2025-11-03@13:38:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2601
«jiragen yaki»:
Bayanai daga Falasdinu na cewa a kalla Falasdinawa 97 ne sojojin Isra’ila suka kashe tare da jikkata wasu 230 tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta fara aiki a Gaza a ranar 10 ga watan Oktoba. A cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar, ya ce ‘yan mamayar sun...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanyar Babban Sara zuwa Malam Bako zuwa Shabaru zuwa Kirgi zuwa Albasu, mai tsawon kilomita 28.2, a Karamar Hukumar Sule Tankarkar,wanda kudinsa ya kakaNaira Biliyan 4.47, a ci gaba da shirin Gwamnati da Jama’a. Aikin hanyar zai hada fiye da kauyuka 60 tare da...
NLC ta kuma buƙaci gwamnati ta bi shawarar UNESCO wacce ta ke cewa ya kamata a ware aƙalla kashi 25 cikin 100 na kasafin kuɗi na kowace shekara ga ilimi. Ajaero, ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin makonni huɗu, NLC za ta haɗa dukkanin ma’aikata na ƙasa don gudanar da...
Wata kotun majistare da ke Kano ta umarci Hukumar Hisbah ta jihar da ta shirya ɗaura aure tsakanin wasu fitattun ’yan TikTok guda biyu — Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda — cikin kwanaki 60. Kotun ta bayar da wannan umarnin ne bayan yaɗuwar bidiyon Mai Wushirwa da ’Yar Guda a kafafen sada zumunta,...
Najeriya: ‘Yansanda A Abuja Sun Yi Amsani Da Hayakin Mai Sa Hawaye Kan Masu Neman A Saki Nnamdi Kanu
A jiya litinin ce masu goyon bayan Nnamdi Kanu shugaban kungiyar neman kafa kasar Biafara (IPOP) daga tarayyar Najeriya, wanda ake tsare da shugaban kungiyar tare da tuhumar ayyukan ta’addan sun fito zanga-zanga suka kuma tushe wata babban titi a Abuja. ‘Yansanda sun jefa masu hayakin teargas don tarwatse su a jiya litinin. Kamfanin dillancin...
Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati ta samu nasarar tara dukiyar da ta haura naira biliyan 500 a tsawon shekaru biyu na gwamnatinsu. Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana haka ne a yayin wani taron bita da ƙara wa...
Fitaccen jarumin barkwancin finafinan Indiyan nan Asrani ra rasu. Asrani, wanda asalin sunansa shi ne Govardhan Asrani, ya rasu yana mai shekaru 84, kuma ya shafe sama da shekara 50 yana fitowa a finafinan Indiya, inda ya fito a finafinai sama da 350. Dan wasan finafinan, ya shahara wajen taka rawar barkwanci da kuma ƙaramin...
Wakilin Amurka Na Musamman A Siriya Ya Matsa Don Ganin Kasashen Saudiyya Da Lebanon Da Kuma Siriya Sun Kulla Alaka Da Isra’ila
Wakilin Amurka na Musamman a kasar Siriya ya matsa kaimi domin ganin kasashen Saudiyya da Lebanon da kuma Siriya sun kulla alakar jakadanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Wakilin Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack, ya gabatar da manufofinsa na sake fasalin yankin Gabas taTsakiya a siyasance bayan kawo karshen yakin Gaza. A cikin dogon...
Hukumar gudanarwar Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars ta dakatar da Babban Kocinta Ahmed Garba Yaro Yaro da bai ba da shawara ga Kocin, Ogenyi Evans, nan take. Ta kuma nada tsohon kyaftin kuma Mataimakin Koci, Gambo Muhammad nan take, ya jagoranci lamuran fasaha na ƙungiyar. Mai horar da masu tsaron raga, Suleiman Shuaibu, zai...
Don haka, an nada “tsohon kaftin din kungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, tare da mai horar da masu tsaron gida, Suleiman Shuaibu, su maye gurbin wadanda aka sallama na dan wucin gadi. Bugu da kari, Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai taimakawa wadanda aka nada na dan wucin gadin”. LEADERSHIP ta...
Dakarun kare juyin musulunc na kasar iran ta bayyana cewa tana da cikakken shiri na kafa fadada dabarun yin hadin guiwa da dakarun karejuyin musulunci na kasar yamen wajen kalubalnatar kasashe ma’abota girman ai da kuma yan sahyuniya. A cikin sakon da kwamandan dakarun kare juyin musulunci na iran ya fitar a jiya lahadi mojor...
Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi ya bayyana kwarin gwiwar cewa, za a iya warware takkadama kan shirin Iran na makamashin nukiliya ne ta hanyar diflomasiyya kadai. Grossi ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Neue Zeitung ta kasar Switzerland a jiya Lahadi. Shugaban hukumar ta IAEA ya...
An saki ɗan jarida, Ibrahim Ɗan’uwa Rano, bayan da ƴansanda suka tsare shi a shalƙwatar Rundunar Ƴansanda ta Zone 1 Kano bisa zargin batanci ga wani mutum. Sakin nasa ya biyo bayan suka da matsin lamba daga ƙungiyoyin fararen hula irinsu Cibiyar Fasahar Bayanai da Ci Gaban Jama’a (CITAD), da Amnesty International, da sauran ƙungiyoyin...
Ƴansandan sun kuma yi kira ga ƴan jarida da su tabbatar da daidaito a rahotanninsu, tare da tuntuɓar sashin hulɗa da jama’a na yankin kafin yaɗa labaran da ke da sarƙakiya. AIG Garba ya gargaɗi ƴan jarida da su guji tsoma baki a cikin binciken da ke gudana, yana mai cewa “a bar doka ta...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana talauci a matsayin babban abokin gabar ɗan Adam. Ya ce ƙaruwar talauci a Najeriya na ci gaba da jawo rashin lafiya, jahilci, rashin tsaro, da rashin fata a tsakanin jama’a. ’Yan sanda sun tsare ɗan jarida kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano Mahukunta sun kai samame...
Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar rage kaso 30 cikin 100 na sinadarin gishiri (sodium) a kowane nau’in abincin ɗan fakiti da ake sayarwa a kantuna da wuraren kasuwanci a kasar. Aminiya ta ruwaito cewa gwamnatin za ta soma aiwatar da wannan shirin ne a bana domin daƙile cutar hawan jini da dangoginta a ƙasar. Mahukunta...
Yanzu kuma za a ci gaba da tattaunawa kan yadda za a aiwatar da sauran sharuddan da ke ke kunshe a yarjejeniyar. Masu sanya ido na ganin cewa aikin sake ginan yankin Gaza wanda aka rushe kusan daukacinsa a yakin da aka yi na shekara biyu, zai zama babban kalubale. Wannan ce ranar...
Ofishin Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a ranar Asabar cewa “Mashigar Rafah a Gaza za ta kasance a rufe har sai abin da hali ya yi a nan gaba.” Ofishin Netanyahu ya kara da cewa, bude mashigar ya dogara ne bisa ga yadda Hamas ta aiwatar da tsarin yarjjeniyar da aka cimmawa wajen...
A wani jawabin da aka yada ta kafar sadarwar zamani ta shafin Facebook jiya, ma’aikatar ta kara da cewa tun lokacin da shi Gwamnan ya dare kan Kujerar mulkin Jihar, mulkin gwamna Inuwa ya kafa dokar ta baci kan lamarin daya shafi ilimi, inda ya bullo da tsare tsare da zuba jari da zummar bunkasa...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kuduri mai lamba 2231 ya ƙare aiki a yau A cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ministan harkokin wajen kasar Iran ya tabbatar da cewa a karshe kuduri mai lamba 2231 ya kare...
Shi ma a nasa jawabin yayin gudanar da taron, shugaban kwamitin Alhaji Abdullahi Abdulmalik Digi, ya ce, a shekaru hudu da ya yi yana jagorancin kwamitin sun yi abin da yakamata su yi, inda ya ce, a Azumin bara an dauki yara marayu 2000 da aka raba musu abinci da suka hada da buhunan shinkafa...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa a Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya yi iƙirari cewa ministoci da manyan hafsoshin sojin ƙasar sun taya shi murnar bayan bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala. Issa Tchiroma Bakary ya bayyana cewa ministoci da manyan jami’an tsaron da ministocin sun kira...
A yayin da Najeriya ke karkata zuwa amfani da kayan tsaro na zamani na cikin gida domin ƙarfafa gwiwar jami’an tsaronta a fagen fama, wani ɗan Jihar Katsina ya fara ƙera motar yaƙi nau’in Track Armored Personnel Carrier (TAPC). Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewa da suka fi fama da hare-haren ’yan bindiga,...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda bayani kan cewa daga yau Asabar 18 ga watan Octoban shekara ta 2025, kudurin kwamitin tsaro na MDD wanda aka samar don goyon bayan aiwatar da yarjeniyar Nukliyar kasar Iran wacce aka fi sani da JCPOA ya kawo karshe. Don haka daga yau shirin Nukliyar kasar Iran ta...
Kauyukan kasar Iran guda uku, Soheili a kan tsibirin Qeshm, da Kandelous a lardin Mazandaran, da kuma Shafiabad a lardin Kerman na kasar Iran sun shiga cikin zababbun kauyuka a duniya na yawon shekatawa saboda kyauwunsu da kuma samar da dukkan abin kyautata rayuwa a cikinsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto...
Tashar talabijin ta CNN ta bayar da rahoton cewa, Janar Alvin Holsey, kwamandan rundunar sojin Amurka ta Kudu, ya yanke shawarar yin murabus nan da watan Disamba, saboda takun-saka tsakaninsa da sakataren tsaron Pete Hegseth, kan rashin jituwar da aka samu game da batun ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean. Rahoton ya bayyana cewa, a...
Tawagar sun gabatar da kansu ga babban sakataren hukumar gudanarwar ci gaban Jihar Katsina, Dakta Mustapha Shehu. Tawagar sun ce ziyarar wani bangare ne na shirye-shiryen gudanar da aikace-aikace domin inganta zaman lafiya da kuma sanar da tallafin jin kai ga ‘yan gudun hijira. Gwamnan Katsina ya yaba wa Bankin Duniya da ya yi...
Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya Sun Ce: Sake Dawo Da Takunkumin Da Aka Kakaba Kan Iran Baya Kan Doka
Abokan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa: Sake dawo da takunkumi bayan karewarsa baya da wani tushe na doka ko tsari Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa game da cikar kudiri mai lamba 2231 kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran a ranar 18 ga watan Oktoba, inda ta...
Majalisar Zartarwar Jihar Jigawa ta amince da wasu manyan kwangiloli da kudinsu ya haura Naira Biliyan 6, domin karfafa bangarorin noma, ilimi da ci gaban tattalin arziki a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar da aka gudanar a fadar gwamnatin Dutse, kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da...
A taron majalsar zartarwar, Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa zabinsa na Amupitan ya yi ta’allaka ne a kan rashin nuna son kai na siyasa, gaskiya da kyakkyawan tarihinsa. Mambobin majalisar, ciki har da shugabanni na yanzu da na baya, sun amince da nadin, suna bayyana Farfesa Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya....
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Ismail Baqaei yayi maraba da dakatar da bude wuta da aka yi tsakanin kasashen Pakistan da Afghanistan, kuma yayi kira ga kasashen biyu da su warware sabanin dake tsakanin ta hanyar tattaunawa da kuma diplomasiya. Iran ta dade tana ba da shawarwarin magance matsalolin tsaro a yammacin Asiya da...
Rahotanni sun bayyana cewa shakih Naim Qassim babban sakatare janar din hizbullah na kasar labanon ya bayyana a jiya Alhamis a gaban mambobin kungiyar Kashafat Al-Mahadi cewa Amerika da Isra’ila ba za su iya yin galaba akan hizbullah ba, Babban hadafin kafa wannan kungiyar shi ne kokarin wayar da kan yara matasa yan shekara 6...
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin...
Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da KuraAfuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da Kura
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin...
Kasar Saudiyya ta rage yawan guraben kujerun aikin hajjin da take ware wa Najeriya daga 95,000 zuwa 66,910 daga shekarar 2026. Aminiya ta ruwaito cewa a baya Najeriya ta shafe tsawon shekaru uku tana samun guraben na 95,000 a yayin Aikin Hajjin. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a Zamfara...
A yammacin jiya Alhamis ne sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda ya isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ga shugaban na Rasha. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da...
Hakazalika, ta bai wa mata 30 masu kananan sana’o’i tallafin buhun gawayi, da kilo 10 na Shinkafa da litar man girki. Bugu da kari, ga kungiyoyi shida na mata manoma, kowacce za ta karɓi fanfunan feshi, famfun ruwa, da kuma maganin feshin ciyawa. Hajiya Shema’u, ta yaba da karuwar adadin mata a harkar...
Sashen kashe radadi domin gudanar da aikin tiyata ga marasa lafia na asibitin gwamnatin tarayya FMC da ke garin Birnin Kudu a jihar Jigawa ya gudanar da bikin ranar bada maganin radadi ta duniya ta bana. Kungiyar ma’aikatan bada maganin kashe radadi dan yin aikin tiyata ta Duniya ce ta kebe ranar 16 ga wata...
Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa a koda yaushe makiya suna neman haifar da rikici tsakanin kasashen musulmi domin raunana su, yana mai nuni da barkewar tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan. Mr. Pezeshkian ya bayyana haka ne a yayin wani taro inda ya fayyace matsayin kasar Iran dangane da takun saka...
Kungiyar Euro-Med ta bukaci bangarori su shiga Gaza domin tattara bayanai kan kisan kiyashin Isra’ila
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-med mai hedkwata a Geneva ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da shiga Gaza ba tare da ‘yan jarida, masu bincike, da masana harkokin shari’a don tattara bayanan kisan kiyashin da Isra’ila a Gaza da kuma hukunta wadanda suka aikata laifin. A cikin wata sanarwa da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a jawabin da ya gabatar a taron tsakiyar shekara ta ministocin harkokin wajen kungiyar yan ba ruwammu wato NAM a birnin Kampala babban birnin kasar Uganda a jiya Laraba, ya jadda bukatar hadin kai da goyon baya a tsakanin kasashen kungiyar, wajen fuskantar rashin mutunta dokokin kasa...
Baba-Ahmed, ya bayyana cewa, abin da danginsa suka fuskanta a hannun masu garkuwa da mutane a bara ya tabbatar masa da cewa rashin tsaro a yanzu yana da nasaba da siyasa. Ya kuma danganta kisan jama’ar da aka yi wa mabiya Shi’a a Zariya a shekarar 2015 da wani shiri na gwamnati don murƙushe masu...
Shugaban Majalisar Dabarun Kula da harkokin waje kuma mamba a Majalisar fayyace manufofin kasar Iran ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta tattauna amma ta kin juya akalarta Shugaban majalisar dabarun kula da harkokin waje kuma mamba a majalisar fayyace manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Kamal Kharrazi, ya jaddada cewa: Iran a shirye take...
Ministan harkokin wajen kasar Iran da takwaransa na Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falasdinu na bukatar kawo karshen mamayar da ake yi Ministocin harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falastinu na bukatar kawo karshen mamaya da kuma tabbatar da hakkin al’ummar Falastinu na cin gashin kansu. Wannan...
Kakakin Majalisar Nasarawa ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa al’ummar Nindama, in ji Govt. ya dauki matakan da suka dace. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Dr. Danladi Jatau ya jajantawa al’umma da iyalan harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a kauyen Nindama...
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wani kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa hukuncin daurin shekaru takwas ba tare da zaɓin tara ba, kan laifin luwadi da ɗan wasan kulob dinsa mai karancin shekaru. Kotun dai wacce ke ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dahuru Muhammad a ranar Laraba ta sami kocin mai suna Hayatu Muhammad da...
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, ta sauka zuwa kashi 18.02 a watan Satumba, 2025, idan aka kwatanta da kashi 20.12 da aka samu a watan Agusta. A cewar rahoton hukumar, hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya a watan Satumba ta kasance kashi 0.72, yayin da farashin kayan abinci...
Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin kasar Iran sun samar da sabbin hanyoyin fuskantar makiya wadanda ta daukosu daga abinda ya faru a yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka duka dorawa kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Khatami yana fadar haka a...
Shugaban Kasar Columbia Ya Soki Donald Trump Akan Bai Wa Isra’ila Makamai Shugaban na kasar Columbia Gustavo Petro ya ce, Bugun kirjin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na bai wa “Isra’ila” makamai tare da cewa ta yi amfani da su da kyau, ba wani abu ne da ya cancanci a yi...
Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin aikewa da Ogugua Christopher zuwa gidan gayarn hali bisa zarginsa da hannu a sata da kuma safarar yara daga jihar Kano zuwa kudancin Najeriya. Ana dai zargin mutumin ne da mallakar wani gidan marayu a jihar Delta ba bisa ka’ida ba, sannan yana amfani...