Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wannan Alhamis din zai bar Abuja domin fita ziyarar aiki a ƙasashen Japan da Brazil, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ta tabbatar.
Sai dai gabanin isa ƙasashen biyu, Tinubu zai soma yada zango a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa sannan daga bisani ya ƙarasa Japan.
A yayin da shugaban yake Japan, zai halarci taron Tokyo International Conference on African Development (TICAD9) karo na tara a birnin Yokohama daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Agusta.
Taken taron na bana shi ne “Haɗa Hannu da Afirka Wajen Ƙirƙirar Sabbin Hanyoyin Ci Gaba”, inda za a tattauna kan yadda za a sauya yanayin tattalin arzikin nahiyar da inganta kasuwanci.
Haka kuma taron na TICAD9 zai mayar da hankali kan ƙarfafa zaman lafiya, tsaro, da daidaito.
Baya ga wannan taron, Shugaba Tinubu zai yi zama na musamman da wasu shugabanni, tare da ganawa da shugabannin manyan kamfanonin Japan da ke da jarin kasuwanci a Nijeriya.
TICAD, wanda gwamnatin Japan ta ƙaddamar tun 1993 tare da haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), da Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU), da kuma Bankin Duniya, ana gudanar da shi duk bayan shekara uku a tsakanin Japan da Afirka, inda karo na ƙarshe ya gudana a Tunisia a Agustan 2022.
Bayan kammala ziyarsa a Japan, Shugaba Tinubu zai wuce Brasília, babban birnin ƙasar Brazil, daga Lahadi 24 zuwa Litinin 25 ga watan Agusta, bisa gayyatar shugaban ƙasar Luiz Inacio Lula da Silva.
A Brazil, Shugaba Tinubu zai yi ganawa ta musamman da shugaban ƙasar, sannan ya halarci babban taron kasuwanci da ‘yan kasuwar Brazil.
Tawagarsa wadda ta ƙunshi ministoci da manyan jami’ai, za ta tattauna da mahukunta kan batutuwan haɗin gwiwa tare da sanya hannu kan yarjejeniyoyi da takardun fahimtar juna.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Brazil
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Daga Sani Sulaiman
Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Emmanuel Bello, ya sanyawa hannu.
Gwamnan ya ce rasuwar wannan babban malami babban rashi ne ga kasa, yana mai nuna cewa a wannan lokaci ne ake matuƙar bukatar irin gudummawar da yake bayarwa, duba da kalubalen da kasar ke fusfuskanta.
Ya kara da cewa marigayi Sheikh ya koyar da ilimi da zai ci gaba da jagorantar kasa kan batun zaman lafiya tsakanin addinai.
Haka kuma, Dr. Kefas ya yabawa halayen Sheikh Bauchi, wanda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tawali’u, jin kai, da haƙuri.
Saboda haka, Gwamna Agbu Kefas ya yi kira ga jama’a da su yi koyi da jagorancin wannan fitaccen malami.
Ya ce al’ummar kasa za su ci gaba da bin tsarin ladabi da tarbiyyar da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya koyar.
A wani bangaren, Dr. Kefas ya ja hankalin ‘yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da addininsu ba.
Ya jaddada muhimmancin jurewa da girmama ra’ayin juna maimakon nacewa a kan namu ra’ayin, tare da tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da hidima ga dukkan ‘yan Jihar Taraba bisa adalci ba tare da la’akari da addini ko kabilarsu ba.