2025-10-24@22:47:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2538

«yankin Yammacin Kogin Jordan»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wasu matasa sun zabi tallata ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta na zamani ta yadda bai kamata ba a wasu lokutan.   Tallata ‘yan siyasa da matasan suke yi kan haifar da hatsaniya, ko kiyayya, a intanet ko ma a zahiri a tsakanin su. NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya Karu DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa suka zabi zama “sojojin baka” ko “karnukan farautar” ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta. Domin sauke shirin, latsa nan
    Ya kuma kara da cewa, a Benuwe, sama da mutane 5,000 ne suka rasa rayukansu a gwamnatin baya.   Nuhu ya bayyana cewa, ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi a yankin Arewa-maso-Yamma sun kai ga ceto mutane 11,259 da aka yi garkuwa da su a watan Mayun 2025. An kuma kashe wasu manyan kwamandojin ‘yan bindiga da tawagarsu a jihohin Zamfara, Kaduna, da Katsina.   A wajen taron, akwai manyan shugabannin Arewa da suka hada da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe, Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume, tare da gwamnoni na yanzu da tsofaffi, Ministoci, Hakimai, da masu rike da mukaman siyasa.   Ribadu ya kammala da jaddada kudirin gwamnati na tabbatar...
    A cewar mahaifin marigayen, Dankama, ya bayyana cewa ba ya gida lokacin da katangar ta fado, inda ya ce ya kadu da jin labarin.   “Wannan lamarin ya faru da kusan mutane goma, amma mutane 6 sun riga mu gidan gaskiya. A yanzu haka, uku suna kwance a asibiti suna karbar magani,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sashen cinikayyar samar da hidimomi na Sin ya ci gaba da bunkasa yadda ya kamata cikin watanni shida na farkon shekarar nan ta 2025, inda ya karu da kaso takwas bisa dari kan mizanin shekara. A cewar ma’aikatar cinikayya ta Sin, darajar hidimomin shige da fice a wannan wa’adi ta kai kudin Sin tiriliyan 3.89, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 544.9. Cikin wannan adadi, alkaluman hidimomin da aka fitar daga kasar Sin ya karu da kaso 15 bisa dari, wato darajar da ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 1.69, yayin da na wadanda aka shigo da su kasar ya karu da kaso 3.2 bisa dari, daidai da kudin Sin tiriliyan 2.2. Sai kuma gibin cinikayya a fannin na bayar da hidimomi...
    Matar Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Hajiya Hadiza Ahmad Sama’ila Yakawada, ta kaddamar da Makon Shayar da Nono na Duniya na bana, tare da kira ga iyaye mata da mazajensu da su ba wa jarirai nono kacokam na tsawon watanni shida na farko. A yayin kaddamarwar, Hajiya Hadiza ta bayyana cewa shayar da jarirai nono na da muhimmanci matuƙa wajen tabbatar da lafiyar yara da kuma inganta cigaban su tun daga ƙuruciya. Ta kuma bayyana cewa makon yana da nufin wayar da kan jama’a musamman a tsakanin iyalai game da amfani da shayar da nono, tare da ƙarfafa gwiwar ma’aikatan lafiya da su ci gaba da fafutukar wayar da kai a fadin karamar hukumar. A nata jawabin, Sakatariyar Lafiya...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya reshen Abuja ta sanar da cafke wasu mata ’yan gida ɗaya da ake zargi da kitsa garkuwar ƙarya da zummar karɓar kuɗin fansa na naira miliyan biyar a wurin mahaifinsu. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar. Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 17 a Borno da Adamawa Buni ya shirya bikin karrama daliban da suka lashe gasar duniya Ta bayyana cewa sun samu tushen faruwar lamarin ne bayan da wani Mista Innocent, ya kai rahoton ɓacewar ’yarsa mai shekaru 16 a ranar 18 ga Yuli, 2025. Mista Innocent ya shaida wa ’yan sandan cewa ’yar tasa ba ta dawo gida ba tun bayan da ta fita domin...
    Tosin Demehin ta nuna godiya da jin daɗinta, tana mai cewa wannan girmamawa daga jiharta na ƙarfafa mata gwuiwa da sauran ’yan mata masu burin taka leda a matakin duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata tawagar jami’an tsaron Isra’ila da suka yi ritaya su 600 ciki har da tsaffin shugabannin hukumomin leƙen asiri sun aika wa Shugaban Amurka, Donald Trump wasiƙa domin neman ya matsa wa Isra’ila da ta gaggauta kawo ƙarshen yaƙin da ake a Gaza. Jami’an sun ce “tunaninmu ne cewa Hamas ta daina zama wata barazana ga Isra’ila”. “Amincin da kake da shi a wajen Isra’ilawa zai ƙara ba ka damar sanya Firaiminista [Benjamin] Netanyahu da gwamnatinsa a kan hanya daidaitacciya: A kawo ƙarshen yaƙin, a dawo da mutanen da ke tsare a kuma daina gallaza wa Falasɗinawa,” kamar yadda suka rubuta. Roƙon nasu na zuwa ne daidai lokacin da rahotanni ke cewa Netanyahu na ƙoƙarin faɗaɗa ayyukan soji a Gaza...
    Gwamnatin Tarayya ta gabatar da karramawar kasa da kuma tukuicin kudade ga kungiyar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin kwallon kwando na mata ta FIBA karo na biyar a jere.   A wata liyafar karrama su da aka yi a fadar shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, mai wakiltar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa kowane dan wasa zai karbi dala 100,000, yayin da koci da kungiyar kwararru za su samu dala 50,000 kowanne, tare da karramawar kasa ga daukacin kungiyar. Ya kuma yi alkawarin karin tukuicin da zai zo.   Shettima ya ce ba wai don murnar nasarar da kungiyar ta samu a cikin shekaru 78-64...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da karin kudin da gwamnatoci a matakin jiha suke samu daga asusun tarayya, ’yan Najeriya da dama suna korafin ba sa gani a kas.   Manazarta dai sun ce ko kafin karin ma ya kamata ya yi a ce ayyukan da gwamnatcin jihohi suke yi sun fi da ake gani Ko mene ne ya sa jihohi “ba sa kashe karin kudaden da suke samu yadda ya kamata”? NAJERIYA A YAU: Yadda Talauci Ke Hana Shayar Da Yara Nonon Uwa Zalla A Najeriya DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin,...
    Rundunar sojin kasar Sin (PLA) ta yi sintiri a yankin tekun kudancin Sin daga ranar 3 zuwa 4 ga wata. Kakakin rundunar PLA ta kudancin kasar Tian Junli ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin ta dauki matakin ne biyo bayan matakan Philippines na sanya kasashen dake wajen yankin cikin abun da ta kira da sintirin hadin gwiwa, wanda ke neman lalata zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin. A cewarsa, dakarun rundunar ta kudancin kasar za su ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana da kare ikon kasar kan yankunanta da muradunta na teku ba tare da yin kasa a gwiwa ba, yana mai cewa za a dakile duk wani matakin soja dake nemen tada hankali da rikici a...
    Sama da mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab 50 ne suka halaka a yankin kudu maso yammacin birnin Mogadishu fadar mulkin kasar somaliya Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya ta sanar a ranar Lahadin da ta gabata cewa; Sama da mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab 50 ne suka halaka a wani samame da dakarun sojin Somaliya suka kai a garin Bireire da ke kudu maso yammacin Mogadishu fadar mulkin kasar. Tawagar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: “A samamen hadin gwiwa da sojojin kasar Somaliya domin kwato garin Bireire a ranar 1 ga watan Agusta, ya haifar da hasara mai yawa ga ‘yan ta’addar, tare da kashe mayakan Al-Shabaab fiye da 50, wasu...
    Sakamakon wannan mummunan ta’annuti, Mataimakin Gwamnan ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar tawaga, wacce ta haɗa manyan ma’aikatan gwamnati da jami’an tsaro zuwa Banga da sauran wurare uku da waɗannan hare-hare ya shafa, don a jajanta masu, tare da ba su tallafi na abinci da kuɗaɗe.   Mataimakin Gwamnan ya kuma tabbatar wa da waɗannan al’ummu cewa gwamnatin na nan tana duk abin da za ta iya yi don kawo dawwamammen zaman lafiya a yankin.   Lokacin da ya ke mayar da jawabi, shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, Manir Haidara ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar na ganin ta samar da tsaro a duk faɗin jihar Zamfara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun gwamnati. Sanarwar ta bayyana cewa tuni aka fara aikin, inda aka  zayyana yadda gine-ginen za su kasance, kuma sauran abubuwa za su biyo baya da zaran an amince da karin kasafin kudin. Sanarwar ta kara da cewa wannan ba wani aiki ne mai zaman kansa ba, illa wata sabuwar babbar gudummawa daga gwamnati don kara habaka aikin da take yi tun da farko. Ta kara...
    Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya. Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a majalisar masarautar Gudi. Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule Wasu Kungiyoyi Sun Yi Kira Ga Dan Majalisa Aminu Sani Jaji Ya Fito Takarar Gwamnan Zamfara  Kwamishinan ilimi mai zurfi, kimiyya da fasaha na jihar, Farfesa Muhammad Bello Kawuwa ne ya mika takardar nadin ga sabon sarkin a madadin gwamnan. Da yake isar da sakon Gwamnan, Farfesa Kawuwa ya bayyana muhimmiyar...
    Shugaban kungiyar malaman addinin musulunci ko –Council Of Ulema-na Tafawa Balewa a jihar Bauchi na tarayyar Najeriya Sheikh Dan’azuki Musa tafawa balewa, yayi kira ga kasashen musulmi da kuma sauran kasashen duniya da su dauki darasi a jajircewar JMI da turjiyarta ga HKI, a kuma matsayin hanya tilo ta kawo karshen HKI. Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko IP na kasar Sheikh Dan’azumi yana fadar haka a lokacinda yayi hira da shi a Bauchi. Sheikh Dan’azumi ya kara dacewa , gwamnatin Amurka ce bayan dukkan ayyukan ta’addancin da HKI take aikatwa a Gaza. Ya ce kafin yakin kwanaki 12 da HKI ta kallafawa JMI, musulmi sun debe kauna da samun mafita ga matsalar al-ummar Palasdinu wacce aka dade ana fama...
    Akalla mutane 11 ne aka kashe a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a unguwannin Kagara da San-Isa da ke karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara. Majiyoyi daga yankunan biyu sun shaida wa wakilinmu cewa an kai hare-haren ne a unguwannin Kagara da San-Isa tare da wasu kauyukan da ke kewaye. Waɗanne Ƙasashe Ne Suka Amince Da Kafa Ƙasar Falasɗinu? Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi Wata majiya daga dan garin Kagara wanda ya bayyana sunansa da Abubakar Sani ya shaidawa LEADERSHIP cewa ya rasa ‘yan uwansa guda biyu a harin wanda ya afku a ranar Asabar din da ta gabata. Ya ce, ‘yan fashin da suka yiwa kauyen su kawanya da...
    Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa.   Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau, ya hada malaman addinin Musulunci, da sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, da kuma daruruwan al’ummar jihar baki daya, duk sun ba da hadin kai wajen ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.   A nasa jawabin, Kabiru Mai Palace, ya bayyana taron a matsayin wani shiri na ruhi da nufin neman taimakon Allah wajen magance matsalar rashin...
    ADC ta ce, duk da cewa an tsara filin jirgin ne don karbar fasinjoji miliyan 14 a cikin shekara guda, amma rahotannin da ake da su sun nuna cewa, filin jirgin ya karbi fasinjoji miliyan 6.5 ne kawai a shekarar 2024, kasa da rabin karfinsa.   Don haka, ADC ta yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su yi watsi da wannan aiki na “rashin hankali”, inda ta bukaci a dakatar da shi nan take, sannan a karkatar da kudaden zuwa ayyukan da al’umma suka fi bukata, wadanda su ya kamata kowacce gwamnati ta fi ba su muhimmanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ga alama kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu a fafutukar da ake yi ta ganin iyaye mata sun shayar da jariransu nono zalla a wata shida na farko. Rahotanni sun ce duk da daɗewar da aka yi ana wayar da kai har yanzu matan da suke shayar da yara nono uwa zalla ba su haura kashi 29 cikin ɗari ba. NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi? DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suke hana mata shayar da ’ya’yansu nono zalla na watanni shida. Domin sauke...
    A cewar sanarwar, AIHS za ta taimaka wajen haɓaka tambarin dangote da haɓaka dabarun haɗin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki. Kodinetan shirin Barista Festus Adebayo ya shaida wa manema labarai cewa, za a iya cike giɓin gidaje a ƙasar ta hanyar haɗin gwiwar Haɗin kan Jama’a masu zaman kansu (PPP). Ya ce: “Kwarewa da haɗin gwiwa su ne manyan abubuwan da muka a gaba, idan aka yi la’akari da saurin ci gaban fasaha a cikin gine-ginen gidaje, samar da kudaɗe da kuma inganta tsarin.” Ya ce taken taron na wannan shekara, Maimaita Gidaje Ta Hanyar Sabuntawa, wanda daidai yake da ainihin darajar kamfanin. Barista Adebayo ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa haɗin gwiwa da kamfanin Simintin dangote...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da babban shirin dashen bishiyoyi miliyan biyar a shekarar 2025. An fara dashen ne yankin Yanbawa da ke Ƙaramar Hukumar Makoda. Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai  Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi Gwamnan ya ce wannan shiri na nufin yaƙi da sauyin yanayi, farfaɗo da ƙasar da ta lalace, da kuma kare muhalli. Ya ce an fara dashen bishiyoyin a wannan fili tun shekarar 1972, amma aka bari ya lalace. Yanzu gwamnatinsa ta gyara shi don ya taimaka wajen shawo kan matsalolin fari da sauyin yanayi. Ya ƙara da cewa wannan shiri yana daga cikin ayyukan muhalli da gwamnatinsa ta aiwatar cikin shekara guda....
    Auwalu Labarina, wanda ke cikin matasa jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a Masana’antar Kannywood, ya fito a manyan fina-finai da dama da suka hada da darasi, Kwana Casa’in, Gidan Sarauta da kuma shirin nan na Labarina, ya kuma samu kyautuka da dama da suka danganci wannan sana’a tasa ta fim a lokuta daban-daban. Kazalika, ya yi nuni da cewa; yanzu mafi akasarin mutane, ba sa son abin da zai taimaka musu; kawai dai sun fi mayar da hankali wajen sharholiya iri-iri. da yake amsa tambaya a kan me yasa ya fi mayar da hankali wajen ɗora bidiyo, musamman na jarumai mata a Masana’antar Kannywood a shafukansa na sada zumunta, musamman kuma ‘Facebook’? Sai Baba Sadiƙ ya ce; ba komai ba...
    Sojojin HKI sun kashe falasdinawa 62 daga safiyar jiya Asabar zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Lahadi. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa mafi yawan wadanda aka kashen masu neman abainci ne, a cibiyoyin karban abincin wadanda HKI da Amurka suka kafa. Kafafen yada labarai daga asbitocin Gaza sun bayyana cewa a jiya Asabar yahudawan sun kashe mutane 38 masu neman abinci. Labarin ya kara da cewa, duk tare da sanarwar da gwamnatin HKI ta bayar na tsagaita wuta a wani bangar na zirin gaza, saboda bawa Falasdinawan dama samun agaji daga wasu wurare amma sojojin HK sun ci gaba da kashe Falasdinawan . Zuwa ranar jumma’an da ta gabata, sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa...
    Minista Idris ya bayyana damuwa da irin martanin da al’umma da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai suka nuna dangane da lamarin. Amma ya jaddada cewa hukumar da ke da hurumin dakatar da lasisin gidajen rediyo da talabijin ita ce Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), kamar yadda doka ta tanada.   Sanarwar da Gwamnatin Tarayya ta bayar kan lamarin ta ce: “Saboda haka, ministan yana maraba da matakin da Gwamnatin Jihar Neja ta ɗauka na kai koken da ta ke da shi kan zargin rashin ɗabi’a da Badeggi FM ta yi a hukumance zuwa ga NBC domin a warware batun.”   Idris ya roƙi dukkan ɓangarori da su kwantar da hankalin su, yana...
    Ya danganta mutuwar ta ƙanana da matsakaitan sana’oi a ƙasar, kan rashin samun rancen kudaɗen da za su ci gaba da ka kasuwancin su da rashin kayan aiki, da rashin kasuwa da ba a samu sosai da kuma rashin gudanar da ingantaccen shiri, kafin su fara gudanar da kasuwancinsu. Ya sanar da cewa, ya zama wajibi, ƴan kasuwa musamman ƙanana da matsakaitan sana’oi a su sani cewa, bab wani batun yin wani holewa, na jin daɗi Ya bayyana cewa, sama da ƙanana da matsakaitan sana’oi 40 a ƙasar nan, burin su ba shi ne, na ƙara yawan adadin alƙaluma ba, anna burin shi ne, na ƙarfafa zurewar kasuwancinsu. “Alƙaluma sun nuna cewa, akwai ƙanana da matsakaitan sana’oi 40 a ƙasar...
    “Kazalika sarkin ya bayyana cewa, mun kuma duba yanayinmu. Me muke da shi? Me za mu iya yi? Me ya kamata mu yi domin inganta rayuwar mutanenmu? Allah ya albarkaci ƙasarmu, ƙasa ce mai faɗi sosai, kuma ta dace da ayyukan noma. Mun kuma yi la’akari da fannin ilimi. Jihar Neja, an san tana gaba a fannin ilimi. To, kwatsam, sai wannan mataki ya samu tasgaro, yara ba su iya cin jarabawar WASC, zuwa makaranta ya yi ƙasa da ƙasa, ba a kula da malamai yadda ya kamata. Wasu makarantun ba su da malamai. Za ka ga makaranta mai yawan dalibai 300 tana da malami daya ko biyu, hakan ba abu ne mai yiwuwa ba,”in ji shi. Ya ci gaba...
    Wani fim mai suna “Dead to Rights”, wanda aka shirya game da kisan kiyashin da aka yi a birnin Nanjing, ya mamaye kasuwar fina-finai ta lokacin zafi ta kasar Sin, inda kudin shigar da aka samu da shi ya zarce yuan biliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 140 cikin kwanaki takwas kacal. Wanda aka yi amfani da ingantattun shaidun hotuna na ta’asar yakin da Japanawa suka aikata a lokacin kisan kiyashin Nanjing, Fim din na “Dead to Rights” ya ba da labari ne na wani rukunin fararen hula na kasar Sin da suka nemi mafaka a dakin daukar hoto a lokacin muguwar mamayar da azzaluman Japanawa suka yi a birnin Nanjing. A wani yunkuri na neman tsira da rayukansu hajaran-majaran,...
    Fiye da shekaru goma da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dora samun ci gaba marar gurbata muhalli a matsayin wata muhimmiyar manufar raya kasa. Ya taba fitar da manufar raya kasa ta hanyar bayar da muhimmnci ga “Muhalli”, wadda ta yi nuni da cewa ingantaccen yanayin muhalli abu ne mai matukar daraja don samun ci gaba. Tun daga wannan lokacin, kasar Sin ta ci gaba da yin sauye-sauye masu kiyaye muhalli, inda ta zama kasa mafi girma a duniya wajen kera batir na lithium da motocin masu amfani da lantarki. Game da hakan, a yayin da ake tattaunawa da Jorge Moreira da Silvas, babban darektan ofishin kula da ayyuka na MDD, a wani shiri mai suna “Leaders Talk” da...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna fatan haɓakar musayar kasuwanci tsakanin Iran da Pakistan ta haura dala biliyan 10 Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bar birnin Tehran a wannan ranar Asabar din zuwa Islamabad na Pakistan a wata ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yi masa. Shugaba Pezeshkian a cikin wata sanarwa da ya fitar kafin ya bar Tehran ya ce: “Zasu ziyarci Pakistan ne tare da tawaga bisa gayyatar da dan uwansu fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yi musu.” Ya kara da cewa: “Akwai kyakykyawar dangantaka, mai karfi da kuma zurfafa a tsakanin Iran da Pakistan. Wannan alakar ba ta shafi tattalin arziki, kimiyya, al’adu, masana’antu, da kan iyaka...
    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da barazanar kungiyoyin ta’addanci na ISIS da Al-Qaeda a nahiyar Afirka Wani sabon rahoto da kwararrun Majalisar Dinkin Duniya suka fitar ya yi gargadin karuwar barazanar da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke da alaka da ISIS da Al-Qaeda suka yi kan kasashen nahiyar Afirka. Rahoton ya yi nuni da cewa: Nahiyar Afirka na fuskantar karuwar barazanar ayyukan ta’addanci da ba a taba ganin irinsa ba, yayin da wata gungun jama’a da take karkashin kungiyar al-Qaida ke ci gaba da fadada ikonta a arewacin Mali da Burkina Faso tare da samun ‘yancin kai, gami  da samun goyon bayan ayyukan ci gaba da suka hada da jiragen sama marasa matuka ciki da nau’o’in makamai na zamani....
    A cewar NANNM, sun dakatar da yajin aikin ne domin ci gaba da tattaunawa bisa alƙawarin da gwamnati ta ɗauka na aiwatar da buƙatun cikin ƙanƙanin lokaci. Takardar ta ce, “Kwamitin zartarwa na ƙasa ya yaba da matakan da gwamnatin tarayya ta fara ɗauka, musamman yadda ta bayyana lokacin da za ta aiwatar da buƙatunmu guda tara da muka gabatar.” Takardar da shugaban ƙungiyar NANNM, Kwamared Haruna Mamman, da sakataren janar, Dr. A. Shettima suka sanya wa hannu, ta umarci mambobinsu da su koma bakin aiki nan take. Haka kuma shugabannin na ƙasa za su ci gaba da lura da yadda gwamnati za ta cika alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyar ta kuma gargaɗi duk wata cibiyar lafiya ko hukuma da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa JMI ba za ta taba manta da shi ba. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana bayyana wannan juyayin a ranar da  Haniya yake cika shekara guda da shahada, sannan shahadarsa ya zo dai dai da ranar da Pezeshkiyan ya fara shugabancin kasar. Labarin ya kara da cewa shugaba Pezeshkiyan ya bayyana haka ne a shafinsa na X ya kuma kara da cewa a ranar da na fara aiki a matsayin shugaban kasa kenen, makiya HKI da kuma Amurka suka sanyamu cikin bakin ciki tare da kashe bakommu wanda ya zo ya taya mu...
    An yi jana’izar Marigayi Sarkin Gudi da ke Jihar Yobe, Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Khaji, ranar Juma’a a Abuja, inda ya rasu a wani asibiti bayan fama da jinya. Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya ranar Juma’a ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen hakartar taron. Sanarwar da Mamman Mohammad daraktan yada labarai na gwamna Buni ya fitar ta ce, gwamnan da ke halartar wani taro a Abuja ya yanke ziyarar tasa domin halartar jana’izar marigayi Sarkin da kansa. Gwamna Buni ya samu rakiyar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Alhaji Chiroma Buba Mashio, Sanata Ibrahim  Mohammed Bomoi, Sanata Musa Mustapha, da ’yan Majalisar Wakilai. Sauran sun haɗa da sakataren gwamnatin jihar, Baba Malam Wali, ’yan majalisar dokokin jihar, da  kwamishinoni,...
    Bincike a kan zargin da ake wa Hukumar Raya ƙasashe ta Amurka (USAID) da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na ƙasa da ƙasa game da tallafa wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP da sauran masu tayar da ƙayar baya a Nijeriya har yanzu bai kammala ba. Kawo yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da aka gabatar da ke tabbatar da wannan zargi, wanda hakan ya sa binciken ya tsaya. Kimanin wata biyar ke nan da Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai na Nijeriya suka fara bincike kan zargin, amma har yanzu babu wani sakamako ko rahoto. Aminiya ta gano cewa tun sama da shekara goma da suka wuce, ake zargin wasu ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa da...
    daga ƙarshe, kwamitin ya tabbatar da cewa zai miƙa dukkan shawarwarin da al’ummar yankin suka bayar gaban Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina Malam ɗikko Raɗda don daukar matakin da ya dace.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta tabbatar da naɗin Sa’idu Yahya, mai shekaru 47, jami’i a fannin bincike kan cin hanci, inda ya shafe fiye da shekaru 18 yana aiki a Hukumar ICPC. Za A Kammala Aikin Titin Jirgin Ƙasan Kaduna-Kano A 2026 – Gwamnatin Tarayya Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya An bayyana cewa Yahya na da digiri a fannin tattalin arziki daga Jami’ar Bayero Kano,...
    Gwamnan Jihar ta Gwambe, ya tunatar da cewa; a lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya tsaya a gabanmu a matsayin ɗan takara a yaƙin zaɓen 2023, ya yi wa Arewacin Nijeriya alƙawura na musamman. Kazalika, Arewa ta amince da manufofin shugaban ƙasar, ta kuma yi tsayin daka wajen zaɓensa, inda suka bayar da gudunmawa na kimanin kashi 60 cikin 100 na ƙuri’un da Tinubun ya samu. “A yau, ga shi mun taru, domin yin nazari a kan waɗancan alƙawuran tare kuma da tantance irin ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu, abubuwan da muka samu su ne; sauye-sauyen da aka samu duk kuwa da irin ƙalubalen da ake fuskanta a wannan ƙasa. Wannan na nuna cewa, demokuraɗiyyarmu za ta...
    Akalla ’yan gudun hijira miliyan daya da dubu 400 da ke Arewa maso gabashin Najeriya ne suke fuskantar barazanar yunwa bayan yanje tallafin da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke bayarwa. Wani rahoton majalisar a kan abinci da tsaro wanda gwamnatin Najeriya, Shirin Kula da Abinci na Majalisar (FAO) da sauran masu ruwa da tsaki a baya dai sun yi hasashen ’yan Najeriya miliyan 33.1 za su iya fuskantar matsanancin karancin abinci daga tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2025. Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTN Za a kashe biliyan 712.26 don yi wa filin jirgin saman Legas garanbawul Hakan dai na nufin a yanzu yan kasar miliyan 34.7 ne ke nan suke...
    Ya nuna rashin jin daɗinsa da rabon ayyukan tituna kamar yadda aka samu a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ayyuka ta fitar a watan Mayun 2025, wanda a cewarsa, an ware Naira tiriliyan 1.394 wa yankin Kudu-maso-Yamma, yayin da ɗaukacin yankin Arewa-maso-gabas suka samu Naira biliyan 30, sai kuma yankin Arewa-maso-Yamma Naira 105 biliyan. “Rashin tsaro ya zama babban abin damuwa, ƴan fashi, tada ƙayar baya, da kuma garkuwa da mutane na ci gaba da wanzuwa a sassan Arewa da dama, inda jihohi kaɗan ne kamar Kaduna da Bauchi suka samu kwanciyar hankali,” in ji shi. Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fito da manufofin siyasa don kawo ƙarshen rikicin. ɗalhatu ya kuma soki manufofin gwamnatin tarayya kan...
    Tauraron dan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen, ya kammala komawarsa ƙungiyar Galatasaray ta ƙasar Turkiyya daga Napoli, a wata yarjejeniya ta dindindin da ta kai Yuro miliyan 75. Ƙungiyar Galatasaray ta sanar da kammala ɗaukar Osimhen a shafinta na yanar gizo a ranar Alhamis, inda ta bayyana cewa yarjejeniyar ta fara aiki daga nan take. Ɗan wasan mai shekaru 26 ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru huɗu tare da zakarun na ƙasar Turkiyya, kuma za a biya shi Yuro miliyan 15 a kowace kakar wasa. Hakazalika, zai karɓi ƙarin Yuro miliyan 5 a matsayin hakkinsa na mallakar hoto, yayin da Napoli za ta sami kashi 10 cikin 100 na duk wani kudi da za a sayar da shi...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Kwanturola Janar na Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa, Bashir Adewale Adeniyi na ta shan suka daga mutane daban-daban. Yayin da wasu ke ganin abin da shugaban ya yi da cewa ya dace, wasu kuwa na ganin hakan ya yi hannun riga ga tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa. Shin ko me dokar kasa ta ce game da wannan karin wa’adi da shugaban kasan ya yi? NAJERIYA A YAU: Tinubu ya yi wa Arewa adalci a ayyuka da mukamai — Bayo Onanuga DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci...
    Yayin da yajin aikin gargadi na kasa baki daya da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) ta kira ya shiga rana ta biyu, iyalai sun fara kwashe ‘yan uwansu daga asibitocin gwamnati zuwa masu zaman kansu a jihar Filato. A Asibitin Kwararru na Jihar Filato, dogon layin masu amsar katin asibiti don neman kulawa da lafiyarsu ya yi batan dabo a lokacin da wakilinmu ya ziyarci asibitin. Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka Wata mata mai suna Misis Mary David, wacce ta yi rajista a asibitin duba lafiyar mata masu juna biyu, ta shaida wa wakilinmu cewa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A nasa tsokaci game da batun, wakilin musamman na kasar Sin a yankin kahon Afirka Xue Bing, ya ce Sin ta dade tana goyon bayan matakan wanzar da zaman lafiya da ci gaba a yankin. Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ta fuskar shawo kan tarin kalubale dake addabar duniya. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Melaye wanda shi ne dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben jihar Kogi a 2023, har yanzu bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba a nan gaba. Sai dai rahotanni na nuni da cewa, yana iya sauyawa zuwa jam’iyyar ADC – wata gamayyar jam’iyyar adawa da a baya-bayan nan ta jawo hankalin wasu jiga-jigan masu sauya sheka da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin waje na kasar siriya ya isa birnin Mosco a yau Alhamis don bude sabon shafi da kasar Rasha bayan kifar da gwamnatin Bashar Al-asad a shekarar da ta gabata. Shafin yanar gizo na larabai Arabnews na kasar Saudiya ya bayyana cewa Asaad Hassan al-Shaibani tuna ya gana da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov sannan ya fada masa cewa, kasar Siriya tana son ta kara tabbatar da wasu yarjeniyoyi dake tsakanin Rasha da Siriya a can baya, sannan a samar da sabbin wuraren wadanda sabuwar gwamnatin rikon kasar Siriya take son ta kulla da Rasha, a cikin yanayin mutunta juna. A nashi bangaren Sergey Lavrov ya bayyana cewa kasar Rasha a shirye take ta taimakawa sabuwar gwamnatin...
    Tawagar kananan yan wasan damben gargajiya na kasar Iran sun zama zakara a wasannin da aka gudanar a na wannan shekara ta 2025 tare da Zinari guda, azurfa guda da kuma Tagullah 4. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gasar wasan na damben gargajiya na kasar Iaran suna fadar haka a birnin Athen na kasar Girka. Sun kuma kara da cewa tawagar yan wasan zun zama zakara a wannan gasar ne duk da cewa mutum guda daga cikinsu bai shaga wasan ba. Labarin ya kara da cewa matasan kasar Iran sun kware a wammam wasan gargajiya, wanda ake kiransa damben Roma. Tawagar ta sami, zinari 1, azurfa 1 da Tagulla 4 , ta kuma sami maki...
    Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin wa’adin shekara guda ga shugaban hukumar Kwastan ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi. Kafin wannan ƙarin wa’adin, aikin Adeniyi zai kare ne a ranar 31 ga Agusta, 2025. Sai dai sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis ta ce wannan mataki na Tinubu zai ba Adeniyi damar kammala muhimman gyare-gyare da ayyuka da gwamnatin ke aiwatarwa a hukumar. Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Ziyarci Jama’a, Ya Daina Sauraron Gwamnoni — ADC Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje A cikin manyan ayyukan da ake son a kammala akwai shigar da...
    Tsohon ɗan wasan tsakiyar Barcelona, Carles Perez, yana kwance a asibiti a ƙasar Girka bayan da wani kare ya cije shi a al’aurarsa yayin da yake yawo da nasa karen a Thermi, a wata unguwa a Thessaloniki, ranar Talata. Perez, mai shekaru 27, yana ƙoƙarin raba karensa da wani da suke fada lokacin da ya ji ciwo mai tsanani a wajen. An garzaya da shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa a Panorama inda aka ɗinke masa raunin da ƙwayoyin da suka kai guda shida. Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro Diaz Ba Na Sayarwa Bane – Liverpool Ta Fadawa Barcelona Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aris FC, wacce ta karɓi Perez aro daga Celta Vigo, ta tabbatar...
    Binciken likitoci da ‘yansanda ya tabbatar cewa gubar ce ta yi sanadin mutuwarsa. Haka kuma, kotun ta yanke wa wani mutum mai suna Sani Sa’adu hukuncin ɗaurin shekara biyar saboda ɓoye gaskiya da ya yi dangane da wata Gift Bako, wadda ake zargi da hannu a kisan. Lauyoyin waɗanda aka yanke wa hukunci sun nemi sassauci saboda suna da iyalai, amma lauyan gwamnati ya bayyana jin daɗinsa da hukuncin, inda ya ce an yi adalci kamar yadda doka ta tanada. Rabe Nasir, ya taɓa zama ɗan majalisar tarayya da kuma kwamishinan Jihar Katsina a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Aminu Bello Masari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta saki tare da hada wadanda aka yi garkuwa da su talatin da biyar tare da iyalansu.   Sun kunshi mata goma sha shida da yara goma sha tara daga Kagara, Tegina da Agwara, bayan sun shafe makonni a hannun ‘yan sanda da ke tsare da kuma kawar da hankalinsu daga barayin da ke Minna.   Kwamishinan ‘yan sanda mai kula da jihar Neja Adamu Abdullahi Elleman ya bayyana haka a lokacin wani takaitaccen bayani da ya mikawa shugaban karamar hukumar gidan rediyon Ayuba Usman Katako a Minna.   Kwamishinan ‘yan sandan wanda mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Ibrahim Adamu ya wakilta, ya bayyana cewa za’a sake haduwa da wadanda abin ya shafa da iyalansu domin...
    Sama da mutum 5,000 ne suka tsere daga gidajensu a Jihar Katsina, sakamakon sabbin hare-haren da ’yan bindiga suka kai a Ƙananan Hukumomin Bakori da Faskari. Mutane daga ƙauyuka sama da 10 sun nemi mafaka a garin Bakori, inda da dama ke zaune wajen ’yan uwansu, yayin da wasu ke kwana a waje ba tare da masauki ko abinci ba. Wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu saboda ɗan Kudu ne — Onanuga Tallafin matar Tinubu na N1bn ga ’yan gudun hijirar Binuwai ya bar baya da kura Wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun bayyana cewa, maharan sukan shiga ƙauyuka da yawa, inda suka dinga harbi, ƙone gidaje, sannan suka sace mutane ciki har da mata da ƙananan yara....
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta zargi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kin yin adalci wurin ayyuka da raba mukamai tsakanin Arewa da Kudancin Kasar nan. Wadannan zarge-zarge suka sa fadar Shugaban Kasa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai Bayo Onanuga mayar da martani ga kungiyar ta ACF. Ko wadanne irin martani fadar shugaban kasar ta mayar ga kungiyar? NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Dama Da Matan Arewa A Fannin Kimiyya DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin tallafi guda biyu da suka kai fiye da naira miliyan 392, ga membobin kungiyar direbobi ta NURTW da kuma ƴan kungiyar mahauta a jihar Jigawa. Wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsa na inganta rayuwar masu sana’o’in  da ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum. A wajen kaddamar da shirin a filin wasa na Dutse, Gwamna Namadi ya bayyana cewa shirin yana da manufa ta musamman domin tallafa wa jama’a kai tsaye. Ya ce ƙungiyoyin NURTW da mahauta suna da matuƙar tasiri, ba kawai ga membobinsu ba, har ma da al’umma gaba ɗaya, shi ya sa gwamnatinsa ta ga dacewar tallafa musu. Gwamnan ya kara da cewa taimakon...
    Dangane da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka da aka gudanar a kwanan nan, Guo Jiakun ya bayyana cewa, ana fatan bangaren Amurka zai yi aiki tare da Sin wajen amfani da tsarin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, don sa kaimi ga bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka cikin kwanciyar hankali. Dangane da batun Falasdinu kuwa, Guo Jiakun ya ce, “manufar kafa kasashe biyu” ita ce hanya daya tilo ta hakika ta warware matsalar Falasdinu, kuma kasar Sin tana goyon bayan al’ummar Falasdinu wajen kafa kasa mai cin gashin kanta.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
      A shekara ta 2009, hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya ta dauki Yusuf aiki a matsayin mataimakin koci ga Samson Siasia  wanda ke rike da mukamin babban kocin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Yusuf har yanzu yana aiki da Siasia, ya taimakawa Pillars samun gurbin shiga gasar cin kofin CAF, a shekarar 2012 ya koma Enyimba inda ya maye gurbin Austin Eguavoen a matsayin koci kuma ya taimaka masu wajen lashe kofin gasar Federation Cup na shekarar 2013. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wadannan ’yan wasan kwallon kafa na mutum-mutumi sun sake nuna bajintar da kasar Sin ke nunawa a fagen kere-keren mutum-mutumi masu siffar dan’adam da kuma yadda masana’antar bangarensu ke samun ci gaba cikin hanzari a kasar. A watan Agusta mai kamawa ne kasar Sin za ta karbi bakuncin gasar wasannin motsa jiki na mutum-mutumi masu siffar dan’adam. Kuma wannan wasan kwallon kafa na mutum-mutumi da aka gwabza fafatawar karshe a dandalin wasannin motsa jiki na fasahar zamani da ke birnin Beijing, wata kyakkyawar shaida ce a kan yadda kasar ta shirya wa karbar bakuncin wannan gasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Adamu ya bayar da hujjar cewa, Sarkin Musulmi ne ke shugabantar daular gargajiya mafi girma a Arewacin Nijeriya, tare da dukkan sarakunan yankin karkashin jagorancinsa na ruhi da al’adu.   Ya yaba da shugabancin Sarkin Musulmi Abubakar na tsaka-tsaki, samar da zaman lafiya, da jagoranci na hadin kai.   Sun bayyana shi a matsayin mutum mai kishin kasa wanda ya yi namijin kokari wajen inganta tattaunawa tsakanin addinai da hadin kan kasa.   Kungiyar ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa, da fadar shugaban kasa, da sauran al’ummar Nijeriya da su goyi bayan nadin, inda ta ce hakan zai karfafa cibiyoyin gargajiya da kuma samar da hadin kai a tsakanin sarakunan gargajiya a fadin kasar. Daga kanmu, magana...
    Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin yankin. Chen Binhua, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Larabar nan, ya ce kalaman Lai na cike da yaudarar kai, sun kuma fayyace manufar da ya dage a kanta ta “neman ’yancin kan Taiwan”. Kazalika, mummunan kayen da DPP ta sha a kuri’un da aka kada ranar Asabar din karshen makon jiya, ya fayyace ajandarta ta yin fito-na-fito da Sin, tare da fafutukar...
      Ministan Ƙasa na Ci Gaban Yankuna, Uba Maigari Ahmadu, ya yaba wa ci gaba da tattaunawa tsakanin jami’an gwamnati da shugabannin arewa yana mai cewa wannan “tattaunawa ce mai tarihi kuma cike da ƙarfi,” yana nuna cewa hangen nesa na Shugaba Bola Tinubu ga Arewa ya fara samo asali kuma yana haifar da sakamako.   Yayin jawabi a taron gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello a rana ta biyu na zaman tattaunawa tsakanin gwamnati da alumma, ministan ya jaddada cewa wannan zama shi ne karo na farko a tarihin mulkin Najeriya inda ministoci, daraktocin hukumomi, shugabannin kwamitoci, da sauran manyan jami’an gwamnati daga Arewa suka “mika kansu don a yi musu tambayoyi” daga mutanen da suke yi wa hidima....
    Sanata Aniekan, ya gargaɗi jama’a da su daina yaɗa jita-jita ko bidiyo na ƙarya da ka iya tayar da hankali, tare da yaba wa da ƙoƙarin da ofisoshin jakadancin Nijeriya da Ghana da kuma ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ke yi wajen warware matsalar. Ya ƙara da cewa: “Zaman lafiya, haɗin kai da girmama juna su ne ci gaba da zama ginshikin dangantakar ƙasashenmu biyu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamandan, Nigerian Defence Academy NDA, Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya bukaci dalibai da su jajirce wajen ganin sun samu nagartar ilimi. Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya yi wannan kiran ne a yayin bikin yaye dalibai da jawabai da kuma bayar da kyaututtuka da aka yi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Malali Kaduna. Kwamandan NDA wanda tsohon dalibi ne a kwalejin ya bayyana jin dadinsa da yadda dalibai ke gudanar da ayyukansu ya yabawa mahukunta da ma’aikatan FGC Kaduna bisa yadda suke kiyaye ka’idoji. A nasa jawabin shugaban kungiyar tsofaffin dalibai ta FGC Kaduna, Kwamared Seyi Gambo ya ce kungiyar za ta ci gaba da bayar da gudummawar ta wajen daukaka darajar kwalejin ta hanyar daukar matakai na koyar...
    An ceto dukkanin mutane 14 ba tare da wani ya ji rauni ba, amma abin baƙin ciki, wani matashi ɗan shekara 27 mai suna Abba daga garin Funtua ya rasa ransa kafin isowar ’yansanda. A wani lamari da ya faru a ranar 28 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 11:27 na dare, an sake kiran ’yansanda daga ƙauyen Zagaizagi, inda aka sanar da su cewa wasu ’yan bindiga sum hari tare da sace wasu mutane ƙauyen. ’Yansanda sun isa wajen suka gwabza da ’yan bindigar, kuma sun samu nasarar ceto wasu mutane 14 da kuma ƙwato shanun da aka sace guda biyu. Amma, mutane biyu daga cikin mazauna ƙauyen sun rasa rayukansu a harin. Rundunar ta ce har yanzu tana...
    Sakatariyar kungiyar kasashen yankin Caribeans  ( Caricom) ta bayyana cewa; kasashen yankin suna son ganin bunkasa alakar kasuwanci da abokansu na nahiyar Afirka.  Sakatariyar kuniyar ta kasashen Caribbian ta bayyana hakan ne a lokacin jawabin bude taron karawa juna sani a taron kasuwanci da zuba hannun jari a tsakanin yankin da nahiyar Afirka da aka yi a Grenada. Ta kuma kara da cewa:  Wajibi ne mu bude sabuwar kafar kasuwanci a tsakanin yankunan biyu, kuma ya kamata ace giman kasuwanci a tsakanin bangarorin biyu ya karu da kaso 3% na jumillar kasuwancinmu.” Kamfanin dillancin labarun “Reuters’ya bayyana cewa wannan matakin na kasashen Caribbean yana nuni da sauyi a huldarsa ta kasunwaci da Amurka da Canada da kuma kasashen turai da...
    ’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina sannan suka mayar da sama da 6,000 ’yan gudun hijira. Maharan dai sun rika kashe mazauna kauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa. Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan, ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka tarwatsa kauyuka kamar su Guga da Kandarawa da Kakumi da kuma Monono. Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Har ila yau lamarin ya shafi ƙauyukan anguwar ’Yar Dabaru da anguwar Ɗan Marka, da Sabon Gida da ƙauyan Doma da dai sauran su....
    Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sauke Farfesa Muhammad Sani Bello daga matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai kuma memba na majalisar zartarwa ta jihar. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Talata, an bayyana cewa Ahmed Maiyaki, wanda shi ne Manajan Darakta na Kamfanin Yaɗa Labarai na Kaduna (KSMC), ne za a maye gurbinsa. Sin Da Benin Da Thailand Za Su Aiwatar Da Matakan Saukaka Tantance Kaya Na Kwastam Babu Wata Karamar Hukumar Da Ke Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang Gwamna Sani ya gode wa Farfesa Bello bisa ayyukan da ya gudanar, inda ya ce shi ne kwamishinan ilimi na farko a gwamnatinsa, kafin daga baya ya...
    Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar wata kungiya mai suna Partnership for Agile Governance and Climate Change (PACE) ta kaddamar da manufofinta na sauyin yanayi a hukumance. Wannan manufa mai mahimmanci ta samar da taswirar dabaru don ragewa, daidaitawa, da tsarin tafiyar da yanayi mai hadewa a duk sassan ci gaba a jihar.   Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da taron wanda aka gudanar a dakin taro na Armani Event Centre dake Kano, Gwamna Abba Yusuf wanda sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Farouk ya wakilta, ya bayyana taron a matsayin wani babban ci gaba a kokarin gwamnatinsa na mayar da jihar Kano a matsayin mai ci gaba a harkokin tafiyar da yanayi da muhalli.   Gwamna Yusuf ya...
    ’Yan bindiga sun tarwatsa kauyaku sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina. Maharan dai sun rika kashe mazauna kauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa. Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan, ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka tarwatsa kauyuka kamar su Guga da Kandarawa da Kakumi da kuma Monono. Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Har ila yau lamarin ya shafi ƙauyukan anguwar ’Yar Dabaru da anguwar Ɗan Marka, da Sabon Gida da ƙauyan Doma da dai sauran su. Hakan dai ya haifar da kauracewa ƙauyukan ga mazaunansu da...
    Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da jarirai (MNCHW) na shekarar 2025 tare da raba fakiti 6,000 na kayan haihuwa da na’urar (C/S) 500 ga cibiyoyin lafiya a fadin jihar.   Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta shi ne ya jagoranci bikin kaddamar da shirin a hukumance da aka gudanar a cibiyar lafiya matakin farko na Birji da ke karamar hukumar Madobi.   Ya yi nuni da cewa, wannan aikin ya hada da na rigakafi na yau da kullun ga yara, karin sinadarin Vitamin A, Rarraba gidajen sauro masu maganin kwari ga mata masu juna biyu.   Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na karfafa...
    Fira ministan Birtaniya ya bayyana cewa: Za su amince da kasar Falasdinu a watan Satumba idan yanayin Gaza bai canza ba Keir Starmer ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne domin kare tsarin kasashe biyu, kuma kasarsa na da wani nauyi na musamman da ya rataya a wuyanta wajen ganin an samar da zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu. Ya ce tallafin da kasarsa ke baiwa Tel Aviv yana nan daram. Fira ministan na Burtaniya ya jaddada cewa kin amincewar da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi na samar da kasashe biyu kuskure ne kuma kuskure ne na dabi’a da dabaru. Ya jaddada cewa dole ne a bude mashigar kasa sannan kuma a bar manyan motocin...
    Har ila yau, Ribadu ya ce yanzu mutane suna iya zuwa gonakinsu a wuraren da a baya ba a iya shiga saboda barazanar ‘yan bindiga. Sai dai duk da wannan ikirari, har yanzu wasu yankunan kamar Zamfara, Benuwe da Filato na fama da hare-haren ‘an bindiga da rikicin ƙabilanci. A ƙarshen makon da ya gabata, ‘yan bindiga sun kashe mutane a Kauran Namoda a Jihar Zamfara. Sannan ƙungiyar Boko Haram har yanzu na ci gaba da zama barazana a Arewa Maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
    Kwamitin neman sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba daga Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa, ya gabatar da takardar bukatarsa ga kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kirkiro jihohi da kananan hukumomi a zaman da aka yi a jihar Kano. A yayin mika takardar, Shugaban kwamitin kuma Hakimin Kanya Babba,  Makaman Ringim, Malam Mohammed Ibrahim ya bayyana cewar wannan yunkuri ya bi duk sharuddan da kundin tsarin mulki ya shimfida don kafa sabuwar karamar hukuma.   Makaman na Ringim ya kara da cewar, daukacin al’ummar yankin Kanya Babba, ciki da wajen mazabar na matukar goyon bayan hakan domin bunkasa ci gaban tattalin arziki da al’umma a yankin. Da yake karbar takardar, Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yau Talata, kwamitin kwaskwarima da raya kasar Sin, ya fitar da kudin Sin RMB yuan miliyan 200, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 28, domin tallafawa wajen farfado da sassan birnin Beijing da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa, musamman ma fannin sake gina ababen more rayuwar jama’a na sufuri, da samar da ruwan sha, da kiwon lafiya, da na hidimomin al’umma a gundumomin Miyun da Huairou, a kokarin ganin rayuwa ta dawo kamar yadda take a wuraren, an kuma dawo da ayyuka kamar yadda aka saba. Ban da haka kuma, ma’aikatar kudi, da ma’aikatar lura da ayyukan gaggawa ta kasar sun zuba kudin Sin yuan miliyan 350, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 49 don tallafawa biranen Beijing, da Tianjin, da lardunan Hebei, da...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminai, ya bayyana cewa a cikin yakin kwanaki 12 da ya gabata JMI ta bayyanawa duniya karfinta da jajircewar a ga duniya. Da kuma tabbatan JM tayi a kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a taron cika kwanaki 40 da shahadar wadanda suka yi shahada a yankin. Labarin ya kara da cewa mafi yawan wadanda suka halarci tarun iyalan shahidan yakin kwanaki 12 ne da jami’an gwamnati da kuma manya-manyan sojojin kasar da sauran Jama’a. Jagoran ya kara da cewa, HKI da Amurka basu fadawa JMI da yaki don shirin ta makamashin Nukliya ko don take hakkin...
    Likitoci a jihar Lagos na tarayyar Najeriya sun fara yajin aiki na gargadi na kuma kwanaki 3 saboda nuna rashin amincewasu da rage hakkokinsu da kuma hanasu kudadensu wanda gwamnatin jihar take yi. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa duk tare da kokarin da ma’aikatar kiwon lafiya ta yi don kada likitocin su shiga yajin aiki amma a safiyar jiya litinin likitocin sun dakatar da ayyuka a dukkan asbitocin gwamnatin Jihar. A bangaren kasha na jami’ar koyon aikin likita na Jami’ar Lagos marasa lafiya da dama sun fito don ganin likotocinsu amma sai aka fada masu duk sun shiga ya jin aiki. Wanta marasa lafiya wacce taki fadar sunanta ta fadawa Premium times kan cewa ta zo ganin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin. Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin da wasu manoma ke dawowa daga gonakinsu a ƙauyen Zangon Maje, inda suka hau kwale-kwalen. Ya ce, jami’an bada agajin gaggawa  na yankin sun samu nasarar ceto mutane 7 a kokarin da suka yi na ceto wadanda lamarin ya shafa. Ya ƙara da cewa, masu ceton sun gano gawar mutum guda a yankin Yalleman da ke ƙaramar hukumar Kaugama. Dr Shuaibu ya bayyana cewa,...
    Mahara sun kashe akalla mutane biyar a Dajin Madam da ke yankin Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi. Wannan na zuwa ne bayan a makon jiya ’yan bindiga sun kutsa kauyukan da ke kusa da garin Mansur a karamar hukumar, inda suka kashe mutane hudu, suka kwashe kayayyaki a shagunansu. Daga bisani ’yan sanda sun sun bi su, inda suka fatattake su suka gudu zuwa cikin kungurmin Dajin Madam. Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ne ya sanar da mutuwar mutanen a yayin taron zaman lafiya da aka gudanar a garin Nahutan Darazo a kokarinsa na sasanta rikicin baya-bayan nan tsakanin manoma da makiyaya da ya yi sanadin jikkatar wassu mutane a Darazo. Gwamnan ya kuma nuna matuqar damuwarsa kan...
    Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu. A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau Talata, dan majalisar ya kuma yi bayani akan kallafaffen yakin kwanaki 12, ya yi ishara akan yadda HKI ta yi amfani da kirkirarriyar fasaha da kuma wasu hanyoyi na leken asiri,amma duk da haka ta ci kasa, saboda jagoranci mai cike da fasaha na jagora, da kuma yadda al’ummar kasar ta yi tsayin daka da goyon bayan tsarin musulunci. Haka nan kuma ya ce; Daga...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata a Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da dama a fannin karantar kimiyya. Akwai darussan da a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba, har da mazan na kaurace musu. NAJERIYA A YAU: Matakan Da Muke Dauka Don Karfafawa ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwar Kada Kuri’a —INEC DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari  ne kan dalilan da suka sa matan Arewacin Najeriya ke tsoron karantar ilimin kimiyya. Domin sauke cikakken shirin, latsa nan
    Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne. Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa na X cewa: “Trump yana wasa, irin wasan gargadi tare da Rasha: Na kayyade mata kwanaki 50 ko 10 … amma ya kamata ya tuna abubuwa biyu: Na daya Rasha ba Isra’ila ba ne ko kuma Iran. Na biyu. duk wani sabon gargadi yana matsayin barazana ne kuma matakin kunna wutar yaki ne. Ba tsakanin Rasha da Ukraine ba, amma tare da kasarsa. Amurka ta...
    Mummunar yunwa a Gaza.. Wakilin gidan talabijin na Al-Alam ya bayyana cewa: Shi da iyalansa kwana biyu ba su ci abinci ba Wakilin gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran ya ruwaito cewa: An samu barkewar yunwa mai tsanani a Gaza, inda ya tabbatar da cewa ya kwashe kwanaki biyu bai ci komai ba. Basil Khairudden wakilin gidan talabijin na Al-Alam a Gaza, ya ce: “A ranar Juma’a, shi da iyalinsa da daukacin al’ummar Gaza ba su iya samun ko da biredi guda da za su ci ba, sakamakon yunwa da ake fama da ita a Gaza.” Ya tabbatar da cewa a Gaza akwai mutanen da ba su ci abinci ko da sau daya a tsawon kwanaki uku. A ranar...
    Amma yanzu, babu matsalar gaba ɗaya a ƙananan hukumomi 11, yayin da aka samu sauƙi a wasu tara. Ya ce har yanzu ana fama da hare-hare a ƙananan hukumomi huɗu: Faskari, Ƙankara, Safana da Matazu. Kwamishinan ya jaddada cewa jami’an tsaro suna iyakar ƙoƙarinsu, kuma gwamna yana ci gaba da tattaunawa da manyan jami’an tsaro domin kawo ƙarshen matsalar. Ya buƙaci al’umma da su daina suka, su kuma tallafa wa jami’an tsaro da addu’a da fahimta, ganin irin sadaukarwar da suke yi domin kare rayukan jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Sama da mutum 100 daga cikin jami’an tsaron al’umma da  Gwamnatin Katsina ta samar ne suka suka mutu a yayin aikin karaɗe ’yan bindiga da suka addabi al’ummomin jihar. Wannan ƙari ne a kan sojoji da kuma aƙalla jami’an ’yan sanda 30 da suka rasu a yayin aikin tabbatar da tsaron rayuwa da duniyoyin al’umma, a cewar ma’aikatar tsaron jihar. Kwamishinan tsaron jihar, Nasir Mua’zu ya sanar da haka ne a martaninsa kan wasu rahotanni da ke yawo a kafofin sada zumunta, waɗanda ya ce ana amfani da su domin tayar da hankalin jama’a. Mu’azu ya ce Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa yana yin iya bakin koƙarinsa wajen shawo kan matsalar ’yan ta’adda kuma ana samun nasara a kansu. Kwamishinan...
    Ya bayyana halin da aka shiga mara daɗi, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka yi asarar dukiyoyi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta tallafa musu wajen sake gina musu gidajen su da sauya muhallinsu. Fintiri ya kuma soki waɗanda ke yaɗa rahotannin ƙaryar game da lamarin, ba tare da fahimtar ainihin abin da ke faruwa ba, inda ya ce hakan yana da nasaba da tuggun siyasa da son zuciya. Ya bayyana cewa maƙasudin ambaliyar sun haɗa da ruwan sama mai yawa da toshewar hanyoyin ruwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Umarnin NYSC ta amince da sanya siket ga mata masu hujjar sanya wa saboda addininsu. Umarnin NYSC ta dawo da su ta ‘yan matan da suka shigar da ƙarar tare da ba su takardar shaidar kammala NYSC. Kotun kuma ta bayar da umarnin bai wa kowacce daga cikinsu kuɗaɗe har ₦500,000 a matsayin diyya saboda tauye musu ‘yancin su. Kotun ta kuma bayyana cewa cin zarafi da muzantawar da suka fuskanta daga hannun jami’an NYSC ya ci karo da ‘yancinsu na yin addini da bayyana shi a aikace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya bukaci shuggaban kasar Amurka Donal  Trump ya taiama ya kawo karshen yaki a Gaza, ya kuma kawo karshen walar da Falasdinawa suke ciki. Jaridar The Nation ta kasar Amurka ta nakalto shugaba Sisi yana fadar haka a wani jawabinda ya gabatar a yau Litinin, inda yayi alkawaliwa mutanen kasar masar kan cewa masar bazata taba kyale mutanen Gaza a halin da suke ciki ba har abada. Ya ce: Gwamnatin kasar Masar tana daga cikin kasashen da suka tsaya don ganin an kawo karshen wannan yakin, tare da Amurkan da kuma kasar Qatar don tabbatar da cewa an kawo karshen yakin . Shugaban daga karshe ya gabatar da shawarar samar da kasashe biyu a matsayin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Tsarin Fansho na Hadin Gwiwa tsakanin Jiha da Kananan Hukumomi a Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta raba sama da Naira Biliyan 1 da dubu 500 ga tsofaffin ma’aikata 569. Yayin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar shirin a gaban Gidan Fansho kafin fara rabon kudin, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya bayyana tsarin fansho na jihar a matsayin daya daga cikin mafi nagarta a kasar nan. A cewarsa, fiye da jihohi ashirin sun kai ziyara jihar Jigawa domin koyon yadda take tafiyar da shirin fansho. Ya jinjina wa Gwamna Umar Namadi saboda dagewarsa da kuma jajircewarsa wajen dorewa da inganta tsarin fansho a jihar. Alhaji Dagaceri ya yabawa Gwamna Namadi kan...
    A kokarinsa na gano hakikanin dalilan da suka sa aka bayar da beli ga wani sanannen mai safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu, da aka ce an sako shi bisa umarnin Kwamishinan Sufuri na Kano, Ibrahim Ali Namadi, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wani kwamiti na mutum takwas domin gudanar da bincike mai zurfi. Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ne ya kaddamar da kwamitin a madadin gwamnan. An umurci kwamitin da ya gudanar da binciken cikin mako guda, domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma ba da shawarwari kan matakin da ya dace a dauka. Shugaban kwamitin shi ne Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Dokoki,...
    Ministan Harkokin Tsaron Ƙasa, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya baiwa iyalan marigayi Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, gudummawar naira miliyan biyar da kuma kayan abinci, bayan rasuwarsa a ranar Alhamis da ta gabata a birnin Abuja sakamakon gajeruwar rashin lafiya.   Dakta Matawalle, ya bayyana alhininsa bisa wannan rashi na Mai Martaba.   Baya ga gudummawar kuɗi, ministan ya kuma bada buhunan shinkafa 20, gero 10, masara 10 da kuma dawa 10 ga iyalan mamacin.   Wata tawaga mai ƙarƙashin jagorancin Sanata Hassan Muhammad Nasiha, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara a zamanin mulkin Matawalle ne suka miƙa gudummawar a madadin ministan. Dakta Matawalle ya bayyana marigayi Sarkin Gusau a matsayin shugaba mai ɗabi’a ta gari, wanda ya kasance...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasar Amurka ta sanar da dakatar da bai wa mutanen Nijar bisa ta shiga cikin kasarta har illa masha Allahu. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ne ya tabbatar da cewa an dakatar da bayar da bisa din ga ‘yan kasar Nijar da suke son shiga cikin kasar, saboda abinda ya kira matsala da ake da ita da gwamnatin Nijar, ba tare da yin Karin bayani ba.  Sai dai kuma sanarwar ta yi togiya akan jami’an diflomasiyya da sauran jami’an gwamanti,kamar yadda wani sako na diplomasiyya ya nuna a ranar 25 ga watan Yuli. Wannan matakin na  Amurka ya biyo byan rashin jituwar da ake da shi a tsakanin gwamatin Amurka da gwamnatin Jamhuriyar Nijar. A watan Satumba...
    A yau Litinin ne za a yi jana’izar sanannen mawakin kasar Lebanon wanda ya yi fice da wakokin gwgawarmaya da kishin kasa wanda zai sami halartar wakilan gwamnatin kasar da kuma al’umma. Jana’izar za ta kasance ne a majami’ar  Raqad Sayyida dake garin Bakfaya. Asibitin Khuri da Rahbani ya rasu ya cika da mutane tun da safiyar yau domin daukar jana’izarsa zuwa garin Bakfaya. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai Rahbani ya rasu yana dan shekaru 69 bayan da ya yi gajeruwar rashin lafiya. A lokacin rayuwarsa ya shahara da wakoki na gwgawarmaya da kishin kasa, daga cikin da akwai wakar da ya yi wa Shahid Sayyid Hassan Nasarallah.
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar makamashin nukiliya wani zaɓi ne mai mahimmanci wanda ya ƙarfafa matsayin Iran a duniya Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa; Kasarsa ta shiga shawarwarin makamashin nukiliya ba na                         kai tsaye ba da Amurka bisa wata cikakkiyar shawarar kasa. Ya kara da cewa; Wannan mataki na diflomasiyya ya karfafa kimar Iran a duniya, bayan da ta samu goyon bayan kasashe fiye da 120 wadanda suka yi Allah wadai da cin zarafin da yahudawan sahayoniyya suka yi wa Iran a baya-bayan nan. Hakan dai ya zo ne a yayin wata ganawa da aka yi da Araghchi, inda ya yi nazari kan batutuwan da suka shafi makamashin nukiliyar...
    Babban jami’in kungiyar Hamas a Zirin Gaza ya bayyana cewa: Makiya yahudawan sahayoniya suna rufe gazawar sojojinsu da kisan kare dangi Khalil al-Hayya babban jami’in kungiyar gwagwarmayar Musulunci  ta Hamas a zirin Gaza ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna rufe gazawar sojojinsu ta hanyar kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen hula. A cikin wani jawabi kai tsaye ta gidan talabijin, Al-Hayya ya bayyana cewa: “Ya ku ‘ya’yan Dakarun Qassam, da na Quds Brigade, da kuma sauran kungiyoyin gwagwarmaya, abin da kuke yi ya kawo cikas ga farmakin da motoci masu sulke na makiya suke yi. Khalil ya jaddada cewa: Babban hafsan hafsoshin sojin makiya yana rufe gazawar sojojinsa da kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen...