2025-12-12@22:27:25 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2902
«yankin Yammacin Kogin Jordan»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da shirinsa na ɗaga darajar Kwalejin Jinya ta Nafisatu da ke Kwankwaso zuwa cikakkiyar Jami’ar Kiwon Lafiya albarkacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa. Taron na wannan Talatar, 21 ga watan Oktoban 2025, ya gudana ne a garinsa na Kwankwaso da ke Karamar Hukumar Madobi, inda aka yaba da ci gaban da makarantar ta samu tun daga kafuwarta a 2019 zuwa yanzu. Tinubu ya naɗa sabon Minista Alƙaluman wucin-gadi na nuna Paul Biya ya lashe zaɓen Kamaru Kwankwaso ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin ƙara buɗe damammaki ga mata matasa su sami ilimin kiwon lafiya mai zurfi. Ya jaddada cewa makarantar ita ce ta farko a Najeriya da ke karɓar dalibai...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanyar Babban Sara zuwa Malam Bako zuwa Shabaru zuwa Kirgi zuwa Albasu, mai tsawon kilomita 28.2, a Karamar Hukumar Sule Tankarkar,wanda kudinsa ya kakaNaira Biliyan 4.47, a ci gaba da shirin Gwamnati da Jama’a. Aikin hanyar zai hada fiye da kauyuka 60 tare da karfafa harkokin kasuwanci da zamantakewa a yankin. Haka kuma, gwamnan ya bude sabuwar cibiyar kula da lafiya ta farko, da makarantar Tsangaya ta zamani, da kuma rukunin samar da ruwa a yankin. Gwamna Namadi ya bayyana cewa shirin Gwamnati da Jama’a hanya ce ta karfafa gaskiya, bayyana ayyuka da kuma baiwa jama’a damar fadin ra’ayoyinsu. “Mun zo ne mu nuna abin da muka...
Harkokin kasuwanci sun tsaya cik a wasu sassan Abuja sakamakon zanga-zangar neman a saki shugaban ƙungiyar ’yan ta’addan IPOB da ke neman ɓallewa daga Najeriya, Nnamdi Kanu, inda masu ’yan kasuwa da ma’aikata da dama suka yi asarar kuɗaɗen shiga. A yankunan Wuse, Banex da Mararaba, shaguna da kasuwanni da dama sun kasance a rufe saboda fargabar tashin hankali. Wasu ’yan kasuwa da suka gwada buɗe shaguna sun ce babu ciniki. “Na kasa buɗe shagona yau saboda kowa yana tsoron tashin hankali. Ko da ka bude, babu wanda zai fito saye da wannan yanayin tsoro,” in ji Peter Ayuba, mai sayar da na’urorin lantarki a kasuwar Wuse. A Smart Bridge Plaza da Zuma Garden da ke unguwar Utako, yawancin shaguna...
Najeriya: ‘Yansanda A Abuja Sun Yi Amsani Da Hayakin Mai Sa Hawaye Kan Masu Neman A Saki Nnamdi Kanu
A jiya litinin ce masu goyon bayan Nnamdi Kanu shugaban kungiyar neman kafa kasar Biafara (IPOP) daga tarayyar Najeriya, wanda ake tsare da shugaban kungiyar tare da tuhumar ayyukan ta’addan sun fito zanga-zanga suka kuma tushe wata babban titi a Abuja. ‘Yansanda sun jefa masu hayakin teargas don tarwatse su a jiya litinin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa Kanu wanda yake da Passport na kasar Burtania ya yi kokarin wanke kansa daga tuhumar da ake masa tun 2021 amma ya kasa. Kanu yana jagorantar kungiyar IPOP tun da dadewa, da nufin samar da kasar Biafara a yankin kudu maso gabacin Najeriya. Kafin haka dai yan kabilar Ibo sun yi kokarin bellewa daga tarayyar Najeriya a...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar Cerebral Palsy, wato tsukewar ƙwaƙwalwa, na daga cikin manyan matsalolin lafiyar yara da ke tasowa tun daga haihuwa. Wannan cuta tana faruwa ne sakamakon rauni ko lalacewar wani ɓangare na ƙwaƙwalwa da ke kula da motsi, magana, da daidaiton jiki. A mafi yawan lokuta, cutar tana bayyana ne tun daga ƙuruciya, a wasu lokutan kuma kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayyana, cutar na faruwa ne tun kafin a haifi yaro. Ko ta waɗanne irin hanyoyi wannan cuta take kama yaro? NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu? DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027 October 17, 2025 Siyasa Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu October 16, 2025 Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025
Fitaccen jarumin barkwancin finafinan Indiyan nan Asrani ra rasu. Asrani, wanda asalin sunansa shi ne Govardhan Asrani, ya rasu yana mai shekaru 84, kuma ya shafe sama da shekara 50 yana fitowa a finafinan Indiya, inda ya fito a finafinai sama da 350. Dan wasan finafinan, ya shahara wajen taka rawar barkwanci da kuma ƙaramin jarumi wanda ake kira da mai taimaka wa jarumi wato supporting actor. Daga cikin fina-finansa da suka yi fice akwai Sholay, inda ya fito a matsayin ɗansand da Bawarchi da Chupke-Chupke da Hera Pheri da Muqabla da Dhamaal da Yamla Pagla Deewana da Dillagi da Welcome da Bhool Bhulaiya da Garam Masala da Baghban da The Burning Train da Ajnabee da Seeta aur Geeta da...
Wakilin Amurka Na Musamman A Siriya Ya Matsa Don Ganin Kasashen Saudiyya Da Lebanon Da Kuma Siriya Sun Kulla Alaka Da Isra’ila
Wakilin Amurka na Musamman a kasar Siriya ya matsa kaimi domin ganin kasashen Saudiyya da Lebanon da kuma Siriya sun kulla alakar jakadanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Wakilin Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack, ya gabatar da manufofinsa na sake fasalin yankin Gabas taTsakiya a siyasance bayan kawo karshen yakin Gaza. A cikin dogon hangen nesa, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, Barrack ya yi ikirarin cewa abu mafi muhimmanci shi ne samar da zaman lafiya a yankin, da kwance damarar Hizbullah, da shigar da kasashen Labanon da Siriya cikin yarjejeniyoyin kyautata alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa Saudiyya ma tana dab da kyautata alakarta da haramtacciyar kasar Isra’ila. Barrak ya bayyana cewa: Taron Sharm...
Kungiyar kare hakkin dan Adama ta Amnesty International ta ce: Gwamnatin Tanzaniya ta wurga yanayin tsoro tare da tsananta danniya gabanin babban zaben kasar Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi mahukuntan Tanzaniya da haifar da yanayin tsoro da kuma tsananta danniya gabanin babban zaben da aka shirya yi a ranar 29 ga watan Oktoba, tare da yin amfani da dabarun yaki da ‘yan adawa, ‘yan jarida, kungiyoyin farar hula, da masu kare hakkin bil’adama. Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin shugaba Samia Hassan na ci gaba da ayyukanta na danniya da suka hada da kama mutane ba bisa ka’ida ba, tilasta bacewar mutane, da kuma kashe-kashen ba bisa ka’ida ba, ba tare da hukunta wadanda suka...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta October 20, 2025 Manyan Labarai Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi October 19, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna October 19, 2025
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Alkalan Najeriya su kasance masu gaskiya, rikon amana da tsoron Allah wajen yanke hukunci. Ya ce duk wata al’umma tana fara rushewa ne idan bangaren shari’a ya lalace. Ya bayyana cewa gwamnati na kokarin inganta walwala da albashin Alkalan domin karfafa ikon cin gashin kansu. Da yake bude taron bita na EFCC da NJI a Abuja, Shugaban wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta ya ce adalcin Alkalai ne ginshikin ci gaban kasa. Ya nuna damuwa kan yadda ake jinkirta shari’o’in manyan laifukan rashawa, yana mai cewa an fi hanzarta shari’ar masu laifin yanar gizo. Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba a taba kare kowa saboda siyasa a gwamnatinsa ba, inda ya bayyana cewa EFCC...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Alkalan Najeriya su kasance masu gaskiya, rikon amana da tsoron Allah wajen yanke hukunci. Ya ce duk wata al’umma tana fara rushewa ne idan bangaren shari’a ya lalace. Ya bayyana cewa gwamnati na kokarin inganta walwala da albashin Alkalan domin karfafa ikon cin gashin kansu. Da yake bude taron bita na EFCC da NJI a Abuja, Shugaban wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta ya ce adalcin Alkalai ne ginshikin ci gaban kasa. Ya nuna damuwa kan yadda ake jinkirta shari’o’in manyan laifukan rashawa, yana mai cewa an fi hanzarta shari’ar masu laifin yanar gizo. Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba a taba kare kowa saboda siyasa a gwamnatinsa ba, inda ya bayyana cewa EFCC...
Morocco ta ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 a karon farko a tarihin gasar, bayan ta doke Argentina da ci 2 da nema, tawagar da ta fi kowace ƙasa a duniya lashewa a tarihi Wannan gagarumar nasara ya sa ta zama ƙasar Afirka ta biyu da ta ɗaga wannan kofi bayan Ghana, wadda ta yi nasara a shekarar 2009. Gwamnonin Kano, Katsina da Jigawa sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa wutar lantarki Kano Pillars ta dakatar da Kocinta A yammacin jiya Lahadi ce aka gudanar da wasan ƙarshe a filin wasa na Estadio Nacional Julio Martínez Prádanos da ke birnin Santiago na Chile, gidan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Universidad de Chile da kuma babbar tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar. ‘Yan wasan tawagar ƙwallon...
Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada kudirinta na inganta harkar kiwon lafiya a fadin kasar nan, daidai da manufar sabunta kudiri na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wato Renewed Hope Agenda. Wannan tabbacin ya fito ne daga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, yayin da yake ziyarar duba ayyukan gine-gine da ke gudana a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), wanda shi ne ya tallafa wajen samar da su. Yayin da yake magana da ’yan jarida a lokacin ziyarar, Sanata Barau ya ce wadannan ayyuka na da nufin kara karfin cibiyoyin kiwon lafiya a cikin gida, tare da rage yawan tafiyar da ake yi zuwa kasashen waje domin neman magani, ta hanyar samar da ingantattun kayan aiki a asibitocin cikin gida....
Don haka, an nada “tsohon kaftin din kungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, tare da mai horar da masu tsaron gida, Suleiman Shuaibu, su maye gurbin wadanda aka sallama na dan wucin gadi. Bugu da kari, Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai taimakawa wadanda aka nada na dan wucin gadin”. LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kungiyar mai taken ‘Sai Masu Gida’ tana fama a ‘yan makonnin nan. Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta kuma ci tarar kungiyar tarar kudi sama da Naira miliyan 9 biyo bayan rikicin da ya ɓarke a yayin da suke karawa da wata kungiya a filin wasa na Sani Abacha. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja October 20, 2025 Labarai Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba October 20, 2025 Manyan Labarai ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta October 20, 2025
An ce wanda ake zargi da kisan, sananne ne a garin Zing saboda yawo a kan tituna, sanye da fararen kaya yana yin kamar yana wa’azi. Wakilinmu ya ruwaito cewa, lamarin da ya faru da misalin karfe 11 na daren ranar Asabar, ya jefa al’ummar garin Zing da kewaye cikin rudani kan hakikanin yanayin lafiyar wanda ake zargin. “Daga cikin wadanda suka jikkata akwai ’yan banga guda biyu, wadanda a baya suka yi kokarin hana wanda ake zargin shiga jama’a saboda irin halayyarsa,” in ji wani ganau. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta October 20, 2025 Labarai Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC October...
“Rundunar ‘yansandan sashi ‘C’, Asaba, karkashin jagorancin CSP Ogbe Emmanuel, sun samu nasarar tare wata mota ɗauke da alburusai da aka nufi jihar Edo da su. “A yayin da jami’an suke gudanar da binciken motoci na yau da kullum a kan babbar gadar Asaba, jami’an sun yi nasarar tare wata mota kirar ‘Toyota Hiace Hummer Bus’ mai lamba NGK 16 XB, wacce wani Ozoemenam Sylvanus ke tukawa. “Yadda Direban, ke amsa tambayoyi cikin rashin nutsuwa, ya jawo jami’an suka fahimci cewa, ba shi da gaskiya inda suka gudanar da bincike sosai a kan motar, inda aka gano alburusai 400 da aka ɓoye a cikin motar. “Wanda ake zargin da farko ya yi karyar cewa makullai ne aciki,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan fara shari’ar Nnamdi Kanu a shekarar 2021 mutane da dama suke bayyana ra’ayoyinsu a kan sake shi ko a kyale shari’a ta yi halinta. Hasali ma har zanga-zanga wasu ‘yan Najeriya suka kira don bayyana bukatar sakin shugaban na ‘yan aware. NAJERIYA A YAU: Yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimakawa Dalibai Shiga Jami’a DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan ko ya dace a saki Nnamdi Kanu? Domin sauke shirin, latsa nan
An saki ɗan jarida, Ibrahim Ɗan’uwa Rano, bayan da ƴansanda suka tsare shi a shalƙwatar Rundunar Ƴansanda ta Zone 1 Kano bisa zargin batanci ga wani mutum. Sakin nasa ya biyo bayan suka da matsin lamba daga ƙungiyoyin fararen hula irinsu Cibiyar Fasahar Bayanai da Ci Gaban Jama’a (CITAD), da Amnesty International, da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, waɗanda suka bayyana tsarewar tasa a matsayin mataki na keta haƙƙin ɗan Adam da kuma yunƙurin danne ƴancin ƴan jaridu. Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya Ƙungiyoyin sun buƙaci a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba, suna mai cewa tsarewar ta saɓawa...
Sunana Aisha Isah Abubakar (Mai Waka) Gama: A gaskiya bawa yara kanana kudi wannan ba dabi’a ce mai kyau ba, saboda wata rana idan babu wannan kudi da aka sabawa yaro da shi wallahi illa ce babba. Sabida yau da gobe sai Allah idan suka rasa wannan kudi komai zai iya faruwa za su iya saka hannu su diba ako’ina, saboda su biya wa kansu bukatar su. Shawara ya kamata masu dabi’ar aiken yara su basu kudi dan Allah su daina, gara ku siyi ‘sweet’ idan yaro ya dawo a bashi ya fi a dauki kudi a bashi. Allah ya sa mu dace. Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa: To magana ta gaskiya sam-sam hakan bai dace...
’Yan sanda sun kama ɗan jarida Ibrahim Ishaq Dan’uwa Rano, kan zargin ɓata sunan Babban Hadimin Gwamnan Kano kan Al’amuran Fadar Gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo. Rahotanni sun bayyana cewa jami’an ’yan sanda daga Hedikwata ta Ɗaya ne suka kama Dan’uwa Rano a ranar Asabar yayin da yake aiki a ofishinsa da ke Kano. Magidanci na neman shawarar ’yan sanda kan ƙara aure a Kano Gwamnati ta ɗauki matakin rage shan gishiri a Nijeriya Shaidu sun ce an kama shi ba tare da gabatar da takardar izinin kama shi ba. Ana tsare da ɗan jaridar ne bisa zargin ɓata sunan hadimin cikin wani shirin barkwanci mai suna ‘Imalu’ da yake wallafawa a shafinsa na YouTube mai suna ‘Dan’uwa TV‘. An ce...
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, wanda ake zargin wanda aka ce shi ne Shugaban kungiyar ‘yan acaɓa reshen Ejiba, ya amsa cewa, ya siyo ƙwayoyin ne a wani shagon sayar da magunguna da ke Egbe domin kai wa abokan hulɗar sa da ke cikin dajin. Babban sakataren yaɗa labarai na shugaban karamar hukumar Yagba ta yamma, Adeyemi Babarinde Sunday, ya ce an kuma samu wanda ake zargin da kuɗi har ₦600,000, wanda ake zargin kudaden hada-hadar ta’addanci ne. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza October 19, 2025 Labarai Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani October 19, 2025 Manyan...
A ta bakin shugaban bikin, kuma gwamnan Jihar Tillabery Maina Boukar, taron na wannan karo ya shaida aniyar gwamnatin Nijar, ta bai wa wadanda suka rungumi shirin ajiye makamai damar sauya rayuwarsu, da taimaka musu wajen cimma nasarar komawa cikin al’umma cikin mutunci. Boukar ya ce, “Wannan muhimmin zabi, ya nuna aniyar gwamnatin Nijar ta kare ikon mulkin kai, da wanzar da tsaro, da tabbatar da zaman lafiya karkashin kyawawan manufofin kasa, ba tare da dogaro ga wasu ajandoji daga ketare ba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi October 19, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki October 18, 2025...
Haka zalika, an yi zargin cewa; bai kammala karatun digirinsa na farko ba, sannan kuma takardar shaidar yi wa kasa hidima (NYSC) da ya mika wa majalisar dokokin kasar da shugaban kasa ta bogi ce. Sai dai, ya zargi Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, da daukar nauyin zarge-zargen da ake yi masa na takardar shedar bogin, sakamakon dalilai na siyasa. Da yake magana ta bakin mai magana da yawunsa, Dakta Robert Ngwu, ministan ya ce; zargin da suke na siyasa ne, inda ya yi zargin cewa; gwamnan yana shirin shiga jam’iyyar APC mai mulki ne, wadda shi Nnaji ke da karfi a cikinta. Ya kara da cewa, “Mbah yana so ya fitar da Nnaji daga tsarin ne kwata-kwata, domin kuwa...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kuduri mai lamba 2231 ya ƙare aiki a yau A cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ministan harkokin wajen kasar Iran ya tabbatar da cewa a karshe kuduri mai lamba 2231 ya kare a yau, kuma duk wani kira na farfado da shi ko dawo da wa’adin kudirorin da ya kare, ba shi da wani tushe na shari’a, kuma ba zai iya haifar da wani tasiri na tilasta aiki da shi ba. Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Sayyid Abbas Araqchi ya aike da wasika zuwa ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugaban kwamitin sulhu...
Ya bayyana cewa a ‘yan watannin da suka gabata, rundunar ta kara kaimi wajen kai samame a wuraren da ake zargin yin laifuka a fadin jihar, a wani bangare na kokarinta na rage yawan shan miyagun kwayoyi da laifukan da suka shafi hakan, wadanda hukumomi ke cewa sau da dama su kan zama sanadin tashin hankali da aikata laifuka musamman tsakanin matasa. “Lokacin da barayin suka hango tawagar sintiri na kusantowa, sai suka tsere, suka bar tarin miyagun kwayoyi da wasu haramtattun abubuwa a wurin,” in ji Abdullahi. Mai magana da yawun rundunar ya lissafa abubuwan da aka kwato da suka hada da kwayoyin “Suck and Die,” Tramadol da Diazepam, inda ya ce an kwashe su gaba daya...
Jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Ruguza Gaza “ba abin da za a gaskata ba ne” domin an rusa yankin gaba daya Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai, Tom Fletcher, ya ce: Girman barnar da aka yi a zirin Gaza abu ne da ba za a taba mantawa da shi ba, yana mai jaddada cewa, “an ruguza komai tare da mai da yankin baraguzai,” yana mai nuni da irin barnar da aka yi wa ababen more rayuwa, da gidaje, da kashe fararen hula. A cikin wata sanarwa ga gidan talabijin na Al Jazeera, Fletcher ya nuna cewa an riga an fara shirin ba da agajin jin kai na kwanaki 60. Shiri ne mai...
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103 October 18, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai October 18, 2025 Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka October 18, 2025
Gwamna Radda ya jaddada cewa hukumomin tsaro kadai ba za su iya fada da ‘yan ta’adda ba, sai dai da gudummuwar ‘yan kasa. Ya yi kira ga ‘yan Nijeria da su zama masu sanya ido da kai rahotanni cikin gaggawa da bayar da ingantattun bayanai ga jami’an tsaro. Ya yaba wa gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu bisa inganta tsaro da maido da martabar tattalin arzikin kasar nan. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi October 18, 2025 Labarai Fitar Da Kudi Ta Haramtacciyar Hanya Na Kara Dagula Matsalar Tattalin Arziki – IMF October 18, 2025 Labarai Majalisar Wakilai Ta Gayyaci CBN Da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn October 17, 2025 Manyan Labarai Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja October 17, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda bayani kan cewa daga yau Asabar 18 ga watan Octoban shekara ta 2025, kudurin kwamitin tsaro na MDD wanda aka samar don goyon bayan aiwatar da yarjeniyar Nukliyar kasar Iran wacce aka fi sani da JCPOA ya kawo karshe. Don haka daga yau shirin Nukliyar kasar Iran ta koma karkashen yarjeniyar NPT, kuma za’a yi mu’amala da shirin kamar sauran kasashen karkashin kula na hukumar IAEA. Tsahar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na bada wannan sanarwan a safiyar Asabar ta kara da cewa dama kudurin na tsawon shekaru goma ne daga yau ta gama aiki. Daga yau shirin Nukliyar JMI zai ci gab aba tare da wani karin ka’idojin...
Tawagar sun gabatar da kansu ga babban sakataren hukumar gudanarwar ci gaban Jihar Katsina, Dakta Mustapha Shehu. Tawagar sun ce ziyarar wani bangare ne na shirye-shiryen gudanar da aikace-aikace domin inganta zaman lafiya da kuma sanar da tallafin jin kai ga ‘yan gudun hijira. Gwamnan Katsina ya yaba wa Bankin Duniya da ya yi hadin gwiwa da Jihar Katsina don fuskantar matsalolin tsaro da kuma tallafa wa ‘yan gudun hijira. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja October 17, 2025 Rahotonni Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya October 17, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu...
Shin menene makasudin shirya irin wannan taro na masu ruwa da tsaki akan sha’anin ilimi da aka gudanar a yau? Makasudin wannan taro shi ne a fadakar da mutane ayyukan wannan hukuma ta TETFUND da take yi, sannan kuma a yi magana da wadanda suka fi amfana da shi wannan tsari na TETFUND. Kamar jami’ai da makarantu da kuma dalibai sannan kuma a karbi shawarwari ga jama’a akan yadda za a bunkasa wannan aikin na hukumar tallafawa manyan makarantu na gaba da Sakandire a Nijeriya. Wannan shi ne makasudi kuma na farko da ake san a jawo al’umma a ciki su dan abinda ake yi da yadda ake kashe kudaden da kuma yadda ake tarawa da makasudin tara su...
Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka, inda ta gudanar da samame a wata maɓoya da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci da safarar ƙwayoyi a cikin jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ta bayyana cewa jami’an da ke ƙarƙashin Gombe Division ne suka gudanar da samamen da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Alhamis 10 ga Oktoba, 2025. Dantawaye ya zama sabon kwamishinan ’yan sandan Abuja Wani mutum ya ƙona tsohuwar budurwarsa a Oyo A cewar sanarwar, jami’an sun kai samamen wata maɓoya da ke bayan jerin shagunan Ƙaramar hukumar Gombe, (Local Government Shopping Complex), inda ake zargin...
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ta sanar da nadin CP Dantawaye Miller a matsayin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja. Ya karɓi ragamar aikin ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Oktoba, 2025, daga hannun CP Ajao Adewale, wanda Babban Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa, Kayode Egbetokun, ya sauya wa wajen aiki. Wani mutum ya ƙona tsohuwar budurwarsa a Oyo Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar, sabon kwamishinan ya bayyana cewa zai ci gaba da inganta tsaro tare da bunkasa haɗin kai tsakanin ’yan sanda da al’ummar Abuja. Ta ce CP Miller ya yi alkawarin...
Abin da ya rage yanzu shi ne za a zuba ido don ganin irin sauyin da zai kawo na tsaro a birnin tarayyar, sakamakon taɓarɓarewar tsaro da ya addinin garin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025 Manyan Labarai Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa October 16, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC October 16, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima October 17, 2025 Labarai Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma October 17, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025
Baya ga yi masu afuwa, Shuagaba Tinubu, ya kuma karama su da lambar yabo ta kasa. ‘Yan Ogonin su tara, sun dai fuskanci shari’a ne, bisa zarginsu da kitsa kisan sarakunan Ogoni Albert Badey, Edward Kobani, Theophilus Orage da kuma Samuel Orage. Kotu ta tuhumi ‘yan Ogonin su tara, ta kuma yanke masu hukuncin rataya a ranar 10 ga watan Numambar 1995. Hukucin na Kotun, a wancan lokacin, ya haifar da hatsaniya tare da yin suka daga bangaren manyan shugabannin kasasshen duniya, daidaikun mutane da sauran kungiyoyi, musaman duba da cewa, an yanke masu hukuncin ne, a lokacin da ‘yan kasar ke nuna tsanar mulkin soji, biyo bayan soke zaben shugaban kasa, da ake da yakinin an yi sahihin zabe...
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, taron goron gayyata ne na kafa Nijeriya a matsayin cibiyar samar da makamashi tare da sabuntawa a Afirka, sannan kuma sauyin da aka samu na makamashi Nijeriya, ya bayar da damar zuba jari na sama da dala biliyan 410, daga tsakanin yanzu zuwa shekarar 2060. Ya kara da cewa, “Daga cikin wannan, ana kuma bukatar sama da Naira biliyan 23, domin fadada hanyoyin samar da makamashin da kuma hada miliyoyin ‘yan Nijeriya, wadanda har yanzu suke rayuwa cikin matsalar wutar lantarki, amma yanzu babban burinmu shi ne, samar da tsarin samar da wutar lantarki mai karfin mega wat 277, nan da shekarar 2060. Cikar wannan buri, ya wuce batun zuba hannun jari kadai, domin...
Saboda haka mu saki ilimi, mu ba ilimi hanya kar mu ji tsoro, mu je mu nemo shi duk inda yake kayanmu ne. Manzon Allah ya ce “ilimi hikima ce kayan mumini ne, saboda haka kar ka ji tsoro, ba wanda ya fi karfin Allah, ba wanda ya fi karfin Manzon Allah (S.A.W.). saboda haka ba wanda zai je ya shiga halwa ko ya shiga wani tunani ko ya shiga kaza har ya zo “summa dana fatadalla”, ba wanda zai zo nan sai dai Manzon Allah (S.A.W.). Dan haka Sufaye ba sa jin tsoron ko waye zai yi maganar ilimi, ba sa jin tsoron ko wane littafi bare damuwa, haka kuma ba a iya kada su, saboda duk abin da...
A baya- bayan nan ‘yan ta’addan wadanda suka daura damarar hanawa al’umma kwanciyar hankali sun kashe daruruwan mutane, kona gidaje tare da garkuwa da mutane ciki har da mata da kananan yara. Rahotanni daga yankunan sun tabbatar da yadda al’umma suka gaji suka kosa da jin alkawura marasa adadi daga gwamnati wadda ke kasa cikawa a yayin da hare-hare ke karuwa a duk shekara duk da karin kudaden tsaro da ake warewa.. A Sakkwato, kauyuka da dama kamar Giyawa, Kurawa, da Unguwar Lalle a gabascin Sakkwato hedikwatar gawurtaccen dan ta’adda Bello Turji sun fuskanci hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a baya- bayan nan. A Karamar Hukumar Sabon- Birni, wasu mazauna yankin sun tsere domin tsira da...
Tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Bayelsa, Israel Sunny-Goli, ya shawarci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da ya guji duk wata matsin lambar da wasu ƴan siyasa ke yi masa na ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Sunny-Goli ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin halartar shirin Politics Today na tashar Channels, inda yake mayar da martani kan ficewar gwamnan Bayelsa, Douye Diri, daga jam’iyyar PDP. Ya ce, “Ina ganin Jonathan zai karɓi wannan lamari da zuciya ɗaya saboda mutum ne mai son cigaban jiharsa. Duk da maganganun da ake yi kan zai tsaya takara, bana ina ganin zai yi kuskuren hakan saboda lokaci ya riga ya wuce.” Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya...
Sashen kashe radadi domin gudanar da aikin tiyata ga marasa lafia na asibitin gwamnatin tarayya FMC da ke garin Birnin Kudu a jihar Jigawa ya gudanar da bikin ranar bada maganin radadi ta duniya ta bana. Kungiyar ma’aikatan bada maganin kashe radadi dan yin aikin tiyata ta Duniya ce ta kebe ranar 16 ga wata Oktobar kowacce shekara domin bikin wannan rana. Shekaru 170 ke nan da fara amfani da maganin kashe radadi, inda wasu likitoci su ka yi gwajin wannan magani a asibitin birnin Massachusetts na kasar Amurka, abin da ya kawo sauyi wajen yi wa marasa Lafia aikin tiyata daga shekara 1846. Malam Aliyu Umar Yusuf na sashen bada maganin kashe radadi na asibitin gwamnatin tarayya FMC...
Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa a koda yaushe makiya suna neman haifar da rikici tsakanin kasashen musulmi domin raunana su, yana mai nuni da barkewar tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan. Mr. Pezeshkian ya bayyana haka ne a yayin wani taro inda ya fayyace matsayin kasar Iran dangane da takun saka tsakanin kasashen musulmi a gabashin kasar Iran. Shugaban ya kara da cewa rikicin baya-bayan nan tsakanin Afghanistan da Pakistan ya haifar da damuwa sosai a tsakanin dukkanin kasashen yankin ciki har da Iran da ke da iyaka da kasashen biyu. Ya kara da cewa, Iran za ta yi iyakacin kokarinta na ganin an rage zaman dar-dar, da inganta tattaunawa, da karfafa dankon zumunci a tsakanin...
“Muna roƙon Allah (T) Ya kawo mana ƙarshen wannan matsala ta tsaro a duk faɗin Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya.” Lamarin ya jawo damuwa daga al’umma da shugabannin siyasa, yayin da hukumomin tsaro ke ƙara ƙoƙari wajen gano waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi da tabbatar da zaman lafiya a yankin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC October 16, 2025 Labarai Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku October 16, 2025 Manyan Labarai Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025
Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi
Haka kuma, shugabar kasar Iceland Halla Tomasdottir ta ce, a matsayin wata babbar kasa, kiran da kasar Sin ta yi yana da muhimmanci ga sauran kasashen duniya. Ayyukan da kasar Sin ta yi a fannin tabbatar da ci gaban mata da daidaiton jinsi, sun kasance abin koyi ga kasashen duniya. Bugu da kari, shugabar kasar Dominica Sylvanie Burton, ta ce jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a yayin taron kolin mata na duniya, ya samar da sabon karfi ga raya ci gaban mata bisa dukkan fannoni, kuma kasarta na fatan ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni da dama. (Mai Fassara: Maryam Yang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ɗaga...
Hichilema ya kuma jinjinawa kamfanonin Sin, bisa yadda suke inganta darajar albarkatun dake kasarsa ta hanyoyin zuba jari, kana ya godewa Sin bisa yadda ta bude kasuwanninta ga Zambia da ma sauran sassan nahiyar Afirka baki daya. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan October 15, 2025 Daga Birnin Sin Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji October 15, 2025 Daga Birnin Sin Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia October 15, 2025
An fara tantancewar da misalin ƙarfe 12:55 na rana, inda ake sa ran Farfesa Amupitan zai gabatar da tarihinsa da kuma amsa tambayoyin da ‘yan majalisar za su yi masa, kafin yanke shawara kan tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban INEC. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025 Manyan Labarai Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki October 16, 2025 Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP October 15, 2025 Manyan Labarai 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa October 15, 2025
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama gungun mutane 11 da ake zargi da kasancewa ’yan fashi da makami da ke addabar matafiya a kan hanyar Katsina zuwa Kano. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abubakar Aliyu, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba a Katsina cewa waɗanda ake zargin sun kware wajen tare hanyoyin zuwa Sha’iskawa-Charanchi da Katsina-Kankia-Kano, suna kwace dukiyoyin matafiya. DSS ta cafke tsoffin jami’anta 2 kan aikata zamba Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi Ya bayyana sunayen waɗanda aka kama da suka haɗa da Dikko Ma’aru, Dardau Kabir, Muntari Musa, Labaran Amadu, Usman Ma’aru, Lawal Zubairu, Nasiru Sanusi, da Adamu Kabir. Sauran sun haɗa da Abdullahi Zubairu, Muhammad...
Baba-Ahmed, ya bayyana cewa, abin da danginsa suka fuskanta a hannun masu garkuwa da mutane a bara ya tabbatar masa da cewa rashin tsaro a yanzu yana da nasaba da siyasa. Ya kuma danganta kisan jama’ar da aka yi wa mabiya Shi’a a Zariya a shekarar 2015 da wani shiri na gwamnati don murƙushe masu sukarsu a wancan lokaci. Ya jaddada cewa El-Rufai da jam’iyyar APC ba za su iya tserewa daga alhakin halin da Nijeriya ke ciki na rashin tsaro ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025 Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Sanata Ahmed Wadada Aliyu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bayyana shi a matsayin ma’aikaci mai tawali’u, mai aminci, kuma mai kishin kasa wanda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasa abin a yaba ne. Shugaban ya yaba wa Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma kuma shugaban kwamitin majalisar dattijai kan asusun gwamnati bisa “kishin sa na gaskiya, rikon amana, tsarin kasafin kudi, da dokoki masu tasiri da ke magana kan makomar kasarmu.” Da yake karin haske kan tarihin Sanata Wadada a Majalisar Dokoki ta kasa, Shugaba Tinubu ya lura cewa “a cikin shekaru biyu kacal a Majalisar Dattawa, kun bambanta kanku a cikin doka, wakilci, da kuma kulawa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cire darasin Lissafi daga jerin wajibcin da ake buƙata domin samun shiga manyan makarantu ya samu karɓuwa daga wasu ɓangarori na dalibai da malamai. Wasu dalibai sun nuna farin ciki da wannan mataki, suna ganin zai sauƙaƙa musu damar samun shiga jami’a da sauran manyan makarantu ba tare da shan wahalar lissafi ba. Sai dai wasu masana sun bayyana cewa, duk da wannan sauƙin, ya kamata a yi taka-tsantsan saboda lissafi na taka muhimmiyar rawa wajen gina tunani da fahimtar ilimin fasaha, kimiyya da injiniya. Wannan ya sa ake tambaya ko cire lissafi daga wajabcin shiga manyan makarantu ba zai iya rage ingancin dalibai a nan gaba ba. NAJERIYA A YAU: Shin...
Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya
An tallafawa ‘yan Kasuwa ƙanana, kuma an rage fitar da hayakin da ke gurɓata muhalli a faɗin nahiyar Afirka. Gwamna Uba Sani ya bayyana wannan nasara a matsayin babbar gagarumar bajinta da kuma abin alfahari ga Jihar Kaduna da NIjeriya baki ɗaya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire domin bunƙasa tattalin arziki da bai wa matasa dama. “Wannan nasara ta sake tabbatar da ƙwarewar ƙirƙira da ƙarfin tunanin matasan Jihar Kaduna. Muna gina tattalin arzikin da ke dogaro da kirkira wanda ke daraja ra’ayi tare da haɓaka baiwa” in ji Gwamna Uba Sani. “Daga ajujuwa zuwa manyan matakan duniya, matasan Kaduna suna jagorantar makomar...
Rahotanni sun bayyana cewa rikici na kara Kamari tsakanin kasashen Pakistan da kuma Afghanistan inda dakarun sojin kasar Pakistan suka sanar da cewa sun tarwatsa tankokin yakin kasar Afghanistan guda 6 kuma an samu mummunar asara a cikin dakarunta a arangama da aka yi a yankin Kurram. Bayan tsagaita wuta na dan wani lokaci fadan ya sake rikicewa tsakanin dakarun sojin Pakistan da na mayakan Taliban, inda Islam abad ta zargi Kabul da bada mafaka ga kungiyoyin yan ta’adda dake kawo rashin zaman lafiya a yanki, arangamar da akayi a baya bayan nan ta nun irin tashin hankali da ake ciki a iyakokin kasashen biyu Kakakin sojin kasar Pakistan ya bayyana cewa dakarun kungiyar Taliban sun kaddamar da hari kan...
A ɓangaren hauhawar farashin abinci a watan Satumba na 2025, ya dawo kashi 20.9 cikin 100 a maimakon kashi 37.77 cikin 100 a cikin watan Satumban 2024 ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa October 15, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako October 15, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara October 15, 2025
Bugu da kari, shugaba Xi ya ce a shirye yake ya hada hannu da Patrick Herminie wajen aiwatar da sakamakon taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC a matsayin wata dama ta ci gaba da daukaka dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa manyan matakai da kara kyautatawa jama’arsu. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya October 14, 2025 Daga Birnin Sin Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani October 14, 2025 Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka...
Ministan Yada Labarai Mohammed Idris, ya bayyana Jihar Borno a matsayin jiha mafi juriya a Najeriya, yana jaddada gagarumar nasararta wajen shawo kan ƙalubale da dama tsawon shekaru. Yayin wata ziyarar ban-girma da ya kai wa Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Umar Isa Kadafur, a Maiduguri, Ministan ya yaba wa mutanen jihar bisa jajircewarsu da himmarsu wajen fuskantar matsaloli. Wannan ziyara na daga cikin shirye-shiryen taron Kwamitin Kwamishinonin Yada Labarai na jam’iyyar APC. Ya bayyana cewa abubuwan da suka faru a Borno cikin shekaru goma da suka wuce sun nuna jarumtaka da haƙurin mutanen jihar, waɗanda ke ci gaba da ginawa da tafiya gaba duk da matsalolin da suka fuskanta. Ministan ya jaddada cewa ƙarfin gwiwar mutanen Borno abin alfahari...
Amma ya nuna damuwa cewa jinkiri wajen aiwatar da yarjejeniyar da gwamnati ta yi da ASUU na ƙara haifar da rashin jituwa. Ya roƙi Shugaba Tinubu, da ya sa baki kai-tsaye don kawo ƙarshen rikicin, yana mai gargaɗin cewa jinkiri wajen ɗaukar mataki na iya gurgunta ci gaban da aka samu a fannin ilimi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa October 15, 2025 Labarai Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu October 15, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako October 15, 2025
’Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da sace dabbobi da dama a wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Kankia a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin, inda aka kashe wani mazaunin ƙauyen Kwadawa da ke yankin Gachi, yayin da wani kuma ya jikkata. Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP Kotu ta umarci a tono gawarwakin wadanda gobara ta kashe a Legas don yin bincike Shaidu sun ce kimanin ’yan bindiga 100 ne suka kai harin, inda suka kuma mamaye ƙauyen Bogga; ƙauyen Fulani da ke kan hanyar Kankia zuwa Ingawa. Sakamakon haka, mazauna ƙauyukan Bogga, Taiba Badole, Arahiya Kwandawa, Rumawa, Gangara da Rugar Bindo duk da ke yankunan Gachi da Fakuwa/Kafindangi, sun tsere daga...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya kungiyar kwallon kafa ta kasaSuper Eagles murnar nasarar da suka samu ta ci 4 da nema a kan Cheetahs ta Jamhuriyar Benin, tare da yabawa ƙungiyar bisa ƙoƙarin da take yi na ci gaba da kokarin cika al’umma, yayin da suke neman cancantar zuwa gasar cin Kofin Duniya ta FIFA a shekarar 2026. Shugaban ƙasar ya jinjina wa Super Eagles bisa ƙwazo, da jajircewar da suka nuna a filin wasa na Uyo, yana mai cewa wannan gagarumar nasarar ta sake karfafa ‘yan Najeriya kan harkar ƙwallon ƙafa. “Yanayin farin ciki da ake ciki a fadin ƙasar nan na nuni da yakinin da muke da shi cewa Najeriya ta cancanci samun gurbi a gasar...
Yansanda a kasar Italia sun kara da masu zanga zanga masu kuma goyon bayan Falasdinawa, don hana a gudanar da wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta HKI da kuma ta kasar Italia a filin wasa na Udine a jiya Talata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Italia ta aika yansanda fiye da 1000 guda, tare da jiragen sama masu saukar ungulu don hana masu zanga –zangar isa filin wasan. Labarin ya kara da cewa zanga-zangar wacce kwamitin masu goyon Falasdinawa ya shirya. Zanga-zangar don hana wasan ta ilimunation wato fidda goni na masuhalattar gasar duniya ta FIF 2026. Daga karshe dai an yi gasar kuma kasar Italiya ta lallasa HKI da 3-0....
Ya kuma roƙi shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka su haɗe kai wajen yaƙi da ƙungiyoyi masu amfani da ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, inda ya bayyana cewa irin waɗannan ayyuka suna ƙara haifar da tashin hankali da talauci. Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, shi ma ya yi kira ga ƙasashen yankin su amince da yarjejeniyar ECOWAS kan cin hanci, domin hana masu rashawa samun wajen ɓuya. “Mu tabbatar babu inda ɓarayi za su ɓuya. Duk wanda yake tayar da hankali a ƙasashenmu bai kamata ya samu natsuwa ba,” in ji Fagbemi. Ƙungiyar NACIWA ƙungiya ce ta hukumomin yaƙi da cin hanci daga ƙasashen ECOWAS, wadda ke aiki tare wajen yaƙi da rashawa. Shugaban ƙungiyar na yanzu shi ne Ola Olukoyede, wanda kuma...
“Kusan kullum muna cikin tashin hankali a Shinkafi,” in ji shi. Mutumin ya kuma zargi gwamnati daga matakin tarayya har zuwa ƙaramar hukuma da zuba wa matsalar ido. “Hare-haren suna ci gaba a Birnin Yero, Jangeru, Shanawa, da Shinkafi kanta. Ko jiya da safe sun kawo hari sun kama manoma.” A cewarsa, manoma da dama sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron za a sace su. Wasu kuma suna zuwa da dare ne kawai don samun ɗan abin da za su ci. Sai dai, gwamnatin Jihar Zamfara ta ce tana sane da matsalar da jama’ar yankin ke fuskanta, kuma tana ɗaukar matakai don magance ta. Mai magana da yawun gwamna, Mustafa Jafaru Kaura, ya ce: “Gwamnati tana yin duk abin da...
‘Yansanda sun kuma samu kuɗi Naira 92,460 da wasu abubuwan maye kamar giya da sauransu. “Wannan samame sakon gargaɗi ne ga duk masu hannu a fataucin miyagun ƙwayoyi,” in ji SP Adam. “Yaƙinmu da fataucin miyagun ƙwayoyi yana ci gaba, kuma muna kira ga jama’a su riƙa sanar da mu duk wani abin da suka gani na zargi.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara October 15, 2025 Manyan Labarai Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima October 15, 2025 Labarai Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria October 14, 2025
Shugaban Kasar Columbia Ya Soki Donald Trump Akan Bai Wa Isra’ila Makamai Shugaban na kasar Columbia Gustavo Petro ya ce, Bugun kirjin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na bai wa “Isra’ila” makamai tare da cewa ta yi amfani da su da kyau, ba wani abu ne da ya cancanci a yi masa tafi, sunan shi tarayya a aikata laifi. Shugaba Gustavo Petro yana mayar da martani ne akan zancen da shugaban kasar Amurka ya yi a Majalisar “Knesset’ ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya ce; Isra’ilan ta yi amfani da makaman da ya ba ta da kyau. Shugaba Gustavo ya kara da cewa; wadannan makaman na Amurka sun kashe mutane 70,000 sannan kuma sun jikkata wasu 200,000....
“Salon shugabancinsa da amincewa da cancanta sama da son rai ne ya sa kowane mai kishin ci gaba daga ƙarshe yake samun mafaka a APC,” in ji shi. Gwamna Mbah ya bayyana shiga jam’iyyar APC bayan tattaunawa da magoya bayansa, yana mai cewa hakan “sabuwar tafiya ce” ga Jihar Enugu da yankin Kudu maso Gabas wajen samun babban matsayi a siyasar ƙasa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta October 14, 2025 Manyan Labarai Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato October 14, 2025 Siyasa PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai October...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yadda ‘ya’yan jamiyyar PDP ke ficewa suna komawa jam’iyya mai mulki na cigaba da nuna yadda take kara samun koma baya a siyasar Najeriya. Banda haka, rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa na cigaba da yi mata dabaibayi. Shin ko hakan na nufin jam’iyyar ta fara gushewa ne a siyasar Najeriya? NAJERIYA A YAU: Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Yajin Aiki? DAGA LARABA: Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraci Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Sojoji sun kama wata mata da mijinta da suka yi kaurin suna wajen safarar makamai a yankin Saminaka da ke Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna. Dubun ma’auratan ta cika ne a wani shingen binciken inda sojojin Rundunar Operation Fansan Yamma suka gano harsasai 1,207 hannunsu. Kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom ya ce an kama su ne a hanyars ta kai wa ’yan ta’addan da ke addabar yankin Arewa maso Yamma makaman. Ya ce matar mai shekaru 18 mijin masi shekaru 40 suna tsare suna amsa tambayoyi, yana mai jinjina wa sojoji da ’yan banga bisa kwarewar da suka nuna wajen kama miyagun. Kofin Duniya: Da sauran rina a kaba duk da Najeriya ta ci Jamhuriyar Benin 4-0 Na yafe...
Tawagar Super Eagles ta Najeriya sun kara da Cheetahs na Jamhuriyar Benin a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026. Wasan da suka fafata a filin wasa na Godswil Akpabio da ke Jihar da Uyo ya kasance tamkar mai zafin gaske kuma an nuna bajinta. Tun kafin a fara wasan, an samu sauye-sauye hudu daga tawagar da ta doke Lesotho, inda Wilfred Ndidi ya hau matsayin kyaftin, yayin da Moses Simon ke shirin yin buga na 85 a wasannin kasa da kasa. A gaba kuma, an hada Victor Osimhen da Akor Adams domin tayar da kura. Wasan ya fara da sauri — ina minti na uku kacal, Osimhen ya zura kwallo ta farko bayan Chukwueze yi mika...
Dandazon ’yan bindiga sun kai hari a yankin Kankia da ke Jihar Katsina inda suka halaka mutum daya tare da jikkata wasu da dama. Shaidu sun ce ’yan bindiga kimanin 100 a kan babura ne suka kai harin a yankin Kwadawa da ke Gundumar Gashi da ke Karamar Hukumar Kankia, inda ake Ana zargin maharan sun kai harin daukar fansa ne, Maharan da suka kai farmaki a yankin da ke Gabahsin karamar hukumar, sun sace dabbobi da ba a san adadinsu ba, suna masu barazanar halaka duk mutanen yankin. Wakilinmu ya ruwaito cewa a halin yanzu mazauna yankunan Bogga, Taiba Badole, Arahiya, Kwandawa, Rumawa, Gangara da Rugar Bindo da ke gundumar Gachi da kuma Fakuwa/Kafindangi suna yin kaura domin tsira...
Rukaiya Abdullahi mawakiya ce a Masana’antar Kannywood wacce daga bisani kuma ta dawo yin fim duk a masana’antar. A hirarta da Aminiya ta bayyana yadda ta fara aiki a matsayin sakatariya ta ofishin daya daga cikin masu shirya fim. Ga yadda hirar ta kasance: Gabatar da kanki ? Sunana Rukaiya Abdullahi Yaushe kika shigo Masana’antar Kannywood? Na shigo Masana’antar Kannywood a shekarar 2020, amma zan samu kamar shekara 15 ina tare da su sai dai ban fara yin fim ba sai a 2020. Me ya jawo hankalinki kika shigo harkar fim? To da farko dai ba harkar fim na fara da ita ba a Kannywood, na fara da aikin sakatariya ne a wurin ’yan fim, yayan Nasiru Sarkin waka wato...
’Yan Majalisar Tarayya uku daga Jihar Kaduna sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Shugaban Majalisar Wakilai Abbas Tajuddeen ya sanar a ranar Talata cewa masu sauya shekar sun hada da Honorabul Abdulkarim Hussain Mohammed, Aliyu Mustapha Abdullahi da kuma Sadiq Ango Abdullahi. Tajuddeen, wanda shi ma dan asalin Jihar Kaduna ne, ya sanar da cewa, Gwamnan jihar, Uba Sani ya halarci zaman majalisar domin shaida dawowar ’yan majalisar zuwa APC daga PDP. Masu sauya shekar sun bayyana cewa rikin cikin gida da rabuwar kai da suka dabaibaye tsohuwar jam’iyyarsu ta PDP ce ta sa suka yanke shawarar sauya sheka. Shugaban Hukumar Zaɓen Yobe Jihar Yobe ya rasu Faɗa ya ɓarke tsakanin Palasɗinawa da Hamas bayan sulhu da Isra’ila...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa jami’an tsaron JMI suna cikin cikken shiri na kare kasar daga makiya, a duk lokacinda ta sake farma kasar da yaki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baghaei yana fadar haka a jiya litinin a taron yan jaridu da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin. Ya kuma kara da cewa JMI zata saurari shawarorin kawayenta amma kuma tana cikin shirin ko ta kwana idan makiya sun yi kuskure sun fadawa kasar da yaki. Baghaei ya na nuni ne da zantawar firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a makon da ya gabata, inda kuma ya bukaci shugaba...
“Idan mutum ya shiga jarrabawa kuma Allah Ya kawo dama ta afuwa, dole ne ya yi farin ciki. Ni da iyalina da masoyana mun yi murna ƙwarai,” in ji Lawan. “Na gode wa Allah da kuma Shugaba Tinubu saboda ya yi abin da ya kamata a yaba masa.” Ya bayyana cewa rayuwa a gidan yari ta koya masa juriya da fahimtar cewa komai ƙaddara ce. “Tun kafin na bar kotu na sallama komai ga Allah. Na sani cewa duk inda mutum ya samu kansa, akwai darasi a ciki,” in ji shi. Bayan fitowarsa daga gidan yari, Faruk Lawan ya sauya tafiyarsa ta siyasa. Ya ce ya rabu da tafiyar Kwankwasiyya da aka san shi da ita, duk da cewa har...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shekara da shekaru kungiyar malaman jami’oi ASUU ta kwashe ta na gudanar da yajin aiki ba tare da samun biyan bukata ba. Irin wannan yajin aiki da kungiyar malaman ke shiga ya jefa dalibai da malaman da ma harkar ilimi cikin halin ni ‘yasu a Najeriya. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa DAGA LARABA: Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraci Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wasu hanyoyin da kungiyar malaman ASUU za ta iya bi don warware matsalar ta ba tare da dogaro da gwamnatin tarayya ba. Domin sauke shirin, latsa nan
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) ta mayar da martani kan barazanar gwamnatin tarayya ta “ba aiki, ba a biya”, tana mai cewa ba za ta bari a tsoratar da ita da irin wannan gargaɗi ba. Shugaban ASUU, Chris Piwuna, ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today a ranar Litinin. Piwuna ya ce ASUU ta tsaya tsayin daka tare da sauran ƙungiyoyin Malamai kamar CONUA, da NAMDA, da SSANU, da NASU, wajen goyon bayan yajin aikin da ke gudana. Ya zargi Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, da ƙoƙarin rarraba malamai ta hanyar yin alƙawarin biyan wasu ma’aikata albashi. “Ya na ƙoƙarin rarraba kan mu, amma kan mu a haɗe yake. Babu wanda...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baqahea yayi gargadin game da barazanar da ake fuskanta na bazuwar fadan da ake yi a kan iyaka tsakanin kasar Afganistan da kuma kasar Pakistan, a yankin, inda dukkan bangarorin biyu suke musayar wuta a wurare daban daban dake kusa da iyakokin kasashen. Yace babban abin da ke da muhimmanci a wajen mu shi ne batun tsaro da zaman lafiya a kasashen dake makwabtaka da su, kasashen Pakistan da Afghanistan yan uwan mu ne musulmi dake makwabtaka da mu, kuma ya yi amanna cewa duk wani kace-nace tsakanin kasashen biyu to zai iya fantsama zuwa wasu kasashe, Jamhuriyar musulunci ta Iran ta yi kira ga kasashen biyu da su koma teburin tattaunawa, kuma...
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar wa al’ummar jihar a shirye ta ke ta ci gaba da kare mutuncin daidaikun mutane da kungiyoyin da suka sadaukar da kansu domin samar musu da sahihin bayanan sirri da za su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijar. ‘Yan sanda a jihar Neja da ma Nijeriya ƙwararru ne don haka za su ci gaba da aiki da kuma nuna basira da ƙwarewa tare da ƙa’idarta ta sirrin rashin bayyana tushen bayanansu don samun sakamako mafi girma. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Adamu Abdullahi Elleman wanda ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna, ya bayyana cewa a kwanan baya ya halarci wani taron...
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya caccaki matakin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dauka na fara yajin aiki na tsawon makonni biyu, yana mai bayyana matakin a matsayin wanda bai kamata ba kuma bai dace ba ganin irin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na biyan kusan dukkanin bukatun kungiyar. Da yake magana a wani shiri na gidan Talabijin na Channels, ‘The Morning Brief’ a ranar Litinin, Alausa ya bayyana rashin jin dadinsa da matakin da ASUU ta dauka na tsunduma yajin aiki duk da kokarin da gwamnatin ke yi akansu. “A cikin shekaru biyun da suka gabata, babu wani batun yajin aikin ASUU, saboda kokarin da gwamnati ke yi akan biyan duk bukatunsu. “A cikin sa’o’i 24 da...
Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar. Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta. Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako. Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista...
Na farko, hada kai don samar da yanayi mai kyau ga ci gaban mata. Na biyu, a karfafa abubuwan da za su habaka ingancin ayyukan mata cikin hadin kai. Kana na uku, a gina tsarin kare hakkin mata tare. Sai na hudu, a bude sabon babin hadin gwiwa tsakanin mata a duniya. Za a gudanar da taron kolin mata na duniya a yau da gobe Talata a birnin Beijing. Kuma tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, suka yi musafaha da shugabannin tawagogin kasashe, da kungiyoyin duniya da suka halarci taron, tare da daukar hotuna tare da su. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025 Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22 October 12, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025 Manyan Labarai Trump Da Al-Sisi Za Su Jagoranci Taron Zaman Lafiya Dawwamammiya Ta Gaza A Masar October 12, 2025 Manyan Labarai Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor October 12, 2025
Gwamnatin Tarayya, ta gargaɗi Ƙungiyar Malaman Kami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta aiwatar da dokar “babu aiki, babu albashi” idan malaman suka ci gaba da yajin aikin da ka iya zai kawo cikas ga harkokin karatu. A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar da yammacin ranar Lahadi, Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, da Ƙaramar Ministan Ilimi, Suwaiba Sa’id Ahmed, sun ce gwamnati tana da niyyar magance ƙorafe-ƙorafen ASUU ta hanyar tattaunawa cikin lumana. Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja “Gwamnati ta nuna gaskiya, haƙuri da kyakkyawar niyya a tattaunawarta da ƙungiyar,” in ji sanarwar. Ministocin sun bayyana cewa yawancin buƙatun ASUU, kamar ƙarin kuɗin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan October 12, 2025 Daga Birnin Sin Sharhi: Lai Qingde Ba Zai Iya Jirkita Gaskiya Ba October 12, 2025 Daga Birnin Sin Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza October 11, 2025
Wasu jerin shirye-shiryen neman ‘yancin kan Taiwan da hukumomin yankin suka gudanar a baya bayan nan, sun sha suka sosai daga al’ummomin kasa da kasa. Wani nazari da kafar CGTN ta Sin ta gudanar ya nuna cewa adadin mai rinjaye na wadanda suka shiga nazarin, watau kimanin kaso 89.8 sun yi ammana cewa, manufar kasar Sin daya tak ta zama wata matsaya da kasashen duniya suka amince da ita, inda suka soki hukumomin yankin Taiwan bisa shirinsu na neman ‘yanci da takala. Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne cikin harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 13,650 suka bayar da amsa cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sharhi:...
Sai dai duk da cewa Ousmane Dembele na kungiyar kwallon kafa ta PSG ne ya lashe gasar- Yamal ya samu nasarar kyautar gwarzon matashin dan wasa na Ballon d’Or karo na biyu a jere. Lamine Yamal, ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yanwasa mafiya farin jini tsakanin masoya kwallon kafa, musamman ma matasa saboda karancin shekarunsa da kuma yadda yake buga wasa cikin raha. Shekara da shekaru, duniya ta dauka cewa zama fitacce a fagen kwallon kafa na bukatar jajircewa da sadaukarwa. Saboda kafin dan wasa ya iya lashe wannan kyauta sai ya yi aiki tukuru. Sai dai duk da nuna kuruciyarsa, hakan bai hana Yamal cimma burinsa a fagen kwallon kafa ba. A baya ya bayyana...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar. Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi. Asuu ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata. “Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana. RN
A zahiri, zamanin da kasashen yammacin duniya ke ba da umarni ga kasashe masu tasowa ya riga ya wuce. An taba bin tsare-tsaren da kasashen yamma suka tanada, amma ba a samu nasarar da aka sa ran samu ba, wannan sakamako ya sa kasashe masu tasowa daina amincewa da huldar kasa da kasa da kasashen yamma suka tsara. Sai dai, ko wace irin sabuwar dangantakar sassan kasa da kasa muke bukata a zamanin yau? A matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta sha yin kira da a kafa sabon nau’in huldar kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna. Wannan tunani shi ma ya bayyana sarai...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Trump Da Al-Sisi Za Su Jagoranci Taron Zaman Lafiya Dawwamammiya Ta Gaza A Masar October 12, 2025 Manyan Labarai Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor October 12, 2025 Labarai Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa October 12, 2025
Garin Girfa (cinnamon), Garin kaninfari Clove) Yadda za a hada: Za’a samu garin girfa kamar cokali 5 garin kaninfari cokali 7 za a hade waje daya, sai a rika diban rabin karamin cokali ana zubawa a ruwan shayi ana sha sau 2 a rana ayi kamar sati daya. Za a samu waraka da yardar Allah. Ciwon Sanyi Abubuwan bukata: Hulba, Bagaruwa, Man Habbatussauda yadda za a hada: A hada Bagaruwa da Hulba a tafasa su, sai idan ya dan huce sai a zauna a ciki, sannan kuma za a shafa man Habbatussauda a gaban, a sashi kamar yadda za’a yi matsi. In sha Allah za a samu sauki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Adon Gari Ko Kin San… Dalilin...
Irabor ya ce, littafin nasa na ƙoƙarin kawo tarihin “tasirin Boko Haram a Nijeriya ta fannoni daban-daban” da kuma “hakikanin gaskiya a kan Boko Haram, wanda na samo a lokacin ina matsayin kwamandan soji na yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.” Tsohon babban hafsan tsaron ya ce, babban abinda ya fi tayar da hankali a yaki da Boko Haram shi ne yawan rayukan da aka rasa. A cewarsa, “irin rayukan mutanen da aka kashe a rikicin Boko Haram yana da yawa kuma ana iya kwatanta shi da annoba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna October 12, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Yi...
Abubuwan da ake bukata: Semovita (kamar kofi 3-4), Yis (Babban Cokali da rabi, idan kuna so ya tashi sosai), Suga (Babban cokali 2), Gishiri ( rabin cokali), Man gyada ko buta (Babban Cokali 2), Ruwa mai dumi (kusan 1–1½ kofi, gwargwadon yadda Semon ya sha) Yadda za a hada: Za a samu roba sai a zuba Semobita, yis, Sikari da Gishiri a kwano, a juya su da kyau, sannan a zuba ruwa, a zuba ruwan dumi a hankali a cikin hadin, a na gaurayawa har sai ya koma kulli. Sai a zuba man gyada ko Bota a ciki, a ci gaba da murzawa har kullun ya yi laushi ba ya manne ba. Sannan sai a rufe rubar da leda...
Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF) ta tabbatar da cewa ta dauki matakin gaggawa bayan faruwar lamarin inda aka aike da wani jirgin sama daga Legas domin jigilar tawagar zuwa Uyo, sai dai lamarin ya haifar da tsaiko a shirin da tawagar ta ke yi na tunkarar jamhuriyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0 October 9, 2025 Wasanni Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane October 7, 2025 Wasanni Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni October 6, 2025
Daga cikin wadanda shugaban kasar ta Nigeria ya yi wa afuwa da kawai Maryam Sanda ‘yar shekaru 37 wacce aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunta da kashe mijinta da wuka a 2017. Mai Magana da yawun shugaban kasa Bayo Onangua ya saki bayanin afuwar da shugaban kasar ya yi, wacce kuma ta hadad a Faruka Lawan tsohon dan majalisa da aka samu da laifin cin hanci da rashawa a 2021. Sai kuma Ken Saro-wiwa wanda dan fafutuka ne mai rajin kare muhalli a yankin Ogoni da aka zartarwa hukuncin kisa a 1995. Har ila yau afuwar ta shugaba Tunibu ta shafi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa wanda aka zartarwa da hukuncin kisa a 1986 saboda juyin Mulki....
Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa wannan titin ba na yankin Arewa kadai ba ne, ya bayyana shi a matsayin jijiyar ƙasa da ƙasa ne wadda ke haɗa yankuna daban-daban tare da ƙarfafa haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki. Ya kara da cewa titin Abuja- Kaduna da Kano na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Manufar Sabon Fata na (Renewed Hope Agenda), wadda ke nufin sabunta manyan gine-ginen ƙasa da inganta tattalin arziki. Yace “Wannan titi ba hanya ce kawai ba inda yace wata hanya ce ta tattalin arziki wadda ke haɗa mutane, kasuwanni, da dama a fadin Arewacin Nijeriya da ma bayan haka,” A nasa jawabin, Sanata Umahi ya yaba...
Nasarorin da kasar Sin ta samu a cikin gida, sun kafa ginshikin jagorancin duniya, wajen samar da ci gaban harkokin mata, musamman ta hanyar fitar da darussa, ta hanyar kyautata mu’amala tsakamnin bangarorin biyu. Babban misali shi ne yadda ake samun bunkasar dangantakar mata tsakanin kasashen Kenya da Sin, wadda aka inganta yayin ziyarar aiki da shugaban Kenya William Ruto ya kai kasar Sin a watan Afrilun bana. Kasashen biyu sun yi alkawarin zurfafa mu’amalar al’adu, ciki har da mu’amalar mata da matasa bisa tsarin dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Wadannan matakai sun kunshi fannoni kamar su tallafin karatu da horar da sana’o’i, kuma dukkansu sun haifar da babban sakamako. (Safiyah Ma) ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata. Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum. Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran...