2025-09-17@21:53:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9005

«Ihar Losik»:

    Kwace makaman kungiyar Hizbullah… Fadan ne da ba zai yi nasara, inda daga karshe zai zame siyasa bayan gazawar nuna karfi Ana ci gaba da tabka muhawara kan batun neman kwance damarar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah a kasar Labanon, a daidai lokacin da ‘yan sahayoniya da Amurka ke kokarin cimma wannan buri a siyasance...
    Majiyar ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 na daban suka jikkata a Gaza cikin sa’o’i 24 Ma’aikatar lafiya a zirin Gaza ta sanar da cewa, adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin kisan kiyashi da sojojin mamayar Isra’ila suke ci gaba da...
    Kungiyar Zabarmawa ta Najeriya ta karrama Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, da sarautar Garkuwan Zabarmawa, saboda gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma da tallafa wa ƙungiya. Da yake bayyana dalilin bai wa gwamnan sarautar a madadin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Sarkin Zabarmawa, Alhaji Bello Zabarmawa, ya ce: “An ba da wannan sarauta...
    Bugu da kari, kasashe membobin kungiyar sun amince da kafa bankin bunkasa harkokin SCO, wanda a cewar Wang, zai yi matukar bunkasa samar da ababen more rayuwa, da raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummun kasashe membobin kungiyar. Dadin dadawa, kasar Sin ta sha alwashin kafa sabon dandalin hadin gwiwa, da cibiyoyi masu nasaba da makamashi,...
    Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya da ke Sakkwato ta bayyana aniyar karrama Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli CFR, da lambar yabo ta musamman saboda rawar da ta ce yana takawa wajen ƙarfafa haɗin kai da raya zumunci tsakanin ’ya’yan Daular Usmaniyya. A cikin sanarwar da cibiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun...
    Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatu na makarantun firamare zuwa sakandire wanda zai fara aiki a sabon zangon karatu na bana da za a soma a watan Satumbar nan. Wannan na zuwa ne bayan kammala nazari mai zurfi kan manhajoji karatu a fannin ilimi a matakin farko da na manyan makarantun sakandire da...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta ɗauki mai tsaron ragar PSG, Gianluigi Donnarumma ɗan asalin ƙasar Italiya. Donnarumma wanda tsohon mai tsaron ragar AC Milan ne ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar a Etihad, inda zai zai ci gaba da tsare ragar ƙungiyar zuwa kakar 2030. Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko...
    Hukumar NDLEA a Kano ta kama kwalabe 8,000 na Akuskura da ake zargin na ɗauke da ƙwayoyi, tare da tabar wiwi guda 48. An cafke wani mutum mai shekara 37, Ali Muhammad, bayan an gano kayan a cikin tirela ɗauke da kekuna a kan hanyar Zariya zuwa Kano a Gadar Tamburawa. ’Yansanda Sun Kama Masu...
    Sanata Mohammed Ali Ndume, ya koka kan yawaitar sabbin hare-haren mayaƙan Boko Haram ƙananan hukumomin Gwoza da Askira/Uba, inda suka kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a ƙarshen mako. A safiyar ranar Asabar din da ta gabata a garin Ngoshe da ke Gwoza an kashe manoma biyar a lokacin da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi tir da kissan da sojojin HKI suka yiwa firay ministan kasar Yemen Ahmad Al-Rahawi da wasu jami’an gwamnatinsa. Ya kuma kara da cewa irin wadan nan hare-haren suna zagon kasa ga zaman lafiya a duniya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana...
    Mutanen sudann daga yammacin kasar kimani dubu guda ne suka raya rayukansu sanadiyyar zai-zayar kasa, kuma kan tsaunukan Marre. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto Abdulwahid Muhammad Nour na kungiyar ‘The  Sudan Libration Movementa’ Wato (SLM) wacce take iko da yankin yana fadar haka. Ya kuma kare da cewa, zaizeyar kasa ta...
    Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi na Najeriya (ALGON), ta yi kira ga Ƙungiyar ’Yan Jarida Masu Rubuta Labaran Wasanni (SWAN) da ta ƙara mayar da hankali wajen yada labarai kan wasannin gargajiya, irin su langa da kokawa. Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe wanda shi ne shugaban ALGON reshen Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya bayyana haka ne...
    Hukumar bada agaji ta MDD mai kula da Falasdinawa UNRWA ta bayyana cewa yara fiye da 660,000 a gaza aka haramtawa karatu a wannan shekarar saboda yakin da HKI ta dorawa yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Philippe Lazzarini shugaban hukumar UNRWA yana fadar haka a wani sakon da ya...
    Gwamnatin kasar Belgium ta bada sanarwan cewa zata bayyana amincewarta da samuwar kasar Palasdinu mai cikekken yenci, a babban taron MDD a cikin wannan watan a birnin NewsYork. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Belgium Maxime Prevot yana fadar haka a shafinsa na X a yau Talata. Ya...
    Kasar Venezuela ta sami sakon tallafi daga kasar Iran a lokacinda ministan harkokin wajen kasar Vanezuela ya gaba da jakadan Iran a Caracas. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, jami’an gwamnatocin kasashen biyu sun bayyana cewa zasu kara karfafa dangantaka ta musamman dake tsakaninsu na tsaro da sauran bangariri masu musammancin...
    Ta ce cikin ƙasa da shekara biyu, Kaduna ta fito daga durƙushewar tsari zuwa zama jihar da ake ganin tsari. Haka kuma, gwamnatin ta yi zargin cewa El-Rufai ya ƙara ƙoƙarin tayar da rikici bayan abokan siyarsarsa sun sha kaye a zaɓen cike gurbi na ranar 16 ga watan Agusta. Ta ce sakamakon ya nuna...
    Al’ummar kurame sun koka bisa matsalolin da suke fuskanta a fannin kiwon lafiya, sakamakon rashin masu yi musu fassara a asibitoci a Jihar Yobe. Malam Kolo Abba, Shugaban Ƙungiyar Kurame a Ƙaramar Hukumar Damaturu, ya ce kurame majinyatan sukan koƙarta wajen fahimtar ƙa’idojin likitoci da na kiwon lafiya, amma duk da hakan suna cikin haɗari....
    ’Yar Najeriya kuma Shugabar Jam’iyyar Conservative a Birtaniya, Kemi Badenoch, ta shiga tsaka mai wuya kan iƙirarinta na cewa Jami’ar Stanford ta ba ta gurbin karatun horon shiga likitanci bisa rangwamen kuɗi tun tana ’yar shekara 16. An fara sanya alamar tambaya a kan iƙirarinta ne bayan da wani tsohon jami’in kula da ɗaukar ɗalibai...
    Kan batun yiwuwar Obi zai koma PDP, Wike ya yi watsi da shi, ya ce hakan zai jawo wa jam’iyyar matsala. “Obi ya zargi PDP, ya ce jam’iyyar ta lalace. Yanzu kuma jam’iyyar ta gyara kenan a gare shi? Wannan zai kashe jam’iyyar,” in ji shi. Wike ya ce dawo da Obi saboda kawai neman...
    Rahotanni sun bayyana cewa Kotu a kasar Finland ta yanke wa dan Najeriya mai ‘rajin kafa kasar Biyafara’, Simon Ekpa hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa laifukan ta’addanci. Kotun ta same shi da laifin koƙarin harzuka jama’a da niyyar ta’addanci da kuma shiga cikin ayyukan kungiyar ta’addanci. Haka kuma ta same shi da...
    An gudanar da janazar manyan jami’an gwamnatin kasar Yemen 9 da suka yi shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar a kansu,a  lokacin da suke gudanar da wani zama na gwamnati, domin bin kadun ayyukan ma’aikatun da suke jagoranta. Dubban daruruwan mutane ne dai suka halarci janazar wadda ta gudana a birnin...
    ’Yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da safarar makamai masu haɗarin gaske, tare da tarin harsasai, a wani samame a Jihar Katsina. A farkon wannan mako ne ’yan sanda da ke sintiri suka tare wata mota ƙirar Volkswagen Golf, da asubahi, inda suka  gano bindiga ƙirar GPMG da sauran makamai a...
    shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewa, Aikewa da sojojin ruwan Amurka a yankin Caribbean itace barazana mafi girma ga al’ummomin yankin a cikin wannan karni. Da yake magana a wani taron manema labarai, Maduro ya ce an jibge jiragen ruwan sojan Amurka guda 8 dauke da makamai masu linzami 1,200 da kuma na...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce shi da takwarorinsa na Rasha da China sun aike da wasika ga Majalisar Dinkin Duniya, inda suka yi watsi da matakin da Birtaniya da Faransa da Jamus suka dauka a baya-bayan nan na yunkurin maido da takunkumin kasa da kasa kan Iran a matsayin mataki marar ma’ana....
    A lokacin wani taro da ya gudana tsakanin shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan da kuma babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio gutteres a kasar china ya bayyana cewa iran tana da hakkin ta mallaki fasahar nukiliya na zaman lafiya, kana ya nuna damawarsa game da batun takunkumi da kasashen turai ke son sake kakabawa iran,...
    Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami ya tsallake rijiya da baya a garin Birnin Kebbi yayin da wasu matasa suka kai wa tawagarsa hari. Abubakar Malami da tawagarsa, wasu ’yan bangar siyasa sun tare su, a unguwar GRA, inda suka yi amfani da sanduna da addun da sanduna suka farfasa motocin Malami tare da jikkata mutanensa,...
      Kazalika, shugaba Xi ya yi kira da a yi kokarin hada karfi da karfe wajen kiyaye kyawawan sakamakon da aka samu bayan yakin duniya na biyu, da samar da karin alfanu ga daukacin bil’adama ta hanyar yin kwaskwarima ga tsarin shugabancin duniya, da gina al’umma mai makoma ta bai-daya ga bil’adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere)...
    Mutum sama da 800 sun mutu, yayin da wasu fiye da 2,500 suka jikkata sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6 da ta auku a lardin Kunar da ke gabashin Afghanistan, kusa da iyakar Pakistan. Girgizar ƙasar wadda ta auku da misalin ƙarfe 12 na daren Lahadi ta rusa gidaje da dama da aka gina...
    A yau ranar 1 ga watan Satumba da yamma, uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan da matan shugabannin kasashe membobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO masu halartar taron kolin SCO na shekarar 2025 sun ziyarci kogin Haihe na birnin Tianjin tare.   Peng Liyuan da sauran matan shugabannin sun hau jirgin ruwa tare...
    Mukaddashin daraktan ofishin bunkasa tattalin arziki, hada kai da raya cinikayya a hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, mista Patrick Ndzana Olomo, ya ce nahiyar Afirka da Sin na da makoma mai haske a fannin raya hadin gwiwa, don bunkasa harkokin noma da shawo kan matsalar kamfar abinci a Afirka. Olomo, wanda ya yi...
      Ya ba da tabbacin cewa, Majalisar za ta kara sanya ido domin tabbatar da gaskiya da rikon amana ga yadda ake sarrafa kudaden jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    A yau Litinin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya iso birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya. Shugaba Mnangagwa ya sha ziyartar kasar Sin, inda a shekarar da ta gabata ma ya zo birnin Beijing...
    Jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) sun cafke wani mutum mai shekaru 48, Ibrahim Haruna, tare da ɗansa mai shekaru 15, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyaɗe a unguwar Jekadafari da ke Jihar Gombe. Wakilinmu ya ruwaito cewa an gabatar da waɗanda ake zargin ne a hedikwatar hukumar a ranar Litinin. An...
    Ya bayyana cewa, matan sun fito ne daga jihohin Kano, Katsina, Borno, Jigawa, da Zamfara, inda aka yi musu alkawuran samun ingantattun ayyukan yi a kasar ta Saudiyya.   An kama daya daga cikin wadanda ake zargi da safarar matan mai suna Mohammed Saleh mai shekaru 45 da haihuwa.   Babale ya ce, ana ci...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne kungiyar hadin gwiwar Shanghai ta dauki matakai wajen samar da duniya mai zaman lafiya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi imanin cewa, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a matsayin muhimmin ginshiki na tsarin kasa da kasa, dole ne...
    Shawarar da Iran ta gabatar ga kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai zai durkusar da darajar kudin dalar Amurka A jawabin da ya yi a wajen taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a kasar China, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ba da shawarar kafa tsarin hada-hadar kudi ga kungiyar da rage dogaro da kudin dala....
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar...
    Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Afghanistan ya haura 800, yayin da ake sa tsammanin karuwar wadanda suka jikkata Hukumomin kasar Afganistan sun sanar da cewa: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta afku a gabashin Afghanistan ya haura 800, yayin da sama da 1,500 suka jikkata, adadin da ake sa...
    Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta kasar Sudan sun kai hare-hare kan sansanin Abu Shouk da ke birnin El Fasher da manyan bindigogi Majiyar sojojin Sudan ta shaidawa gidan talabijin na Al Jazeera cewa, dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) sun yi luguden wuta kan sansanin ‘yan gudun hijira na Abu Shouk da...
    Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, wanda ya shigo kasar Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO na bana, ya zanta da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a birnin Tianjin, inda ya ce, Xi Jinping shugaban kasa ne mai sanin ya...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kama wani dattijo mai shekaru 60, Ajayi Femi, bisa zargin yi wa wata budurwa mai shekaru 24 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi. An kashe mutum 5 an sace limamai da hakimi a Sakkwato Simon Ekpa: An ɗaure...
    Yayin da yake zantawa da ’yar jaridar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, firaministan kasar Pakistan Shehbaz Sharif, ya bayyana cewa, Xi Jinping shugaban kasa ne mai matukar hangen nesa. A cewar firaministan, Xi Jinping, shugaban kasa ne wanda ke mayar da hankali sosai kan kyautata rayuwar jama’a, kuma a...
    Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ya rushe majalisar kwamishinoninsa. Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Bologi Ibrahim, ya ce gwamnan ya sanar da rushe majalisar kwamishinoninsa ne a yayin taron Majalisar Zartarwa ta jihar a safiyar Litinin ɗin nan. Ya kuma yaba musu bisa gudunmawar da suka bayar wajen kawo ci-gaba mai ma’ana a...
    Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan harkokin Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ya musanta zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa Gwamnatin Shugaba Tinubu tana biyan kuɗaɗen fansa ga ’yan bindiga don sako waɗanda suka sace. El-Rufai ya yi wannan zargi ne a wani shirin talabijin na Channels, inda ya ce matsalar tsaro a Arewacin...
    Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sallami dukkan mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar. Gwamnan ya bayyana labari sallamar ta su ne a taron majalisar da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Minna, babban birnin jihar, da safiyar yau Litinin 1 ga Satumbar 2025 Girgizar Ƙasa Ta Kashe Sama da Mutune 600 A Afghanistan Daje...
    ’Yan gudun hijira daga sama da kauyukka 10 a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkwato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan azabar da suke sha hannun ’yan bindiga a yankinsu. Mata da mazan sun buƙaci daukin gwamnati kan abin da ke addabar su, sun rufe babbar hanyar da ta...
    Ana jin tsaron daruruwan mutane ne suka rasa ransa sanadiyyar girgizan kasa mai karfin ma’aunin richter 6 da ta fadawa yankin tsaunuka na kasar Afganistan dake kan iyaka da kasar Pakisatan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran rauters na cewa an jirage masu saukar ungulu suna sauke wadanda suka...
    A safiyar yau litininn ce aka fara jan’izar shugaban gwamnatin kasar Lemen Ahmad Ghalib Arrahwi da ministocinsa da suka yi shahada a hareharen da HKI ta kai kansu a lokacinda suke taro a birnin San’a babban birnin kasar. Tashar talabijin ta al-amayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa an gudanar da taron janaizar ne a...
    Sojojin kasar Yemen sun bada labarin kai hari kan wani jirgin daukar man fetur na HKI a arewacin tekun maliya a safiyar yau litinin. Mai magana da yawun sojojin kasar ta Yemen Burgediya Yahyah Saree ne ya bada wannan sanarwan a wani jawabin da ya gabatar a faifai bidiya a safiyar yau Litinin, tare da...
    Sojojin HKI sun kashe wata yar jarida mai aikiwa tashar talabijin ta “Qudsul- Yau” a wani harin da ta kai a zirin gaza. Islam Abed ta hadu da ajalinta a lokacinda jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan birnin gaza a jiya Lahadi da yamma. Wanda ya kara yawan yan jaridan da HKI ta...