Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno
Published: 5th, April 2025 GMT
Wasu da ake zargin Boko Haram ne sun kai hari sansanin horas da ‘yan sanda na PMFTC da ke Limankara, a Gwoza, inda suka kashe Sufeton ’yan sanda guda ɗaya.
Sun kai harin da misalin ƙarfe 6 na safiyar ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025, yayin da jami’an tsaro suka fita sintiri a ƙafa.
Kakakin APC na Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu An ceto yara ’yan Taraba da aka yi safararsu zuwa KuduSufeto Andrawus Musa daga rundunar 6PMF da ke Maiduguri ya samu rauni a harin, inda maharan suka ƙwace bindigarsa ƙirar AK-47.
An kai shi asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), amma rai ya yi halinsa.
Rundunar dai na gudanar da bincike kan hari, tare da ƙoƙarin ganin ta kama waɗanda suka kai hari.
Ta kuma nemi jama’a da suke sanya ido kan duk wani abun zargi, tare da bai wa jami’an tsaro rahoto.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Ɗan Sanda hari
এছাড়াও পড়ুন:
Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri
Ruwan sama mai ƙarfi da ya sauka da safiyar ranar Laraba a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, ya haddasa ambaliya.
Ruwan wanda ya fara sauka tun da misalin ƙarfe 5 na Asuba, ya cika tituna da gidaje musamman a unguwannin Dala, Bulunkutu, titin Damboa, filin Polo, da Federal Low Cost.
Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasuAmbaliyar ta haifar da cikas a rayuwar jama’a, inda ruwa ya lalata dukiyoyi mutane masu tarin yawa.
Mutane da dama dun fice daga gidajensu domin neman mafaka, musamman waɗanda gidajensu ruwa ya mamaye.
Hakazalika, wasu tituna sun shafe sakamakon mamakon ruwan, lamarin da ya hana mutane fita ko komawa gidajensu da kuma yin ayyukansu na yau da kullum.
Wasu daga cikin mazauna garin sun ce ambaliyar ta tsananta ne saboda magudanan ruwa sun cika da shara irin su robobi, datti da tarkacen kayan gini.
Hakan ya hana ruwa tafiya yadda ya kamata.
Wani da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce mafi yawan magudanan ruwan Maiduguri ba sa aiki yadda ya kamata saboda sun toshe da shara.
Ya ƙara da cewa rashin kula da tsaftar muhalli ne ya haddasa irin wannan matsala.
A halin yanzu, akwai buƙatar gwamnati ta ƙara sanya ido, ta tsaurara dokokin muhalli, da kuma wayar da kan jama’a kan muhimmancin tsaftar gari.
Har ila yau, akwai buƙatar a gyara magudanan ruwa domin gujewa irin wannan ambaliya a nan gaba.
Masana sun gargaɗi jama’a cewa ana sa ran samum mamakon ruwan sama a makonni masu zuwa.
Amma an buƙaci jama’a su ɗauki matakan kariya da kuma haɗa kai da hukumomi domin shawo kan lamarin.