Kotu ta yanke wa tsohon Shugaban Peru ɗaurin shekaru 15 kan laifin rashawa
Published: 16th, April 2025 GMT
An yanke wa tsohon shugabar ƙasar Peru, Ollanta Humala hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari.
Wata kotu a ƙasar ce ta yanke masa hukuncin bisa samunsa da laifin halatta kuɗin haram a badaƙalar cin hanci da katafaren kamfanin gine-gine na Brazil Odebrecht ke yi don samun kwangila.
Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Juma’a da LitininHaka kuma, ita ma mai ɗakinsa, Nadine Heredia, an yanke mata makamancin wannan hukuncin, duk da cewa ba ta halarci zaman kotun ba, saboda haka alƙalin ya bayar da umarnin kamo ta.
Ollanta Humala, mai shekaru 62, ya kasance tsohon shugaban ƙasar Peru na biyu da aka samu da laifi, lamarin da ya sa nan take aka kai shi wani gidan yari da ke gabashin Lima, inda ake tsare da tsoffin shugabannin kasar Peru Alejandro Toledo da Pedro Castillo.
Wannan hukuncin na zuwa ne sama da shekaru uku da fara shari’ar Humala wanda ya mulki ƙasar Peru daga 2011 zuwa 2016 —amma dai lauyoyinsa sun bayanna cewa za su ɗaukaka ƙara.
Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta ce Kamfanin Odebrecht ya ba da cin hanci dala miliyan 788 a cikin shekaru goma ga gwamnatocin yankin Latin Amurka domin samun kwangilar gine-gine.
Kamfanin ya bayyana cewar ya bayar da dala miliyan 29 na cin hanci ga Peru a tsakanin 2005 da 2014.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Cikakken jadawalin rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), ta kammala fitar da jadawalin Rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Za a gudanar da gasar ne a Amurka, Kanada da Mexico daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026.
Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan KwaraRabon jadawalin ya gudana ne a birnin Washington na ƙasar Amurka a ranar Juma’a, inda Ingila ta samu kanta a rukuni ɗaya Croatia.
Brazil za ta kara da Maroko, yayin da Amurka za ta kara da Australia.
Faransa za ta ɓarje gumi da Senegal, sannan Argentina za ta fafata da Austria.
Ga jerin yadda kowane rukuni na gasar Kofin Duniya na 2026 ya kasance:
Rukuni A: Mexico, Afirka ta Kudu, Koriya ta Kudu, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar.
Rukuni B: Kanada, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar, Qatar, Switzerland
Rukuni C: Brazil, Maroko, Haiti, Scotland
Rukuni D: Amurka, Paraguay, Australia, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar.
Rukuni E: Jamus, Curaçao, Ivory Coast, Ecuador.
Rukuni F: Netherlands, Japan, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar, Tunisia.
Rukuni G: Belgium, Masar, Iran, New Zealand.
Rukuni H: Spain, Cape Verde, Saudi Arabia, Uruguay
Rukuni I: Faransa, Senegal, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar, Norway
Rukuni J: Argentina, Aljeriya, Austria, Jordan.
Rukuni K: Portugal, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar, Uzbekistan, Colombia
Rukuni L: Ingila, Croatia, Ghana, Panama