2025-12-12@22:27:26 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2902
«yankin Yammacin Kogin Jordan»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta samu nasarar ceto mutum 10 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su tsawon watanni huɗu da suka gabata a Ƙaramar Hukumar Kagarko. A cikin sanarwar da kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka ceto har da yara masu shekaru ɗaya, uku da kuma 13. Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro DSP Mansir, ya ce ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen Kushe Makaranta, inda suka sace mutanen daga gidajensu sannan suka kai su dajin da ke kusa da Rijana. Rundunar, ta ce aikin ceto mutanen ya samu ne ta haɗin gwiwar...
Shugabannin masana’antu sun kuma yi kira ga gwamnati da ta daidaita tattalin arziki, inganta saukin gudanar da harkokin kasuwanci, da aiwatar da shirye-shiryen tallafi ga masana’antu na cikin gida. Bugu da kari, masana sun nuna cewa rikicin kudin waje da rashin daidaito a kimar musayar kudi su ne manyan matsaloli ga kamfanoni masu zaman kansu daga kasashen waje, inda kalubalen samun damar mayar da ribar kamfani zuwa kasashen waje da samun kudin waje ke rage amincewar masu zuba jari sosai kuma yana karfafa su su bar kasar. Binciken da LEADERSHIP Sunday ta gudanar ya nuna cewa yanayin tattalin arzikin Nijeriya ya sha wahala tun daga shekarar 2020, inda wasu kamfanoni suka rufe ayyukansu, ko suka yi kaura, ko...
Baya ga Maryam Sanda, Shugaba Tinubu ya kuma yafe wa wasu mutane da dama, ciki har da Janar Mamman Vatsa, Herbert Macaulay, da Faruku Lawan, wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne daga Jihar Kano. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025
Li ya ce kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jam’iyyar WPK, don ta bayar da jagoranci ga al’ummun kasar Koriya ta Arewa, wajen neman ci gaba bisa halin da kasar take ciki. A sa’i daya kuma, kasar Sin tana fatan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama, kamar aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare da kara musayar manyan jami’ai, da mu’amala kan manyan tsare-tsare, ta yadda za a inganta fahimtar siyasa a tsakanin kasashen biyu, tare da cimma sakamako mai kyau bisa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Koriya ta Arewa. (Mai Fassara: Maryam Yang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ma’aikatar Wajen...
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar wasu sojoji huɗu, bayan ’yan ta’adda sun kai hari yankin Ngamdu na Jihar Borno. Jihar Borno ta daɗe tana fama da hare-haren ta’addanci, musamman daga ƙungiyar Boko Haram. Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno An yi jana’izar sojojin da ’yan bindiga suka kashe a Kebbi Ko da yake wasu mazauna yankin sun ce sojoji 10 ne suka mutu, sai dai mai magana da yawun rundunar Operation Haɗin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, bai tabbatar da hakan ba cikin sanarwar ya fitar a ranar Juma’a. Amma rahotanni sun bayyana cewa sojoji huɗu ne suka mutu, yayin da wasu biyar suka jikkata a yayin harin. A cewar Kanar Sani, ’yan ta’addan sun yi amfani da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 9, 2025
Ya bayyana cewa an riga an hada wadanda aka ceto da iyalansu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike da aikin ceton domin gano wadanda suka aikata laifin da kuma kubutar da sauran wadanda ake tsare da su, idan suna nan. A halin da ake ciki kuma, kwamandan Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba da saurin daukar mataki da hadin kai tsakanin sojoji da ‘yansanda wanda ya kai ga nasarar aikin ceton. Ya sake jaddada kudirin rundunar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Jihar Taraba. Sai dai, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa sojoji da sauran hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar...
Mataimakin shugaban kasar Iran Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, batun kifar da gwamnatin JMI bayan yakin kwanaki 12 ya kuma fita daga abinda makiya zasu iya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar yanakalto mataimakin shugaban kasa na farko yana fadar haka a ranar Alhamis da ta gabata, ya kuma kara da cewa a cikin yakin kwanaki 12 wanda kasashen Amurka da HKI suka dorawa kasar sun so su kifar da gwamnatin JMI a cikin kwanaki 3 zuwa 4 amma suka kasa. Ya ce hatta babban sakataren MDD Antonio Guterres ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da shi dangane daha. Ya kuma tabbatar da cewa makiyan JMI ba zasu iya tumbuke tsarin ba. Yasashen yamma musamman Amurka suna kokarin...
Masu zanga-zanga a nan Iran a jiya jumma’a a manya-manyan garuruwan kasar bayan sallar Jumma’a sun bayyana goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu a Gaza, sannan sun bukaci HKI ta aiwatar da yarjeniyar da ta cimma da kungiyoyi masu gwagwarmaya. Har’ila yau sun bukaci a gaggauta shigo da abinci da magungunacikin zirin Gaza. Tashar talabijin talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga zangar wadanda suka hada da mata da maza, malaman addini, daliban jami’o’i da sauransu suna tattaki daga dandalin inkilab zuwa dandalin azadi. Har’ila yau sun rera wakoki na goyon bayan masu gwagwarmayar, dauke da hotunan shahidai da kuma shuwagabannin kawancen masu gwagwarmaya a yankin. An gudanar da jerin gwanon a cikin manya manyan biranen...
Rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwarta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara October 5, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ October 4, 2025 Tsaro Bayan Sulhu Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina September 22, 2025
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wani Shirin zaman lafiya da ya hada da dakatar da kisan kiyashi a Gaza Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan duk wani mataki ko wani yunkuri da ya hada da kawo karshen yakin kisan kiyashi a Gaza, janyewar sojojin mamayar Isra’ila, shigar da kayan agajin jin kai, sakin fursunonin Falastinawa, da kuma tabbatar da dukkanin hakkokin Falasdinawa. Haka kuma ta kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mai goyon bayan halastacciyar gwagwarmayar al’ummar Falastinu samun tabbatar da ‘yancin kai, ta yi amfani da dukkanin karfinta na diflomasiyya a cikin shekaru biyun da suka gabata, musamman...
Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya
Kasar Venezuela ta yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya tabbatar da cewa Amurka tana yin barazana zaman lafiyar duniya Kasar Venezuela ta yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince cewa; Lallai Amurka tana yin barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, saboda yadda sojojin Amurka suke shisshigi a tekun Caribbean, wannan batu ya zo ne a yayin zaman gaggawa na majalisar a jiya Juma’a. Wakilin dindindin na Venezuela a Majalisar Dinkin Duniya, Samuel Moncada, ya ce: “Suna ba da shawarar ayyuka uku ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya: Na farko, amincewa da barazanar zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa da sojojin Amurka suka haifar a cikin...
Ministar wadda ta je kamfanin domin daukar sabuwar motarta ta alfarma kirar Nord Demir SUB da kamfanin ya hada nataimakin Shugaban jami’ar na sashen kula da ilimi da gudanar da bincike Farfesa Bola Oboh da kuma Shugaban kamfanin Mista Oluwatobi Ajayi ne, suka karbi bakuncinta. A jawabin da ta gabatar a lokacin ziyarar ministar ta bayyana cewa,Duba da yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci wajen fitar da kaya zuwa ketare kamfanin zai iya yin amfani da wannan samar waken fitar da motocinsa zuwa ketare. Ta kara da cewa, Nijeriya na da gurare biyu ne da ake hada motoci da suka hada da, na wannan jami’ar da kuma na EPs, inda ta yi nuni da cewa, karfin da kamfanin ya ke da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata October 10, 2025
“Ta yaya Jonathan zai zama barazana? Mun doke shi a baya lokacin da PDP take kan mulki. “Idan mutum yana ganin cewa PDP ita ce kololuwar jam’iyya a Nijeriya, kuma ya sha kaye a lokacin da yake ganiyarsa, ina ganin sai makiyinsa ne kawai zai tilasta masa ya kara tsayawa takara a zaben 2027,” in ji shi. Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce a yanzu haka Jonathan ya kasance dan siyasa mai daraja, yana mai cewa komawa fagen siyasa na iya rage masa kima da kuma zubar masa da darajar da yake da shi a idon duniya. Ya jaddada cewa Jonathan ya samu damar nuna cewa mulki bai tsole masa ido ba, domin haka ne...
Aƙalla mutum takwas ’yan Ƙungiyar tsaro ta Civilian JTF ko ’yan ƙato da gora aka sanar an kashe a ƙauyen Dan Loto da ke Ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Harin dai na zuwa ne makonni biyu kacal bayan da wasu ’yan bindiga suka kai hari a wani masallaci tare da kashe wasu masallata biyar ciki har da wani Limami a ƙaramar hukumar. ’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali — Likita Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe Dan Loto yana cikin yankin Yandoton Daji, unguwar da ’yan bindigar suka kashe masu ibada biyar a ranar 26 ga Satumba, 2025. Binciken Daily Trust ya nuna cewa, ’yan bindigar sun yi wa ’yan ƙungiyar...
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, a gefen wani taro a kasar Tajakisatan da yake halatta a kasar ya bayyana ce firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya fada masa cewa ya isar da sakonsa ga gwamnatin JMI kan cewa yana son a warware matsalolin da ke tsakaninsa da JMI cikin lumana ba tare da tashin hankali ba. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana shugaba shugaban yana son yazama mai tsaga tsakani a rikicin da JMI take yi da HKI da kuma hukumar maikula da makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA, a dai dai lokacinda yake kiyaye dangantakarsa ta diblomasiyya da kasashen biyu. Putin ya kara da cewa ya sami sakonni daga HKI kan cewa mu fadawa Tehran HKI...
Wani Likitan ƙwaƙwalwa a Asibitin Neuropsychiatric Aro, a Abeokuta, Jihar Ogun, Dokta Emmanuel Abayomi ya ce kimanin mutane miliyan 60 ne ke fama da taɓin hankali a halin yanzu. Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma’a a Abeokuta a wajen wani taron ƙarawa juna sani da Ƙungiyar likitoci ta NAS ƙarƙashin Ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta ƙasa ta shirya domin tunawa da ranar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa ta duniya ta bana. Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna Shirin da Ash Montana Deck tare da haɗin gwiwar Atlantis, Americana 1 da Longhorn Deck suka yi wanda ya ja hankalin ‘yan sanda da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta samu nasarar ceto wasu mutum uku da aka sace, bayan wani samame da ta kai a jihohin Kano da Kaduna. Wannan na daga cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi domin yaƙi da laifuka da tabbatar da tsaron jama’a. ’Yan sanda sun manta hularsu a motar dalibi bayan karɓar ‘cin hancin’ N99,000 NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne tsakanin ranar 7 zuwa 9 ga watan Oktoba, 2025, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori. A cewar Kiyawa, samamen farko ya gudana ne a ranar...
“Akwai da yawa malamai marasa cancanta a cikin aikin. Muna da wadanda ke koyarwa a ajujuwa amma ba su da takardun shaidar koyarwa, musamman a makarantu masu zaman kansu,” in ji ta. Ta bayyana cewa, yayin da wasu mutane ke da sha’awar koyarwa da gaske, rashin horo na hukuma ya hana su shiga aikin koyarwa. Dr. Soyombo ta bayyana cewa TRCN a halin yanzu na da malamai masu rijista kusan miliyan 1.4, tare da shirin kara wannan adadi zuwa miliyan 20 cikin shekaru biyu masu zuwa ta hanyar dijital da saurin rajista. “Mun zamanantar da tsarinmu domin mutane da yawa su sami damar yin rijista,” in ji ta. “Kowane malami yana da bai wa ta musamman...
Wani dalibi mai suna Olawale Ayomide ya zargi wasu ’yan sanda da ke aiki a ofishin Igbeba da ke yankin Ijebu Ode a jihar Ogun da tatsar Naira 99,000 daga hannunsa ba bisa ka’ida ba. Ayomide ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, inda ya ce ɗaya daga cikin ’yan sandan da ake zargi ya manta hular aikinsa a cikin motar bayan sun aikata abin da ake zarginsu da yi. A cewarsa, ’yan sandan sun tsayar da shi ne a lokacin da yake tafiya daga Shagamu zuwa Ijebu-Ode a cikin motar mahaifiyarsa, inda suka zarge shi da tuƙi ba tare da lambar mota ba. Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya ’Yan...
Kazalika, tarihin Dimokiradiyyar kasar ya sha cin karo da kwam gaba kwam baya kusan za a iya cewa, tun bayan dawowar mulkin Demokaradiyya a 1979 da kuma sake dora kasar a wata turbar ta Demokiradiyyar a 1999. Alal misali, jamhuriyya ta hudu ta kasance ta jima sosai, amma kusan babu wasu ayyukan na inganta rayuwar ‘yan kasar da za a bigi Kirji a ce gasu an gani a kasar a zahiri. Idan aka dubi bangaren samar da hasken wutar lantarki kusan za a iya cewa, karni da dama da suka bace, har zuwa yau Nijeriya ta gaza samar da karfin wutar da kuma rabar da ita da ta kai karfin Megawatts 5,000 musamman duba da cewa, wannan adadin...
Yawan mace-mace ta hanyar cutar kwalarar, na faruwa ne duk da biliyoyin Nairori da aka ce gwamnati da abokan huldar kasa da kasa suna kashewa, domin kokarin ganin an dakile ta. Wadannan kudade sun hada da kason kasafin kudi na shekara-shekara, wanda ya kunshi miliyoyin Nairori; akwai dala miliyan 700 da bankin duniya ya bayar domin samar da tsaftataccen ruwa sha, tsaftar muhalli a fadin kasa baki-daya, tallafin dala miliyan 2 daga Majalisar Dinkin Duniya, dubban daruruwan allurar rigakafin cutar kwalara da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka bayar da sauran makamantansu. Alkaluman da aka samu daga cibiyar NCDC, sun nuna cewa a cikin 2020, kasar ta samu rahoton...
Ministan albarkatun mai na Jamhuriyar Nijar Sahabi Oumarou, ya gana da Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Nijar. A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna kan muhimamn batutuwa da suka shafi alakoki da ke tsakanin kasashe biyu da kuma yadda za a kara inganta su. Sannan kuma sun yi musayar ra’ayi kan hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta fuskar cin moriyar juna. Jamhriyar Nijar da Iran suna da kyakkawar alaka ta diflomasiyya, kamar yadda kuma suna yarjeniyoyi da dama da ayyukan hadin gwiwa a fagage daban-daban na diflomasiyya, cinikayya da bunkasa harkoki tattalin arziki da kimiyya da fasaha. Bangarorin biyu sun jaddada wajabcin ci gaba da tuntubar juna domin aiwatar da dukkanin yarjejeniyoyi da aka rattaba hannu a kansu a...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama mutum 26 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kwato makamai da kudade daga hannunsu. Daga cikin abubuwan da aka samu nasarar kwatowar har da bindigogi na gida guda huɗu, makamai masu hatsari da kuma tsabar kuɗi Naira 546,000 da ake zargin wani ɓangare ne na kuɗin fansa. Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC An kama waɗanda ake zargin ne a cikin jerin samame da aka gudanar daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2025, a sassa daban-daban na jihar. Samamen ya haɗa jami’ai daga sashen ’yan sanda na Anchau, Hukumar Kula da Tsaro...
Dare ya jaddada cewa Nijeriya kasa ce mai addinai da dama, wacce aka gina bisa juriya, zaman lafiya, da girmama juna tsakanin mabambantan addinai, al’ummomin da ya ce Tinubu ya shugabanta. Dare ya ambaci maganar Shugaban Kasa inda ya jaddada cewa Nijeriya “kasa ce mai cikakken ‘yanci da girma, wadda aka gina bisa bangaskiya da juriyar jama’arta,” ya kara da cewa “Babu wani addini da ake zalunta, kuma babu wata al’umma da aka ware.” Yana nuna misali da rayuwar Shugaban Kasa a matsayin shaida ta juriya da fahimtar addinai, Dare ya bayyana cewa Shugaba Tinubu, Musulmi ne da yake auren fasto mai bin addinin Kirista. Ya kuma ruwaito Shugaban yana cewa, “Gaba da kiyayya ba su da gurbi...
‘Yan majalisar dai sun amince da naɗin, inda Gwamna Ahmed Usman Ododo ya bayyana Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya. Dangane da kundin tsarin mulkin 1999 (kamar yadda aka gyara), yanzu Shugaba Tinubu zai aika da sunan Amupitan zuwa Majalisar Dattawa don tantancewa. Amupitan, mai shekaru 58, daga Ayetoro Gbede, karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi, Farfesa ne a fannin shari’a a Jami’ar Jos, Filato, kuma tsohon ɗalibin jami’ar ne. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta October 9, 2025 Manyan Labarai Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin October 9, 2025 Siyasa Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso...
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko October 8, 2025 Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025 Daga Birnin Sin Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana October 8, 2025
A yayin yanke hukuncin, kotu ta bayyana cewa: “Na farko (INEC) da na biyu (Farfesa Mahmood Yakubu) an yanke musu hukuncin tura su gidan gyaran hali saboda rashin bin hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Osogbo, Jihar Osun, ta bayar a shari’a mai lamba FHC/OS/CS/194/2024 a ranar 17 ga 5 Fabrairu, 2025.” Kotu ta kuma umarci Sufeton ‘yansanda na ƙasa da ya kama Yakubu tare da tabbatar da fara shari’ar hukuncin raina kotu cikin kwanaki bakwai daga ranar da aka yanke hukuncin. Bugu da ƙari, kotu ta ci tarar INEC da Yakubu Naira 100,000 domin biyan masu shigar da ƙarar saboda raina umarnin kotu. Masu shigar da ƙarar sun haɗa da Action Alliance, Farfesa Julius Adebowale, Injiniya Olowookere Alabi, Barrista...
ShareTweetSendShareMASU ALAKA WasanniBa Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane October 7, 2025WasanniYanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni October 6, 2025WasanniKwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar October 6, 2025
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi, za su fuskanci martani mai tsanani Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) Manjo Janar Mohammad Pakpour ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi a mashigar tekun Farisa, da mashigar Hormuz da tsibirin Iran, za su fuskanci hukunci mai tsauri, nan take, murkushewa, da kuma nadama. A cikin sakon taya murnar zagayowar ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, Manjo Janar Pakpour ya bayyana cewa: “A jajibirin ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, yana mika sakon taya murna ga babban matsayi na kwamandoji da mayakan da suka yi...
Shugaban kasar Ecuador ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi da aka yi Ministan Makamashi na Ecuador, Ines Manzano ya sanar a ranar Talata cewa: An yi yunkurin kashe shugaban kasar Daniel Noboa kuma an kama wasu mutane biyar da ke da hannu a ciki makarkashiyar. Manzano ya ce “Motar Noboa na kewaye da gungun mutane kusan 500 da suke jefanta da duwatsu a lokacin da yake tafiya a cikin ayarin motocin zuwa lardin Cañar, inda aka shirya zai sanar da jerin ayyukan samar da ababen more rayuwa.” Ta kara da cewa: “Daga baya an samu alamun harsashi a motar, amma Noboa bai samu rauni ba a harin.” Hukumomin kasar sun sanar da cewa: Wadanda ake tsare...
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da sabuwar cibiyar taro ta Ahmadu Bello da aka gina a Bauchi, inda ya bayyana ta a matsayin alamar ci gaba a gwamnatin Gwamna Bala Mohammed. Da yake jawabi a wajen taron, Obasanjo ya jaddada muhimmancin dunkulewar duniya, inda ya ce babu wata al’umma da za ta iya rayuwa a ware ba tare da yin hulda mai ma’ana da sauran kasashen duniya ba. Ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed bisa ayyukan raya kasa, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, wanda a cewarsa hakan zai karawa Bauchi damar karbar bakuncin taron kasa da kasa da kuma jawo hankalin masu zuba jari. Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa irin wadannan...
Gwamna AbdulRazaq ya yabawa Shugaba Tinubu yayin da Sojoji suka tura cikakken birgediya domin fatattakar masu garkuwa da mutane daga dazukan Kwara. Hedkwatar sojojin Najeriya ta aika da cikakken birgediya da manyan kayan aiki a sassa daban-daban na Kwara ta Kudu, domin rage matsalolin tsaro a yankin. Wata sanarwa da sakataren yada labarai gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar ta ce Tuni dai sojojin suka yi ta luguden wuta ta cikin kauyukan Oke Ode da Babanla, dukkansu a karamar hukumar Ifelodun. Har ila yau, rundunar ta kara da cewa, aikin ya zarce zuwa Edu da Patigi domin ratsa dazuzzukan da masu garkuwa da mutane suka fara kai hare-hare na matsorata a kan al’ummomi daban-daban tare da yin...
Cristiano Ronaldo ya zama biloniya na farko tsakanin ƴan wasan kwallon kafa a duniya Bloomberg mai sharhi da kididdiga tarin dukiya tsakanin attajiran duniya, ta fayyace tarin kudin da mai shekara 40 dan kwallon tawagar Portugal mai taka leda a Al-Nassr ta Saudiya ke da shi. Ta ce yana da dalar Amurka biliyan daya da miliyan 400 daga kudin da yake samu na albashi da ladan wasa da tallace-tallace da zuba hannun jari. Ya samu albashin sama da dalar Amurka miliyan 550 tsakanin 2002 zuwa 2023 da kwantiragin da ya kai dalar Amurka miliya 18. Lokacin da Ronaldo ya koma Al-Nassr ta Saudiyya a 2022, ya zama wanda ke kan gaba da ake biya albashi mafi tsoka a tarihi. da...
Haka kuma, ya jaddada buƙatar ƙara zuba jari a fannin ilimi, lafiya, da gine-gine don samar da ci gaba mai ɗorewa.Bankin ya ƙara da cewa, idan gwamnati ta ci gaba da aiwatar da waɗannan sauye-sauyen cikin tsari, tattalin arziƙin Nkjeriya zai iya ƙaruwa zuwa kashi 4.4 nan da shekarar 2027.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiTinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas October 8, 2025Manyan LabaraiKwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi October 8, 2025Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025
Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar iran Mohammad Eslami da manyan jami’a daga hukumar rasatom ta hadin guiwar ayyukan makamashin nukiliya sun gana a birnin Tehran kuma sun tattauna kan yadda za su yi aiki tare a bangaren shirin ta na nukiliya na zaman lafiya, Nikolai Spassky ya kawo ziyara iran ne a birnin Tehran tun bayan ziyarar da Eslami ya kai birnin mosko a ranar 24 ga watan satumba, inda bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, na yin aiki tare wajen gina karamar tashar nukiliya iran. Haka zalika bangarorin biyu sun tattauna kan yarjejeniyar da aka kula lokacin da Eslami ya kai ziyara da ya hada da yin aiki tare a cibiyar nukiliyar iran...
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinBabban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025Daga Birnin SinYawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana October 8, 2025Daga Birnin SinAdadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7 October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinAdadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7 October 8, 2025Daga Birnin SinSin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa October 8, 2025Daga Birnin SinSin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare October 8, 2025
Kakakin majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai na kafa tsarin ‘yansandan jihohi a kasar nan domin magance kalubalen tsaro da ake fuskanta.Abbas ya bayyana haka ne a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin dokar hukumar leken asiri da binciken sirri ta shekarar 2024, wanda kwamitin majalisar kan harkokin tsaro da leken asiri ya shirya a harabar majalisar dokokin kasar da ke Abuja ranar Laraba.Kakakin majalisar wanda ya samu wakilcin mamba mai wakiltar mazabar Ilorin ta Yamma/Asa, Honarabul Muktar Shagaya, ya ce, kawo sauye-sauye a fannin tsaro ya zama abinda aka fi mayar da hankali, kuma yanzu dole a tashi daga rubutu kawai zuwa aiwatar da cikakken tsari.Shugaban majalisar ya ce kafa ‘yansandan jihohi ta...
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinSin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa October 8, 2025Daga Birnin SinSin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare October 8, 2025Daga Birnin SinKasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata October 7, 2025
Jaridar Daily Mail ta kasar Burtaniya ta nakalto firay ministan HKI Benyamin Natanyahu yana gargadin Amurka kan abinda ya kira, makamai masu linzami masu keta nahiyoyi wadanda JMI take ginawa barazana ce ga Amurka. Ya ce makaman suna iya isa biranen Amurka daga cikin har gidan Trump da ke ‘Mar-a-Lago’, a bakin ruwa na Palm Beach a jihar Florida. Daily mail ta nakalto Natanyahu yana fadar haka a hirar da ta hada shi da wani dan jirada mai suna Ben Shapiro. Ba tare da bada wata hujja ko dalili ba, Natanyahu ya ci gaba da cewa, makaman wadanda suke iya zuwa wurare masu nisan kilomita 800 zasu kai biranen washington da kuma NewYork har da kuma gidan shugaba Trump dake...
Alkaluman da kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin wato China Railway ya gabatar, sun nuna cewa, ana sa ran jigilar fasinjoji kimanin miliyan 21 da dubu 750, ta jiragen kasa a kasar Sin a yau Laraba. Kana tun daga ranar 29 ga watan Satumban da ya gabata, wato ranar da aka kaddamar da aikin jigilar fasinjojin da suka yi tafiye-tafiye, a lokacin hutun bikin tunawa da kafuwar kasa da na Zhong-Qiu, zuwa jiya Talata, an riga an kwashe fasinjoji fiye da miliyan 160 ta jiragen kasa a kasar Sin.Yau ce ranar karshe a hutun na wannan karo, don haka ake sa ran ganin karuwar zirga-zirgar mutane da suke kokarin komawa gidajensu daga wuraren da suka yi bulaguro. Hakan ne...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum da ake zargin ɗan bindiga ne da ke aiki tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru. Rundunar ta kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai 80 da wasu tarin makamai. Gwamnatin Gombe ta kafa hukumar bunkasa fasahar zamani da tattalin arziƙi Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa wanda aka kama, Adamu Adamu, mai shekaru 30, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Song a Jihar Adamawa. Amma wanda aka kama mazaunin unguwar Jauro Jatau da ke Akko, Jihar Gombe. An kama shi ne ranar 4 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihan bayanai da suka nuna cewa yana tare da wata...
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun tare hanyar Gusau zuwa Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama. Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun tare motoci sannan suka yi awon gava da fasinjojin da ke ciki. Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Wani shaida ya ce ’yan bindigar sun ɗauki lokaci suna sharafinsu kafin daga bisani suka tafi da mutanen da suka kama. Daga cikin waɗanda suka sace akwai Malam Sadis Isa, shugaban Majalisar Malamai ta Ƙaramar Hukumar Gummi, abin da ya jefa al’umma cikin tsoro da damuwa. “Da yammacin ranar Talata, ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ƙaddamar da sabon ginin Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa, wadda aka sanya wa sunan Sir Ahmadu Bello a Jihar Bauchi. An ƙaddamar da cibiyar ne kafin babban taron zuba jari da nufin bunkasa kasuwanci da masana’antu a jihar. Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC A jawabinsa, Obasanjo ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed, bisa irin ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa, waɗanda ke inganta rayuwar jama’a. “Na yi farin ciki da abin da na gani da kuma abin da na ji. Ban zata cewa zan dawo Bauchi cikin ƙanƙanin lokaci don buɗe irin wannan katafaren waje...
“Yanzu muna kammala sabbin sharuɗan aikin da ASUU ta gabatar, kuma za mu bayyana amsar gwamnati nan ba da jimawa ba,” in ji shi.“Shugaba Tinubu yana da niyyar kawo ƙarshen wannan matsala gaba ɗaya.”Ya roƙi ASUU da ta ci gaba da tattaunawa maimakon fara yajin aiki, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na da niyyar gaskiya da jajircewa wajen warware matsalar.LEADERSHIP ta ruwaito cewa ASUU ta fara shirin tursasa wa mambobinta fara yajin aikin gargadi, yayin da wa’adin kwanaki 14 da ta bai wa gwamnati zai ƙare a ranar Lahadi mai zuwa.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Labarai‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato...
Ya buƙaci jama’a suke bambanta “gaskiya da siyasa.”ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa October 7, 2025
Ya gargaɗi masu aikata laifuka da su daina, ko kuma su fuskanci hukunci, inda ya bayyana cewa waɗanda aka kama tuni aka miƙa su kotu.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Labarai‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025LabaraiCika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya October 7, 2025
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ziyarci Banki bayan harin, inda ya yaba da jarumtar mazauna garin tare da alƙawarin bunƙasa tsaro a yankin.Zulum, ya kuma sanar da shirin sake mayar da mazauna ƙauyuka uku; Kumshe, Tarmu’a da Bula Yobe, sannan ya tabbatar da cewa aikin gyaran hanyar Banki ya an fara shi.Ya buƙaci matasa su yi rajistar katin zaɓe, tare da jan hankalin ‘yan kasuwa su haɗa kai da jami’an tsaro domin ɗorewar zaman lafiya.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025LabaraiCika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya October 7, 2025LabaraiSSANU, NASU Za Su Gudanar Da...
Haka kuma ya buƙaci a aiwatar da gyare-gyare don farfaɗo da tattalin arziƙi, inganta ilimi da kiwon lafiya, tare da samar da damammaki ga matasa.Ya ƙara da cewa majalisar za ta sake duba Kundin Tsarin Mulki na 1999 domin bunƙasa dimokuraɗiyya da inganta mulki a Nijeriya.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa October 7, 2025Manyan LabaraiTinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026 October 7, 2025
Uche Nnaji, Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, ya yi murabus daga mukaminsa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata. Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Jerin ministocin da zargin takardun bogi ya tabaibaye su Nnaji na fuskantar zarge-zarge kan sahihancin takardun karatunsa, inda binciken da jaridar Premium Times ta gudanar ya gano cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ta ce ba ta ba shi takardar kammala digiri ba. A cewar jami’ar, tsohon Ministan bai kammala karatunsa a cikinta ba, kuma ba ta taɓa ba shi takardar shaidar kammala ta ba. A cewar jaridar, Simon U. Ortuanya, Shugaban Jami’ar UNN, ya...
Shirye-shiryen sun kammala domin Shugaban Ƙasa ya sanar da sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), bayan da Farfesa Mahmood Yakubu ya kammala wa’adin mulkinsa na shekara goma a ranar Talata. Kafin Yakubu ya sauka daga mukaminsa, rahotanni sun nuna cewa fadar shugaban ƙasa na nazarin mutum uku da ake has ashen za su iya maye gurbinsa: Farfesa Joash Ojo Amupitan, Mai Shari’a Abdullahi Mohammed Liman da Farfesa Lai Olurode. Wata majiya a fadar shugaban ƙasa ta shaida wa Aminiya cewa an kammala nazari, kuma Farfesa Amupitan ne ke kan gaba a jerin waɗanda ake hasashen don maye gurbin tsohon shugaban INEC. Majalisa za ta yi dokar kula da harkar Crypto da POS Ya kamata a karɓe...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci. Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri baya bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takardun Shaida Na Bogi Ga Rayuwar Al’umma DAGA LARABA: Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan zamani da ma irin halin da almajirai suka tsinci kan su a ciki. Domin sauke shirin, latsa nan
Wannan sanarwar ta baya bayan nan da kasar Sin ta yi, ya samu yabo sosai, musammam daga sakatare janar na MDD, yana jaddada cewa, shirin na Sin na da muhimmanci matuka ga tunkarar sauyin yanayi. Su ma kafafen yada labarai na kasa da kasa da manyan jami’an hukumomi da kasashe da dama, sun yaba wa shirin, wanda ya nuna cewa, ana kara ammana da irin rawar da kasar Sin ke takawa a harkokin da suka shafi duniya. Ba alkawari da gabatar da shirin kadai take yi ba, ta kasance mai aiwatar da su a aikace kuma ana ganin nasarorin da take samu a zahiri. Zuwa yanzu, babu wata kasa da ta bayar da gudunmuwa a wannan bangare kamar kasar Sin, kuma...
ShareTweetSendShareMASU ALAKA LabaraiTinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk October 7, 2025Ra'ayi RigaCikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka October 7, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025
Jami’an kare hakkin dan’adam na MDD sun nuna jin dadinsu dangane da hukuncin da kotun duniya ta manyan laifuka ( ICC) ta yanke akan mutum na farko da aka tuhumka akan laifukan Darfur na kasar Sudan. A jiya Litinin ne dai kotun manyan laifuka ta duniya ta yanke hukunci akan Ali Muhammad ali Abd-Al-Rahman wanda ake yi wa lakabi da Ali Khushayb, bisa samunsa da laifi akan laifukan yaki a Darfur shekaru 20 da su ka gabata. Daga cikin laifukan da aka tabbatar da akan Ali Kushayb da akwai bayar da umarnin yi wa mutane da dama kisa, da kashe fursunoni biyu da gatari. Alkalai uku ne su ka yi zaman shari’ar da aka yanke hukuncin tare da samun wanda...
Tinubu, a cikin wata wasika da ya aikewa kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen wanda ya karanta a zaman majalisar a ranar Talata, ya kuma buƙaci majalisar ta amince da batun shirin Sukuk da zai kai kusan dala miliyan $500 a cikin ICM.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Ra'ayi RigaCikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka October 7, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025LabaraiGwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu October 7, 2025
Hukumar kula da yan gudun hijirar a majalisar dinkin duniya ta jinjinawa kasar Iran game da kokarin da tayi wajen kulawa da miliyoyin yan gudun hijira kasar Afghanistan , da suka zauna a kasar na tsawon shekaru, Babban darakta na hukumar ta IOM shi ne yayi wannan bayani ga Mohammad Batgae mtaimakin ministan harkokin cikin gidan kasar iran a birnin janeva a jiya litinin, a wani taro da suka gudanar a bayan babban taron Majalisar dinkin duniya karo na 76 da hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya take gudanarwa. Ana sa bangaren bathaei babban jami’I na kasar Iran ya bayyan yadda jamhuriyar musulunci suka bada kula ta musamman ga dubban yan gudun hijiran kasar ta Afghanistan...
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu
A cewarsa, gyaran yana taimakawa wajen samun bayanai daidai domin tsara ci gaba da kuma rarraba albarkatun ƙasa bisa adalci daga gwamnatin tarayya.“Wannan tsarin yana daidai da yadda ake yi a wasu jihohi, inda ake amfani da bayanan masarautu, yankuna da ƙauyuka wajen tsara ci gaba da rarraba kuɗaɗe,” in ji shi.Gwamnan ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen haɗa kan jama’a da tallafa wa ayyukan ci gaba, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da sabon tsarin cikin gaskiya.Ya yaba wa kwamitin bisa jajircewarsu da yadda suka gudanar da aikin cikin gaskiya da tsari.Tun da farko, shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya bayyana cewa sun karɓi buƙatu 196, wanda 17 don kafa sabbin masarautu, 166 don sabbin yankuna, da...
Ya gode wa Shugaba Bola Tinubu da shugabannin tsaro bisa goyon bayansu wajen yaƙi da rashin tsaro a Kogi.Tags: KogiOdodoTsaroShareTweetSendShare Sadiq Related LabaraiMajalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya 1 hour agoManyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa 2 hours agoManyan LabaraiTinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026 3 hours ago
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya NAHCON da ta rage kuɗin Hajjin bana, inda ya buƙaci hukumar ta fito da sabon kuɗin nan da kwana biyu. Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya bayyana wannan buƙatar a ganawarsa da shugabannin hukumar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja a ranar Litinin. Ya yi kira da a samu ƙarin haɗin kai tsakanin hukumar a matakin ƙasa da takwarorintna na jihohi ciki har da gwamnoni domin a samu sauƙin gudanar da aikin Hajjin na bana. Da yake ganawa da manema labarai bayan taron, mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia ya ce an yi taron ne domin ƙarƙare shirye-shiryen Hajjin na...
Mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Nasarawa sun zabi sabbin jami’anta da za su gudanar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa. Shugaban kwamitin zaben, Mista Samson Osuo, ya sanar da Abubakar Abdullahi na jaridar Daily Trust a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 21 da Danjuma Joseph na National Accord da kuri’u 9 a matsayin shugaban kungiyar. Ya kuma bayyana cewa Mista Chris Nyamtu na gidan rediyon Najeriya ne ya yi nasara da kuri’u 21 yayin da Augustine Kuza na jaridar Pilot na Najeriya ya samu kuri’u 9 a matsayin Sakatare. Mista Abel Daniel na jaridar Guardian a matsayin mataimakin shugaba Awayi Kuje na NAN a matsayin Mataimakin Sakatare, Michael...
Ƙungiyar shugabannin jam’iyyun siyasa (IPAC) ta ce lokaci ya yi da za a cire ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) daga hannun Shugaban ƙasa. Ƙungiyar ta ce kamata ya yi a kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai riƙa yin naɗin shugaban INEC da kwamishinoni da sakatare na hukumar domin tabbatar da gaskiya da cin gashin kai na hukumar. Shugaban ƙungiyar IPAC, Dakta Yusuf Mamman Ɗantalle, ne ya bayyana haka a wani taro da suka yi da kwamitin Majalisar Wakilai da ke nazarin kundin tsarin mulki a Abuja. Ya ce tsarin da ake amfani da shi yanzu na bai wa shugaban ƙasa damar zaɓar shugaban INEC na iya rage amincewar jama’a da hukumar. Jerin...
Irabor ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta bi hanyoyi daban-daban wajen magance matsalar tsaro, ba ta hanyar amfani da sojoji kaɗai ba.Ya ce ya kamata a samar da manufofi masu inganci da za su rage talauci, rashin aiki da yawan yara marasa zuwa makaranta.“Idan muka rage yara marasa zuwa makaranta da kuma marasa aikin yi, za mu rage yawan mutanen da ‘yan ta’adda ke iya ɗauka aiki,” in ji shi.Ya kuma gargaɗi ‘yan siyasa da su daina sa siyasa a batun harkar tsaro.A ranar bikin cikar Nijeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa dakarun Nijeriya suna samun nasara a yaƙi da ta’addanci da garkuwa da mutane, amma jam’iyyun adawa sun ce matsalar...
Sakataren harkokin wajen Vatican, Cardinal Pietro Parolin, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa, “yakin da sojojin Isra’ila suke yi a yankin zirin Gaza yaki ne a kan mutane raunana marasa kariya.” Cardinal Parolin ya yi ishara da cewa “dole ne kasashen duniya su nuna shakku kan sahihancin ci gaba da samar da makamai wadanda ake amfani da su kan fararen hula a Gaza.” A lokuta da dama Paparoma Leo na 14 ya yi Allah wadai da yakin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza, yana mai yin kira da babbar murya ga kasashen duniya da su kawo karshen yakin da ake yi a zirin Gaza, wanda aka kwashe kusan shekaru biyu ana yi. Share 0 0...
A gobe Talata ce 7 ga watan Otoba, yakin tufanul-Aksa ya ke cika shekaru 2 tsakanin HKI da kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye. Jaridar ‘The National’ na kasar Amurka ta nakalto firay ministan HKI Benyamin Natanyahu yana cewa gwamnatinsa tana samun nasara a yakin, duk da cewa abinda yake kasa yana nuna akasin haka. Musamman idan an dubi manufofin HKI na fara shiga yakin. Wasu masana a HKI basu amince da da cewa Natanyahu yana samun nasara a wannan yakin ba. Wanda shi ne yaki mafi tsawo wanda HKI ta shiga tun bayan kafata shekaru kimani 80 da suka gabaya. Jaridar ‘The Nation’ ta yi hira da Nimrod Novik daya daga...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyanawa kwamitin al-amuran harkokin waje na majalisar dokokin kasar iran kokarin da ma’aikatarsa take na kare muradun JMI na amfana da fasahar makamashin nukliya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa an gudanar da taron ne, a ma’aikatar harkokin wajen kasar a jiya Lahadi. Kuma ministan ya bayyana wa kwamitin dalla dalla kan irin sabbin kokarin diblomasiyya wanda ma’aikatar take yi don ganin ta kare halattaccen shirin makamashin nukliya na kasar Iran. Ministan ya bayyanawa kwamintin, irin ayyukan da ma’aikatarsa ta yi a shekarar da ta gabata a bangaren makamashin Nukliya, kara kyautata dangantaka da kasashe makobta, da ci gaba da karfafa zumunci da manya-manyan kungiyoyi da kasa shen...
A zaman da aka yi a yau, lauyan Ministan ya shaidawa kotu cewa an isar da takardun shari’ar ga dukkan waɗanda ake ƙara, yana mai zargin Shugaban Jami’ar UNN da saɓa umarnin kotu ta hanyar rubuta wasika ga jaridar yanar gizo Premium Times, inda ya ƙalubalanci ikirarin Nnaji na cewa tsohon ɗalibin jami’ar ne. A cewar lauyan, wannan wallafa ta karya umarnin kotu na barin komai a yadda yake har sai an saurari shari’ar. Sai dai lauyan jami’ar ya musanta yin wani kuskure, amma ya ce za su ja hankalin jami’an su don bin umarnin kotu yadda doka ta tanada. Tags: MinistaNnajiUNN ShareTweetSendShare Naziru Adam Ibrahim Related Ilimi Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa...
Tags: KwaraNPFL ShareTweetSendShare Rabilu Sanusi Bena Related Wasanni Kwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar 5 hours ago Wasanni Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or 2 days ago Wasanni Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya 2 days ago
Talaucin Da Ya Ninku Fiye Da Sau Biyu A Gwamnatin Tinubu, An Ƙuduri Aniyar Kawar Da Shi Nan Da Shekaru 5
A cewar Bankin Duniya, talauci a tsakanin mazauna karkarar Nijeriya ya kai kashi 75.5 cikin dari, wanda ke nuna ƙaruwar rashin daidaito da kuma tsananin matsin tattalin arziki a fadin kasar. Ministan ya ce, gwamnati ta kuma kuduri aniyar inganta hasashen tattalin arziki da inganta sauye-sauyen da zai sanya Nijeriya ta samu ci gaba mai ɗorewa. Bagudu ya jaddada cewa, gwamnatin da shugaban kasa Bola Tinubu ke jagoranta tana ba da fifiko wajen samar da ayyukan yi ta fuskar fasahar zamani, noma, tattalin arziki da ƙirƙire-ƙirƙire. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Sanarwar ta ce, hare-haren kakkaɓe maɓoyar ‘yan bindigar na zuwa ne a karkashin shirin ‘Operation Lafiya Nakowa’, da nufin fatattakar ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar Taraba. Ya kara da cewa, harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ta’addan a kusa da Tarhembe, Tornyi, TY Farm, da ɗaukacin yankin Kando da ke yankin Tati, karamar hukumar Takum, da kuma rahotannin lalata gonaki a karamar hukumar Ussa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga Abdullahi Usman, Kaduna Sardaunan Ikulu, Alhaji Dr. Isma’īl Yusuf Ashafa, ya kira mata da matasa a garin Ikulu da su shiga harkokin siyasa domin kawo ci gaba a yankinsu. Ya fadi hakan ne a lokacin Taron Ikulu da aka shirya a Kaduna karkashin jagorancin Ikulu Political Forum (IPF). Ya jaddada cewa babu wata al’umma da za ta bunkasa sai an samu hadin kai tsakanin jama’a da kuma cikakkiyar rawar da matasa da mata ke takawa a siyasa. Ya kara da cewa wajibi ne a wayar da kan matasa da mata, a ilimantar da su, sannan a motsa su su gane muhimmancin jagoranci ta hanyar jam’iyyun siyasa. Hakazalika, ya gargadi ‘yan siyasa a yankin da su guji “siyasar do ko...
Ana tsaka da Sallah ’yan bindiga suka karbe wani mutum har lahira sa’annan suka yi garkuwa da basarake a ƙauyen Rani Ramat da ke Ƙaramar Hukumar Patigi a Jihar Kwara. Al’ummar yankin sun ce maharan sun kai farmaki ne a kan babura a yayin da ake Sallar Magariba ranar Lahadi inda suka rika harbi babu ƙaƙƙautawa. A yayin da jama’a ke guje-gujen neman tsira ne ’yan bindigar suka harbe wani mutum. Daga nan suka yi awon gaba da basaraken ƙauyen mai suna Alhaji Ndako, zuwa inda ba a sani ba. Mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun shafe sa’o’i suna cin karensu babu babbaka kafin su koma cikin daji. Kwamitin gwamnati ya ba da shawarar ƙirƙirar sababbin masarautu 13...
A cewar Sakataren Zartarwa na Hukumar Fansho ta Jihar Kaduna, Ibrahim Balarabe, yace sabon rukuni na biyan kudi zai amfanar da tsofaffin ma’aikata 661 da iyalan waɗanda suka rasu a matakan Gwamnatin Jiha da ta Kananan Hukumomi naira biliyan 1.736 za a biya ga tsofaffin ma’aikata 511 karkashin tsarin ( CPS) sannan kuma naira miliyan 585 za a biya ga tsofaffin ma’aikata 315 da iyalan mamata karkashin tsarin (DBS). Hukumar ta bayyana cewa, ga waɗanda ke karkashin fanshon hadin gwiwa na (CPS), hakkokin su za a tura kai tsaye cikin asusun fansho (Retirement Savings Accounts – RSAs) ɗin su, yayin da waɗanda ke karkashin tsarin (DBS) za a gayyace su nan gaba don yin tantancewa kafin a biya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Halin matsin tattalin arziki ya tilasta da yawa daga cikin mutane zama a bacoci a garin Abuja da wasu biranen Najeriya. Mutane a birane kamar Abuja da Legas Da Fatakwal na cikin halin matsi sakamakon rashin ingattaccen muhalli. Ko wannen irin rayuwa irin wadannan mutanen ke yi? NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan DAGA LARABA: Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai a yau da ake bikin ranar muhalli ta duniya. Domin sauke shirin, latsa nan
Yawan Mutanen Da Suka Yi Zirga-zirga A Rabin Farkon Hutun Bikin Kafuwar PRC Da Bikin Zhongqiu Ya Kai Biliyan 1 Da Miliyan 243
Bisa labarin da ma’aikatar kula da harkokin sufuri ta kasar Sin ta bayar, a ranar 4 ga wannan wata, yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a kasar Sin ya kai miliyan 301 da dubu 291 da dari 1, wanda ya karu da kashi 6.1 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a rabin farko na hutun bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin PRC da bikin Zhongqiu ya kai matsayin koli a tarihi, wato ya kai biliyan 1 da miliyan 243, wannan ya shaida cewa, an fi yin zirga-zirga a lokacin hutun. Game da hanyoyin zirga-zirga a lokacin wannan hutu, an fi zabar hanyoyin mota. Game da yankunan da aka fi sha’awar ziyarta, an...
Jaridar Ma’ariv ta HKI ta buga labarin da yake cewa gwamantin HKI ta kwace kudaden gwamnatin kwarya-kwarya ta Faladinu da sun kai dala miliyan 7.54 ta rabawa wasu iyalan yahudawa 41 da su ka riya cewa hare-haren Faladinawa sun yi sadaniyyar kashe musu ‘ya’ya da dangi. Jaridar ta kuma kara da cewa; An rabawa iyalan yahudawan kudin da sun kai Shakel miliyan 25 wanda shi ne kwatankwacin Dala miliyan 7.54, ta hannun lauyoyinsu. Haka nan kuma jaridar ta ce hukumar dake kula da haraji da ke karkahsin ma’aikatar shari’a ce ta aiwatar da raba kudin a matsayin abinda su ka kira diyyar ayyukan t’addanci.! Jaridar ta kuma ce tun a 2019 ne wadannan ‘yan sahayonioyar su ka bukaci a biya...
Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya yaba wa Gwamna Babagana Zulum da Sojojin Operation Hadin Kai bisa gaggawar da suka nuna wajen ziyartar garin Kirawa bayan hare-haren da Boko Haram ta kai, wanda ya yi sanadin mutuwa da ƙone gidaje da fadar dagaci. Sanatan ya bayyana cewa harin ya tilasta wa mazauna da dama guduwa zuwa ƙasar Kamaru. A wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri ranar Lahadi, Ndume ya gode wa gwamnan bisa alƙawarin tura Sojoji domin kare garin da kuma amincewa da gina asibiti, da rijiyoyi, da wasu muhimman ayyukan raya ƙasa a yankin. Ya ce irin waɗannan matakai za su taimaka wajen dawo da ƙwarin gwuiwar jama’a. Zulum Ya Rabawa Talakawan Dikwa Tallafin...
Mahaifiyar Yilwatda ta rasu a watan Agustan 2025, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, tana da shekaru 83. Da yake mayar da martani, Atiku ya ce shugaban kasar ya zaɓi ya yi ziyarar jana’izar siyasa maimakon ziyarar jama’ar da taɓarɓarewa tsaro ta shafa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya samu yabo musamman a kan ƙwarewarsa a fagen nazari kan al’amuran yau da kullum na cikin gida da ƙasashen waje tare da fahimtar da masu sauraro cikin sauƙi. Marigayi Getso, ya bar mata uku da ‘ya’ya da jikoki, inda abokai da sauran ‘yan uwa suka bi sahun alhinin rasuwarsa, tare da bayyana hakan a matsayin babban rashi ga fannin yaɗa labarai a Kano da Nijeriya baki ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
BICTOR IKPEBA – 1997 Dan wasan Nijeriya Bictor Ikpeba, ne da ake yi wa lakabi da suna “Prince of Monaco,” Ikpeba ya samu shiga ne bayan ya taimaka wa kungiyar Monaco ta samu nasarar lashe kofin Ligue 1 ta Faransa. Danwasan ya samu kuri’a 2, inda ya kare a mataki na 32 a cikin jerin wadanda suka samu karramawa a shekarar ta 1997. ADEMOLA LOOKMAN – 2024 A kakar bara, wanda ya lashe gwarzon dan kwallon kafa na Afirka, Ademola Lukman, wanda a lokacin yake buga wasa a kungiyar Atalanta ne ya zo na 14 a bikin karramawar. Lookman ya lashe gasar Europa da Atalanta, inda ya zura kwallo uku rigis a raga, sannan ya taka rawar gani sosai a...
Burgediya JanarEsma’il Qa’ani babban kwamnadan dakarun “Qudus'” IRGC a nan Iran ya bayyana cewa kungiyar Hamas ta boye ranar fara yakin tufanul Aksa har shugaban kungiyar Shahid Isma’il Haniyya da shahida Nasarallah duk basu san da lokaci fara yakin ba, sai suka ji an fara. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Qa’ani yana fadar haka, a jiya jumm’a a hirar da aka yi da shi a tashar talabijin ta cikin gida a nan Iran. Ya kumakara da cewa a lokacinda aka fara yakin shugaban kungiyar ta Hamas yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Iraki, yana dawowa ne ya ji labarin fara shi. Janar Qa’ani ya kara da cewa, amma duk da haka, shahida Nasarallah ya zauna...
’Yan sanda sun harbe wasu mayaƙan Lakurawa har lahira a yayin da ragowar suka tsere a yankin Gorun Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Dandi da ke Jihar Kebbi. Kakakin rundunar, SP Nafi’u Abubakar , a cikin wata sanarwa a ranar Asabar ya ce bayan samun rahoton harin ’yan ta’addan a yankin ne ’yan sanda suka je suka yi musayar wuta na tsawon awannin da su, inda suka halaka mutum 3 a cikin maharan, ragowar kuma suka cika bujensu da iska. Sanarwar da ya fitar a ranar Asabar ta ce bayan samun rahoto ne DPO na yankin Lamba ya tura ’yan sanda da ’yan banga domin fatattakar maharan, Ya ce an ƙwace babur guda ɗaya da mayaƙan na Lakurawa suka tsere...
Da farko za ki wanke tsamiya sai ki dafa ta ki tace sannan ki wanke danyar citta sai ki nika ta, sannan ki samu roba mai kyau sai ki tace tsamiya tare da cittar kisa suga da filebo sai ki juya sosai ki sa a firij ko ki sa masa kankara. Asha dadi lafiya. Hadadden Lemon Shayi: Abubuwan da uwargida za ki tanada: Kankana, kokumba, sitoru beri na ruwa, lemo, tea bag, danyar citta, abarba, Lemon juice, na’a na’a. Yadda zaki hada: Da farko za ki wanke kankana da danyar citta sai ki nika su, sannan ki tace ki zuba a cikin tukunya, sai ki dora akan wuta ki wanke abarba da kokumba, ki yanka ki zuba a cikin tukunya...
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya yayi tsokaci kan martanin kungiyar Hamas kan yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana jin dadinsa da martanin da kungiyar Hamas ta mayar dangane shirin shugaban Amurka Donald Trump kan Gaza, yana mai bayyana hakan a matsayin abin karfafa gwiwa. Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a cikin wata sanarwa a yau Asabar cewa: Guterres ya bukaci bangarorin da abin ya shafa da su yi amfani da wannan damar wajen kawo karshen yakin Gaza da kuma kawo karshen bala’in jin kai da fararen hula ke fuskanta. Ya kara da cewa, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya tabbatar da shirin Majalisar Dinkin Duniya na goyon bayan duk...
’Yan bindiga sun sace wata matar aure da ’ya’yanta biyu a yankin Bareke-Egbe a Ƙaramar Hukumar Yagba ta Yamma da ke Jihar Kogi. ’Yan bindigar sun kai farmaki gidan wani manomi mai suna Tokpe Gody da misalin karfe 2 na dare ranar Juma’a, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su sace matarsa da ’ya’yansa biyu. Rahotanni sun ce Gody ya sha da ƙyar amma ya samu raunukan harbin bindiga a jiki da ƙafafuwansa, kuma yana karɓar magani a asibitin Egbe, inda likitoci ke cewa yana cikin mummunan yanayi. Wani mazaunin yankin mai suna Samuel Adeyemi ya ce: “Tokpe Gody manomi ne mai fama da yadda zai ciyar da iyalinsa. Ya tsira da ƙyar daga ’yan bindigar, amma matarsa da ’ya’yansa...
“Rushewar wannan gada na haifar mana da matsala sosai. Gwamnati ta taimaka ta gyara,” in ji Wayu Bamga, mazaunin yankin. Nanlong Nyas ya ƙara da cewa, “Gyaran da aka yi bai daɗe ba kafin ruwa ya sake lalata gadar.” Wasu direbobi kamar Umar Sa’adu da Abubakar Haruna sun ce duk lokacin da suka isa wurin gadar, sai sun biya ma’aikata su tura motarsu kafin su iya tsallaka rafi kana su ci gaba da tafiya. Rushewar Gadar Namne Ta Taraba Ta Tsayar Da Zirga-Zirga A Jihar Taraba kuwa, Gadar Namne dake kan hanyar Jalingo–Wukari ta rushe a watan Agustan 2024 bayan ruwan sama mai yawa, kuma har yanzu shekara guda bayan haka, babu wani gyara da gwamnatin tarayya ko ta jiha...
’Yan bindigar da ke addabar yankunan karkara sun kaƙaba sun ƙaƙaba musu haraji da ke kaiwa Naira miliyan 10 a Ƙaramar Hukumar Mashegu Jihar Neja. Rahotanni sun nuna cewa an umarci al’ummomin yankunan Babban Rami da Kaboji su su biya Naira miliyan biyu-biyu. Yankin Sabon Rijiya da Sabon Rami an umarce su da su Naira dubu 500, yayin da aka umarci ƙauyukan da ke kusa da Dajin Keji su tara Naira miliyan 10 gaba ɗaya. Haka nan, ana ƙaƙaba wa al’ummar Khizi an kaƙaba musu harajin Naira miliyan shida, da wa’adin ranar Juma’a, 3 ga Oktoba, 2025. Wata mata ta banka wa kanta wuta a Bauchi Sharri Jonathan ke wa Buhari don lashe zaɓen 2027 —Garba Shehu Wani mazaunin yankin...
Fim na Nezha 2 na kasar Sin ya kara samun lambar yabo. A gun bikin nune-nunen littattafan zanen hotuna na kasa da kasa na kasar Sin karo na 18 da aka kaddamar a jiya 2 ga wannan wata, fina-finai guda 10 ciki har da fim na Nezha 2, da The Legend of Hei 2, da Curious Tales of a Temple sun samu lambobin yabo na Golden Dragon na kasar Sin karo na 22. Ya zuwa yanzu, fim na Nezha 2 ya samu kudin tikitin kallo Yuan biliyan 15.44 a duniya gaba daya, yawan kudin tikitin fim din da aka samu a kasashen waje ya kai Yuan miliyan 400. Fim din ya hau matsayi na farko na fim na kagaggun hotuna...
Jami’in MDD: Kayataccen Hutun “Golden Week Plus” Na Kasar Sin Ya Nuna Tasirin Yawon Bude Ido A Duniya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bayanan sun bayyana cewa; “Jimillar makarantu 228 suka ci gajiyar shirin, inda kimanin dalibai 829,423 suka nema. Ya zuwa yanzu kuma, dalibai 510,378 ne suka samu wannan tallafi na bayar da rance. “Zuwa 10 ga watan Satumba, an biya kimanin Naira 53,801,717,293.00 a matsayin kudaden makaranta na daliban, yayin kuma da aka biya Naira 45,751,360,000.00 a matsayin alawus-alawus na daliban. Idan aka tattara kudaden baki-daya, jimillarsu ta kama Naira 99,553,077,293.00,” a cewar rahoton. Duk da nasarar da aka samu a fadin kasar, shirin ya fuskanci kalubale wajen ganin an yi adalci a rabon a dukkanin shiyoyin fadin kasar guda shida da ake da su. Alkaluman da LEADERSHIP ta tattara a watan Mayun 2025, sun nuna dimbin gibin da ke tsakanin...
Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da sabon Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC) da aka gina a garin Kumo, Ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne tare da halartar Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya da kuma Ministan Kula da Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate. NAFDAC ta lalata magungunan jabu na N15bn a Oyo Fashewar tukunyar gas ya haddasa gobara a jami’ar Gombe A jawabinta, uwargidan shugaban Ƙasar ta ce wannan asibiti na nuna sakamakon jagoranci irin na hangen nesa ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ta ce, asibitin zai ƙara inganta damar samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Jihar Gombe da ma maƙwabtan jihohi, tare da...
Kudubi yana tare da kwayar zarrar kowace halittar Allah, shi yake isar mata da sakon magana, wanda bai zauna da wadannan mazaje ba sai ya ji magana ce mai girma, sai ya ga kamar an maida shi Allah, ya ce mai aka bar wa Allah ragowa, abun ba haka yake ba, abun mammaki da mai fadar wannan yana da wayewar da yake ganin fina-finai na Turawa, da ya ga wannan magana kai-tsaye a sarari. Misali a kan Kudubi, Turawa suna da wani fim da suke shiryawa na Dirakula (Dracula) wani mai shan jini, abun kamar tatsuniya ce suke shiryawa, amma wani ya ce an yi fada ne da Daular Usmaniyya, wato daular Turkiya, akwai abubuwa da ya ba su tsoro...
Yayin da yake kira ga ‘yan kasa kan cewa, kada su karaya ko fitar da rai daga rabo, Atiku ya tunatar da ‘yan Nijeriya cewa; shekarar 2027, wata dama ce da za a iya amfani da ita wajen kawar da wannan mulki na zalunci, domin tabbatar da ganin gobenmu ta yi kyau. “Babban kyawun demokuradiyya shi ne, ‘yancin samun damar kada kuri’a, duk wadanda ake zalunta; musamman mutanenmu a halin da ake ciki yanzu, za su samu damar kawar da wannan azzalumar gwamnati a zabe mai zuwa. Babu shakka, wannan shi ne ikon da babu wani dan takara da zai iya kwacewa daga al’umma,” in ji shi. Atiku ya kara da cewa, a shekara 65; Nijeriya ta kasance kasa wadda...
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Filato, ta sha alwashin ba da misali da masu yanke hukunci da kansu ba tare da barin doka ta yi aikin ta ba. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, CP Emmanuel Adesina ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Jos yayin da suka kama wasu manyan mutane tara (9) da ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutane da wasu laifuka daban-daban. Ku tuna cewa a wasu lokutan a cikin watan Agustan wannan shekara ta 2025, an kashe jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a karamar hukumar Bassa sakamakon aikata irin wannan danyen aiki. An bayyana cewa dan sandan ya tafi...
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya isa birnin bandar Abbas a jiya alhamis gari na 10 ke nan a ci gaba da ziyarar aiki yi a fadin jihohin kasar, da yake kaddamar da ayyukan ci gaba da aka kammala. Ziyarar ta shugaban kasa a jihohi tana taimakawa wajen samar da cundanya tsakanin gwamnati da jama’a, kuma tana bawa shugaban kasa dama gane ma idonsa irin kalubalen da ake fuskanta da kuma bada umarnin kawar da duk wani abu da ka iya kawo cikas wajen ayyukan raya kasa. Gwamnatin iran ta mayar da hankali wajen karfafa damammaki a bangaren ilimi da ci gaban tattalin Arziki a jihohi daban daban, ziyarar lardin Hormuzgan wani bangare ne na babban...
Wani abu da ya ja hanklan mutane shi ne, irin muggan makaman da ‘yan bindigar suka hallara da su a wajen kulla yarjejeniyar, wadanda kuma babu wani mahaluki da ke da ikon kwace makaman daga hannunsu, a yayin kulla yarjejeniyar, ta jeka nayi ka. Kazalika, a cikin daya daga cikin faifan Bidiyon, an ga yadda daya daga cikin shuwagabannin ‘yan bindigar ya yi bazaranar shedawa gwamnati da sauran jami’an gwamnatin da suka halarci wajen kulla sulhun cewa, idan har gwamnati ta kuskura ta kashe ‘yan bindiga dubu goma, suma za su hallaka adadin mutane kamar hakan. Wasu ‘yan Nijeriya dai, sun yi ittifakin cewa, kasar nan, ta koma tamkar, a hanun tafin ‘yan bindigar. Kulla wannan yarjeniyra dai, ta nuna...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin yau na fasahar zamani, musamman fasahar kirkirarriyar basir ta (AI), harkokin sana’o’i da dama suna fuskantar sauye-sauye masu girma. Daya daga cikin sana’o’in da ke cikin babban hadari shi ne sana’ar ɗaukar hoto musamman irin wadanda ke kashe makudan kudi wajen sayen kyamara da bude katafaren gidajen daukar hoto. A da, mutane kan je shagon daukar hoto domin samun hoto mai kyau na fasfo ko na bikin aure ko bikin suna, ko kuma kowane irin taron biki. Amma yanzu, manhajojin AI suna ba wa mutane damar kirkirar irin wadannan hotuna daga wayoyin su ko kwamfuta cikin mintuna kadan ba tare da zuwa shagon daukar hoto ba. Wannan yanayi na iya jefa...