyu – Hedikwatar Tsaro 
  • Daga Xi’an Zuwa Astana: Me Muka Koya Daga Taron Kolin Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya
  • Gwamnatin Tarayya Ta Gurfanar Da Natasha A Kotu Kan Zargin Ɓata Sunan Akpabio Da Yahaya Bello
  • Gwamnonin APC Sun Nemi Tinubu Ya Ƙirkiri ‘Yansandan Jihohi Don Yaƙar Matsalar Tsaro
  • An Kashe Wasu ‘Yan Bindiga 12, An Kwato Makamai A Katsina
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Kwaso ‘Yan Nijeriya Da Suka Maƙale A Isra’ila Da Iran
  • DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro?
  • Iran ta kai hari hedikwatar hukumar leƙen asirin Isra’ila
  • An garzaya da ’yan Isra’ila 154 asibiti bayan harin Iran
  • Tankokin Isra’ila sun kashe mutum 51 a wurin karbar abinci a Gaza