Aminiya:
2025-08-01@01:55:04 GMT

Kisan Janar Alƙali: Kotu ta ɗage shari’a zuwa 28 ga Mayu

Published: 8th, April 2025 GMT

Kotu ta dage shari’ar kisan Manjo Janar Idris Alkali mai ritaya zuwa ranakun 28 da 29 ga watan Mayu, 2025, domin waɗanda ake tuhuma su fara gabatar da shaidunsu.

Babbar kotu da ke zamanta a Jos, Jihar Filato, ta ɗage shari’ar ne biyo bayan bayan ɓangaren masu ƙara su. gabatar da ga Manjo Janar U. I. Mohammed mai ritaya  game da kisan.

Janar Alkali, wanda ya kasance tsohon shugaban gudanarwa a Hedikwatar Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, ya ɓace ne makwanni kaɗan bayan ya yi ritaya daga aikin soja, a lokacin da yake hanyar tafiya Bauchi daga Abuja. Mamacin ne yake tuƙa kansa a lokacin da yake tafiyar inda ya biya ta Jihar Filato.

A lokacin da ya ba ce a shekarar 2018, Janar Mohammed shi ne Kwamandan Sansanin Runduna ta 3 kuma ya jagoranci aikin neman da ceto jami’in da ya ɓata.

Mahara sun yi garkuwa da fiye da mutum 50 a Katsina NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu

Shi ne ya jagoranci aikin da ya kai ga gano motar Janar Alkali a wani rami mai zurfi a yankin Du, daga baya kuma aka gano gawarsa a wata tsohuwar rijiya a kauyen Guchwet da ke gundumar Shen a Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

A zaman kotun na ranar Litinin, lauyan masu kare kai ya yi wa Janar Mohammed tambayoyi tare da neman ƙarin haske kan bayanan da ya bayar a baya da kuma shaidarsa dangane da mutuwar Janar Alkali.

Tambayoyin, wadanda suka dauki kimanin awanni biyu, sun mayar da hankali ne kan bayanan da ya bayar na farko da kuma waɗanda suka biyo baya game da lamarin.

Bayan zaman kotun, Mai Shari’a Arum Ashom ya sallami shaidan kuma ya tsayar da ranar sauraron karar na gaba.

Lauyan masu gabatar da ƙara, Simon Mom, wanda ya wakilci Babban Lauyan Jihar Filato, bai nuna adawa da dage shari’ar ba.

Daga bisani, alƙali ya dage shari’ar zuwa ranakun 28 da 29 ga watan Mayu domin masu kare kai su fara gabatar da nasu bayanan kare kansu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Shari a Jihar Filato

এছাড়াও পড়ুন:

Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata 

Wani mutum ya rasu yayin da yake ƙoƙarin raba wani mutum da matarsa da fada a yankin Babban Birnin Tarayya.

Da farko mutumin ya faɗi ne a sume kafin daga bisani rai ya yi halinsa a yankin Dogon-Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji.

Wani ganau, Barnabas Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da yamma ne ma’auratan, waɗanda makwabta ne ga mamacin, suka fara faɗa ne bayan wata rashin fahimta, shi kuma Ayuba, bayan jin hayaniyar, ya fito daga ɗakinsa don shiga tsakani.

A cewarsa, mamacin ya dawo ne daga gonarsa kuma yana shirin yin wanka lokacin da ya ji maƙwabcinsa yana dukan matarsa.

Ya ce, Ayuba nan take ya ajiye soso da gugar ruwansa ya ruga don shiga tsakani amma ya faɗi sumamme a yayin.

Ayuba, wanda aka yi imanin yana cikin koshin lafiya kafin faruwar lamarin, an garzaya da shi asibiti a garin Gawu, inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwarsa.

Sarkin yankin, bayan samun labarin lamarin, ya sanar da ’yan banga tare da ba da umarnin kama ma’auratan, waɗanda daga baya aka mika su ga jami’an tsaro a Gawu.

Ibrahim, daya daga cikin ’yan bangan, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa, “Mun fahimci cewa ƙaramar rashin fahimta ce kawai ta kai ga faɗan tsakanin makwabcin mamacin da matarsa.”

Ya ƙara da cewa an kai gawar mamacin kauyensa na Paiko a Jihar Neja don binnewa.

’Yan sanda a yankin Gawu sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce har yanzu ana ci gaba da bincike.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato
  • INEC Ta Gudanar da Taron Masu Ruwa da Tsaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi na Babura/Garki
  • Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti Allah
  • Dalilan Da Suka Sa Canada Ta Goyi Bayan Kafa Kasar Falasɗinu
  • Tinubu ya karɓi baƙuncin Abdulmumin Jibrin Kofa
  • Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya
  • Gwamna Namadi Ya Naɗa Shugabannin Hukumar Hisbah Ta Jihar Jigawa
  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
  • Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba
  • Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata