Aminiya:
2025-07-30@23:17:04 GMT

Yadda masu safarar ɗan Adam ke yaudarar mutane ta intanet

Published: 10th, April 2025 GMT

Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda masu safarar mutane ke ƙara amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaudarar mutane da kuma yi musu cin zarafi, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana wadda ba ta da iyaka kuma mai saurin yaɗuwa wadda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na ƙasa karo na 27 kan safarar mutane da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, Babbar Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi SAN, ya ce dole ne Najeriya ta ɗauki mataki ta hanyar zamani daidai yadda matsalar take saurin faɗaɗa.

Ministan shari’an ya ce, “Safarar mutane ta koma ta intanet. Dole ne mu gaggauta ɗaukar mataki ko kuma mu fuskanci barazanar wuce gona da iri daga masu aikata laifuka waɗanda yanzu suke amfani da manhajoji na zamani wajen samun waɗanda za su yi safara, juya su, da kuma yi musu cin zarafi ta intanet.”

Fagbemi ya bayyana safarar mutane a matsayin sana’ar laifi ta uku mafi samun riba a duniya, bayan safarar miyagun ƙwayoyi da fatauci makamai.

NAJERIYA A YAU: Tasirin ’Yan Uwantaka Ga Rayuwar Al’umma ’Yan bindiga na neman N100m kafin sakin Faston da suka sace a Kaduna

Daga nan ya yi kira da a ƙara ƙarfin dokoki, hukumomi, da kuma hanyoyin fasahar zamani wajen magance matsalar.

Ya ce, “yaƙi da safarar mutane ba magana ce da ta tsaya kan bayar da alƙaluma ko wasu tsare-tsare ba, batu ne da ke buƙatar a yi a aikace domin tabbatar da adalci da ’yancin walwalar ɗan Adam da kuma kare martabar ƙasa.”

Don haka ya buƙaci kwamishinonin mata a duk jihohin Najeriya su yi ƙoƙarin damar da tsare-tsare da dokoki tare da kafa kwamitocin aiki da cikawa da kuma kasafi da za su taimaka kai-tsaye wajen yaƙar matsalar.

A nata ɓangaren, Babbar Daraktan Hukumar Hana Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP), Binta Adamu Bello, ta bayyana cewa hukumar ta riga ta fara ƙara ƙarfinta a fannin fasahar zamani.

Ta ce, “Yaƙinmu ya koma intanet, kuma martaninmu ma ya koma can,” inda ta bayyana cewa an horar da jami’an tattara bayanai sama da 160 a faɗin ƙasar, yayin da aka kuma ƙaddamar da sabbin manhajoji na zamani domin bibiyar batutuwan safarar ɗan Adam da kuma haɗin gwiwa.

Binta Bello ta ce hukumar ta ceto tare da gyara rayuwar sama da mutane 7,000 tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024, kuma an samu nasarar hukunta mutane 205 a cikin wannan lokacin.

Kazalika ta ƙaddamar da jami’an da kai guda 205 domin yaƙi da safarar mutane da kuma cin zarafi a faɗin Najeriya.

Haka kuma ta ƙaddamar da sabbin manhajojin zamani domin inganta tsarin tattara bayanai da kai rahoton safarar ɗan Adam, da haɗin gwiwar Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da Muggan Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC) da kuma gwamnatin ƙasar Switzerland.

Sauran sun haɗa da farfaɗo da shafin hukumar na kai rahoto da tattara bayanan cin zarafin jinsi, kafa cibiyar zamani a Katsina da kuma farfaɗo da cibiyarta ta zamani a Legas, da gudummawar hukumomin ƙasa da ƙasa irin su ƙungiyoyin ECOWAS, EU da kuma gwamnatin ƙasar Netherlands.

Wakilin UNODC a Najeriya, Cheikh Toure, ya yaba wa ƙoƙarin Najeriya wajen yaƙi da safarar ɗan Adam, inda ya jaddada cewa “manufa ba ta da wani amfani ba tare da aiki a matakin ƙasa ba.”

Ya buƙaci a ƙarfafa dokokin da kuma tsarin tattara bayanai da yanayin kula da waɗanda aka ceto, yana mai jaddada muhimmancin goyon bayan masu ruwa da tsaki a wannan gagarumin aiki.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Safarar ɗan Adam safarar ɗan Adam safarar mutane

এছাড়াও পড়ুন:

Kungiyar Gwamnonin Jihohi Ta Jajintawa Jihar Adamawa Bisa Ambaliyar Ruwa A Yola

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana alhinin sa kan rahotannin ambaliya mai tsanani da ta faru a Yola, Jihar Adamawa, wacce ta yi sanadiyar  mutuwar mutane, da asarar dukiyoyi da kuma raba dimbin jama’a da muhallansu.

A cikin wata sanarwa, Gwamna AbdulRazaq ya ce kungiyar NGF na jajantawa gwamnatin Jihar Adamawa ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yayin da suke kokarin tara kayan agaji da daukar matakan rage illar wannan iftila’in.

Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar ta yaba da matakin gaggawa da ‘yan sanda da kuma dakarun sojin Najeriya suka dauka na tura rundunonin ruwa, bisa gayyatar gwamnatin jihar, domin taimaka wa al’ummar da abin ya shafa a wannan lokaci na halin kaka-ni-ka-yi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa kungiyar za ta bayar da nata tallafin domin taimakawa al’ummar jihar bisa halin da suka tsinci kansu a ciki.

 

Ali Muhammad Rabi’u

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Tallafin Miliyoyin Naira Ga Ƴan NURTW da Mahauta a Jigawa
  • Ma’aikatar Bunƙasa Harkar Kiwo Za Ta Taimaka Wajen Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya — Jega
  • Binciken CGTN: Za A Ci Gaba Da Nuna Kyakkyawan Fata Ga Bunkasar Sin Nan Da Shekaru 5
  • Shugabannin Hukumomin Watsa Labarai Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari
  • Kwamandan NDA Ya Bukaci Dalibai Su Dage da Karatu a Taron FGC Malali
  • An Kaddamar da Makon MNCH na 2025, Ya Rarraba Fakitin Bayarwa 6,000, Kayan C/S 500
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Dama Da Matan Arewa A Fannin Kimiyya
  • Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci
  • Kungiyar Gwamnonin Jihohi Ta Jajintawa Jihar Adamawa Bisa Ambaliyar Ruwa A Yola
  • NAJERIYA A YAU: Matakan Da Muke Dauka Don Karfafawa ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwar Kada Kuri’a —INEC