Sudan: Mutane sama da rabin miliyan sun koma Khartoum duk da matsalar yaki
Published: 26th, August 2025 GMT
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta bayar da rahoton a ranar Litinin cewa mutane sama da rabin miliyan ne suka koma Khartoum a cikin watan Yuli, wanda ke nuna karuwar komawa babban birnin Sudan da yaki ya daidaita.
A cewar hukumar, kimanin mutane 500,074 ne suka koma birnin, wanda ya karu da kashi 400 cikin 100 idan aka kwatanta da alkaluman da aka samu a watan Yuni.
Wannan ya biyo bayan kwato birnin ne da sojojin Sudan suka yi daga hannun mayakan Rapid Support Forces (RSF) a cikin watan Maris, a ci gaba da kokarin da gwamnatin kasar ke yi na kaddamar da shirye-shiryen sake gine-gine da kwantar da hankula.
Hukumar ta IOM ta lura cewa kimanin ‘yan Sudan miliyan biyu ne suka koma gidajensu a fadin kasar cikin watanni tara da suka gabata. An samu mafi yawan mutanen da suka dawo a jihar al-Jazira, sai kuma Khartoum, wadda yanzu haka ta karbi sama da mutane 600,000 da suka dawo baki daya.
Duk da wannan, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa har yanzu ana cikin mawuyacin hali, tare da karancin samun damar gudanar da ayyukan yau da kullum da kuma barazanar sake barkewar rikici, musamman a yankunan da suka yi fama da rikici.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta godewa Rasha Dangane Goyon bayanta Kan Hakkinta Na Tace Yuranium August 25, 2025 Iran da saudiya Sun Bukaci Hadin Kan Musumi Don Kawo Karshen Yaki A Gaza August 25, 2025 Iran Ta Yi Kira Ga Kasashen Musulmi Su Yanke Hulda Da HKI A Taron OIC A Jedda August 25, 2025 Iran Da Kasahen E3 Zasu Tattauna Batun Shirin Nukliyar Kasar A Sitziland A Gobe Talata August 25, 2025 Bangaladesh Ta Kasa Samun Kudaden Kula da Yan Gudun Hijiran Rohinga August 25, 2025 Jagora: Hadin Kan Al’umma, Jami’ai Da Sojojin Kasa Da Suke Dauke Da Makamai Jan Layi Ne August 25, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Bukatar Gudanar Da Hidima Ga Al’umma Daga Kowane Dan Kasa August 25, 2025 Kwamandan Sojojin Iran Ya Jaddada Aniyar Iran Na Wurga Makiya Cikin Nadama August 25, 2025 Kafofin Watsa Labaran Isra’ila Sun Ce: Ba Za A Iya Hana Sojojin Yemen Kai Hare-Hare Kan Isra’ila Ba August 25, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Kai Hari Kan Kungiyar Red Crecent A Kasar Sudan August 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadi a matsayin martani ga sanarwar Washington na ci gaba da gwajin makaman nukiliya, yana mai kiran hakan a matsayin wani mataki na koma-baya da Rashin yin da’a ga dokokin kasa da kasa.
Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya soki Washington saboda sauya wa Ma’aikatar Tsaron kasar suna zuwa Ma’aikatar Yaki, kuma ya yi Allah Wadai da Shirin Amurka na yin gwajin makaman nukiliya, tare da bayyana hakan a matsayin yunkurin tayar da zaune tsaye da jefa duniya a cikin bala’i.
Wanda yake aikata irin wannan halayya ne ke ci gaba da yin barazanar sake kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Iran bisa hujjar hana Iran mallakar makaman nukiliya da sunan kare kansu daga Iran domin kada ta mallaki makaman kare dangi.” in ji ministan harkokin wajen Iran.
Ya yi Allah wadai da Amurka saboda sukar da ta dade tana yi wa shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran yayin da ita kuma take ci gaba da gwajin makamanta na nukiliya, wanda hakan ya saba wa dokokin duniya.
Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Laraba ya bayyana cewa makaman nukiliya na Washington su ne mafi girma a duniya, kuma ya danganta wannan matsayin da gyare-gyare da aka yi a lokacin gwamnatinsa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci