De Bruyne zai yi bankwana da Manchester City a ƙarshen kaka
Published: 6th, April 2025 GMT
Ɗan wasan ƙasar Belgium, Kevin De Bruyne, ya sanar da cewa zai yi bankwana da ƙungiyar Manchester City ta Ingila a ƙarshen kakar bana.
Fitaccen ɗan wasan tsakiyar mai shekaru 33 ya sanar da hakan ne cikin wata saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X.
Tsohon Gwamnan Oyo Olunloyo ya riga mu gidan gaskiya Finafinan Kannywood da suke tashe da kuma manyan marubutansuDe Bruyne ɗan asalin ƙasar Belgium ya tabbatar da cewa waɗannan su ne watanninsa na ƙarshe a matsayin ɗan wasan Manchester City.
De Bruyne ya je Manchester City a shekarar 2015 daga Wolfsburg, inda ya lashe duka manyan gasar ƙwallon ƙafa tare da ƙungiyar ta City, ciki har da gasar Firimiya ta Ingila da Gasar Zakarun Turai.
Kwantaraginsa a City zai ƙare a ƙarshen Yunin bana, amma har yanzu ba a tabbatar ko zai haska ba a wasannin da City za ta buga daga 14 ga Yuni zuwa 13 ga Yuli.
“Kowane labari yana zuwa ƙarshe, amma lallai wannan ya kasance babi mafi kyau a gare ni.
“Mu mori waɗannan lokutan tare har zuwa ƙarshe,” a cewarsa.
De Bruyne ya buga wasanni 280 a gasar Firimiya, kuma ya ci ƙwallaye 70 da tallafin ƙwallaye 118.
Hakan ya sa shi yake biye da Ryan Giggs tsohon ɗan wasan Manchester United, wanda yake riƙe da kambun wanda ya fi ba da tallafin cin ƙwallo a tarihin Firimiya, da ƙwallaye 162.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF
Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya sabunta hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa tun daga shekarar nan ta 2025 har zuwa 2026.
IMF ya bayyana sabon hasashen a watan Yulin da muke ciki wanda a ciki ya yi ƙiyasin samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya.
Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasaAsusun ya yi hasashen samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya da kashi 3.4 a 2025, ƙari a kan hasashen kashi 3.0 da ya yi a watan Afrilu.
Haka kuma, IMF ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai samun ƙarin bunƙasa da kashi 3.2 a 2026, saɓanin hasashen kashi 2.7 da ya yi a watan na Afrilu.
Sai dai duk da wannan, wani rahoto IMF ya fitar a watan Yunin bana, ya ce Nijeriya na mataki na 12 a cikin jerin kasashe mafiya talauci a fadin duniya.
IMF ya ce talauci na kara karuwa a cikin kasar da ta dauki shekaru biyu tana kokarin sauya fuskar tattalin arziki, amma kuma take dada fadawa cikin duhu na tattalin arziki.
A cikin kasashe 189 da aka gudanar da bincike a cikinsu, Nijeriyar na a mataki na 178, inda ta zarta kasashe irin su Yemen da Sudan ta Kudu da Kwango da Nijar da Sudan, wadanda kusan dukkaninsu ke fama da rigingimu a halin yanzu.