2025-10-14@19:27:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10178

«Masu zanga zangar»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin soma karɓar haraji daga hannun mata masu zaman kansu waɗanda suka mayar da karuwanci sana’a. Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kuɗi da gyaran dokokin haraji, Taiwo Oyedele, ya ce kuɗaɗen da masu sana’ar karuwanci ke samu za a riƙe cire musu haraji a ƙarƙashin sabuwar dokar haraji ta ƙasar. Oyedele ya yi wannan bayani ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin X a jiya Litinin, inda ya kawo misalan hanyoyin samun kuɗin da ake sanya wa haraji. Masanin harajin ya bayyana cewa sabbin dokokin ba su bambanta tsakanin hanyar halal ko ta haram wajen samun kuɗi ba — abin da suke dubawa kawai shi ne ko kuɗin ya fito daga...
    Fadar Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa duk da tana maraba da tsayawa takarar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a Zaɓen 2027, amma ya kwana da sanin cewa har yanzu ’yan ƙasar ba su mance da badaƙalar da aka tafka a lokacin gwamnatinsa ba. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar da yammacin ranar Litinin, ta ce ’yan Najeriya na sane da “rashin takaɓus” a mulkin Jonathan ɗin na shekarun baya. Jama’ar gari sun kama ’yan bindiga 3 a Kastina An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja Sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasar ta fitar mai taken “Muna maraba da tsohon shugaban ƙasa zuwa takarar shugabancin ƙasa”, “amma ’yan Najeriya na sane...
    Tsohon Shugaban Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Neja (SUBEB), Alhaji Alhassan Bawa Niworo, ya shiga hannun ’yan bindiga. An yi garkuwa da shi tare da wasu fasinjoji da dama a yammacin Litinin, 29 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 4 na yamma, tsakanin ƙauyukan Felegi da Ibi a kan hanyar Mokwa zuwa New Bussa a Ƙaramar Hukumar Borgu. Wata majiya ta ce Niworo tare da wasu ciki har da wani lauya, Barista Ahmad, na kan hanyarsu zuwa Minna ne lokacin da ’yan bindigar suka tare hanyar, suka kuma yi awon gaba da su cikin daji. Wasu daga cikin waɗanda aka sace ’yan kasuwa ne da suka fito daga kasuwar mako ta New Bussa. Abin da ya faru a zaman...
    A lokacin, sun yi wa motar ‘yansanda ruwan harsasai yayin da ɗaya daga cikin jami’an ya ji rauni, amma an garzaya da shi asibiti. Ya ƙara da cewa daga baya ‘yan bindigar sun sake tare wata hanya a gaba, inda suka sace fasinjoji a motoci uku. Abiodun, ya ce an tura ƙarin jami’an ‘yansanda tare da sauran jami’an tsaro da mafarauta don bin sahun ‘yan bindigar, da nufin ceto waɗanda aka sace da kuma cafke masu laifin. A wani samame daban, Abiodun ya bayyana cewa rundunar ‘yansandan tare da mafarauta sun kai farmaki wani dajin da ake zargin maɓoyar masu garkuwa, a cikin dajin Kokolo da ke Ƙaramar Hukumar Magama. A lokacin arangamar da aka yi da ‘yan bindigar, an...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ce kawo yanzu bata samu ba ta samu rubutaccen shirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump kan Gaza ba. Mahmoud Mardawi wani babban jami’in kungiyar ta Hamas ya bayyana cewa har yanzu kungiyar ba ta samu daftarin shirin, wanda kafofin yada labaran Amurka suka wallafa bayanansa. Amma ya bayyana cewa tabas shirin wanda bai da garanti yana kusa da hangen nesa na Isra’ila. Dangane da furucin da Trump ya yi na kwance damarar kungiyar, ya fayyace cewa Hamas ba a taba amfani da makamanta ba da nufin kai hari ba, sai dai kawai domin kare ‘yancin cin gashin kan Falasdinu. Mardawi ya soki shirin na Trump, yana mai imani cewa wani yunkuri ne...
    Jami’an Isra’ila da dama da suka hada da Ministoci masu tsattsauran ra’ayi irin su Itamar Ben-Gvir da Bezalel Smotrich, sun soki Firaminista Benjamin Netanyahu kan neman gafarar Qatar bayan harin da gwamnatin Tel Aviv ta kai kan shugabannin Hamas a kasar a ranar 9 ga watan Satumba. Netanyahu ya nemi uzurin ne a wata ganawa tsakaninsa da shugaban Amurka, lokacin da Netanyahu ya kira firaministan Qatar, inda ya bayyana cewa Tel Aviv ta yi nadamar harin da aka kai ta sama. Kiran da Netanyahun ya yi ta wayar tarho ya jawo suka daga jami’an Isra’ila, ciki har da minista mai tsatsauran ra’ayi Itamar Ben-Gvir, wanda ya kira harin “mai muhimmanci.” A cikin wani sako a shafin X, Ben-Gvir ya sake...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya soki Amurka da kasashen Turai nan uku na (E3) kan haifar da koma baya a yarjejeniyar nukiliyar 2015 ta hanyar mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran. Mista Araghchi ya yi wadannan kalamai ne, yayin ganawa da babban sakataren MDD Antonio Guterres, Ya kira sake sanya takunkumin a matsayin wani abin da ba a taba ganin irinsa ba ga harkokin diflomasiyya, kuma alama ce ta rashin kyakkyawar fata daga bangaren kasashen da abin ya shafa. Ministan harkokin wajen na Iran ya yi Allah wadai da matakin da Amurka da manyan kasashen Turai suka dauka, yana mai cewa hakan bai dace ba kuma ba bisa ka’ida ba ne. A ranar 19 ga watan...
    Shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina ya sanar da korar daukacin mambobin gwamnatinsa biyo bayan mummunar zanga-zangar da aka shafe kwanaki ana yi a kasar. A wani jawabi da ya yi na tsawon mintuna 17, ranar Litini, , Andry Rajoelina ya sanar da cewa ya ji kiran matasa tare da korar firaministansa da gwamnatinsa. Ya fara jawabinsane da jajanta wa wadanda suka rasa yan uwa da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Da yake jawabi ga matasan da suka fusata, ya bayyana cewa: “Na saurari muryoyinku, da bukatunku, Kuma ina ba da hakuri idan akwai mambobin gwamnati da ba su yi aikin da mutane suke tsammani […].” Shugaban ya bayyana a gidan talabijin na kasar cewa, “A bisa...
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci jihohin Arewa 19 da su tsaya ƙyam su jajirce su yi magana da murya ɗaya kan harkokin tsaro da tattalin arziki. Gwamnan ya jagoranci taron ranar farko ta bangaren Zuba Jari da Bunƙasa Masana’antu ta Arewacin Nijeriya a ranar Litinin a otel ɗin Abuja Continental. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa Ƙungiyar Dattawan Arewa ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi ce ta shirya taron zuba jarin. Sanarwar ta ƙara da cewa, taken taron shi ne “Buɗe Dabarun Damarmaki”, kuma ya tattaro duk masu ruwa da tsaki a sassan Arewacin Nijeriya. A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya yaba wa Ƙungiyar Dattawan Arewa bisa jajircewar da...
    Mutanen gari sun kama mutum uku da ake zargin suna da hannu a harin da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Ƙadisau da ke Ƙaramar Hukumar Faskari da ke Jihar Katsina. Al’ummar yankin ne suka kama mutanen suka damƙa su ga jami’an tsaron al’umma na jihar domin gudanar da bincike. Yankin Ƙadisau da kewaye ya sha fama da hare-haren ’yan bindiga waɗanda suka kashe mutane da dama suka jikkata wasu tare da sace dabbobi masu yawa. Na baya-bayan nan shi ne wanda mahara suka kashe mutane uku suka yi garkuwa da mata biyar sannan suka yi awon gaba da dabbobi da ba san adadinsu ba. Abin da ya faru a zaman sulhun PENGASSAN da Matatar Ɗangote Netanyahu ya ba da haƙuri...
    Mahukuntan Taliban a Afghanistan sun sanar da rufe dukkanin hanyoyin sadarwa a fadin kasar, makonni bayan da suka fara katse intanet, domin hana abin da suka bayyana a matsayin tabarbarewar tarbiyya. Wata kungiya mai sa ido kan harkokin yanar gizo ta ce yanzu baki ɗaya ana fama da rashin intanet a kasar. Wani jami’in Taliban ya ce rufewar za ta ci gaba har sai an bayar da wata sanarwa a nan gaba. Shugaban Taliban, Hibatullah Akhund-zada, ya bayar da umarnin fara cire wayoyin sadawar dake ƙarkashin kasa na intanet tun a farkon wannan wata. BBC ta rawaitu cewar kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce ya rasa ji ta hanyoyin sadarwa daga ofishinsa na Kabul, ciki har da ta wayar...
    Gwamnatin tarayya ta soke bikin faretin da aka shirya gudanarwa domin murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba. Wannan sanarwar ta fito ne a ranar Litinin daga Ofishin sakataren gwamnatin tarayya. “Soke faretin bikin ƴancin kai da gwamnati ta shirya gudanarwa a ranar Laraba, 1 ga Oktoba ba zai rage darajar wannan muhimmiyar rana ta tarihi ba,” in ji sanarwar. Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati na ba da haƙuri kan wannan sauyi, amma sauran ayyukan da aka tsara domin zagayowar ranar za su ci gaba kamar yadda aka tsara. Wannan ya haɗa da jawabin shugaban ƙasa, bukukuwan al’adu, da wasu abubuwa da aka shirya.
    Ƙungiyar manyan ma’aikatan kamfanonin iskar gas da fetur PENGASSAN ta ce tana nan kan bakarta na ci gaba da yajin aiki bayan kasa samun maslaha tsakaninta da matatar Dangote. Bangarorin biyu sun tashi baran-baran a tattaunawar da suka yi karkashin jagorancin ministan kwadago na Najeriya Mohammed Dingyadi a ranar Litinin. A ranar Litinin ne ƙungiyar PENGASSAN ta shiga yajin aiki na sai baba ta gani saboda matakin matatar Dangote na korar wasu ma’aikatanta kimanin 800. Babu dai wata sanarwa daga ɓangaren Matatar Dangote bayan tattaunawa da kungiyar PENGASSAN, amma a sanarwar da ta fitar ranar Lahadi ta ce ta sallamar ma’aikatan ne a wani mataki na ƙoƙarin daidaita tsarin aikin matatar. Matatar Dangote ta kuma bayyana matakin yajin aikin PENGASSAN...
    Sudan ta fitar da gargaɗin gaggawar samun ambaliyar ruwa a jihohi biyar bayan matakin ruwa a Kogin Nilu ya ƙaru kamar yadda rahoton gidan jaridar gwamnati Suna ya ruwaito. Rahotanni sun danganta ƙaruwar matakin ruwa da babban dam ɗin Ethiopia da aka buɗe a wannan watan. Ma’aikatar nomar rani ta Sudan ta sanar da gargadin ne a ranar 28 ga watan Agusta, inda ta ce ya shafi jihohin Khartoum da River Nile da White Nile da Sennar da kuma Blue Nile. Ma’aikatar ta yi gargaɗin cewa ruwa na iya mamaye gidaje da gonaki, tare da kira ga ɗaukar matakan gaggawa. Farfesa Abbas Sharaky na jami’ar Cairo, masani a fannin ƙasa da albarkatun ruwa, ya bayyana cewa ƙaruwar matakin ruwa a...
    Gwamnatin Tarayya ta sanar da gobe Laraba a matsayin ranar hutu a ƙasar somin bikin cikar ƙasar shekara 65 da samun ƴancin kai. Cikin wata sanarwa da ministan cikin gida na ƙasar, Olibunmi Tunji-Oja ya fitar, ya taya ƴan Najeriya murnar cimma wannan ”babban matsayi”. Ministan ya kuma buƙaci ƴanƙasar su ci gaba da nuna kishin ƙasa da hadin kai da juriya, waɗanda ya ce su ne ke taimaka wa ƙasar wajen dunƙulewa tun lokacin samun ƴancin kai a 1960. A ranar 1 ga watan Otoban 1960 ne dai Najeriya ta samun ƴancin kai daga Turawan mulkin Birtaniya da suka yi mata mulkin mallaka.
    Shugaban hukumar kula da fice ta kasa iran frud askari ya bayyana cewa yawan adadin huldar kasuwancin na kasashen waje na kasar iran yana ci gaba da gudana tsakaninta da fiye da kasashen duniya 100. Kuma yawansa ya kai dala biliyan 54.311a cikin wata shidan farko na wannan shakarar. Da yake hira da manema labarai ya fadi cewa a cikin wannan lokacin an samu kudi da yawansu yakai dala biliyan 25 da miliyan 944 a kayayyakin da ba na man fetur ba. Yace yawan kayayyakin da aka fitar a tsawon wannan lokaci ya kai tan miliyan da dubu 997, yayin da nauyin kayayyakin da aka shigo da su kuma ya kai tan miliyan dubu 18 zuwa 757. Da yake kwatantan...
    Gwamnatin Tarayya ta wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima NYSC. Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka kammala karatu. Bisa haka, daga yanzu babu ɗalibin da za sahalewa zuwa NYSC ba tare da ya miƙa takardar shaidar kammala binciken karshe na kammala digirinsa ba. Gwamnatin Tarayya ta ce hakan zai taimaka wajen yakar matsalar amfani da takardun kammala karatu na bogi da kuma adana ilimi...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban mai ba da shawara kan harkokin soji ga Imam Khamenei ya bayar da rahoton cewa, a kalla matukan jirgi 16 na sojojin gwamnatin sahyoniyawan ne aka kashe sakamakon harin makami mai linzami da Iran ta kai a yakin kwanaki 12. Babban mai baiwa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara kan harkokin soji Manjo Janar Seyed Yahya Safavi ya bayyana a jiya Litinin game da yakin kwanaki 12 da gwamnatin yahudawan sahyuniya suka yi, inda ya ce kamar yadda Amurka da Isra’ila suka gaza cimma manufarsu a yakin da aka yi musu, su ma ba su yi nasara ba a wannan yakin. A cewar Manjo Janar Safavi, a yayin wannan yakin, Iran ta harba makamai masu linzami sama da 500...
    A ranar Talatar nan ake sa ran ci gaba da tattaunawa tsakanin Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur (PENGASSAN) da Kamfanin Matatar Man na Ɗangote kan taƙaddamar da ke tsakaninsu. Ana sa ran za a ci gaba da zaman sulhun, wanda Gwamnatin Tarayya ta kira domin sasanta ɓangarorin ne zuwa da yamma. Hakan ta faru ne bayan an tashi taron a cikin tsakar daren ranar Litinin ba tare da an cimma wata matsaya ba. Gwamnatin Tarayya ta kira zaman sulhun ne bayan ƙungiyar PENGASSAN ta zargi Kamfanin Ɗangote da kora da kuma sauyin aikin mambobinta kimanin mutum 800. PENGASSAN ta yi barazanar yajin aiki muddin ba a dawo da ma’aikatan ba, a yayin da kamfanin ke cewa ga sallame su ne...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ɗangote, PENGASSAN Ba Su Yi Ba Don Magance Rikicinsu DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke cikakken shirin, latsa nan
    Buƙatun da ASUU ke nema sun haɗa da: sake duba yarjejeniyar 2009 tsakaninsu da gwamnati, samar da ƙarin kuɗaɗen bunƙasa jami’o’i, biyan bashin albashin da suke bi, da samar da ingantaccen tsarin kuɗi mai ɗorewa ga jami’o’i. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ba wa Gwamnatin ƙasar Qatar haƙuri kan harin da ƙasarsa ta kai a birnin Doha, wanda ya yi ajalin wani jami’in tsaron Qatar. Netanyahu ya bayar da haƙuri ne a yayin wata tattaunawa da shugaban Amurka, Donald Trump ya shirya tsakaninsu da Fira Ministan Qatar, Mohammed Al-Thani. A saƙon da Netanyahu ya wallafa a X, ya ce, “Mai girma Fira Minista, ina sanar da kai cewa Isara’ila ta yi nadamar abin da ya faru na rasuwar wani ɗan ƙasarka a  harin da muka kai,” da makami mai linzamina ranar 9 ga watan Satumba a birnin Doha. Fadar White House ta Amurka da Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar Qatar sun tabbatar da tattaunawar, wadda Shugaba Donald...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a fadar White House jiya litinin cewa, yana fatan samun zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya. Trump ya sanar da kaddamar da abin da ya kira “Ka’idojin Zaman Lafiya” a hukumance, tare da yin la’akari da abin da ya kira  amincewar shugabannin kasashen Larabawa da na musulmi tare da tabbatar da goyon bayansu ga shirinsa na samar da mafita a zirin Gaza, in ji shi. A cikin cikakkun bayanai kan shirin da Trump ya gabatar, za a saki dukkan fursunonin Isra’ila a zirin Gaza cikin sa’o’i 72 idan Hamas ta amince da shawarar. Shugaban na Amurka ya...
    An zartar da hukuncin kisa a kan daya daga cikin manyan ma’aikatan leken asiri a Iran da ke aiki da hukumar leken asiri ta gwamnatin Isra’ila, Mossad, kamar yadda ma’aikatar shari’a ta Iran ta tabbatar. An zartar da hukuncin ne a kan Bahman Choubi-Asl a ranar Litinin bayan samunsa da laifin haɗa  kai tare da hukumar  leƙen asiri ta  Isra’ila a fagen tattara bayanai. Ya kasance kwararre kan harkokin bayanai wanda ya shigo cikin muhimman ayyukan sadarwa na kasar ta hanyar kasancewarsa a wani kamfani na ayyukan kimiyya da fasaha. Saboda kwarewarsa ya kasance a matsayin manaja a cikin dukkanin ayyukan kamfanin kuma yana da damar samun mahimman bayanai na kasar. A cewar rahotannin bangaren shari’a, jami’an Mossad sun fara...
    Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nemi afuwar firaministan Qatar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani a ranar Litinin din nan kan harin da jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka kai kan Qatar a baya-bayan nan wanda ya yi sanadin mutuwar wani jami’in tsaron Qatar, kamar yadda wata majiya mai tushe ta shaida wa Axios. An bayar da rahoton neman afuwar a yayin ganawar Netanyahu da shugaban Amurka Donald Trump, kuma ana kallon shi a matsayin wani muhimmin sharadi da Doha ta gindaya na sake tattaunawa da Hamas a kan yarjejeniyar da za ta kawo karshen yakin Gaza da kuma sako sauran mutanen da aka yi garkuwa da su. Bayan ganawar, fadar White House ta tabbatar da cewa Netanyahu ya bayyana matukar...
    Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, wanda ya ziyarci kasar Lebanon domin halartar bikin zagayowar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah, ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem. Babban labarin jaridar Pars Today na cewa, Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem a ranar Lahadin da ta gabata. A wajen taron, Larijani ya jaddada goyon bayan Iran ga kasar Labanon da tsayin daka, inda ya yi misali da umarnin Imam Khumaini da Ayatullah Khamenei Jagoran juyin juya halin Musulunci tare da goyon bayan gwamnati da al’ummar Iran. Ya jaddada cewa Iran a shirye take ta ba da tallafi ga Lebanon da juriya “a kowane...
    Masana’antar kera makamai ta srael, wacce aka dade ana daukarta a matsayin daya daga cikin manyan ginshikan tattalin arzikin gwamnatin da kuma wani muhimmin makami na amfani da siyasarta, a yanzu na fuskantar kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba. A cewar Pars Today, yayin da yake ambato Kamfanin Dillancin Labarai na Fars, yayin da wannan masana’antar ta taka muhimmiyar rawa wajen samarwa Tel Aviv kudaden shiga na tattalin arziki da kuma karfin diflomasiyya, wani sabon takunkumi na takunkumi da soke kwangilar soji ya haifar da babbar inuwa ga makomarta. Soke kwangilolin Yuro biliyan ta Turai A cewar jaridar Calcalist ta kudi ta Isra’ila, a cikin ‘yan watannin nan – karkashin matsin lambar jama’a da zanga-zangar adawa da yakin...
    Malaman Kwalejin Kimiyya da Ƙere-ker ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a Jihar Kaduna sun tsunduma yajin aiki. Ƙungiyar Malaman Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere (ASUP) reshen makarantar ta fara yajin aikin ne daga yau Talata, 39 ga Satumba, 2025. Ƙungiyar ta fara yajin aikin ne bayan zaman da ta yi da wakilan gwamnatin jihar, inda Babban Sakataren Gwamnatin Jihar, ya buƙaci su ƙara haƙuri, yana mai alamta cewa Gwamna Uba Sani ya ba da izinin biyan buƙatunsu. Sanarwar da Kwamared Usman Shehu Suleiman ya sanya wa hannu ta ce, “Daga Talata , 30 ga Satumba 2025 mu fara yajin aiki har sai abin da hali ya yi.” An shiga taron gaggawa kan takun saƙar PENGASSAN da Matatar Dangote ASUU ta...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An sanar da wannan matakin ne a yau 29 ga watan Satumba, 2025 a karkashin dokokin FIFA, amma kuma har yanzu SAFA suna da kwanaki goma domin daukaka kara a gaban kwamitin daukaka kara na FIFA.   Tawagar Afirka Ta Kudu wadda Hugo Broos ke jagoranta a halin yanzu suna kan gaba a rukuninsu na C na neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya, bayan da suka samu maki 17 daga wasanni takwas, amma kuma yanzu makin ya rikito zuwa 14 sakamakon zabtare maki 3 da hukumar FIFA ta yi musu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
    Yau Litinin ofishin ‘yan jarida na kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai don bayyana nasarorin da Sin ta samu a fannin ban ruwa a lokacin “shirin raya kasa na 14 na shekaru biyar” . Minista mai kula da harkokin ban ruwa Li Guoying ya bayyana cewa, tun daga farkon shirin, Sin ta fara samun ci gaba mai yawa a fannin gina kayayyakin ban ruwa. A shekarar 2022, kudaden da aka kashe wajen gina ayyukan ruwa sun kai sama da RMB yuan tiriliyan 1 a karon farko, kuma sun ci gaba da kafa tarihi har tsawon shekaru 3. A shekarar 2024, kudaden sun kai tiriliyan 1.3529 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 190. Kuma ana sa ran yawan kudaden da za...
    Yau 29 ga wata, an gudanar da bikin karfafa hadin gwiwa tsakanin babban rukunin gidajen rediyo da talibiji na Sin wato CMG, da mabambantan bangarori na yankin Hong Kong. Jagoran yankin musamman na Hong Kong John Lee Ka-chiu ya bayyana cewa, idan aka waiwayi tarihi, gwamnatin Hong Kong da CMG sun kasance suna hadin gwiwa sosai da juna. Sun yi hadin gwiwa da juna a fannonin ba da rahotannin manyan bukukuwa, da fadakar da al’ummu manufofi masu muhimmanci, da daidaita al’amura na gaggawa. Bikin karfafa hadin gwiwa na yau ya alamanta sabon babin hadin gwiwar CMG da al’ummar Hong Kong. Jerin matakan da aka dauka, ba ma kawai sun dace da manufofin kasa ba, sun kuma amsa bukatun al’ummar Hong...
    Shugabannin ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) da wakilan Matatar Dangote na halartar wani taron gaggawa tare da wakilan Gwamnatin Tarayya. Shugaban ƙungiyar PENGASSAN, Festus Osifo, tare da Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (TUC), Nuhu Toro, ne ke jagorantar ɓangaren ƙungiyoyin ƙwadago, yayin da Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Maigari Dingyadi da wasu jami’ai ke wakiltar Gwamnatin Tarayya. Ya zama tilas ɗalibai su gabatar da ‘Project’ kafin rajistar NYSC — Tinubu Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Laraba Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Lahadin da ta gabata ce Gwamnatin Tarayya ta gayyaci shugabannin PENGASSAN da na ɓangaren Matatar Dangote zuwa wannan taro sakamakon rikicin da ke tsakanin ɓangarorin biyu. Sai dai, duk da...
    A taƙaitaccen hukuncin da ya yanke kan ƙarar, Mai shari’a Subilim ya bayyana cewa, ci gaba da yajin aikin zai lalata kasuwancin matatar da gurgunta mafi mahimmancin ayyukan ci gaban tattalin arzikin al’ummar Nijeriya.   Alƙalin kotun ya ce, dokar hana ci gaba da yajin aikin za ta ci gaba da aiki har tsawon kwanaki bakwai ne kacal. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wata hira da gidan talabijin din Aljazeera yayi da sakataren cibiyar kula da yan gudun hijira a kasar Nowy ya fadi cewa babban abin da yake damunsu shi ne inda duniya ta yi shiru kan abubuwan da ke faruwa a Gaza inda israa’ila ke kisan kiyashi. Dubban daruruwan alummar Gaza ne suka tarwatse  da suke fuskantar tsananin bala’I kamar jan Egeland yadda ya bayyana, yace dole ne a a dakatar da kisan kiyashin da isra’ila ke ci gaba da yi a Gaza, Haka zalika ya nuna damuwar sosai game da gum da baki da majalisar dinkin duniya ta yi akan batun gaza, babban abin da muwar shi ne yadda duniya take nuna halin ko in kula da abin da...
    Shugaban kasar Iran mas’ud pezishkiyan ya bayyana a wajen taron ranar yan kwana-kwana ta kasa da aka gudanar a ranar litinin a birnin Tehran cewa yayi tir da takunkumin da kasashen turai suka sake kakabawa iran, yace duk wani kokarin durkusar da kasar iran ba wani abu bane face mafarkin tsaye. Shugaban ya kara da cewa an yi amfani da sanya takunkumin ne don kara matsin lambar siyasa kan kasar iran da kuma wulakanta ta,amma tuni gwamnati ta bullo da dabaru acikin gida na nuna cirjiya kan takunkumin. Matakin na kasashen turai kan kasar iran yazo ne adaidai lokacin da ake cikin mawuyacin yanayi a yanki, da kuma nuna harshen damo game da rikicin dake faruwa a yankin Gaza ,...
    Shugaba Bola Tinubu ya amince da sabon tsari da ya danganci rajistar masu bautar ƙasa (NYSC) da manufofin hukumar da ke tattara bayanai kan ilimi wato NERD. A yanzu dai babu ɗalibin Nijeriya – daga jami’a ko kwalejin kimiyya da fasaha ko kwalejin ilimi, ko jami’o’in ƙasashen waje – wanda za a amince don samun damar shiga ko samun hutu daga aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC) ba tare da kiyaye sharaɗin da NERD ta shar’anta ba. Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Laraba Ɗalibar jami’ar IBB ta faɗi ta rasu A ƙarƙashin sabon tsarin wanda zai soma aiki daga 6 ga watan Oktoba, NERD ta wajabta cewa a yanzu rajistar ɓautar ƙasa tana ta’allaƙa ne da miƙa aikin binciken...
      Ya bayyana cewa, bin wannan ƙa’idojin yana da matukar muhimmanci domin bai wa hukumar damar tattara sahihin jerin sunayen maniyyata da kuma tura dukkan kuɗaɗen zuwa ga hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) a kan lokaci.   Ya shawarci maniyyatan da suka kammala biyan kudadensu da su miƙa takardunsu na tafiya cikin gaggawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masana’antar raya al’adu ta kasar Sin, ta samu ci gaba bisa daidaito yayin shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, wanda aka gudanar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025. A cewar mataimakin ministan ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido na kasar Sin Lu Yingchuan, a shekarar 2024, darajar jimillar kadarorin sashen ta kai yuan tiriliyan 34.4, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 4.84. Lu wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, yayin taron manema labarai, ya ce tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, Sin ta kuma cimma manyan nasarori a fannin bunkasa tasirin al’adunta. Ya ce a shekarar ta 2024, jimillar adadin cinikayya a fannin al’adu na Sin ya kai yuan tiriliyan 1.4, inda karin abubuwan sayayya a fannin da...
    Gwamnatin Nijeriya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025 a matsayin ranar hutu albarkacin cikar ƙasar shekaru 65 da samun ’yancin kai. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a madadin Gwamnatin Tarayya. Ɗalibar jami’ar IBB ta faɗi ta rasu FERMA ta ƙaddamar da aikin gyara tsohuwar hanyar Kano Tunji-Ojo ya taya ’yan Najeriya da ke zaune a nan cikin gida da ƙetare murnar zagayowar wannan rana mai tarihi, kamar yadda babbar sakatariyar ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Magdalene Ajani ta bayyana a ranar Litinin. Ministan ya roƙi ’yan Nijeriya da su ci gaba da rungumar kishin ƙasa, haɗin kai da kuma juriya, domin a cewarsa, su ne ababen...
    Wata ɗalibar aji biyu a sashen nazarin ƙwayoyin halittu da sunadarai na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai da ke Jihar Neja ta riga mu gidan gaskiya. Aminiya ta ruwaito cewa, Fatima Adamu Muhammad, ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta faɗi a wani matsuguninta da ke wajen makarantar. ASUU ta bayar da wa’adin tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya FERMA ta ƙaddamar da aikin gyara tsohuwar hanyar Kano Rahotanni sun ce ta fara ƙorafin cewa ba ta jin daɗin jikinta da alamu na rashin lafiya, inda daga daga bisani ta yanke jiki ta faɗi. Sai dai bayan an garzaya da ita asibitin gwamnati na Lapai, likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi mata halinsa. Fatima Adamu Muhammad,...
      Idan dai ba a manta ba, gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar ilimi ta tarayya ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin babban sakataren ma’aikatar, Abel Enitan, domin duba buƙatar ƙungiyar ASUU, a wani yunƙuri na tabbatar da ci gaban jami’o’in.   Sai dai har yanzu kwamitin bai fitar da wata sanarwa ko sakamakonsa ga jama’a ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da yammacin yau Litinin ne ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya gudanar da taron nazari karo na 22, kan yadda za a sa kaimi ga mayar da addinan Sin zuwa addinan dake da salo na kasar. Yayin da ya jagoranci taron, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada cewa, “Ya kamata mu tattara, da kuma amfani da darussan tarihi, mu mayar da hankali kan hakikanin ayyukan addinai na kasa, da sa kaimi ga mayar da addinan Sin zuwa addinan dake da salo na kasar, da kuma jagorantar addinai don daidaita al’umma mai ra’ayin gurguzu”. Xi Jinping ya kara da cewa, ana bukatar sa kaimi ga dunkulewar addinan kasar Sin, tare da kyawawan al’adun gargajiya na kasar bisa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar kula da gyaran manyan hanyoyi ta ƙasa (FERMA) reshen Jihar Kaduna, ta ƙaddamar da aikin gyaran tsohuwar hanyar Zariya zuwa Makarfi wadda ta haura zuwa Kano. Aikin zai haɗa da tono ciyayi, cike ramuka, da yashe magudanan ruwa tare da samar da ayyukan yi na wucin gadi ga matasa da ke yankin. ’Yan sanda sun kama kwayoyin N165.4m da makamai a Kano ASUU ta bayar da wa’adin tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya Da yake ƙaddamar da shirin a Basawa, Zariya, shugaban FERMA na jihar Kaduna, Injiniya Kabir Iliyasu Danmarke, ya bayyana cewa aikin umurni ne daga shugaban hukumar na ƙasa, Dr. Chuku Emeka Obasi, bisa kudurin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na rage haɗurra a hanyoyi. “Mun ɗauki...
    Sanarwar ta ce, wadannan hare-haren sun sake tabbatar da aniyar NAF na kare jami’an tsaro da fararen hula, da kuma ci gaba da matsin lamba kan masu tada kayar baya.   Ya kara da cewa, duk hare-haren an kammala su cikin nasara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yanzu haka dai akwai jami’o’i da kwalejoji da cibiyoyi da dama da ake koyar da harshen mandarin a kasashen Afirka. Yayin da dalibai masu koyon harshen Mandarin suke ta karuwa a kullum. Misali a kasar Uganda akwai cibiyar koyar da harshen Mandarin wadda ta fara da dalibai 30 a shekara goma da ta gabata, amma a yau tana da sama da dalibai 400. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni biyu domin tsunduma yajin aiki muddin ta ci gaba da sakaci kan wasu buƙatu da take nema a biya. A sanarwar gargaɗi da ASUUn ta fitar yau Litinin, ta ce daga jiya Lahadi, 28 ga watan Satumba, za ta bai wa gwamnatin wa’adin kwanaki 14 domin ta karkata akala kan buƙatun da take nema, ko kuma ta tsunduma yajin aikin gargaɗi na makonni biyu, inda daga nan zai rikiɗe zuwa na sai baba ta gani. An sallami Kwamishinar Mata ta Jihar Bauchi daga aiki ’Yan sanda sun kama kwayoyin N165.4m da makamai a Kano Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da...
    Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya, wato PENGASSAN, ta fara yajin aiki a faɗin Nijeriya daga daren Litinin, 29 ga Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan umarnin da shugabancin ƙungiyar ya bayar tun ranar Lahadi, inda aka umurci mambobi da su tsaida aiki a dukkan kamfanoni da cibiyoyi da hukumomin da suke aiki a su. A sakamakon haka, an kulle ƙofar shiga shalƙwatar hukumar NUPRC da ke Abuja, inda ɗaruruwan ma’aikata suka taru a waje ba tare da an bari sun shiga ba. Wannan mataki ya haddasa tsaiko a gudanar da ayyuka, musamman a sashen kula da harkokin mai da iskar gas na ƙasar. Rikicin Dangote Da PENGASSAN Ba Zai Kawo Wahalar Fetur Ba Majalisa Ta...
    ’Yan sanda sun kama miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira miliyan 165.4 a watan nan na Satumba a Jihar Kano. Daga ciki, jami’an rundunar sun kama kwayoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 82.7 a unguwar Rimin Auzinawa, suka mika ga Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) domin kammala bincike da gurfanarwa a gaban kuliya. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa rundumar ta kuma kama kwayoyin Tramadol da kudinta ya kai Naira miliyan 60.3 da kwayar Pregabalin ta Naira miliyan 22.4 da kuma sinki 523 na tabar wiwi da injinan tura kudi na POS guda biyar daga hannun wadanda ake zargi a sassan jihar. Kwamishinan ya ci gaba da cewa rundunar ta kama...
    Shigowar Ganduje Da Sauya Mallaka A Asirce Sakamakon barazanar soke yarjejeniyar ya sa dole wanda ya kafa kamfanin, Ahmad Rabiu, ya nemi sabon abokin tarayya. A cikin wannan lokacin ne, a ranar 5 ga Maris, 2020, aka gudanar da wani taro na musamman na kamfanin Dala Inland Dry Port. A cikin wannan taron, an cire duk tsoffin daraktocin kamfanin, an kuma naɗa ƴaƴan Ganduje uku da wani ɗan nasa na kut da kut mai suna Abubakar Bawuro, a matsayin sabbin daraktoci. An ba kowane ɗaya daga cikin ƴaƴan Ganduje hannun jari na kashi 20% kowanne, haka kuma aka ba Bawuro da Rabiu kashi 20% kowanne. Wannan shi ne lokacin da aka cire Jihar Kano gaba ɗaya daga cikin masu mallakar...
    Kwamitin harkokin waje da tsaron kasar Iran ya kammala dukkan shirye shirye na ficewar kasar daga yarjeniyar NPT ta hana yaduwar makaman nukliya ko na kissan kare dangi. Isma’il Riza’e shugaban kwamitin ya fadawa ya fadawa tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran kan cewa, kwamitinsa ya kammala shiri na dukkan takardu da tsare-tsaren da ake bukata don ganin kasar Iran ta fice daga yarjeniyar NPT ta hana yaduwar makaman Nukliya saboda kasashen Turai sun maida dukkan takunkuman tattalin arzikin da MDD ta dorawa kasar. Iran a Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0...
    An kashe sojan HKI guda a safiyar ranar Lahadi bayan da wani ba falasdine mai tuka babbar mota ya Burma motarsa kan gungun sojojin HKI a wani yanki kusa da Qalqelia na yankin yamma da kogin jorda. Ya kara da cewa kafin haka sojojin HKI sun kashe Falasdinawa da dama a yankin yamma da kogin Jordan kuma sun ci gaba da kisa da kuma rusa gidajen mutane a yankin tun bayan fara yakin tufanul Aksa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nalaklto majiyar yahudawan na cewa sojan da aka kashen shi ne Staff Sergeant Inbar Avraham Kav , dan shekara 20 a duniya daga rundunar battalion ta 890. Yan kwana-kwana sun dauke shi zuwa asbita amma likitoci sun...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa bukatun gwamnatin Amurka daga kasar Iran ba abar amincewa ba ne. Shugabany a bayyana haka ne a ranar Asabar kafin ya bar birnin Newyork zuwa Tehran bayan ya halarci taron babban zauren MDD na shekara shekara. Yace: Bamu daidaita da su kan snapback ba, sai Amurka tace mu mika mata dukkan makamashin Uranium da muka tashe, su kuma zasu bamu damar watannin uku kacal na Rashin takunkuman tattalin arziki, sannan su sake dawo da su. Shugaban yace wannan ba zai taba yiyuwa ba. Ya ce kasashen turai sun zama mabiyan Amurka kawai, ba zasu iya yin wabu batare da amincearta ba. Ya kuma kara da cewa mun cimma yarjeniya da kasashen turai,...
    Mohammad Bakir Qalibof kakakin majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa abinda kasashen turai uku suka yi na amfani da Snapback baya bisa ka’ida kuma Iran ba zata kiyayesu ba. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa kasashen Rasha da China wadanda suka kasance mambobi na din din din a kwamitin tsaro na MDD sun tabbatar da cewa abinda turawan suka yi baya bisa ka’ida. Ya ce idan wadannan kasashe da Amurka suka dauke wani bataki kan Iran, iran zata maida martini mai tsanani a kansu. Qalibof ya bayyana cewa kasashen sun yi amfani da tattaunawa da a matsayin makami don cimma manufarsu da durkusarwa da...
    Jami’an tsaron kasar Burtania sun kama George Gallaway da matar a birnin londan bayan sun shigo kasar daga kasar Rasha a ranar Asabar. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya bayyana cewa Gallawy da matarsa sun shahara da goyon bayan gwagwarmayan falasdinawa da kuma kiyayya ga HKI. Kafin haka gwamnatin kasar Burtania ta amince da samuwar kasar Falasdinu a babban taron MDD, amma amincewar samuwar kasar falasdinu bai hana ci gaba da kissan falasdinawa. Gallawy wanda ya kasashence tsohon dan majalisar dokokin kasar burtaniya, ya kuma karbi kyautar Isma’il Haniyya. Sannan a cikin watan bayun shekara da 2025 inda ya halarci bikin cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar IRAN. Yansandan kasar Burtania sun tsare...
    Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka kammala karatu. Wannan yana daga cikin sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda ya alaƙanta aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) da Tsarin Tattara Bayan Ilimi ma Kasa (NERD). Ranar Laraba jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki  Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba gyara titin Kano–Maiduguri ba Bisa...
    Hukumar lura da jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta tabbatar da cewa daga ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, za a dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasa na fasinjoji a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Wannan na zuwa ne bayan dakatar da tafiye-tafiye a watan Agusta sakamakon hatsarin da ya rutsa da ɗaya daga cikin jiragen. A cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Callistus Unyimadu, ya fitar, NRC ta ce matakin ya nuna jajircewarta wajen tabbatar da tsaro da kuma inganycin sufuri ga ’yan ƙasa. Hukumar ta bayyana cewa ranar Laraba za ta kasance rana ta Musamman domin yin gyara a kan layin jirgin don gujewa matsaloli a nan gaba. NRC Ta Dakatar Da Sufurin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta koma kan teburin gasar Laliga bayan doke Real Sociedad da ci 2-1 a wasan da suka buga ranar Lahadi. Joules Kounde da Robert Lewandowski ne suka zura ƙwallayen biyu da suka tabbatar da nasarar. Da wannan sakamako, Barcelona ta tattara maki 19 daga wasanni bakwai, tana da tazarar maki daya da Real Madrid wadda ta sha kashi a hannun Atletico Madrid da ci 5-2 a ranar Asabar. Masu riƙe da kofin gasar, Barcelona, na fatan lashe Laliga karo na biyu a jere tun bayan shekarun 2017/2018 da 2018/2019. Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff Atletico Madrid Ta Zazzaga Wa Real Madrid Ƙwallaye 5 A Metropolitano Haka kuma,...
    Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa da ƴan Nijeriya cewa za a ci gaba da samun isasshen man fetur duk da barazanar shiga yajin aiki da ƙungiyar PENGASSAN ta yi kan taƙaddama da matatar man Dangote. Wannan na zuwa ne bayan raɗe-raɗin cewa matatar ta dakatar da tsarin siyar da ɗanyen mai da ake biya sa da Naira. A wata sanarwa daga ma’aikatar kuɗi ta tarayya, daraktan hulɗa da jama’a Mohammed Manga ya bayyana cewa an gudanar da taron kwamitin kula da tsarin “buyqn Naira-don sayen ɗanyen mai” ƙarƙashin jagorancin Ministan Kuɗi, Wale Edun. Taron ya samu halartar Ministan tsare-tsare, da shugaban FIRS, da wakilai daga NNPC, CBN, NMDPRA da Afreximbank. Matatar Dangote Ta Dawo Sayar Da Man Fetur A Kuɗin...
    Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi, ya sallami Kwamishinar Harkokin Mata da Ci-gaban Yara, Zainab Baban Tanko. Sanarwar da kakakin gwamnan, Mukhtar Giɗaɗo, ya fitar ta bayyana cewa sallamar ta fara aiki ne nan take. Ya bayyana cewa hakan ta faru ne a sakamakon sauye-sauye a majalisar zartarwa ta Jihar Bauchi. Ya bayyana godiyar Gwamna Bala ga tsohuwar Kwamishinar bisa gudummawar da ta bayar ga ci-gaban jihar, tare da yi ,ta fatan alheri.
    Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka yi karatu. Wannan yana daga cikin sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda ya alaƙanta aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) da Tsarin Tattara Bayan Ilimi ma Kasa (NERD). Bisa haka, daga yanzu babu ɗalibin da za sahalewa zuwa NYSC ba tare da ya miƙa takardar shaidar kammala binciken...
    A ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, jirgin ƙasan da ke jigilar fasinja tsakanin Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki. Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta ce jirgin farko a ranar zai baro tashar Idu da ke Abuja da ƙarfe 8.45 na safe, ya iso Kubwa 9.05 sannan ya sauka a tashar Rigasa da ke Kaduna da misalin 12.42 na rana. Daga Kaduna kuma jirgi zai baro Rigasa da misalin ƙarfe 2.30 na rana ya isa Kubwa da ƙarfe 8.40 na yamma. Sanarwar ta ƙara da cewa daga bisani za a ware kowace ranar Laraba domin aikin kula da lafiyar jiragen da ke aiki a layin na Abuja zuwa Kaduna. Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba...
    Shekara guda matafiya da direbobi a ƙauyukan Malori-Guskuri da Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi na ci gaba da fama da wahala bayan da ruwan sama ya karya babban titin Kano–Maiduguri. A ranar 7 ga Agusta, 2024 ne ruwa ya cinye babbar hanyar a Malori-Guskuri, ya kuma yanke babban ɓangare na hanya. Mako guda bayan nan kuma wani ɓangaren ya rushe a Sabon Gari. Shekara guda da wata ɗaya bayan faruwar lamarin, wanda ya mayar wuraren da suka rushe sun koma tarkon mutuwa da ke haddasa haɗurra da suka kashe mutane da raunata wasu da dama. Wakilinmu da ya kai ziyara ya samu wani kamfanin gine-gine ya dawo Malori da kayan aikinsa. Mazauna sun tabbatar da...
      LEADERSHIP ta labaro cewa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya rantsar da Hajiya Zainab Baban Takko a matsayin Kwamishina ne a ranar 9 ga watan Satumban 2024 tare da wasu sabbin kwamishinoni biyu.   Kafin ta hau kan wannan kujerar, ta zama shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Bauchi wanda gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya naɗata a watan Yulin 2023. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A jiya Lahadi ne masu tafiyar da ayarin jiragen ruwan dake son keta killace Gaza ” Sumud” su ka sanar da cewa, tsakaninsu da yankin Gaza bai wuce kilo mita 825 Ba. Ayarin jiragen ruwan dai yana kunshe da kananan jiragen da sun kai 50, sun fuskanci hare-hare da jiragen sama marasa matuki na HKI da hakan ya haddasa yankewar hanyoyin sadarwa,ba tare da an sami asarar rayuka ba. Mutanen da suke cikin jiragen ruwan sun hada masu fafutuka da su ka fito daga kasashe 45 na duniya. Daga kasar Malysia kadai da akwai mutane 500 sai Faransawa 54 da kuma ‘yan kasar Belgium 15 daga ciki har da ‘yan gwagwarmayar kare muhalli Greta Thunberg.  Wani daga cikin masu fafutuka...
     A wani taron da jakadun kasashen Fransa, Jamus da Ingila su ka yi, sun yi wa Rasha gargadin cewa, za su rika kai wa jiragenta na yaki hari, idan su ka keta hurumin samaniyar daya daga cikin kasashen mambobi na Nato.  Kamfanin dillancin labarun “Blumberg” ya watsa wani rahoto da a ciki ya bayyana cewa; Manyan jami’an diplomasiyyar kasashen uku na turai sun yi wani taron sirri a birnin Moscow, inda su ka gargadi Rasha akan keta hurumin samaniyar kasashen mambobi,suna masu cewa za su iya kai wa jiragen Rashan hari. Kamfanin dillancin labarun “Blumberg” din ya ambato jami’an kasashen na turai da su ka halarci taron suna nakalto wannan gargadin, bisa cewa cikin ganganci ne jiragen na Rasha su...
    Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 30 domin biyan buƙatun ’ya’yanta, ko kuma ta fuskanci yajin aiki. Wa’adin  na ƙunshe ne a sanarwar Bayan taron ƙungiyar, ɗauke da sa hannun shugaban NARD, Dakta Mohammad Suleiman; Sakatare Janar, Dakta Shuaibu Ibrahim; da Sakataren Yaɗa Labarai, Dakta Abdulmajid Ibrahim. Shugaban NARD, Dakta Suleiman, wanda aka zaɓa a taron domin maye gurbin Dakta Tope Osundara, ya ce wannan wa’adin ba a bayar da shi da wasa ba. “Ba za mu ci gaba da kallo mambobinmu suna aiki cikin yanayi marar tsaro yayin da aka yi watsi da walwalarsu ba. Idan ba a warware matsalolin cikin kwanaki 30 ba, za mu ɗauki mataki,” in ji...
    Kwanaki kadan bayan da aka gudanar da zaben raba gardama akan sabon tsarin mulkin kasar, mahkuntan sojan kasar sun ayyana ranar yin zaben shugaban kasa da zai zama na farko a cikin shekaru 4 na mulkin soja. Sanarwar tsayar da ranar yin zaben shugaban kasar dai, an yi ta ne ta hanyar dokar soja a ranar Asabar din da ta gabata. Sakamakon kuri’ar raba gardamar da ak ayi a ranar 21 ga watan nan na Satumba, ta nuna cewa kaso 89% na wadanda su ka kada kuri’ar, sun nuna amincewa da sabon tsarin mulkin. Har ila yau, wata kididdiga ta nuna cea kaso 86% na wadanda su ka cancanci yin zabe ne su ka kada kuri’a. Jam’iyyun hamayyar kasar ta...
    Gwamnatin Jihar Nasarawa ta yi barazanar rufe Mahautar Akwanga saboda matsalar rashin tsafta. Kwamishinar Muhalli da Albarkatu ta jihar, Magret Elayo, ce ta bayyana hakan a yayin ziyar da ta kai mahautar, bisa wakilcin Babban Sakataren  ma’aikatar, Husseini Babayayi. Elayo ta nuna damuwa kan yadda ake gudanar da ayyuka a mahautar cikin rashin tsafta, lamarin da ta ce yana barazana ga lafiyar al’umma. “Wurin ba shi da tsafta, kuma yana shafar lafiyar al’ummarmu. Gwamnati za ta ɗauki matakin gaggawa domin kare rayuwar al’ummarmu a Akwanga saboda yanayin wurin bai dace ba da yankan dabbobi,” in ji ta. Ta ce idan ba a gyara ba nan da wata guda, to gwamnati ba za ta yi wata-wata ba wajen rufe mahautar gaba...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (PENGASSAN) da Matatar Ɗangote don a sasanta a yau. Hakan ya biyo bayan umarnin da ’yan ƙwadagon suka bai wa mambobinsu ne na shiga yajin aiki bayan da Matatar Ɗangote ta salami ma’aikata fiye da 800. Sai dai wasu masana suna ganin tun farko bai kamata lamarin ya kai ga haka ba, da an bi wasu hanyoyi. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Gubar Cikin Abinci DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Waɗannan hanyoyi shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai binciko. Domin sauke shirin, latsa nan
    Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Ranar 30 ga watan Satumba ita ce ranar tunawa da jarumai ta kasar. A safiyar ranar, shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin JKS da na kasar, tare da wakilai daga sassa daban-daban, za su ajiye furanni don jinjinawa jarumai da suka sadaukar da rayukansu saboda kasa a filin Tian’anmen. A lokacin, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG zai watsa wannan biki kai tsaye.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin, ta ce adadin zirga-zirgar fasinjoji yayin hutun bikin tsakiyar kaka na Sin dake tafe nan da ‘yan kwanaki, zai kai kimanin biliyan 2.36. Da yake karin haske kan hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Lahadin nan, mataimakin ministan ma’aikatar Li Yang, ya ce yayin kwanaki takwas na hutun da za a fara tun daga ranar Laraba, za a samu karuwar tafiye-tafiye na yawon bude ido ko na ziyartar ‘yan uwa. Li, ya kara da cewa, an yi kiyasin ganin tafiye-tafiye kimanin miliyan 295 a duk rana cikin kwanakin hutun masu zuwa, karuwar da ta kai kaso 3.2 bisa dari kan na shekarar 2024 da ta shude. An kuma yi hasashen kaso...
    Al’ummar unguwar Kuntau da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano, sun shiga  jimami bayan rasuwar wani matashin limami, Salim Usman, wanda ake zargin ya rasu a hannun ’yan sanda. An kama Salim mai shekara 24 a gidansa a ranar 22 ga watan Satumba, jim kaɗan bayan jagorantar sallar Magariba. 2027: APC za ta ƙwace Kano ba tare da taimakon Kwankwaso ba – Jigon APC Sojoji sun kama mai yi wa Boko Haram safarar man fetur a Borno An zarge shi da siyan buhun fulawa, wadda aka ce an sace a bara. Mahaifinsa, Sheikh Adam Usman, ya bayyana cewa bidiyon na’urar CCTV ya nuna yadda jami’an ’yan sanda biyu suka yi wa ɗansa dukan tsiya a lokacin da suka zo...
    Wani jami’in ’yan sanda a Jihar Kano, Aminu Ibrahim, ya rasu bayan ya harbi kansa bisa kuskure da bindiga a yayin aiki a unguwar Hotoro. Lamarin ya faru ne da safiyar Asabar ranar da misalin ƙarfe 5:40, a cikin harabar kamfanin Basnaj Global Resources Limited, Hotoro. Limami ya rasu a hannun ’yan sanda a Kano 2027: APC za ta ƙwace Kano ba tare da taimakon Kwankwaso ba – Jigon APC Rahotanni sun nuna cewa jami’in, wanda yake aiki a ofishin ’yan sanda na Hotoro, ya shiga bayan gida ne lokacin da abin ya faru. Wata majiya ta ce, yayin da bindigarsa ƙirar AK-47 ke rataye a wuyansa, sai ya matsa kunamar bindigar bisa kuskure. “An samu bindigar, mai lambar rajista...
    Sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC daga jihar Kano ta samu nasararta ta farko a gasar Firimiyar ta Nijeriya (NPFL) bayan doke Kun Khalifa daga jihar Imo a wasan mako na 5 da aka buga a birnin Aba. Wannan shi ne karon farko da ƙungiyar ta samu nasara tun bayan haurowarta gasar. A minti na 14 da fara wasan ne Kun Khalifa suka fara zura ƙwallo a ragar Barau FC. Sai dai minti biyu kacal bayan haka, Yahaya Ibrahim ya farke wa Barau FC kwallo, wanda ya buɗe musu ƙofar dawowa cikin wasan. Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril Ya Yi Alhinin Rasuwar...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Amurka ta kawo cikas ga yarjejeniya tsakanin Iran da Turai game da batun yin watsi da dawo da takunkumi kan Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: An cimma yarjejeniya da kasashen turai dangane da yadda za’a yi watsi da batun sake dawo da takunkumi kan Iran, amma bangaren Amurka ya kawo cikas ga wannan yarjejeniya. A lokacin da ya iso filin jirgin saman Mehrabad na Iran daga birnin New York, shugaba Pezeshkian ya yi tsokaci kan ganawarsa da wasu shugabannin kasashen Turai da suka yi da ba a taba gani ba, yana mai cewa, “A birnin New York, sun tattauna da Turawa kan batutuwan da suka jibanci lamarin makamashin nukiliyar Iran,...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Ba za a yarda da ƙoƙarin maido da kudurori da suka ƙare ba kan Iran Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Yunkurin da kungiyar Tarayyar Turai Troika da Amurka ke yi na maido da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran, ba abu ne da za a amince da su ba. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da sanarwar mayar da martani ga ikirarin da kasashen Turai uku da Amurka suka yi na maido da kudurorin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran. Ma’aikatar ta yi la’akari da yin amfani da hanyar warware takaddama da aka tanada a cikin yarjejeniyar hadin gwiwa game da...
    Majalisar Dinkin Duniya ta sake sanyawa Iran takunkumin rashin adalci a hukumance A hukumance Majalisar Dinkin Duniya ta sake kakabawa Iran takunkumi mai tsauri kan shirinta na makamashin nukiliya da take gudanarwa ta hanyar lumana, ta hanyar amfani da tsarin da aka fi sani da “Snapback”. Matakin na Majalisar Dinkin Duniya ya samo asali ne daga zargin karya da ake yi wa Iran na karya yarjejeniyar makamashin nukiliyar da aka kulla a shekarar 2015 da Amurka, da Birtaniya, da Rasha, da Faransa, da China da kuma Jamus. Wannan shawarar dai ta zo ne duk da irin jajircewar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kan yarjejeniyar, da ficewar Amurka daga cikinta a shekara ta 2018, da kuma kasashen Turai uku,...
    Kasashen duniya 77 ne suka kauracewa jawabin fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Majalisar Dinkin Duniya Wani bincike da Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kasashe 77 ne suka fice daga zauren Majalisar Dinkin Duniya a lokacin da fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benyamin Netanyahu ke jawabi ga babban zauren Majalisar a birnin New York. Jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta ruwaito cewa: Bayan duba kasashen da suka kaurace wa jawabin, an gano cewa: “dukkan makwaftan Isra’ila hudu, baya ga Saudiyya” na daga cikin mutane 77 da suka kauracewa taron, lamarin da ya sa Netanyahu ya yi magana a wani zauren da ke kusa da babu kowa. Sabanin haka jaridar yahudawa ta yabi wakilan Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da...
    A yau Lahadi ne aka gudanar da biki mai taken “Bude sabon babi a sabon zamani: Bikin zurfafa hadin gwiwa tsakanin CMG da bangarori daban daban na Macao” a yankin Macao na kasar Sin. Shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG Shen Haixiong, ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi. Cikin jawabin nasa, Shen Haixiong ya ce “A yau CMG ya sake kaddamar da ayyukan hadin gwiwa da dama tare da bangarori daban daban na Macao, kamar gabatar da wani fim mai bayana labarai mai suna “Macao: Gidan adana kayayyakin tarihi a fili”, da kuma fitar da “Gadon ruhin kishin kasa: Hanyar yawon shakatawa ta wuraren tarihi dake nuna kishin kasa na Macao”, ta yadda...
     Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Ba dole ba ne Iran ta bi hukunce-hukuncen da ba bisa ka’ida ba Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya tabbatar a cikin jawabinsa yayin zaman majalisar a yau Lahadi cewa: Iran ba ta daukar kanta a matsayin wajibcin aiwatar da kudurorin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da aka bayyana a matsayin haramtacciyar hanya sakamakon daukar matakin sake dawo da takunkuman da kasashen Turai uku suka yi kan Iran. Qalibaf ya yi bayanin cewa: Share fagen hanyar da za a bi wajen sake kakaba takunkuman da kasashen Turai uku suka yi da kuma mayar da takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Iran, ba bisa ka’ida ba ne, yana...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar birnin New York na Amurka, bayan kammala wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA). Ya nufi Jamus domin ganawa da jami’an Bankin Deutsche kan batutuwan haɗin gwuiwa da zuba jari a shirye-shiryen ci gaban Nijeriya. A yayin taron UNGA, Shettima ya samu yabo daga Sakatare-Janar na MDD, António Guterres, bisa ƙoƙarin Nijeriya na neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro. Haka kuma ya gabatar da damar zuba jari a fannin makamashin mai darajar dala biliyan 200, tare da ƙarfafa haɗin gwuiwa da Birtaniya kan harkokin kasuwanci da tsaro da kuma ƙaura (ci rani). Gwamna Yusuf Ya Aike Da Sunayen Kwamishinoni Zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano UNGA: Tinubu Ya...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga makarantun horar da ‘yan jam’iyya da su taka rawar gani wajen kyankyashe hazikai, tare da gabatar da shawarwari ga JKS.   Xi, wanda shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne cikin wani umarni da ya gabatar ga makarantun koyar da jagoranci na ‘ya’yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jigon jam’iyyar APC a Jihar Kano, Seyi Olorunsola, ya ce jam’iyyar za ta iya samun nasara a jihar a zaɓen 2027 ba tare da taimakon Rabiu Musa Kwankwaso ba. A baya-bayan nan an yi ta raɗe-raɗin cewa Kwankwaso zai fice daga NNPP tare da komawa jam’iyyar APC. Sojoji sun kama mai yi wa Boko Haram safarar man fetur a Borno Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa A taron manema labarai da ya yi a Kano ranar Lahadi, Olorunsola, ya ce Shugaba Tinubu da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, sun bai wa Kwankwaso kulawa fiye da ƙima. Ya ce APC na da manyan ’yan siyasa a Kano da za su iya tabbatar da nasarar jam’iyyar....
    Dakarun Operation Haɗin Kai su kama wani mutum da ake zargi yana kai wa Boko Haram man fetur a Jihar Borno. Wanda aka kama, mai suna Thomas James, mai shekaru 54, an cafke shi ne ranar 23 ga watan Satumba a kusa da sansanin Forward Operating Base da ke Ngwom. PENGASSAN ta tsunduma yajin aiki kan korar ma’aikata a kamfanin Dangote Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa An same shi da kwalabe 23 na man fetur da ya ɓoye cikin jaka a lokacin da yake tafiya daga Maiduguri zuwa Gamboru Ngala. Bincike ya gano cewa yana yi wa Boko Haram safarar man fetur, sai dai wannan karon an yi nasarar kama shi. Wanda dai ba shi ne...
    Jami’an tsaro a Jihar Kogi sun ceto mutane takwas daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su har 12 a hanyar Okene–Auchi. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansanda ta jihar, William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin a Lokoja ranar Asabar. Ya bayyana cewa fasinjojin suna tafiya ne a cikin motar haya ta Big Joe mai lambar Edo FUG 13 XY daga Abuja zuwa Benin, da Jihar Edo, kafin ƴan bindiga su tare su a hanya. Gwamnatin Kogi Ta Yi Haɗin Gwuiwa Don Fara Fitar Da Amfanin Gona Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina: Nasara Ko Matsala? Aya ya ce rahoton sace Fasinjoji yana shigowa, DPO na Okene, Nasir Muhammad, tare da haɗin gwuiwar Sojoji da ƙungiyar sa-kai,...
    Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas ta Najeriya (PENGASSAN), ta fara yajin aiki saboda korar wasu ma’aikata a Matatar Mai ta Dangote da ke Jihar Legas. Sakataren ƙungiyar, Lumumba Okugbawa, ya ce sun fara yajin aikin ne daga ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa ‘Yan fashi sun sace mutum 17 a mahadar tekun Akwa Ibom da Kuros Riba Da misalin ƙarfe 6 na safe, mambobin ƙungiyar da ke aiki a ɗakunan kula da na’urori suka daina aiki. Umarnin ya shafi mambobin da ke ofisoshi, kamfanoni, da hukumomin gwamnati a faɗin Najeriya, waɗanda za su daina aiki da misalin ƙarfe 12:01 na daren ranar Litinin, 29 ga watan Satumba. Okugbawa,...
    An kori Lage daga Benfica duk da wasa daya ya yi rashin nasara a dukkan karawa a kakar nan, kuma Mourinho ya gaji kungiyar da take ta shida a teburin Primeira Liga da tazarar maki biyar tsakani da Porto mai jan ragama. Ya fara da wasa ranar Asabar, inda suka ziyarci ABS, wadda take ta 17 a kasan teburin a babbar gasar kasar Portugal. Mourinho, dan kasar Portugal wanda ya bai wa kansa sunan ”the special one’ a 2004 zai ziyarci tsohuwar kungiyarsa wadda ya koyar sau biyu a tarihi wato Chelsea a Champions League da Benfica za ta buga ranar 30 ga watan Satumba. Jerin kungiyoyin da Mourinho ya koyar Porto (2002-04) Primeira Liga biyu, Champions League, Uefa Cup...
    Yayin da yake bayani kan muhimmancin wannan shiri, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce: “Wannan Cibiyar wata gagarumar alama ce ta kudurin Gwamnatin Jihar Kaduna na bunkasa koyon sana’o’i, karfafa matasa, da haɓaka tattalin arziki.   Yace An zaɓi fannonin sana’o’i 14 ne cikin hikima domin su magance manyan bukatun ƙwararrun ma’aikata a bangarorin gine-gine, makamashi, fasahar zamani (ICT), kula da baƙi, da harkokin ƙirƙira. Muna da yakinin cewa waɗanda suka kammala karatu a wannan Cibiyar ba kawai za su samu ayyukan yi ba ne, har ma za su zama masu dogaro da kai kuma su samar da dama ga wasu.”   Shima Shugaban Cibiyar, Malam Husaini Haruna Muhammad, ya jaddada muhimmancin da horon ke...
    Jami’ar Bayero Kano (BUK) da ke Kano ta sanar da korar ɗalibai 57 saboda kama su da laifuka masu nasaba da maguɗin jarrabawa. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da darektan sashen kula da harkokin jarrabawa na jami’ar, Malam Aminu Wada Kurawa ya fitar. Nukiliya: MDD ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman karayar tattalin arziki ‘Yan fashi sun sace mutum 17 a mahadar tekun Akwa Ibom da Kuros Riba Sanarwar ta ce an dakatar da wasu ƙarin mutum 8 da aka kama da laifuka masu nasaba da hakan tare da wanke ƙarin ɗalibai biyu daga zargin. Jami’ar ta ce bincike ya tabbatar da cewa ɗaliban da aka kora sun aikata laifuka daban-daban da suka shafi karya ƙa’idojin jarrabawa. Cikin wadanda...
    Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan fashin teku ne sun yi awon gaba mutum 17 a wani kwale-kwale da ke kan iyakar teku a jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba. Lamarin ya faru ne a lokacin da fasinjojin suka taso daga wani ƙauye a kan iyakar jihohin biyu, inda ‘yan fashin suka afka wa kwale-kwalen a cikin nasu jirgin ruwa, sannan suka yi awon gaba da fasinjoji 17. Matatar Dangote ta ci gaba da sayar da man fetur a naira Nukiliya: MDD ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman karayar tattalin arziki Kwale-kwalen na wani kamfani ne da ke aikin jigilar fasinjoji tsakanin jihohin biyu a kan teku. A ‘yan shekarun baya matsalar satar mutane da garkuwa da su ta...
    Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan fashin teku ne sun yi awon gaba mutum 17 a wani kwale-kwale da ke kan iyakar teku a jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba. Lamarin ya faru ne a lokacin da fasinjojin suka taso daga wani ƙauye a kan iyakar jihohin biyu, inda ‘yan fashin suka afka wa kwale-kwalen a cikin nasu jirgin ruwa, sannan suka yi awon gaba da fasinjoji 17. Matatar Dangote ta ci gaba da sayar da man fetur a naira Nukiliya: MDD ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman karayar tattalin arziki Kwale-kwalen na wani kamfani ne da ke aikin jigilar fasinjoji tsakanin jihohin biyu a kan teku. A ‘yan shekarun baya matsalar satar mutane da garkuwa da su ta...
    Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi zargin cewa, cikin watanni shida, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya samu karin kaso daga gwamnatin tarayya fiye da yadda ya samu a cikin shekaru 8 da ya yi yana gwamna. Batun rabon kuɗaɗen wata-wata ga Jihohin dai ya zama abun muhawara a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Wadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa? Gwamna Yusuf Ya Aike Da Sunayen Kwamishinoni Zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano “A yau zan iya bugun ƙirjina kuma kowanne daga cikin gwamnonin nan zai iya tabbatar da cewa, rabon da ake bai wa jihohin ya ninka sau uku, kuma akwai l isassun kuɗaɗe daga ƙananan hukumomi.” in ji Ganduje Da yake...
    Majalisar Dinkin Duniya ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkumai na karayar tattalin arziki bayan gaza cimma matsaya a tattaunawar ƙarshe kan shirin nukiliyarta da manyan ƙasashen yammacin Turai. Birtaniya, Faransa da Jamus ne suka bijiro da batun maido da waɗannan takunkuman a taron kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda aka yi kan saɓa yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015 da Iran ta yi. NECO ta sake jaddada nasarar ɗaliban Kano a jarrabawar bana Matatar Dangote ta ci gaba da sayar da man fetur a naira Haka kuma, ƙasashen uku sun gargaɗi Tehran kan ɗaukar matakan da za su ƙara dagula lamarin. “Sake ƙaƙaba takunkuman Majalisar Dinkin Duniya ba yana nufin ƙarshen diflomasiyya ba ne,” in ji ministocin harkokin wajen ƙasashen uku...