2025-10-14@02:28:07 GMT
إجمالي نتائج البحث: 561
«Gwamnati Ta Tabbatar da Kungiyoyin Hadaka a Matsayin Ginshikin Ci gaban Al umma»:
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nada Dr. Muheeba Dankaka a matsayin shugaban hukumar kula da da’a ta tarayya (FCC) a wa’adi na biyu na shekaru biyar. Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya ce nadin na daya daga cikin alkawurran da shugaban kasar ya yi na...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) murna bisa ci gaba da riƙe matsayin Maturity Level 3 (ML3) na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wajen kula da magunguna da rigakafi. Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a...
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta yi wa tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, tambayoyi kan zargin fitar da wasu kuɗi har Naira biliyan ₦189 ta hanyar cire kuɗin daga banki. Rahotanni sun nuna cewa, Tambuwal ya isa shalƙwatar EFCC a Abuja da misalin karfe 11:30 na safiyar yau...

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar ‘Yan Sahayoniyya Kan Gaza
Kasashen Turai biyar na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun ki amincewa da matakin mamaye Gaza Wakilin dindindin na Slovenia ya gabatar da wata sanarwa ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a madadin Burtaniya, Faransa, Denmark, da Girka, yana mai cewa: “A matsayinsu na kasashen Birtaniya, Denmark, Faransa, Girka, da Slovenia, sun kira taron gaggawa...
Mahalarta taron masu ruwa da tsaki na yini daya don tabbatar da sakamakon bincike kan al’amuran zamantakewa da suka shafi ilimin ‘ya’ya mata a jihar Zamfara, sun bukaci iyaye, shugabannin al’umma, da gwamnati a dukkan matakai da su magance matsalolin da ke hana yara mata zuwa kammala karatun sakandare. Kungiyar AGILE da ke Jihar...
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a hedikwatar MDD da ke birnin New York a jiya Lahadi, bayan matakin da majalisar ministocin Isra’ila ta dauka na fadada ayyukan soji da kuma mamaye yankin zirin Gaza. Mataimakiyar Sakatare-Janar mai kula da harkokin Turai, Tsakiyar Asiya da Amurka, Miroslav Jenča, ta jaddada...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na mamaye zirin Gaza Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin baya-bayan nan da majalisar ministocin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta dauka na mamaye yankin zirin Gaza da korar al’ummarta, tare da la’akari da...
Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan...
Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan...
Wani lokacin, yanayin shekaru da Jinsin Jini ne ke fayyace irin girma ko ƙantantar Ƙwan da Kajin za su yi. 2- Wajen Kwana: Kajin na buƙatar a tabbatar da ana samar musu da wadataccen ruwan sha a ɗakunan kwanansu da kuma ba su kariya daga kamuwa da cutuka da rage musu wahala da cunkoso da...
Kwamandan Dakarun Qudus na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Gudun da Amurka ta yi daga Yemen wani shan kaye na soji da ba a taba ganin irin sa ba Kwamandan Dakarun Quds na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ismail Qaani, ya kaddamar da wani...
“Kuma za a yi hakan ne saboda a matsayinmu na al’umma, muna ci gaba da ƙoƙarin canza abubuwan da ‘yan siyasa ba sa son canzawa,” in ji shi. Ya kuma bayyana cewa ba yau aka fara aikin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar kan batun cin gashin kan ƙananan hukumomi ba. Ejah ya ƙara da cewa...
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya sanar a yau jumma’a cewa Jamus za ta dakatar da duk wani izinin fitar da kayan aikin soji da za a iya amfani da su a zirin Gaza, biyo bayan matakin Isra’ila na mamaye Gaza. Da yake magana bayan zaman majalisar ministoci ta Isra’ila da kuma amincewarta da shirin...
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa ta kammala shirin amfani da sojoji wajen mamaye ilahirin Zirin Gaza na Falasdinawa domin ya koma karkashin ikonta. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar da safiyar Juma’a, Netanyahu ya tabbatar da shirin inda ya ce, “Sojojin Isra’ila za su shirya karbe iko da Zirin Gaza baki...
Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Abubakar, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira tiriliyan daya da rabi don gina layin dogo na zamani domin saukaka harkar sufuri a cikin birnin Kano. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Kano, inda ya ce aikin zai saukaka...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini kan rasuwar Sadiq Gentle, wani hadiminsa kan harkokin yada labarai a Ma’aikatar Tarihi da Al’adu ta jihar, wanda wasu da ake zargi ’yan daba suka kai masa harin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a Facebook, ta...
Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta bayyana alhinita kan kisan gilla da aka yi wa Umar Abdullahi Hafizi, dalibi da ke matakin karatu na 3 a Sashen Ilimin Zamantakewa (Sociology), wanda wasu masu kwacen waya suka daba wa wuka har lahira a gidansa da ke unguwar Dorayi a ƙaramar hukumar Gwale. Wannan na ƙunshe...
“Ko da yake lamarin ya faru ne a wajen harabar jami’a, Hukumar Gudanarwa ta jami’ar na cikin jimami matuƙa da wannan mummunan lamari, kuma tana miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokansa da sauran ɗalibai,” in ji sanarwar. Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana cewa jami’ar na aiki tare da hukumomin tsaro domin a...
Matasan Kauru Sun zargin Dan Majalisar Dokoki Barnabas Danmaigona da Rashin tabuka komai Wata kungiyar matasa, Kauru Youth Ambassadors (KYA) a karamar hukumar Kauru sun nuna matukar damuwa kan yadda Barnabas Danmaigona, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kauru a majalisar dokokin jihar Kaduna, ya gaza samar da ingantaccen wakilci tun bayan zaben sa. A...
Bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin tubabbun ’yan bindiga da jama’ar gari a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, mazauna yankin sun ce yanzu matsalar tsaron ta dauki sabon salo. A watan Oktoban 2024 ne dai aka kulla yarjejeniyar sulhun tsakanin bangarorin biyu. Yarjejeniyar na zuwa ne bayan shafe sama da shekara 10 ana...
“Bari in yi bayani a fili: ba za mu yarda da duk wata dabi’a wacce za ta ruguza dabi’un da muke tsaye a kai ba. Dole ne kowane jami’in gwamnati ya kasance mai lura da al’amuransa, ba wai kawai ofishin ku kuke wakilta ba, har da mutuncin gwamnati baki daya.” In ji Gwamna Abba Kabir...
Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya. Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi...
Kakakin dakarun juyin juya halin musulun a nan Iran ya bayyana cewa nasarar da JMI ta samu na tunkude hare-harenda HKI ta kawowa kasar ya saya abubuwa da dama a bangaren siyasa da wasu al-amura a yankin da kuma duniya gaba daya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto General Ali Mohammad Naeini...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya nada Ali Larijani babban mai baiwa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara a matsayin sabon babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasar. Larijani ya taba rike mukamin sakataren majalisar koli ta tsaron kasar daga ranar 15 ga watan Agustan shekarar 2005 zuwa ranar 20 ga watan Oktoban shekarar 2007, sannan...

Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida a matsayin martani ga harajin Trump
Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida da kashi 30% na bangaren da harajin Amurka ya shafa a wannan makon, tare da kebe wasu ka’idojin samun wannan tallafin kudi. Kasar mafi karfin tattalin arziki a Afirka ta kwashe watanni tana kokarin tattaunawa da Washington, inda ta yi tayin sayen...
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a jiya Lahadi cewa, Sin da Rasha sun fara atisayen soja na hadin gwiwa mai taken “Tekun hadin gwiwa na shekarar 2025” a tekun Japan, a wani bangare na kokarin zurfafa hadin gwiwarsu ta fuskar “mutumin Amurka.” Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta bayyana cewa, sojojin biyu za su...

Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Sun Bayyana Cewa: Masu Shirin Halaka Gaza Suna Son Mamaye Duniyar Musulmi Ne
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Masu shirin halaka Gaza suna neman hadiye duniyar Musulunci ne Dakarun kare juyin juya halin Musulunci nanIran sun yi gargadin cewa; Bangarorin da ke shirya kisan kiyashi a Gaza ba wai kawai halakar al’ummar Falastinu ba ne kawai, a’a suna neman mamaye yankuna masu...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da babban shirin dashen bishiyoyi miliyan biyar a shekarar 2025. An fara dashen ne yankin Yanbawa da ke Ƙaramar Hukumar Makoda. Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi Gwamnan ya ce wannan shiri na nufin...
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da naɗa Hon. Ismaila Ahmed Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi, bayan rasuwar Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Kaji. Sabon Sarkin na Gudi, Ismaila Ahmed Gadaka, ya shahara da ƙwarewa a fannoni da dama. Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba Ma’aikatan jinya sun...
A cewar shugaban kwamitin, Katsina na kuma goyon bayan batun sauke wasu ikon gwamnati daga matakin tarayya zuwa jihohi, saka sarakunan gargajiya a cikin kundin tsarin mulki da kuma sake fasalin harkokin kuɗi. Sanata Ibrahim ya shaida wa kwamitin cewa an tattara dukkan ra’ayoyi da buƙatun jama’ar Katsina, tare da gabatar da su a cikin...

Babban Jami’in MDD: Kokarin Sin A Fannin Samun Ci Gaba Mai Dorewa Na Da Matukar Alfanu Ga Yanayin Duniya
Fiye da shekaru goma da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dora samun ci gaba marar gurbata muhalli a matsayin wata muhimmiyar manufar raya kasa. Ya taba fitar da manufar raya kasa ta hanyar bayar da muhimmnci ga “Muhalli”, wadda ta yi nuni da cewa ingantaccen yanayin muhalli abu ne mai matukar daraja don samun...
Kasar Spain ta bayyana abin da ke faruwa a Gaza a matsayin abin kunya ga bil’adama Ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya yi kira ga mahukuntan Isra’ila a ranar Alhamis da su bude mashigar ruwa na dindindin domin ba da damar kai agajin jin kai zuwa zirin Gaza, yana mai gargadin cewa;...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta...
Gwamna Zulum ya nuna jin dadinsa ga kwamishinonin biyu, tare da yi musu fatan alheri a cikin ayyukansu na gaba. Sai dai ya sanar da nadin Engr. Mohammed Habib da Ibrahim Hala Hassan domin maye gurbin kwamishinonin biyu da aka sauke. A halin da ake ciki, Gwamna Zulum ya kuma amince da nadin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta zargi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kin yin adalci wurin ayyuka da raba mukamai tsakanin Arewa da Kudancin Kasar nan. Wadannan zarge-zarge suka sa fadar Shugaban Kasa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai Bayo Onanuga mayar...
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta kammala aikin shimfiɗa layin dogo wanda ya taso daga Kaduna zuwa Kano a cikin shekarar 2026 mai zuwa. Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba. Kazalika, takwaransa na sufuri, Sa’idu Ahmed Alkali...
Adamu ya bayar da hujjar cewa, Sarkin Musulmi ne ke shugabantar daular gargajiya mafi girma a Arewacin Nijeriya, tare da dukkan sarakunan yankin karkashin jagorancinsa na ruhi da al’adu. Ya yaba da shugabancin Sarkin Musulmi Abubakar na tsaka-tsaki, samar da zaman lafiya, da jagoranci na hadin kai. Sun bayyana shi a matsayin mutum...

Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar
Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin...
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar wata kungiya mai suna Partnership for Agile Governance and Climate Change (PACE) ta kaddamar da manufofinta na sauyin yanayi a hukumance. Wannan manufa mai mahimmanci ta samar da taswirar dabaru don ragewa, daidaitawa, da tsarin tafiyar da yanayi mai hadewa a duk sassan ci gaba a jihar. ...
Sanarwar New York ya jaddada alƙawarin kasa da kasa na kawo ƙarshen yaƙin a Gaza da aiwatar da hanyoyin samar da ƙasashe biyu Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a cikin “Sanarwar New York” da yarjejeniyar kasa da kasa kan matakan dole da suka dace don kawo karshen yakin Gaza da aiwatar da Shirin samar da...

Birtaniya Ta Yi Barazanar Amincewa Da Kasar Falasdinu A Watan Satumba Idan Yanayin Gaza Bai Canza Ba
Fira ministan Birtaniya ya bayyana cewa: Za su amince da kasar Falasdinu a watan Satumba idan yanayin Gaza bai canza ba Keir Starmer ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne domin kare tsarin kasashe biyu, kuma kasarsa na da wani nauyi na musamman da ya rataya a wuyanta wajen ganin an samar da...
An shawarci gwamnatocin jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da su kirkiro hanyoyi na wayar da kan al’umma dangane da shirye-shiryen tallafi da ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da tsaro a yankunansu. Shugaban sashen kimiyyar zamantakewa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Chika Umar Aliyu,...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗa Muhammad Fa’iz a matsayin Kwamanda Janar na farko na Hukumar Hisbah ta Jihar. Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ne ya tabbatar da naɗin ga manema labarai a Dutse. Ya bayyana cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin Gwamna Namadi na ƙarfafa ayyukan sabuwar...
Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba. Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba....
Gwamna Lawal ya taya sabon sarki murna, tare da roƙon Allah Ya bashi hikima da ikon yin jagoranci na gari. Ya kuma buƙace shi da ya ci gaba da bin kyawawan ɗabi’u da tafarkin tsofaffin sarakuna domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a masarautar Gusau. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...

SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa
Jam’iyyar ta bayyana cewa bayan bincike daga reshen jam’iyyar na jihar Kaduna, ya tabbatar da cewa El-Rufai ba halataccen ɗan SDP bane. Saboda haka, Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Ƙasa ya kafa masa takunkumin shekaru 30, har zuwa shekarar 2055, ya hana shi sake neman zama mamba ko hulɗa da jam’iyyar ta kowace fuska. Daga...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar makamashin nukiliya wani zaɓi ne mai mahimmanci wanda ya ƙarfafa matsayin Iran a duniya Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa; Kasarsa ta shiga shawarwarin makamashin nukiliya ba na kai tsaye ba da Amurka bisa wata cikakkiyar shawarar kasa. Ya kara...

Babban Jami’in Hamas A Gaza; Makiya ‘Yan Sahayoniyya Suna Rufe Gazawar Sojojinsu Da Kisan Kare Dangi
Babban jami’in kungiyar Hamas a Zirin Gaza ya bayyana cewa: Makiya yahudawan sahayoniya suna rufe gazawar sojojinsu da kisan kare dangi Khalil al-Hayya babban jami’in kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a zirin Gaza ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna rufe gazawar sojojinsu ta hanyar kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen hula. A...
Dubban ‘yan Najeriya magoya bayan kungiyar kwallon kafar ta ” Super Falcon” sun yi bikin samun nasarar da kungiyar tasu ta samu, wasan karshe na samun kofin nahiyar Afirka na kwallon kafa na mata. A wasan da aka yi kafin hutun rabin lokaci, ‘yan wasan kasar ta Moroko sun yi bajinta, inda su ka ci...