’Yan bindiga sun harbi alkali da ɗansa, sun sace mutane 13 a Katsina
Published: 11th, April 2025 GMT
’Yan bindiga sun kai hari garin Mahuta da ke Ƙaramar Hukumar Kafur a Jihar Katsina, inda suka harbi wani alkali, Rabiu Mahuta, a hannu da kuma dansa.
A lokacin harin na daren Talata, maharan sun raunata mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane 13, ciki har da matar alƙalin da kuma biyar daga cikin ’ya’ansa.
Wani mazaunin garin da ya zanta ya ce ’yan bindigar sun isa wurin ne da misalin karfe 11:30 na dare, kuma kai tsaye suka nufi gidan alkalin, inda suka kwashe kusan awa guda suna ƙoƙarin karya ƙofar gidan.
Cutar Kwastomomi: NERC ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar N628m ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar kwalekwale a Kogin NejaDuk da kiran da alƙalin ya yi wa DPO na yankin domin neman taimako, jami’an tsaro ba su iso a kan lokaci ba.
Ya ce, “Da suka samu nasarar shiga gidan, nan take sun harbe shi a hannu, sai ya faɗi a ƙasa. An kuma raunata ɗansa da raunin harbi a goshinsa.”
Wani makwabcinsa, wanda kuma mamba ne a hukumar tsaron al’umma ta jihar da ya yi ƙoƙarin kai ɗauki a lokacin harin, shi ma an harbe shi kuma yana karɓar magani a wani asibiti a Katsina a halin yanzu.
Maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mutane biyar a gidan wani mai suna Shehu Maishayi, tare da Malam Sufi Nahi da kuma matar Malam Abdurrazak, wanda ke zaune a wajen garin Mahuta.
Majiyoyi sun ce sojoji sun iso ne kawai bayan da ’yan bindigar suka tsere daga wurin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga garkuwa da mutane
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
A yayin samamen, kakakin ‘yansandan Neja ya ce an kama mutane shida a wurin da ake hakar ma’adinan yayin da wasu kuma suka tsere.
Abiodun ya bayyana sunayen wadanda ake cafken da Aliyu Rabiu, Samaila Ibrahim, Sadiku Auwal, Ibrahim Babangida, Musa Adamu da Sani Hassan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp