2025-10-14@19:29:55 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10178

«Masu zanga zangar»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa. A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli da ta yanke na baya-bayan nan. Matan Sojojin da aka tsare sun nemi a yi wa mazajensu afuwa 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Gwamnan, a yayin wani zama da ya yi da hadimansa domin murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai a gidan gwamnati da ke Fatakwal, ya gode wa jami’an...
    Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana matuƙar alhininta kan mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a kan Kogin Neja, inda aƙalla mutum 26 suka rasa rayukansu. Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo ya fitar a ranar Laraba ta ce wannan mummunan lamari ya rutsa da ‘yan kasuwa da suka taso daga ƙaramar hukumar Ibaji ta jihar Kogi zuwa kasuwar Ilushi a jihar Edo. Gwamna Ahmed Usman Ododo ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma umurci hukumomin da abin ya shafa ciki har da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha da su haɗa kai da ƙananan hukumomin yankin, wajen bayar da tallafi da kuma agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa. Gwamna Ododo ya ƙara da ba da tabbacin cewa gwamnatin...
    Matan Sojoji da aka tsare bisa laifuka daban-daban a yaƙin da ake yi da ’yan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP a garin Maiduguri jihar Borno, a bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin soja da su tausaya musu ta hanyar yi wa mazajensu afuwa. Matan da yawansu ya haura 30 tare da wasu yara ’yan ƙasa da shekara biyu da suka haɗa da ‘yan uwa da abokan arziki sun ziyarci cibiyar ’yan jarida ta Nijeriya (NUJ) da ke Maiduguri a ranar Laraba don miƙa wannan koke na su. HOTUNA: Yadda Boko Haram ta lalata Kwalejin Kagara da ke Neja 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a...
    Matan Sojoji da aka tsare bisa laifuka daban-daban a yaƙin da ake yi da ’yan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP a garin Maiduguri jihar Borno, a bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin soja da su tausaya musu ta hanyar yi wa mazajensu afuwa. Matan da yawansu ya haura 30 tare da wasu yara ’yan ƙasa da shekara biyu da suka haɗa da ‘yan uwa da abokan arziki sun ziyarci cibiyar ’yan jarida ta Nijeriya (NUJ) da ke Maiduguri a ranar Laraba don miƙa wannan koke na su. HOTUNA: Yadda Boko Haram ta lalata Kwalejin Kagara da ke Neja 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a...
    Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane ta Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane tare da kuɓutar da mutum 24 a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe International Airport, da ke Abuja. Jami’in watsa labaran hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ya bayyan a ranar Laraba cewa a cikin waɗanda aka kama akwai wani mutum da ya yi yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi. Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello. Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Makarantar Kwalejin Kagara da ke Jihar Neja, wadda ta yi fice wajen yayi ɗalibai masu hazaƙa, yanzu ta zama kufai. A shekarar 2021, Boko Haram ta kai hari makarantar ta sace aƙalla dalibai da malamai 27. 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Jiya na yi barci mai daɗi bayan na soke faretin samun ’yancin kai Bayan haka kuma an sake kai hare-hare a yankin, lamarin da ya tsoratar da ɗalibai, tare da hana su komawa makaranta. Yanzu makarantar ta daina aiki, inda aka mayar da ita sansanin soja. Wakilin Aminiya, Abubakar Akote, ya ziyarci makarantar, inda ya ɗauki hotunan da ke nuna halin da makarantar ke ciki a yanzu....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da farmakin da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan jiragen ruwan ‘yan fafatuka dake dauke da kayan agaji ga al’ummar Gaza. Kungiyoyin Falasdinawa, kwararru na Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatocin Turai sun bi sahu inda sukayi tir da harin baya bayan nan da aka kai wa jirgin ruwan Global Sumud Flotilla a cikin ruwan kasa da kasa. Hamas ma ta yi Allah wadai da farmakin kan Global Sumud Flotilla a iyaka da Gaza wanda ta danganta a matsayin “laifi na fashin teku da ta’addanci kan fararen hula”, tana mai kira ga “dukkan masu kare ‘yanci a duniya” da su yi Allah wadai da harin. Kungiyar Jihadin Islamic ta Falasdinu...
    Kotun koli ta Soji a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yanke wa tsohon shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa bisa samunsa da laifin cin amanar kasa da laifukan yaki ciki har da jagorantar kungiyar ‘yan tawayen M23. An samu Kabila da laifuffuka da dama da suka hada da shiga wani yunkuri na tayar da kayar baya, cin amanar kasa, azabtarwa, da kuma laifukan yaki, a cewar hukuncin da kotu ta yanke a Kinshasa, babban birnin kasar. An fara shari’ar tasa ne a watan Yuli, bayan da majalisar dattawa ta tsige masa  rigar kariya a watan Mayu, bisa zarginsa da hannu a ta’asar da ‘yan tawayen M23 suka aikata a lardunan gabashin Congo. Kotun ta ce Mista Kabila “ya gudanar da tarurrukan...
    Akalla Falasdinawa 44 ne sukayi shahada a yayin da wasu da dama suka jikkata a ranar Laraba a wasu jerin hare-haren da Isra’ila ta kai kan wasu yankuna na zirin Gaza, a cewar shaidu da majiyoyin lafiya. Sojojin Isra’ila sun yi luguden wuta kan wasu gidaje a sansanin ‘yan gudun hijira na Shati da ke birnin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa 5 tare da jikkata wasu da dama, wasu ma sun makalle a karkashin baraguzan gine-gine. Wasu mutane 11 kuma sun yi shahada, sannan wasu da dama sun jikkata a harin bam din da aka kai a makarantar Al-Falah da ke unguwar Al-Zeitoun a kudu maso gabashin wannan birni. Makarantar tana dauke da iyalai da suka yi gudun hijira. A...
    Ya ce bambancin Nijeriya na ƙabilu, addinai da al’adu bai kamata a ɗauka a matsayin matsala ba, illa ma ya zama ƙarfin ƙasar. “Idan aka tafiyar da bambancin nan da kyakkyawan shugabanci, Nijeriya za ta samu girmamawa a duniya,” in ji shi. Obasanjo ya jaddada cewa ilimi shi ne tushen ci gaba, ba tare da la’akari da ƙabilanci, addini ko al’ada ba. Ya yaba wa Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmed Aliyu, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, da kuma Bishop Matthew Kukah saboda jajircewa wajen haɗa kan jama’a da zuba jari a ilimi. Bishop Kukah ya bayyana cewa cibiyar da mai bayar da tallafi Afe Babalola ya gina za ta bayar da horo kyauta ga kowa a fannin amfani da kwamfuta, ƙirƙirar manhajoji,...
    Iran ta yi kira da a gaggauta kakaba wa gwamnatin Isra’ila takunkumi mai tsauri kan kisan kiyashin da take ci gaba da yi a zirin Gaza, sakamakon rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a baya-bayan nan. Da yake jawabi a wajen taron kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya karo na 60 a birnin Geneva, wakilin kasar Iran Ali Bahreini ya yi ishara da rahoton da kwamitin bincike mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar kan yankin Falasdinu da ta mamaye a watan Satumba, wanda ya kammala da cewa Isra’ila ta aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a zirin Gaza. Hukumar, wacce ke binciken abubuwan da suka faru tun ranar 7 ga Oktoba 2023, ta gano...
    Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta ce ta kama akalla mutane biyar da ake zargi da safarar mutane tare da ceto mutane 24 a Filin Jirgin Sama na Ƙasa Nnamdi Azikiwe, Abuja. Hukumar ta ce daga cikin wadanda aka cafke ɗin, har da wani uba da ya yi ƙoƙarin safarar diyarsa zuwa Baghdad, babban birnin ƙasar Iraq. Jiya na yi barci mai daɗi bayan na soke faretin samun ’yancin kai ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a Neja Jami’in Yaɗa Labarai na NAPTIP, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yawaitar safarar...
    Shugaban Colombia Gustavo Petro ya ce zai kori dukkanin jami’an diflomasiyar Isra’ila daga ƙasarsa a matsayin martani ga kama jiragen ruwa masu ɗauke da agaji zuwa Gaza. Ya kuma ya bayyana cewa an yi garkuwa da yan Colombia guda biyu. Petro babban mai caccakar yaƙin Isra’ila a Gaza, ya zargi Isra’ila da sake saɓa dokokin ƙasa da kasa inda ya buƙaci sakin su cikin gaggawa. Italiya ta kira kutsen jiragen ruwan da Isra’ila ta yi a matsayin fashin teku da kuma ta’addanci. An dai yi ƙokarin shigar da kayan agaji ne ta hanyar teku domin kaucewa shingen Isra’ila a yankin
    Kungiyoyin Kare Muradun Arewa, wato Arewa Defence League, sun fitar da sanarwar da suka kira October Declaration, wadda ta tanadi matakai na gaggawa don magance matsalolin tsaro, koma bayan tattalin arziki da kalubalen rayuwa a Arewacin Najeriya. Shugaban kungiyar, Murtala Abubakar, ya bayyana hakan a taron dabarun da aka gudanar a Arewa House Kaduna, inda ya ce “lokacin alkawura marasa amfani ya wuce, wannan sanarwa kuwa ita ce alkawarinmu ga mutanen Arewa.” Ya yi gargadi kan karuwar ta’addanci da ‘yan bindiga, rashin aikin yi da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, lamarin da ya danganta da gazawar shugabanci da kuma rashin wakilci nagari. A cewarsa, kungiyar ba ta da manufar ballewa daga kasa, amma akwai gaggawar bukatar sabuwar...
    Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce soke faretin zagayowar ranar ’yancin kai karo na 65 da sojoji ke yi ya ba shi damar yin lafiyayyen barci da kuma yin kyakkyawan kari a ranar Laraba. Aminiya ta rawaito cewa Gwamnatin Tarayya ta soke bikin da aka shirya domin murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, daya ga watan Oktoba. Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya Sanarwar ta fito ne daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin. “Gwamnatin Tarayya na sanar da soke bikin zagayowar ranar ‘yancin kai da aka shirya domin murnar cikar ƙasar shekara 65 a ranar...
    Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya yaba da hadin kai, tsayin daka, da ci gaban Gombe da Najeriya a daidai lokacin da jihar ke cika shekaru 29 da samun ‘yancin kai tare da bikin cikar kasar shekaru 65 da samun ‘yancin kai.   A cikin sakon fatan alheri mai dauke da sa hannun babban daraktan hulda da manema labarai na gidan gwamnatin jihar Gombe, Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin sa na mai da jihar Gombe ta zama cibiyar zuba jari da ci gaba mai dorewa, wanda aka dora a kan shirin ci gaban jihar na shekaru 10 (DEVAGOM).   Alh Inuwa Yahaya ya bayyana irin nasarorin da aka samu a karkashin jagorancin sa, da suka hada da inganta harkokin...
    Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, ya taya gwamnati da al’ummar Nijeriya murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, inda ya bayyana ranar a matsayin abin tunawa da hadin kai, juriya, sadaukarwa da suka gina kasar.   A sakonsa na fatan alheri, Gwamna Namadi ya ce bikin ba wai kawai lokacin yin tunani ne kan irin gwagwarmayar da iyayen da suka kafa kasar suka yi ba, har ma wata dama ce ta sabunta sadaukarwar hadin gwiwa don samar da zaman lafiya, ci gaba, da wadata.   “A yau, muna bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai cikin alfahari da godiya. Wannan ranar tana tunatar da mu sadaukarwar da jaruman mu suka yi a baya, wadanda hangen nesa...
    Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibril Ismail Falgore, ya mika sakon taya murna ga ‘yan Najeriya a daidai lokacin da kasar ke cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai.   A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar, shugaban majalisar ya bayyana tafiyar Najeriya bayan samun ‘yancin kai a matsayin wanda ke cike da kalubale da dama, yana mai cewa idan aka yi hangen nesa da tsare-tsare, makoma mai haske tana nan kusa.   Ya lura cewa duk da matsaloli, Najeriya a yau tana tsaye a matsayin kasa mai mutane sama da miliyan 230, galibi matasa da kuzarin da ke da karfi na musamman da kasashe da yawa ba su da su.  ...
    An shawarci ‘yan siyasa a jihar Neja da su kiyaye mutuncin da aka san jihar da su domin tabbatar da nasarar zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe.   Zaben da aka shirya gudanarwa a ranar farko ga watan Nuwamba na wannan shekara, ya yi alkawarin za a yi shi cikin gaskiya ba tare da wata tangarda ba, tare da shirye-shiryen da tuni aka yi nisa.   Mai ba Gwamnan Jihar Neja shawara ta musamman kan harkokin siyasa Alh Mohammed Nma Kolo ne ya bayar da wannan shawarar a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Minna.   Alh Nma Kolo ya kuma tunatar da su cewa a kowace gasa dole ne a samu wanda ya yi nasara...
    Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya taya al’ummar Jihar Nasarawa murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai da kuma Jihar Nasarawa da ta cika shekara 29 da samun ‘yancin kai.   Wata sanarwa da ta sanyawa hannu kuma ta raba wa manema labarai, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin yada labarai Malam Ibrahim Adra ta ce al’ummar kasar nan sun samu gagarumar nasara a dukkanin bangarori na rayuwar dan Adam, haka nan kuma jihar nasarawa ta samu ribar dimokuradiyya tun bayan kafa jihar da marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya kafa.   Sanarwar a yayin bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai a yau, ta yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da...
    Gwamnatin jihar Kwara ta shawarci al’ummar da ke kewayen kananan hukumomin Ekiti, Ifelodun, Isin, Oke Ero, da Irepodun, da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita harkokin a wuraren da sojoji ke aikin musamman.   A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Bolanle Olukoju ya fitar t cea shawarar ta biyo bayan tsaurara matakan tsaro da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi a garuruwan Kogi da Kwara, inda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da su.   “Muna kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita zirga-zirgar ababen da suka dace kawai, wato don gudun kada a kama su ba tare da saninsu ba, yayin da masu garkuwa da mutane ke tserewa maboyarsu, ba...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana damuwarta kan yadda likitoci ke kin zuwa aiki musamman a lokutan da suke kai ziyara wuraren kiwon lafiya da ba a shirya ba.   A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar, Suleiman Isah ya fitar, ya ce kwamishinan lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun ta yi gargadi ga likitoci a babban asibitin garin Gusau, bayan da suka gano rashin zuwan su a wata ziyarar ba-zata.   Dakta Maradun, wadda ta kai ziyarar bazata asibitin, ta ce ta firgita da ganin cewa babu wani likita da ke bakin aiki, inda ta bayyana hakan a matsayin wani abu da ke faruwa a baya.   Ta yi Allah wadai da lamarin a matsayin...
    Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago na daga cikin wadanda suka halarci sallar jana’izar Marigayi Kyaftin Hassan Mohammed Baro, Kwamishinan dindindin a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja.   Sallar jana’izar wadda aka gudanar a kusa da gidan marigayin da ke Minna ta samu halartar babban daraktan kula da harkokin addini Malam Umar Faruk Abdullahi wanda ya samu halartar jama’a da dama da suka hada da mai martaba Sarkin Agaie Alh Yusuf Nuhu.   Gwamnan ya kuma kasance cikin masu jajantawa a makabartar Musulmi ta Kpakungu inda aka yi jana’izar marigayi Captain Baro tare da babban limamin Minna, Malam Jibril Isah ya yi addu’ar Allah ya jikansa.   Daga karshe Umar Bago ya jagoranci tawagar jihar zuwa gidan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina yin maganganu ɓatancin ga ƙasar. Ya ce Najeriya ƙasa ce mai girma, mai cike da damar ci gaba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a Neja Shugaban ya yi wannan jawabi ne a daren ranar Talata a Jihar Legas, lokacin da aka sake buɗe Cibiyar Al’adu ta Ƙasa (National Theatre) da aka gyara. Ya ce dole ne ’yan ƙasa su yi imani da Najeriya kuma su haɗa kai domin gina ta. “Ku daina yin magana mara kyau game da Najeriya. Mu mutane ne masu alfahari, jarumai, da jajirtattu. Mu...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina yin maganganu ɓatancin ga ƙasar. Ya ce Najeriya ƙasa ce mai girma, mai cike da damar ci gaba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a Neja Shugaban ya yi wannan jawabi ne a daren ranar Talata a Jihar Legas, lokacin da aka sake buɗe Cibiyar Al’adu ta Ƙasa (National Theatre) da aka gyara. Ya ce dole ne ’yan ƙasa su yi imani da Najeriya kuma su haɗa kai domin gina ta. “Ku daina yin magana mara kyau game da Najeriya. Mu mutane ne masu alfahari, jarumai, da jajirtattu. Mu...
    Manyan garuruwan da suka shiga cikin wannan jerin sun haɗa da Mubi, Gusau da Azare. Ma’aikatar ta roƙi jami’an gwamnati a jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da su sa ido sosai kan halin da ake ciki kuma su bayar da rahoto a kan lokaci. Haka kuma, ta shawarci jama’a da ke zaune kusa da koguna ko rafuka su ɗauki matakan kariya ko su bar waɗannan wurare domin guje wa ambaliyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemah Mohajerani ta fayyace cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta maraba da yaki, amma tana ci gaba da shirye-shiryen tsaro mafi girma  don kare kanta. Ta kara da cewa Tehran ta bayar  da shawarar tattaunawa da Amurka kai tsaye a wata ganawa tare da  ministocin  Turai, amma wakilin Amurka Steve Witkoff ya ki isa a lokacin da aka tsara. Mai magana da yawun gwamnatin ta Iran ta kuma bayyana cewa, kasarta na ci gaba da musayar sakwanni kai tsaye da kuma a fakaice, kuma tana ci gaba da kokarinta, sai dai kuma gwamnatocin  yammacin duniya su ne ke warware alkawuran da suke dauka. A nasa bangaren, sakataren majalisar kula da harkokin tsaron kasar,...
    Batun siyasar Najeriya ya sake ɗaukar hankali yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Wannan batu ya tayar da muhawara mai zafi a tsakanin masana, da ‘yan siyasa da ma al’umma. Idan za a iya tunawa dai, an rantsar da tsohon shugaban ƙasan, har sau biyu: a karo na farko a shekarar 2010 bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, sannan kuma a karo na biyu a 2011 bayan lashe zaben da ya biyo baya. Amma abun tambayar a nan shine, shin ko me dokar kasa ta bayyana kan takarar tsohon shugaban kasan bayan rantsar dashi har sau biyu kan karagar mulki? Wannan shine batun...
    Kungiyar Global Sumud Flotilla ta fitar da wata sanarwa a daren jiya Laraba inda ta sanar da cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun kai farmaki a kan jiragenta da ke kan hanyar isa Gaza domin kai kayan agaji, inda suka lalata kamarori da kuma sauran kayan ayyukan fasaha da suke cikin wasu daga cikin jiragen Ruwan, sannan kuma suka killace su. Baya ga haka kuma sun kama dukkanin mutanen da suke cikin wasu jiragen sun tafi da su. Sanarwar ta ce, kyamarorin da ke cikin jirgin sun samu matsala, sannan sojojin Isra’ila sun shiga jiragen ruwa da dama, inda suka umurci jiragen da su karkata zuwa tashar jiragen ruwa ta Asdod da ke karkashin ikon su. Rahotanni sun tabbatar da...
    Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzya, ya ce maido da tsarin takunkuman karya tattalin arziki a kan Iran da wasu kasashen yammacin duniya suka yi ya saba wa kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya. Nebenzya ya bayyana hakan ne a wata doguwar wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugaban rikon kwarya na kwamitin sulhun bayan da kasashe 15 suka kada kuri’ar sake kakaba takunkumi kan Tehran, wanda aka soke a karkashin yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekara ta 2015 tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, ciki har da Birtaniya, Faransa, da Jamus. Wakilin na Rasha ya jaddada cewa, an bullo da abin da ake kira tsarin  dawo da takunkumai a...
    Collins mutum ne mai jajircewa da azama. Bayan gaza cin nasara da ya yi a ƙoƙarinsa na kafa tarihi a shekarar 2024, ya ɗauki tsawon shekara guda yana ɗaukar horo da shiri sosai domin wannan rana. Ya ce, “Na koyi darussa da dama daga ƙoƙarina na farko. Yanzu na shirya sosai. Tare da goyon bayan Indomie, domin mu kafa tarihi.” A wajen Collins, fentin fuska ba nishaɗi ba ne kaɗai ba, fasaha ce da ke bayyana fikira da ƙirƙira. Ƙoƙarinsa ya haskaka wa duniya irin baiwar da matasa ’yan Nijeriya suke da ita a idon duniya. Kamfanin Indomie, ya jima yana bayar da gudummawa da goyon baya a fannin ƙirƙira da ilimi a tsakanin matasa, kamfanin ya bayyana farincikinsa da...
    Adadin wadanda suka yi shahahda a yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke aiwatarwa kan al’ummar yankin zirin Gaza ya kai shahidai 66,148 da kuma jikkata wasu 168,716, tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta fitar, adadin wadanda suka yi shahada tun bayan da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka koma yakin kisan kare dangi a ranar 18 ga watan Maris ya kai 13,280, kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai 56,675. A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, mutane 51 ne suka yi shahada wasu 180 kuma suka jikkata a zirin Gaza. A halin da ake ciki dai, wani adadi mai yaw ana  wadanda abin ya shafa...
    A wannan Laraba ce wata kotu a Afirka ta Kudu ta samu madugun ‘yan adawa Julius Malema da laifin harba bindiga a bainar jama’a a shekarar 2018, hukuncin da zai iya sa a hana shi shiga majalisar. Malema ya harba bindiga sama a lokacin bikin cikar shkaru biyar da kafa jam’iyyar Economic Freedom Fighters (EFF)  a lardin Eastern Cape, wanda ya saba wa dokar hana sarrafa bindigogi. Idan har aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari, Malema, wanda ya shafe sama da shekaru 10 yana dan majalisa, za a dakatar da shi  daga ci gaba da zama mamba a majalisar dokoki a karkashin kundin tsarin mulkin kasa. A rahoton kamfanin dillancin labaran Reuters Mai shari’a Twant Olivier ta ce, kwanaki...
    Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Najeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro. ’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji. Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantu 39 a Zamfara, 30 a Jihar Neja, shida a Sakkwato da Kaduna, 52 a Katsina, sannan 55 a Benuwe. Adadin na iya haura haka saboda akwai yankunan da ba za a iya shiga ba don gudanar da bincike ba. Binciken bai haɗa da jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba waɗanda Boko Haram...
    Ɗalibi a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, ya yi ƙoƙarin karya tarihin Kundin Tarihi na Duniya, na zane a fuska mafi yawa cikin mintuna uku. Ɗalibin ya samu tallafi daga kamfanin da ke yin taliyar yara Indomie, inda ya yi zane a fuskar mutum 17 cikin mintuna uku, wanda hakan ya ba shi damar zarce kambun Emilia Zakonnova, wanda ta kafa a watan Yulin 2025 na zane fuskar mutum 12. Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Collins ya gwada sa’arsa a mataki uku: Na farko: ya zane fuskar mutum 17 cikin mintuna 2 da sakan 40 Na biyu: ya zane...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG, ta doke Barcelona a wasan mako na 2 na gasar Zakarun Turai a wasan da suka buga a filin wasa na Luis Companys. Ferran Torres ne ya fara jefa ƙwallon a ragar PSG a minti na 19 da fara wasan, amma gab da tafiya hutun rabin lokaci Senny Mayulu ya farkewa baƙin ƙwallonsu, yayin da Goncalo Ramos ya ci ƙwallon ƙarshe kuma wacce ta bai wa PSG nasara a mintin ƙarshe na wasan. Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP, Sun Kama Wasu Da Miyagun Ƙwayoyi Li Qiang Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Sabon Firaministan Algeria Da wannan nasarar da PSG ta samu ya sa ta koma matsayi na 3 a teburin gasar Zakarun Turai yayin...
    Fitaccen ɗan wasan gaban Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya kafa tarihin zama na farko a ƙungiyar da ya ci mata ƙwallaye 200. Griezmann ɗan asalin Faransa ya kafa wannan tarihin ne a ranar Talata yayin Gasar Zakarun Turai, inda Atletico ta lallasa Eintracht Frankfurt ta Jamus da ci 5-1. Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake tallafawa Ilimin mata Babban malamin Qur’ani da ƙira’a na Masallacin Madinah ya rasu Kocin Atletico, Diego Simeone ya bayyana farin cikinsa kan ƙwazon ɗan wasan, inda yake cewa “ba ruwan hazaƙa da shekaru.” Griezmann mai shekaru 34, ya kwashe kusan shekaru 10 a Atletico kafin ya cim ma wannan mataki. A cewar Simeone, “ina godiya ga Antoine da lokacin da ya kwashe a Atletico Madrid. Ya...
    Majiyoyin tsaro sun ce waɗannan hare-haren wani ɓangare ne na yunƙurin karya ƙarfin ’yan ta’adda da kuma katse hanyoyin samun kuɗaɗensu ta hanyar safarar miyagun ƙwayoyi, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma sata man fetur. Sun kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da ba da bayanai ga hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga a faɗin ƙasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A rana ta farko ta watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta kasar Amurka ta sake tsayar da ayyukanta. Bisa binciken da CGTN ta gudanar na jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,671 daga kasashe 38, an ce, masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna damuwa game da matsalar da aka samu a tsarin kasar Amurka sakamakon matsalar harkokin siyasa da sarrafa harkokin kasar, inda suka bayyana cewa, salon tsarin demokuradiyyar Amurka yana sabawa da ainihin tsarin demokuradiyya, kuma Amurka ba ta zama kasa mafi kyawun ba da jagoranci a wannan fanni ba.   An sake tsayar da ayyukan gwamnatin kasar Amurka bayan shekaru 7, an samu irin hakan a baya yayin wa’adin shugaba Donald Trump karo na farko. Bisa binciken...
    Fitaccen masanin karatu da ƙira’ar Al-Qur’ani kuma babban malamin nan da ke karantarwa a Masallacin Annabi da ke Madina, Sheikh Bashir bin Ahmed Siddiq, ya riga mu gidan gaskiya a yau Laraba. Shafin Al-Haramain ya ruwaito cewa Sheikh Bashir ya rasu ne bayan shafe kusan shekaru sittin yana koyar da Al-Qur’ani a Al-Masjid An-Nabawi da ke birnin Madinah. Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake tallafawa Ilimin mata Sheikh Bashir da aka haifa a shekarar 1358 Hijiriyya, wanda shi ne mafi shahara a cikin sahun bajiman malaman ƙira’a, ya rasu bayan shafe kusan shekaru 90 a doron ƙasa. Fitattu daga cikin malamansa akwai Qari Fath Muhammad Panipati, da Sheikh...
    A yan kwanaki kin nan kasashen duniya sun fuskanci wani lamari mai jan hankali sosai, wanda ya jaddada hakkin falasdinu na kafa kasarsa mai cin gashin kai,  hakika wannan lamari ya kai kololuwasa inda ya kai ga ranar litinin da ta gabata aka kira wani taro a gegen taron majalisar dinkin duniya karo na 80 domin bayyana nuna amincewa da warware rikicin falasdinu na kafa kasashen biyu masu cin gashin kansu, Akwai abubuwa guda buyi masu gayar muhimmancin da suka sanya aka gudanar da taron kafa daula biyu, na farko hakika yazo a yan kwanaki kadan sanar da shimfida taswirar hanya na kafa kasar falasdinu mai cin gashin kai bisa  iyakoyin da aka cimma a wata yuni shekara ta 67...
    Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar yan jarida da bata da iyaka a karon na biyar ta shigar da kara a babban kotun duniya mai hukumta laifukan yaki ICC kan kisan da HKI take yi wa yan jaridu a bakin aikinsu a yankin gaza. A ranar talata ce aka sanar da sake shigar da karar,tun bayan harin 7 ga watan oktoba da isra’ila ta kaddamar a yankin gaza, inda ta kai hari kan yan jarida 30 daga watan mayu na 204 zuwa Augustan shekara ta 2025 ta kashe 25 daga ciki ta jikkata wasu gida biyar kuma. Darakatan sadarwa na kungiyar ta RSF Antoine bernard ya bayyana cewa isra’ila a koda yaushe tana kokari ne wajen rufe bakin yan jarida, Yace...
    Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Pakistan sun bayyana cewa sun yi gwajin makami mai linzami na fatah 4 da aka kara inganta shi,  wanda zai iya kai hari mai nisan kilomita 750 ba tare da wani kuskure ba, wanda ya kara inganta karfin makamai masu linzami na kasar. Babbar nasarar da aka samu wajen gwajin makamai mai linzami da aka kara inganta shi acikin gida na fatah 4,wanda aka karfafa shi da wani tsari na zamani,  makamin zai iya kaucewa harin makami mai linzami na makiya ta hanyar tsarin rungumar kasa yayin da yake kai hari, Wannan wani bangare ne na karfin sojin kasar kuma da sannu za su kara inganta karfin makami mai linzami na fatah 4,...
    Cibiyar nazarin fasahar sadarwa ta kasar Sin ta bayyana cewa, an samu bunkasa sosai a fannin kere-keren fasahar kirkirarriyar basira (AI) ta kasar Sin, inda yawan kamfanonin bangaren ya zarce 5,300 a watan Satumba, wanda ya kai kashi 15 cikin 100 na dukkan adadin na duniya baki daya. Mizanin kudin masana’antar ya zarce yuan biliyan 900 (kimanin dalar Amurka biliyan 126.7) a shekarar 2024, inda aka samu karuwarsa da kashi 24 cikin dari a ma’aunin shekara-shekara. Bangaren fasahar AI na kasar ya kafa cikakken tsarin masana’antu wanda ya kunshi tun daga kan kayayyakin aiki da ake bukata, zuwa fasalin abubuwan da za a aiwatar, da kuma manhajojin aikace-aikacen masana’antu. Cibiyar ta kara da cewa, kayayyakin manhajoji na zahiri da ake...
    Kyawawan sakamakon da aka samu a tsarin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar wanda a bana ake kammala karo na 14, sun nuna muhimmancin da ake bai wa rayuwar al’umma. A halin yanzu kasar Sin tana alfahari da tsarin kula da samar da ruwa mafi girma a duniya, inda ta mallaki manyan tafkunan adana ruwa fiye da 95,000, da manyan ayyuka 200 na janyo ruwa zuwa yankunan da ba su da shi domin aikin gona da inganta rayuwa a birane. Zuba jarin kasar a bangaren bincike da samarwa (R&D) ya karu da kashi 50%, wanda hakan ya haifar da samun nasarorin kimiyya masu yawa a cikin kasa har ma da duniya.   Bangaren samar da ci gaba mara gurbata muhalli...
    Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ya jaddada ƙudirinsa na yin aiki tare da Gidauniyar Malala a ƙoƙarinta na ci gaba da bunƙasa ilimi da magance ƙalubalen da ke hana miliyoyin yara, musamman ’yan mata rashin zuwa makaranta. Da yake yi wa Malala Yousafzai  maraba a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya, Babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai a ofishin Mohammed Malick Fall, ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya zata yi aiki tare da gidauniyar Malala, wacce ta samu kyautar lambar yabo ta Nobel. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi mat An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja “Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake jaddada goyon bayanta ga asusun Malala wajen ganin ‘ya’ya mata da yawa suna samun...
    Rima hassan wani bafranshe mai nuna goyon bayan falasdinu kuma mamba a majalisar tarayyar turai kuma daya daga cikin tawagar Sumud flotilla ya sanar ta kafar sada zumunta cewa gobe ne ake saran tawagar flotilla za ta isa yankin Gaza duk da yake cewa Isra’ila ta tanadi tsauraran matakai na tunkararta. A daren jiya ma isra’ila takai kai hari kan tawagar ta Flotilla , wannan ya zo ne bayan da matukan jiragen ruwa guda biyu suka fitar da bayani cewa Isra’ila ta kai harin kan jiragen ruwansu guda biyu, inda avila yace sojojin Isra’ila sun yi amfani da yakin kwakwalwa ga wasu daga cikin tawagar flotilla inda suka yi musu kawanya Agefe daya mataimakin ministan harkokin wajen kasar Austreliya ya...
    Jakadan Iran na dindin a majalisar dinkin duniya yayi kira da a gaggauta kakabawa HKI takunkumi saboda hujjoji da ake da shi dake tabbatar da cewa tana kisan gillan ne kan alumma Gaza, kuma yayi tir da matsayin kasashen turai game da abin da ke faruwa a yankin gaza. A baya bayan nan kwamitin bincike mai zaman kansa ta majalisar dinkin duniya ya fitar da sakamakon bincike da ya tabbatar da irin kisan  gillan da HKI ke yi kan alummar falasdinu ,a gefe guda kuma kasar iran shugabar yan gwagwarmaya tana goyon bayan alummar falasdinu, Tun bayan harin 7 ga watan oktoba lokacin da kungiyar Hamas ta kai hari kan HKI  mutane da dama sun nuna kin jinin gwamnatin sahyuniya...
    Yau Najeriya ke cika shekaru 65 da samun ƴancin kai daga Turawan mulkin mallaka, inda aka saba gudanar da bukukuwa da kuma nazari dangane da ci gaban da ƙasar ta samu a ƙarƙashin mulkin ƴan ƙasa da kuma ƙalubalen da take fuskanta. Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da jama’ar ƙasar ke rayuwa a cikin mawuyacin hali, sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa waɗanda suka biyo bayan sauye-sauyen da gwamnatocin da suka gabata da kuma mai ci suka ƙaddamar da zummar sake fasalin tafiyar da ƙasar. A irin wannan rana a shekarar 1960, aka rantsar da Dr. Nnamdi Azikiwe a matsayin shugaban ƙasa, tare da Sir Abubakar Tafawa Balewa a matsayin Firaminista, shugabannin da suka yanke...
    A jiya 30 ga watan Satumba, firaministan kasar Sin Li Qiang ya mika sakon taya murna ga Safi Kharib bisa zama sabon firaministan kasar Algeria. Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da Algeria sun sada zumunta mai zurfi da juna. A cikin shekaru 67 da kulla dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu, an raya dangantakarsu yadda ya kamata, da yin kokari tare da nuna goyon baya ga juna. A watan Yuli na shekarar 2023, shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune ya kai ziyara a kasar Sin cikin nasara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da shugaba Tebboune, batun da ya samar da taswirar raya dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare. Sin ta maida hankali sosai kan raya dangantakar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      A cewar Wike, ana sa ran kamfanin CCECC zai kammala aikin gabanin kaddamar da fara amfani da titin nan da watan Yunin shekarar 2026. Tsarin aikin ya kunshi komai da komai, ba kawai shimfida titin ba har ma da gada mai ginshikai guda hudu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
    Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
    Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga y’in wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
    Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas (PENGASSAN), ta dakatar da yajin aikin kwanaki uku da ta fara biyo bayan rikici tsakaninta da matatar Dangote. Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Laraba. Hatsarin Jirgin Ruwa: Adadin waɗanda suka rasu ya kai 26 a Kogi Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare Ƙungiyar ta kuma gargaɗi matatar Dangote da kada ta kaeya yarjejeniyar da aka cimma a ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro. Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, wanda ya sanar da janye yajin aikin, ya ce idan matatar ta karya yarjejeniyar, ƙungiyar ba za ta yi shiru ba. Rikicin ya samo asali ne bayan...
    Bello, ta kuma bayar da umarnin ƙara tsaro a duk faɗin ƙasar na , musamman a tashoshin mota, hanyoyin ruwa a jihohin da ke bakin teku, da kuma filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa. Samamen ya biyo bayan bayanan sirri daga masu ruwa da tsaki da abokan hulɗa, waɗanda suka sanar da hukumar cewa akwai mutane da ake shirin safararsu a filin jirgin Abuja. Bayan kusan sa’o’i 6 da aka gudanar ana bincike, an kama mutane biyar da ake zargi, sannan an ceto mutane 24 da aka so yin safarar su. Adekoye ya ce waɗanda aka ceto, masu shekaru tsakanin 15 zuwa 26 ne, kuma an ɗauko su daga jihohin Kano, Katsina, Oyo, Ondo da Ribas. An shirya kai...
    “Ina kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya rungumi zaman lafiya, kwanciyar hankali, da haɗin kai a gidajenmu, al’ummominmu, da fadin ƙasarmu. Tare, cikin haɗin kai da ƙauna, za mu iya gina Nijeriya ta mafarkinmu. Barka da ranar ‘Yancin Kai!” in ni Shettima.   Akan hakan, Shettima ya jinjinawa ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wanda ya samar da abubuwan ci gaban ƙasa, inda ya ƙara da cewa, idan aka ƙara haƙuri abubuwa za su yi kyau a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa ba za su bar irin waɗannan matakai su ɗauke hankalinsu daga manufar tabbatar da zaman lafiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana alhininta game da rasuwar aƙalla mutum 26 waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su. Mutanen sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Ibaji, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Ilushi a Jihar Edo. Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Kingsley Fanwo ne, ya bayyana hakan a Lokoja a ranar Laraba. Ya ce wannan lamari babban rashi ne, kuma gwamnatin jihar na miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu da al’ummar Ibaji gaba ɗaya. Gwamna Ahmed Usman Ododo, ya aike ta’aziyyarsa, inda ya ce gwamnatin jihar na tare da al’ummar Ibaji a wannan lokaci...
    Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare da kuma takaita zirga-zirgar makiyaya tsakanin kananan hukumomi daga ranar Laraba, daya ga watan Oktoban 2025. Shugaban kwamitin sasanta rikicin manoma da makiyaya na jihar, wanda kuma shi ne kwamishinan Ma’aikatar Noma da Kiwo ta jihar, Dakta Barnabas Malle, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar. Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya Sanarwar ta ce matakin na cikin tsare-tsaren tabbatar da zaman lafiya a lokacin kakar bana, wanda manoma ke girbe amfanin gonarsu. Daga cikin ƙa’idojin da aka kafa akwai hana kiwo daga ƙarfe 6 na yamma zuwa ƙarfe...
      ‘Yan ƙasashen ƙetare da suka karya dokar shige da fice ta Nijeriya za su fuskanci hukunci, wanda zai iya haɗawa da tara, kora, ko kuma yiwuwar hana sake shigowa Nijeriya nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya bayyana a jiya Talata kan cewa yana dab da fara tattaunawa ta karshe dangane da shirin Snapback wanda ya maida takunkuman tattalin arziki na MDD kan kasar bayan daukewa na shekaru 10. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a birnin NewYork na kasar Amurka, a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa tattaunawarsa da babban sakataren MDD kan shirin na Snapback na karshe. Ya ce a tattaunawar zai gabatarwa Antonio Guttres matsayin kasar Iran kan wannan matakin da kasashen E3 suka dauka a kan kasar Iran. Yace wannan ya nuna irin ketan da wadan nan kasashe sukewa JMI da kuma kiyayyar da suke nuna mata....
    Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, a jawabin da ya gabatarwa yan Najiya a safiyar yau Laraba daya ga watan Octoban shekara ta 2025, ya bayyana cewa a lokacinda ya karbi shugabancin kasar daga thohuwar gwamnati tattalin arzikin kasar tamkar ya rushe, amma ya kara dacewa, an wuce mafi munin halin. Shugaban ya bayyana haka ne lokacinda yake gabatar da jawabin ranar samun yencin kai karo na 65. Ya kuma bayyana cewa ya gabatar da sauye sauyen da dama wadanda suka sa al-amura suka fara komawa kamar yadda yakamata.  Daga ciki ya ce cire tallafin man fetur mai cike da cin hanci da rashawa, ya taimaka wajen rage barnan da akewa tattalin arzikin kasar. Ya ce: Mun zabi jin...
    Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdurrahim Musawi yay aba da shirin sojojin ruwan kasar na fuskantar duk wani harin da makiya zasu kawowa kasar daga yanzun, Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Musawi yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda ya kai ziyarar aiki a sansanin sojojin ruwa na sojojin kasar da kuma na rundunar IRGC a lardin Hurmuzgan. Musawi ya ganewa idanunsa makamai na kariya da kuma na kai hare-hare kan makiya wadanda rundunonin ruwa a bangarorin biyu suke da shi da kuma lafiyar sojojin, inda ya bayyana amincewar sa da shirye-shiryen nasu. Musawi ya kara da cewa daga karshen kallafeffen yakin kwanaki 12 wanda HKI da kuma Amurka suka dorawa kasar...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa aiwatar da yarjeniya ta musamman da kasar china a halin da ake ciki a yankin da kuma yadda duniya take sauyawa da sauri ya zama wajibi ga kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin da yake gabatar da sakon murna ga gwamnatin kasar China kan cika shekaru 76 da kafuwar kasar. Wanda kuma itace ranar kasa a kasar ta China. Pezeshkiyan ya kara da cewa wannan ranar ta samuwar kasar China, rana ce da hadin kai da ci gaba da kuma godewa ga irin ci gaban da kasar ta samu daga lokacin zuwa yanzu a cikin gida da kuma fagen kasa da...
    Tawagar jiragen ruwan ‘Usturah’ masu rajin karya kofar ragon da aka yiwa Gaza, sun bada labarin cewa sojojin ruwa na HKI sun kai masu hare-hare a safiyar yau Laraba. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta bayyana cewa, majiyar ta bayyana cewa al-amarin akwai hatsari amma duk da haka zasu ci gaba da hanyarsu ta zuwa Gaza, duk tare da wadannan hattsurran. Labarin ya kara da cewa, jirgin Alman, ya gamu da hare-hare daga yahudawan wanda ya tilasta masa jada baya zuwa wani waje. Banda ya an yanke dukkan kafafen sadarwa da waje. Gwamnatin yahudawan dai sun sha alwashin hana dukkan jiragen Ustura isa gaza, kuma ta bayyana cewa ta tura jiragen ruwan yaki, wadanda suka kama dukka mutanen da suke cikin...
    Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, saboda yadda ya siyasantar da aikinsa. Kiran na zuwa ne bayan kwamishinan tare da ilahirin dakarun rundunar a jihar sun kaurace wa halartar bikin tunawa da ranar samun ’yancin kai da aka gudanar a jihar. A bisa al’ada dai Gwamna kan jagoranci hukumomin tsaro wajen gudanar da faretin bikin ranar a duk ranar daya ga watan Oktoba. To sai dai a bana, ba a ga Kwamishinan ’Yan Sandan na Kano ba, sannan babu ko dan sanda daya a wajen bikin. Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya Sojoji sun kama ’yan sandan bogi da motoci...
      A shekarar da ta gabata, Nijeriya ta ƙuduri aniyar samar da gangar ɗanyen mai 445,000 a kowace rana ga matatar a cikin kuɗin gida (Naira).   Jami’an gwamnati sun yi nuni da cewa, shirin, idan ya yi nasara, za a iya fadada shi zuwa sauran matatun mai na masu zaman kansu da ke cikin kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dakarun sojin Najeriya sun kama wasu mutum biyu da ke sanye da kayan ’yan sanda dauke da motoci biyu kirar Hilux da ke makare da tabar wiwi a jihar Taraba. Dakarun rundunar sojojin ta shida tare da hadin gwiwar jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ne suka sami nasarar cafke mutanen bayan samun sahihin bayanan sirri. Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya An haifi jariri da ‘fuska biyu’ a Bauchi An cafke su ne a tashar Takum da ke karamar hukumar Wukari, suna sanye da kayan jami’an ’yan sandan kwantar da tarzoma. An gano cewa motocin biyu kirar Toyota Hilux da ake tuhuma cike suke da kayan da ake zargin tabar wiwi ce. ‘Yan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Tarayya ta ce Kungiyar Ma’aikatan Harkokin Man Fetur da Gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta amince da janye yajin aikin da take yi, bayan zaman sulhun kwanaki biyu da aka gudanar tare da shugabannin matatar man Dangote. Zaman sulhun da aka gudanar a ranakun 29 da 30 ga Satumba, 2025, ya gudana ne a karkashin jagorancin Ministan Kwadago da samar da Ayyukan Yi, Dr. Mohammed Maigari Dingyadi, tare da halartar manyan jami’an gwamnati, hukumomin tsaro, da wakilan kungiyoyin kwadago. Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya Abin da ya faru a zaman sulhun PENGASSAN da Matatar Ɗangote A cikin sanarwar da aka fitar bayan kammala zaman, Minista Dingyadi ya ce yajin aikin na PENGASSAN ya biyo bayan sallamar...
    Shekara guda bayan shahadar Sayyed Hassan Nasrallah, yanayin siyasa da zamantakewar yankin ya sake yin tasiri da tunawa da shi. Nan da nan kuma shahadarsa ta zama wani muhimmin batu na samun hadin kai a tsakanin kungiyoyi masu adawa da mamaya da kuma sabunta himma ga manufofin tsayin daka. Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya yi shahada a ranar Juma’a 27 ga watan Satumba, 2024, a wani hari da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai a yankin Dahiyeh da ke kudancin birnin Beirut. Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Pars Today cewa, Shahid Hasan Nasrallah ya jagoranci kungiyar Hizbullah tun a farkon shekarun 1990, kuma...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa kasar ta shiga sabon salo na gyaran tattalin arziki, kuma matsin da ake ciki na dab da wucewa su zama tarihi. A cikin jawabinsa ga ’yan kasa don bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yancin kai, shugaban ya ce gwamnatinsa ta damu da radadin da mutane ke ciki sakamakon gyare-gyaren da ake aiwatarwa. Sai dai ya jaddada cewa da Najeriya ba ta dauki matakan da ta dauka ba, da tuni ta shiga halin karyewar tattalin arziki. Yunwa na kashe ’yan Najeriya, amma Tinubu ko a jikinsa – Atiku DAGA LARABA: Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai Tinubu ya tuna da jaruman da suka...
    An kuma amince da cewa ma’aikatan da aka kora za a mayar da su kan ayyukan su cikin wasu kamfanoni na rukunin Dangote ba tare da sun yi asarar albashi ba, kuma babu wani ma’aikaci da za a ci zarafinsa saboda rawar da ya taka a wannan taƙaddamar.     An cimma matsayar ne a gaban manyan jami’an gwamnati da suka hada da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ministan kudi kuma mai kula da tattalin arziki, ministan kasafin kudi da tsare-tsare, karamin ministan albarkatun man fetur (Gas) da shugabannin NMDPRA da NUPRC, da wakilan kamfanin man fetur na kasa (NNPCL).   Haka kuma shugabannin kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) sun halarci tattaunawar tare da shugabannin kungiyar ta...
    Sama da al’ummomi 100 a karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara sun samu ayyukan raya kasa don kyautata rayuwa ga mazauna.   Shugaban zartarwa na karamar hukumar Ifelodun, Alhaji Abdulrasheed Yusuf, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ayyukan gwamnatinsa a cikin shekara daya da ta gabata, yayin da ya ke gabatar da wani shirin Newskeg of the Correspondents’ Chapel na NUJ, majalisar jihar Kwara, wanda aka gudanar a Ilorin.   Ya lissafta ayyuka da dama da aka kammala, wadanda suka hada da gine-gine da gyaran cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a Oke-Ode, Labaka Oja, Adanla, Ofarese, Ijaya-Share, da Ajapa, da samar da kayan aikin likita da samar da muhimman magunguna a fadin cibiyoyin...
    A wani lamari da ba kasafai ake samu ba, wata mata mai suna Hannatu ta haifi jariri mai fuska biyu da kai daya a babban asibitin gwamnatin jihar Bauchi da ke garin Azare. Mahaifin jaririn, Malam Bala Sa’idu wanda yake a kauyen Magonshi, ya bayyana wa Aminiya cewa wannan haihuwar wata alama ce ta ikon Allah da ke tabbatar da cewa babu abin da Allah ba zai iya ba. Ya ce duk da cewa lamarin ya bambanta da yadda aka saba, amma bai zo masa da mamaki ba. Yunwa na kashe ’yan Najeriya, amma Tinubu ko a jikinsa – Atiku Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya A cewarsa, goyon cikin da matarsa ta yi ya...
    Tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliya  ta kasa da kasa,Muhammmad El-Baradei ya ce, Shirin na Trump akan Gaza ba komai ba ne sai kokarin tilasta larabawa su mika wuya, su kuma rusuna. Muhammad El-Baradei ya wallafa a shafinsa na X cewa; na saurari taron manema labaru a fadar White House akan Gaza, amma na fada cikin damuwa mai tsanani akan halin da Gaza take ciki da kuma makomarta, haka nan kasashen larabawa baki daya.” Tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa ya kuma ce; Wannan Shirin ba komai ba ne, sai na neman a mika wuya a kuma rusuna, ba shiri ne na neman zaman lafiya ba.” Har ila yau, ya kuma yi suka akan yadda shugaban na kasar...
      Sauran matakan sun haɗa da haramta sayar da amfanin gona kafin makota su kammala girbi da hana girbi da fitar da amfanin gona da dare, kana ya da umarci manoma da makiyaya da su guji ɗaukar doka a hannunsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa ya bayar da umarnin aikewa da jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa dake dauke da makaman Nukiliya da su karaci gabar ruwan kasar Rasha, a matsayin kandagarko. Trump ya kara da cewa; A cikin kwanakin bayan an aiko mana sakon barazana daga Rasha, don haka na aike da jiragen ruwa masu makaman Nukiliya da shi ne makamai mafi hatsari.”  Shugaban kasar na Amurka ya riya cewa kasarsa tana gaba da kasashen Rasha da China da ci gaban shekau 25 a fagagen kimiyya dakuma kera jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa.” Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my...
    Kungiyoyin gwgawarmaya na Hamas da Jihadul-Islami sun sanar da kai  hari akan sojojin HKI da suke yin kutse a cikin yankin Gaza’ Rundunonin soja na  “Al-Kassam” na Hamas da ‘Sarayal-Qudus” na Jihadul-Islami sun ce sun kai hare-haren ne akan sojojin mamayar da su ka shiga cikin yankunan Arewa da kudancin Gaza. A jiya Talata dakarun na Kassam sun watsa sanarwar a shafinsa na “Telegram’ da a ciki ya kunshi cewa, sun kai hare-haren ne akan ‘yan mamaya a kusa asibitin Jordan da kudancin unguwar “Tal Hawa” a kudancin birnin Gaza. Haka nan kuma rundunar ta Kassam ta ce ta kai wani harin akan motar soja da ta shiga cikin wata makaranta ta ” Rahibatul-Wurdiyyah” dake Tallul-Hawa.”. Har ila yau dakarun...
    Sojojin na Yemen sun sanar da kai hari wani jirgin ruwa mai suna: MINERVAGRACHT’ saboda ya keta dokar hana zuwa tasoshin jiragen ruwan Falasdinu dake karkashin mamaya. Janar Yahya Sari ne ya yi wannan sanarwa yana mai kara da cewa; An kai harin ne akan ruwan tekun Aden ta hanyar amfani da wani makami mai linzami, ya kuwa shafi jirgin ruwan kai tsaye, yana kuma Shirin nutsewa. Kakakin sojojin Yemen din ya bayyana harin da cewa an kai shi ne saboda taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta da yi wa kisan kiyashi. Haka nan kuma ya ce za su ci gaba da kai hare-hare akan duk wani jirgin ruwa wanda ya yi kokarin zuwa HKI ta hanyoyin ruwan tekun “Red-Sea”...
    A yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Inda game da rahoton ci gaban Sin na 2025 da cibiyar nazarin samar da ci gaba ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar, Guo ya ce ci gaban Sin mai inganci ya samar da damammaki ga duniya. Dangane da furucin Amurka na cewa za ta kara haraji kan katako, da kayan da ake sarrafawa daga gare shi, da ake shigarwa kasar daga ketare, Guo Jiakun ya bayyana cewa, ba za a samu nasara a yakin ciniki da yakin haraji ba, kuma babu wata hanya ta fita daga ra’ayin ba da kariya ga kasuwa. Game da shawarar da Amurka ta gabatar...
    A yau Talata ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wani kundi mai kunshe da matsayin kasar dangane da kudurin MDD mai lamba 2758. Kundin ya bayyana cewa, a ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1971, da babban rinjaye taron MDD na 26 ya zartar da kuduri mai lamba 2758, wanda a cikinsa aka fayyace mayar da dukkanin hakkoki ga janhuriyar jama’ar kasar Sin, da amincewa da wakilan janhuriyar jama’ar kasar Sin a matsayin wakilan kasar Sin kadai a hukumomin MDD. Wannan kundi ya kuma fayyace komai dalla-dalla, tare da warware batun wakilcin Sin, ciki har da batun yankin Taiwan, a dandalin MDD a mahanga ta siyasa, da shari’a, da matakan aiwatarwa. Kuma tabbas halasci, da inganci, da...
    Ɓangarorin biyu sun tashi baran-baran a wata tattaunawar da suka yi ƙarƙashin jagorancin Ministan ƙwadago na Nijeriya, Mohammed Dingyadi a ranar Litinin.   Wannan yajin aiki na PENGASSAN ya shafi rufe ɓangarori da dama na harkar mai a Nijeriya, ciki kuwa har da babban kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, tare da dakatar da ba matatar Ɗangote ɗanyen mai.   Kungiyar ta PENGASSAN ta ja daga, inda ta bayyana cewa, “Muna kan bakar mu har yanzu, saboda mutanen mu da aka kora daga aiki, muna so dole a mayar da su.”   Wannan na zuwa ne a yayin da wata kotun Abuja ta bayar da umarnin hana yajin aikin ƙungiyar ta PENGASSAN da ɗaukar matakin hana kai wa matatar Ɗangote ɗanyen...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinjina wa ’yan Najeriya bisa abin da ya kira “juriya, haƙuri da ƙarfin halin da suke nunawa duk da matsin tattalin arziki da matsalolin tsaro” da ƙasar ke fuskanta.  A cikin saƙonsa na taya ’yan Nijeriya murnar zagayowar ranar samun ’yancin kai da ƙasar ta yi shekaru 65 da suka gabata, madugun adawar ya yi zargin cewa, gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki ta yi watsi da halin ƙaƙanikayi da ’yan ƙasar suka tsinci kansu a halin yanzu. A gaggauta binciko makasan ’yar jaridar Arise TV —Tinubu ’Yan sanda sun cafke ababen zargi 4 a Yobe Wazirin Adamawan ya bayyana damuwa kan yadda ’yan Najeriya ke rayuwa cikin ƙangin talauci, da yunwa, da rashin...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga daukacin jama’ar kasar Sin da su yi aiki tukuru, tare da ingiza wanzar da zamanantarwa irin ta Sin. Xi, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin Sin, ya yi kiran ne yayin taron bikin cika shekaru 76 da kafuwar janhuriyar jama’ar kasar Sin, wanda ya gudana yau Talata a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing. Shugaba Xi, ya jaddada cewa a gabar da yanayin harkokin duniya ke saurin sauyawa cikin sama da karni guda, dole ne a yi aiki tukuru wajen yayata akidun bai daya na dukkanin bil’adama, da aiwatar da tsarin cudanyar mabanbantan sassa, da ingiza aiwatar da shawarwarin bunkasa ci gaban...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu sun bayyana alhini kan kisan gillar da aka yi wa  Somtochukwu ‘Sommie’ Maduagwu, waata ’yar jarida mai gabatar da labarai a gidan Talabijin na ARISE TV. A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, shugaba Tinubu da uwargidansa sun yi Allah-wadai da kisan, suna mai bayyana cewa a matsayin babban rashi a ƙasar da kuma fagen aikin jarida. ’Yan sanda sun cafke ababen zargi 4 a Yobe An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa, marigayiyar ta rasu ne bayan wani farmaki da ’yan fashi suka kai gidanta da ke Katampe a Abuja, a ranar Litinin da ta gabata. Tinubu...
    Xi Jinping da sauran shugabannin sun yi tattaki zuwa gaban ginin, inda ya gyara furannin dake cikin kwandunan. Sannan ya zagaya ginin a wani mataki na nuna girmamawa. (Fa’iza Mustapha)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta cafke wasu mutane hudu da ake zargi da aikata laifuka iri-iri a sassa daban-daban na jihar, biyo bayan samamen da aka kai a kan wadanda ake zargi da aikata munanan laifuka. Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar, SP Dungus Abdulkarim ya fitar, ya ce kamen da aka yi ya nuna yadda rundunar ke jajircewa wajen kare doka da oda a fadin jihar. An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya A cewarsa, wannan mataki na daga cikin manyan dabarun tsaro da rundunar ta sanya gaba domin magance laifuka da hana su faruwa gaba daya. “A...
      Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan aiki daya tilo na karamci da adalci ya sake farfado da fatan ma’aikatan jinya da yawa a cikin gwamnatin ku da kuma a cikin ajandar sabunta fata na Shugaban kasa,” in ji sanarwar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da wani shiri na rajistar yara kyauta domin rage adadin waɗanda ke zaune gida ba tare da zuwa makaranta ba. Bincike ya nuna cewa fiye da yara 787,000 ne ba sa zuwa makaranta a faɗin jihar, wanda hakan ya sanya gwamnatin ta tashi tsaye wajen kawo sauyi a ɓangaren ilimi. Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja Uwargidan Gwamnan Gombe, Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, ce ta ƙaddamar da shirin a hukumance, inda ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na ganin kowane yaro ya samu damar karatu. A cewarta, shirin zai taimaka...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Iran zata iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran a yau, kamar irin abubuwan da ta faru a baya, za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali, da kuma cike da zaman lafiya, da abota, da zaman tare, da tattaunawa, kuma za ta iya sanya tausayi ya mamaye harshen bai daya ta hanyar yin amfani da arzikin al’adu. A cikin sakon da ya gabatar a wurin taron karrama mawakan Iran Shams Tabrizi da Mawlana Jalaluddin Mohammad Balkhi, shugaba Pezeshkian ya ce a ranar Talata: An ambaci ranakun 29 da 30 ga watan...
    Mataimakin shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Yakin kwanaki 12 da aka kaddamar kan Iran, gwaji ne na karfinta a fagen kimiyya da fasaha Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Arif ya bayyana cewa: Wani bangare na ci gaban Iran a fannin kimiyya da fasaha na da nasaba da mayar da takunkuman da aka kakaba mata zuwa ga damammaki da bunkasa ci gabanta. Ya yi bayanin cewa: “Yakin kwanaki 12 da gwamnatin Sahayoniyya da Amurka suka kakaba wa Iran, wani gwaji ne kan karfin kimiyya da fasaharta. Ya ce: Iran ta fi karfi tare da mai da hankali a bangarorin kimiyya da fasaha.” Arif ya jaddada cewa: Al’ummar Iran suna bin tafarkin shahidai da kuma ci gaba da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: An yi musayar saƙo kai tsaye da kuma ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka Ministan harlolin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Sakamakon wuce gona da iri da bukatun Amurka da kasashen Turai suke da su, ya sa an kasa cimma matsaya kan batun makamashin nukiliyar Iran. Ya ce: “Iran ba za ta amince da duk wata yarjejeniya da ba ta la’akari da muradun kasarta ba, zata aiwatar da abin da muradun kasar ke bukata, kuma Iran tana da yakinin cewa: Kwamitin koli na tsaron kasarta zai yanke shawarwari masu inganci da kyau.” Araqchi ya kara da cewa ga manema labarai a yammacin jiya Litinin a karshen...
    Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Janar Safawi ya bayyana cewa: An kashe matukan jirgin saman yakin Isra’ila 16 a harin da aka kaddamar kan Iran Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Yahya Rahim Safawi ya sanar da cewa: Iran ta harba makamai masu linzami sama da 500 kan haramtacciyar kasar Isra’ila a lokacin yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa. Ya tabbatar da cewa: An yi nasarar kashe matukan jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila akalla 16 a daya daga cikin hare-haren makamai masu linzami da aka kai kan cibiyar horar da matukan jirgi. Wannan ya zo ne a cikin jawabin da Manjo Janar Yahya Rahim Safavi ya...
    Ambaliyar ruwa a Sudan na barazana ga rayuwar dubban mutane tare da kara munana matsalolin jin kai Kogin Nilu ya mamaye yankuna da dama a Sudan, lamarin da ke barazana ga rayuwar dubban mutane. Ambaliyar ruwa ta lalata gonaki da kadarori a jihar Al-Jazirah da kewaye, lamarin da ya shafi dubban iyalai tare da barin su cikin bukatar tallafin gaggawa da matsuguni da abinci da magunguna. Haka zalika ruwan sama kamar da bakin kwarya ya dakatar da zirga-zirgar wasu jama’a a wasu yankuna, yayin hukumomin cikin gida suke kokarin rage barnar da ake amma lamarin ya foi karfinsu sakamakon karancin kayan aiki. Ambaliyar ruwan ta kara ta’azzara matsalar jin kai a birnin El Fasher da sauran garuruwa, inda mazauna garin...