2025-06-05@17:37:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1100

«Kasa Kungiyar»:

    Shugaban Wanda Alhaji Ahmed Aliyu Zarma ya wakilta ya kara da cewa, wannan cibiya ba itace ta farko ba da shugaban ya fara ginawa ba, a cewarsa ya gina irinsu a sassa daban-daban a fadin kasar nan. Yana Mai Cewa, baya ga cibiyoyin koyar da addinin musulunci ya samar da makarantu a majami’un addnin kirista...
    Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ƙoƙarinsa na yin garambawul a fannin ilimi a jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya biya duk wani bashi a bangaren ilimi da gwamnatocin baya a jihar suka ƙi biya “Rashin biyan kuɗin jarabawar WAEC da NECO ya haifar da koma-baya ga makarantun gwamnati a faɗin jihar Zamfara, wanda...
    Kungiyar gwagwarmayar Hamas ta Falasdinu ta yi kakkausar suka kan kalaman baya-bayan nan da dan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Republican Randy Fine ya yi, wanda ya yi kira da a kai wa zirin Gaza hari da makamin Nukiliya. Kungiyar Hamas, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana kalaman dan ‘majalisar a matsayin...
    Ofishin yada labaran Gaza ya bayar da rahoton mutuwar Falastinawa 299 da suka fada cikin mawuyacin hali na rashin abinci mai gina jiki, da karancin kayan masarufi da magunguna. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar talabijin ta Aljazeera na cewa, taimakon jin kai na cikin hadarin rubewa saboda haramcin da gwamnatin sahyoniyawan ta...
    A karon farko an fara tattaunawa tsakanin kungiyar ECOWAS da ta AES ta kawancen kasashen nan guda uku na Sahel da suka balle. Shugaban hukumar ECOWAS, dan kasar Gambia Omar Touray, ya tattauna a birnin Bamako da ministocin harkokin waje na kasashe mambobin kungiyar AES wato Mali, Burkina da kuma Nijar. Wannan dai shi ne...
    Kafin wasan ƙarshe na bana da za su kara da Crystal Palace a ranar Lahadi, Salah ya riga ya ci ƙwallaye 28 a Firimiyar bana kuma ya taimaka a ci wasu 18. Kusan taimako biyu kawai suka rage masa ya kai tarihin taimako 20 da Thierry Henry da Kevin de Bruyne suka kafa. A wannan...
    Na yi imanin za mu iya hakan Kuma muna fasahar da za mu iya aiwatar da hakan? Idan aka yi la’akari da albarkatun noma da Nijeriya ke da shi, musamman a cikin amfanin gona irin su rogo da rake, da kuma ta hanyar saka hannun jari kan ababen more rayuwa da fasahar kere-kere, akwai gagarumin...
    Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka JohnKerry ya bayyana cewa HKI bata isa ta wargaza cibiyoyin makamacin nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dilancin labaran IP na klasar  Iran ya nakalto Kerry na fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa babban al-amari a cikin duk wani kokari na kauda cibiyoyin Nukliyar kasar Iran...
    Alkaluman da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta samar a kwanakin baya sun shaida cewa, tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da tsarin samar da rangwamen gwamnati ta musayar sabbin motoci da tsofaffi, yawan bukatun da aka mika na yin musayar tuni ya wuce miliyan 10, matakin da ya yi matukar rage kudin...
    “Haƙiƙa muna alfahari da Dr. Sani Dauda Ibrahim da wannan ajin naku, musanman cewa akan ku na fara koyarwa a jami’a, kuma haɗin kan ‘yan wannan ajin ya zama na daban a cikin ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai, musanman saboda ayyuka da kuka gabatar na ci gaban ilimi a jami’ar Bayero da yadda kuke damuwar da al’amuran...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta kama wata yarinya ’yar shekara 15 bisa zargin jefa gawar wani jariri a cikin wani banɗaki da ke sansanin ’yan gudun hijira a Monguno. A cewar wata majiyar ’yan sanda a ranar 22 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 9:15 na safe, an bayar da rahoton cewa, a safiyar...
    Kungiyar ta’addanci ta Da’ish ko ISIS ta zargi shugaban gwamantin kasar Siriya al-Julani da yin sujjada a kofar shiga wajen kafirai Kungiyar ta’addanci ta Da’ish ko ISIS ta bayyana shugaban sabuwar gwamnatin Siriya Abu Muhammad al-Julani a matsayin azzalumi wanda ya sayar da addininsa tare da yin sujjada a kofar shiga wajen kafirai. Ta yi...
    A gefe guda kuma, al’ummar yankin ne suka sadaukar da gonakinsu, domin amfanin jama’a wajen gina sansanin FCDA. An cimma yarjejeniya cewa; a karshen amfani da filin, za a mayar da shi ga al’umma. Malam Ladan, ya dage har aka tabbatar da wannan yarjejeniya a rubuce kuma Marigayi Abubakar Koko, Sakataren FCDA, ya sa hannu...
    ‘Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 dake cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin dake cikin da’irarta, sun kammala jerin ayyukansu na farko a wajen tashar a yau Alhamis. Hukumar kula da ayyukan sama jannati ta kasar Sin (CMSA) ta ce, ‘yan sama jannatin da suka hada da Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang...
    Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya amince da wannan batun na takwaransa cikin gaggawa.   “Na tsaya a madadin Sanatoci 109 da ‘yan Majalisar Wakilai 360 don amincewa da wannan matakin na Akpabio,” in ji Abbas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    Nahiyar Afirkan a karkashin tarayyar Afirka ta kafa cibiyar dake kula da sararin samaniya domin tattara bayanai, wacce ke da matsuguni a birnin “alkahira’ na Masar. Sabuwar cibiyar dai ta fara aiki ne a watan da ya gabata,kuma za ta rika musayar bayanan da take tattarawa da cibiyoyin kasashen da suke a fadin nahiyar. Haka...
    Jaridar ‘yan sahayoniya ta “Ma’ariv’ ta buga labarin da yake cewa; Isra’ila tana fuskantar matsalar diplomasiyya saboda ci gaba da yakin Gaza. Jaridar ta kuma ce; A halin yanzu “Isra’ila” tana fuskantar abinda ta kira “Tsunami Na Diplomasiyya” saboda yakin da take ci gaba da yi a Gaza. Haka nan kuma jaridar ta soki gwamnatin...
    “Hukumar ta amince da ƙirƙiro sashen AI a ƙarƙashin ɓangaren fasahar sadarwa na hukumar domin cin ribar AI da fasahar da take ɗauke da ita da kuma magance ɓarnar da fasahar ka iya kawowa a lokutan zaɓe” a cewar sanarwar   Wannan matakin da INEC ta ɗauka dai ya biyo bayan tarurruka da dama da...
      Gwamnatin Tarayya ta fitar da cikakken rahoto na tsakiyar zangon mulki da ke bayyana muhimman nasarorin da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta cimma daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2025. Rahoton, wanda Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsare-Tsare da Daidaita Ayyuka ya gabatar, ya bayyana ci gaba mai ma’ana da aka samu...
    An gudanar da Jana’izar Malam Maikudi Umar (Cashman) Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a garin Zariya, Jihar Kaduna. Marigayin dan shekaru 62, jarumi ne, mai shirya finafinai kuma ma darakta da ke gudanar da aikace aikacen sa a masana’antar Kannywood da Nollywood. Dan uwan mamacin, Abdul Azeez Muazu, Talban Tudun Jukun yace...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta gaggawar kulla alaka da kasar Siriya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: A halin yanzu babu wata alaka tsakanin Iran da Siriya, kuma Iran ba ta gaggawar kulla alakar. Ya ce: “Lokacin da gwamnatin Siriya ta ga irin yadda...
    Iran ta sanar da lokaci da kuma wurin da za a yi sabon shawarwari tsakanin Iran da Amurka Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa: A gobe Juma’a ne za a gudanar da zagaye na biyar na shawarwari tsakanin Iran da Amurka a birnin Roma. A lokacin da ya isa birnin Shiraz...
    Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da Kamfanin Bayar da Lamuni a Najeriya (CREDICORP), wani muhimmin shiri a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin rage radadin talauci da bunkasar tattalin arziki ta hanyar fadada hanyoyin samun lamuni.   Da yake jawabi a wani gangamin wayar da kan al’adu a Kano, Shugaban...
    Kotun ta bayyana cewa mutanen sun aikata laifin sakaci da kuma jawo asarar dukiyar jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Kotun ta bayyana cewa mutanen sun aikata laifin sakaci da kuma jawo asarar dukiyar jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Bayan sabon farmakin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, kasashen Yamma na kokarin kara matsin lamba kan Isra’ila, wacce ta kauda kai kan kiraye kirayen da duniya ke yi na ta dakatar da yakin a Gaza. Kungiyar ta EU, ta kara mastin lamba ta hanyar sake nazari kan yarjejeniyarta da Isra’ila ta tsawon shekaru...
    Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham Hotspur ta zama zakarar Gasar Europa bayan doke Manchester United da ci ɗaya mai ban haushi. Tottenham ta kafa tarihi a yau Laraba na lashe kofi tun bayan shekara 17 da ta lashe wani babban kofi. Zargin Satar Fasaha: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan shari’ar BBC Sojoji da...
    Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi tattalin arziki zamantakewa ysaro da sauransu, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe kuma mu ji ra’ayin masana dangane da...
    An gudanar da taron dandalin tattaunawa na masanan Sin da Afirka karo na 14 a birnin Kunming dake lardin Yunnan na kasar Sin a yau Talata, 20 ga wata, inda wakilai kimanin 100 daga Sin da kasashen Afirka fiye da 50 suka halarci taron tare da tattauna fasahohin mulkin kasa da tafiyar da harkokin siyasa...
    Amma kuma kariyar ciniki ba za ta taimaka ga raya sana’o’i da masana’antu a duniya ba. Idan mun lura, a cikin shekaru 10 da suka wuce, yadda kasar Amurka ta dauki matakai na kare sana’o’in samar da karafa, a maimakon ya hana raguwar guraben ayyukan samar da karafa, sai ya haifar da karuwar kudaden da...
    Kungiyar Arsenal na shirin ɗaukar ɗan wasan gaban Sporting CP, Viktor Gyokeres kamar yadda jaridar wasanni ta football365 ta ruwaito. Arsenal ta fuskanci matsalolin ‘ƴan wasan gaba a kakar wasan da ke dab da ƙarewa, yayin da ƙungiyar ta gaza lashe kowane irin kofi. Bayan ƙarewa a mataki na biyu a Gasar Premier da samun gurbin...
    Majalisar Wakilai za ta gabatar da kudurori guda biyar da za su magance manyan kalubale da ke hana ingantaccen aiki a harkar man fetur ta kasa. Shugaban kwamitin Majalisar kan Albarkatun Man Fetur, Alhaji Alhassan Ado Doguwa, ne ya bayyana hakan yayin wani taro na hadin gwiwa da kwamitin musamman kan matsalar satar danyen mai...
    Babban Mufti na kasar Oman ya bayyana cewa: Matakin taron kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya fi kankara sanyi da rashin muhimmanci Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya jaddada yabonsa ga fitaccen matsayi na kasar Yemen da kuma matsin lamba da dakarun kasar Yemen suke yi na kai kayan agaji...
    Mahaifinta, Everistus Nnadozie, ya ce an sanar da shi cewa surukinsa Esosa Imasuen ne ya yi wa ‘yarsa duka har ta samu raunika sosai. Ya ƙara da cewa an kai ta asibiti inda likita ya tabbatar da cewa tana fama da zubar jini a cikin jikinta. Ya ce kafin ya isa asibitin, ‘yarsa ta rasu....
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 279 ga  Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta Najeriya (NURTW reshen jihar Jigawa karkashin shirinta na tallafawa masu sana’o’i. Kwamishinan Muhalli, Sabunta Makamashi da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Nura Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan...
    Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) Ola Olukoyede, ya mika katafaren jerin gidaje 750 na alfarma da aka kwace daga hannun tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele ga Ministan Gidaje, Ahmed Musa Dangiwa. An mika takardun ne bayan wani takaitaccen taro da aka yi a Abuja, ranar Talata. ...
    Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda yake mayarwa da Amurka martani ya bayyana cewa: Ya kamata su daina yin Magana maras ma’ana, fadin cewa Iran ba ta da izinin tace sanadarin Uranium, ganganci ne,domin jamhuriyar musulunci ba ta da bukatar izinin wani mahaluki.”  Jagoran juyin musuluncin na Iran wanda...
        Cikakkue bayanai daga baya… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tshouwar Mawakiyar Hausa Hip-Hop, Zainab Ishaq Muhammad, wadda aka fi sani da ‘Queen Zeeshaq’ za ta shiga daga ciki a ranar Lahadi mai zuwa. Duk da cewa ba a yayata batun auren ba, Aminiya ta tabbatar da ganin katin gayyata da ke nuna za a ɗaura auren nata da angonta, Hussain Muhammad Koya, a ranar...
    Malaman makarantu da ma’aikatan ƙananan hukumomi a Babban Birnin Tarayya, Abuja, sun bayyana cewa ba za su janye yajin aikin da suka shiga ba, har sai an biya malaman firamare bashin albashin da suke bi. Yajin aikin ƙarƙashin jagorancin rassan ƙungiyar malamai ta ƙasa (NUT) da ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (NULGE), da na...
    A ganin mista Akanbi, manufofin kasashen yamma ne dalilin da ya haifar da tafiyar hawainiyar tattalin arzikin Najeriya da na sauran kasashe dake nahiyar Afirka. Misali, kamfanonin kasashen yamma sun samu damar mamaye bangaren hakar ma’adinai na Najeriya, kana sun takaitawa kasar damar sarrafa ma’adinai, da ta raya masana’antu. Ban da haka, matsayin musamman na...
    Bayan haka, ‘yansanda sun hanzarta daƙile harin, inda suka kama su a ranar 15 ga watan Mayu, 2025. Da ‘yan fashin suka hango ‘yansanda, sai suka fara harbi. A lokacin musayar wutar ne, Babanle ya mutu. ‘Yansanda sun kama sauran tawagar ƙungiyar guda bakwai a wajen. Wasu daga cikinsu tsoffin fursunoni ne, yayin da ɗaya...
    Ado Aliero ya shahara wajen kai hare-hare, sace mutane da kashe-kashe a Jihar Zamfara da wasu sassan Arewa Maso Yammacin Nijeriya. An daɗe ana nemansa ba a samu nasarar kama shi ba, saboda ƙungiyarsa na da haɗin kai da goyon baya daga wurare da dama. Ko da yake hukumomin Saudiyya ba su tabbatar da sunayen...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani yanki na siyasa mai zaman kansa Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniya ba su da wata kafa ta siyasa mai cin gashin kanta, a maimakon haka dole ne a fahimci matsayinsu...
    Wasu shugabannin kasashen Yamma suna barazana ga gwamnatin mamayar Isra’ila kan daukan matakan ladabtarwa kanta Shugabannin kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Canada sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila da su dakatar da kai farmakin da suke kai wa Zirin Gaza tare da yin barazanar daukar...
    Da yammacin jiya Litinin, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci birnin Luoyang na lardin Henan. A yayin ziyarar, Xi ya ziyarci kamfanin Bearing Group na Luoyang, da gidan ibada na “Farin Doki”, da kuma ramin dutse na Longmen. Ya fahimci yadda aka inganta ci gaban masana’antun samar da...
    Dubun wani ɗan bindiga ta cika a yayin da yake shirin shiga jirgi tare da sauran maniyyata aikin Hajji a Jihar Sakkwato. Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kama ɗan ta’addan mai suna Sani Galadi ne a yayin da ake yi wa maniyyata tantancewar ƙarshe kafin hawa jirgi zuwa Ƙasa Mai Tsarki a Filin Jirgi...
    Jami’an tsaron ƙasar Saudiyya sun kama wasu mata biyu da ake zargin cewa mata da kuma mahaifiyar jagoran ’yan bindiga da gwamnatin Najeriya ke nema ruwa a jallo, Ado Aliero, bayan sun je aikin Hajji. An kama matar Aliero da mahaifiyar tasa ne a birnin Madina bayan sun je yin ziyara gabanin fara aikin Hajji....