Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane
Published: 7th, October 2025 GMT
”Dan wasan gaban Bayern Munich Harry Kane ya bayyana cewar zamansa a Bayern Munich ya bude wani sabon Babi a rayuwarsa don haka a shirye yake ya bude tattaunawa da Bayern Munich kan yiwuwar saka hannu akan sabon kwantaragi, Kane ya shafe rabin shekarun kwantiraginsa a Bayern Munich, Kane ya saka hannu akan shekaru hudu da Bayern Munich wadda ta dauko shi daga Tottenham Hotspur kan fan miliyan 86.
Dan wasan mai shekaru 32, ya zura kwallaye 103 a wasanni 106 da ya buga wa kungiyar ta Jamus, wanda ya taimaka mata lashe kofin Bundesliga na shekarar 2024-25 kofi na farko da ya dauka a tarihinsa na kwallon kafa, Kocin Tottenham Thomas Frank ya ce yana son ganin Kane ya koma Ingila, Kane na bukatar kwallaye 48 don kawar da tarihin da Alan Shearer ya kafa a tarihin gasar Fiimiya da kwallaye 260.
Sai dai kyaftin din na Ingila ya ce baya sha’awar komawa gida kamar yadda yakeyi a lokutan baya, inda yake tunanin tsawaita zamansa a Munich, Kane shi ne wanda ya fi kowa zura kwallo a raga a Tottenham da Ingila, kuma a kwanan baya ya zama dan wasa mafi sauri wajen jefa kwallaye 100 a raga a duka manyan gasannin Turai 5.
“Kafin in samu wani kofi bansan yadda ake ji ifan an lashe kofi ba, amma tun bayan lashe kofi na farko tareda Bayern Munich sai naji cewa ina bukatar lashe manyan kofuna da dama yanzu, hakan ya sa ba zanyi saurin barin wannan kungiya da na lashe kofin farko a cikinta ba, kofin ya kara min kwarin gwiwa na kara yin aiki da kyau, ina ganin na nuna hakan a bana” inji shi.
Tags: Firimiyar IngilaKaneShareTweetSendShareকীওয়ার্ড: Firimiyar Ingila a Bayern Munich
এছাড়াও পড়ুন:
Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad
Ta ce, “Dole ne akwai kalubale da dama, wanda daga cikinmu muke fuskanta a yayin shigowa wannan masana’anta, amma dai ni babu wani abu da zan iya tunawa, illa wani wanda na iske a masana’antar ya karbi zunzurutun kudi har Naira 50,000 a mabanbantan lokuta da sunan zai yi min rijista a masana’antar, kuma bai yi ba, daga karshe ma na gano cewa; kudin rijistar duka-duka Naira 5,000 ne.
A wata hira da Khadija ta yi da gidan Rediyon Hikima, ta bayyana cewa, matukar ta samu abin da ya kawo ta masana’antar (Kudi), to nan da shekara daya ma; za ta iya shiga daga ciki, ma’ana za ta samu miji ta yi aurenta na Sunna.
Khadija, wadda ta ce; ita haifaffiyar birnin Maiduguri ce ta Jihar Borno, wadda zama ya dawo da ita birnin Kanon Dabo, ta kuma bukaci masu kallon su da su dinga nuna musu soyayya kamar yadda suke nuna wa sauran jaruman duniya, musamman wadanda ke cikin masana’antar Bollywood ta Kasar Indiya.
“Akwai bukatar dukkaninmu, mu hada karfi da karfe don ganin mun taimaki junanmu, ba mu koma gefe muna zagin junanmu ba, abin da ya sa na fadi haka kuwa shi ne, akwai lokacin da wani ya zo neman aurena, amma wasu suka zagaya baya suka hure masa kunne a kan cewa; kada ya sake ya aure ni, saboda ni jarumar fim ce. Ta kara da cewa; mu ma Hausawa ne kamar mafi yawan masu kallonmu, sannan kuma bai kamata ku yi la’akari da duk wani abu da kuka gani a cikin fim, wajen yanke hukuncin cewa, halin dan fim kenan ko a zahiri ba.
Daga karshe, Khdadija ta ce; “Dukkanninmu ‘yan fim, muna kokari wajen ganin mun killace kanmu( Sirrinta al’amuranmu), domin kauce wa zargi, duk wani wanda ka ga yana fallasa halayensa na zahiri a shafukansa na sada zumunta, to ba dan fim ba ne, kawai yana zuwa neman taimako wajen masu shirya fina-finai ne su saka shi ya fito sau biyu ko sau uku a fim, domin su samu na cefane, amma ba lallai ne ya zama cikakaken dan fim ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA