Shin kun san, a lokacin da Sinawa suka hadu da juna, gaisuwar da suke yi ita ce, “Shin ka ci abinci?” Wannan gaisuwa mai sauki tana nuna damuwar mutanen dake rayuwa bisa aikin noma, wato ma’ana, tambaya ce a kan ko ana da isasshen abinci?

A halin yanzu, wannan gaisuwa mai cike da nuna damuwa, tana samun sauyi mai ban sha’awa a yankunan karkarar kasar Sin.

Dai Yihui, wadda ba ta wuce shekaru 30 da haihuwa ba, ta koma garinta na lardin Jiangsu, domin kula da gandun noma na iyalinta, inda ta yi kokarin kara yawan amfanin gona da kashi 35 bisa dari ta hanyar amfani da injunan noma na fasahar zamani, sai dai kuma mazauna garin sun canza gaisuwar gargajiya da ake yi daga “Shin kin ci abinci” zuwa “Yaya rayuwarki a garin?” Wannan gaisuwa ta nuna yadda irin gagaruman sauye-sauye da tsarin farfado da karkara a dukkan fannoni da ake kawo wa jama’ar kasar Sin.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11

’Yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 11 mazauna garin Isapa da ke kusa da Eruku a Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara.

Harin ya faru ne sa’o’i kadan bayan sakin wasu masu ibada da aka yi garkuwa da su suna tsaka da ibada a coci.

An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi

A cocin CAC da ke Ekuru, ana gudanar da bikin godiya domin murnar ’yantar da mambobi 18 da aka yi garkuwa da su kusan wata guda da ya gabata, sai ’yan bindiga suka kutsa suka yi garkuwa da mutum 38 bayan sun harbe uku har lahira.

Sabon harin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin Litinin, an ce ’yan bindiga kimanin 20 zuwa 30 ne suka kai shi.

Bayanai sun una cewa maharan su rika yin harbi ta ko’ina yayin da suke kutsa cikin garin, lamarin da ya sa mutane suka ranta a na kare.

Wata tsohuwa ta ji rauni sakamakon harbin kan mai uwa da wabi.

Wani jagoran al’umma da bai amince a bayyana sunansa ba, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce: “Mutane 11 aka yi garkuwa da su, bakwai daga cikin su ’yan gida ɗaya. Waɗanda aka sace sun haɗa da mace mai juna biyu, masu shayarwa biyu da kuma kananan yara.”

Shaidar y ace sunaye mutanen sun hada da Talatu Kabiru, 20, Magaji, 6, Kande, 5, Hadiza, 10, Mariam, 6, Saima, 5, Habibat (mahaifiya), Fatima Yusufu (mahaifiya), Sarah Sunday, 22 (mai juna biyu), Lami Fidelis, 23 (uwa mai shayarwa) da kuma Haja Na Allah, ita ma uwa mai shayarwa.

Shaidun gani da ido sun ce ’yan bindigar sun bi wasu sassa na garin, inda suka bar alamun ramukan harsashin harbe-harbe a bangon gidaje da ƙofofi.

An gano harsashin bindiga AK-47 da aka harba daga wurare da dama bayan ’yan bindigar sun ja da baya tare da mutanen da suka yi garkuwa da su.

Lamarin ya haifar da tsananin tashin hankali a yankin da makotan garuruwa, yayin da jami’an tsaro da ’yan sa-kai ke ƙara ƙoƙari wajen gano maharan da ceto waɗanda aka sace.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya tabbatar da lamarin ga yana mai cewa: “Eh, lamarin ya faru, amma ba zan iya cewa komai da yawa ba yanzu ba. Ina gab da shiga Isapa daga Ilorin. Zan ba da rahoto idan na isa.”

A yanzu haka dai Najeriya na fuskantar ɗaya daga cikin mafi munin matsalolin tsaro a tarihin ta. Hakan dai ya haifar da rufe makarantu da dama, musamman a Arewacin ƙasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan
  • Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
  • Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja
  • Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza