Aminiya:
2025-11-02@17:09:39 GMT

Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista

Published: 18th, September 2025 GMT

Sabuwar mutum-mutumi ta fasahar AI da aka kirkira kuma aka nada mukamin minista a ƙasar Albania ta yi jawabi a karon farko a gaban majalisar dokokin kasar.

A ranar Alhamis ce dai ministan ya bayyana gaban majalisar, inda ya kare rawar da zai taka a gwamnati, yana mai cewa, “Ban zo don na maye gurbin mutane ba, sai dai don taimaka musu.

Yadda jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa yayin tsere wa harin ’yan bindiga a Neja Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn — Ministan Kuɗi

Wannan minista ta AI wacce aka sanya masa suna Diella, ma’ana “rana” a harshen Albania, ita ce ministar gwamnati ta farko a duniya da aka ƙirƙira ta hanyar fasahar AI.

Firaministan Albania, Edi Rama, ne ya naɗa shi a makon da ya gabata.

A cikin wani faifan bidiyo da aka nuna a majalisa, Diella ta bayyana a matsayin mace sanye da kayan gargajiya na Albania, inda ta ce: “Wasu sun ce ba na kan dokar kundin tsarin mulki saboda ni ba mutum ba ce.”

Diella ta ƙara da cewa: “Bari in tunatar da ku, babban hatsarin da ke tattare da kundin tsarin mulki ba na injuna ba ne, na masu mulki ne.”

A makon da ya gabata, Firaminista Rama ya bayyana cewa Diella za ta kula da dukkan al’amuran kwangiloli na gwamnati, domin tabbatar da cewa an kawar da cin hanci gaba ɗaya, kuma duk kuɗaɗen gwamnati da aka sanya a cikin tsarin kwangila za su kasance a bayyane.

An ƙaddamar da Diella a watan Janairu a matsayin mataimakiyar fasahar AI da ke taimaka wa jama’a wajen amfani da dandalin e-Albania, wanda ke bayar da takardu da ayyuka na gwamnati.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano

Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku.

 

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima November 1, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori November 1, 2025 Manyan Labarai Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara