’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun kashe ɗan bindiga a Edo
Published: 19th, April 2025 GMT
Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Edo sun ceto ɗalibai 10 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Edo.
An kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigan, a yayin musayar wuta da ’yan sanda a lokacin aikin ceto, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi.
Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da ɗaliban ne a ranar 16 ga Afrilu, 2025, a kan hanyarsu ta zuwa Jami’ar Babcock don taron shekara-shekara na GYC Africa.
Kakakin rundunar, SP Kontongs Bello, wanda ya tabbatar da ceton, ya ce da samu rahoton sace daliban, kwamishinan ’yan sandan jihar, Funsho Adegboye, ya tura ’yan sanda na musamman tare da ’yan banga da maharba cikin daji domin ceto su da kuma kama waɗanda ake zargi.
Ana kashe ’yan Najeriya amma Tinubu ya fi damuwa da Zaɓen 2027 — SDP Makarantar Bare: Shekara 20 dalibai na karatu a matsanancin yanayiYa ce a lokacin aikin, an kashe ɗaya daga cikin ’yan garkuwan, yayin da sauran suka tsere da raunukan harsashi.
“Jami’an sun yi taka-tsan-tsan don guje wa asarar rayukan fararen hula saboda ’yan garkuwan sun yi amfani da waɗanda aka sace a matsayin garkuwa.”
A cewarsa, wani Sufeton ɗan sanda ya samu raunin harbin bindiga a lokacin aikin, kuma yana samun kulawa a asibiti a halin yanzu.
Ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin cafke ‘yan garkuwan da suka tsere.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Yan Sanda Ɗalibai Garkuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Cikin Wata 2 Ƴansanda Sun Damƙe Mutane 5,488, Sun Ceto 170 Da Aka Sace
IGP ya yabawa tawagar Interpol reshen Nijeriya bisa ceto Ghanawa 46 da aka yi safararsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp