2025-12-12@22:27:26 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2902

«yankin Yammacin Kogin Jordan»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
      Bugu da kari, abu mafi muhimmanci shi ne, kasar Sin ta ba da jagoranci ga kasashen duniya ta fuskar kara bude kofa ga waje. Ta hanyar shigowa da kayayyaki da fitar da kayayyaki, kasar Sin ta ba da gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya, da kara yawan kayayyakin da kasashen duniya suke fitarwa, tare da ba da taimako ga kasashe masu tasowa wajen kyautata harkokin masana’antu. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta ba da taimako wajen shigar da mambobin WTO su 130 cikin yarjejeniyar samar da sauki a ayyukan zuba jari domin neman ci gaba, ta yadda kowa zai cimma moriyar sakamakon dunkulewar duniya cikin adalci. (Mai Fassara: Maryam Yang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CIIE Ya...
    Gwamna Lawal ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana da niyyar haɗa kai da hukumar wajen inganta jin daɗin ‘yan sanda da kyautata yanayin ayyukansu.   Ya ce, “Gwamnatina na ɗaukar matakan da suka dace don tabbatar da cewa an kula da walwala da jin daɗin ‘yan sanda. Wannan ne dalilin da ya sa muke gyaran hedikwatar ‘yan sanda ta Zamfara a halin yanzu.   “Haka kuma, muna gina wasu muhimman gine-gine a hedikwatar rundunar ‘yan sanda na Moble. Mun samu nasarori da dama a wajen, kuma muna da ƙarin shirye-shirye na gaba.   “Na ji daɗin yadda sakataren hukumar ya ambaci batun ginin sabon unguwar ma’aikatan ‘yan sanda. Idan ka duba halin da barikin ‘yan sanda ke ciki yanzu, za...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15 November 11, 2025 Daga Birnin Sin Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa? November 11, 2025 Daga Birnin Sin Jakadun Kasashen Waje: Shirin Raya Kasa Na 15 Na Sin Na Dauke Da Kyakkyawan Sako November 11, 2025
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum biyar, ciki har da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Alkalije da ke Ƙaramar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a Yobe Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun daɗe suna shigowa daga Jihar Kebbi suna kai hare-hare kan al’ummomin yankin. “Sun saba zuwa daga Kebbi da Silame, suna kashe mutane ko su yi garkuwa da su. A wasu...
    An kama mutane 18 bisa laifin fashi da makami, mutane 28 bisa laifin kisan kai, mutane biyar bisa laifin yunkurin kisan kai, mutane 20 bisa laifin fyade da laifukan da ba su dace ba, da kuma mutane 28 bisa laifin ta’ammuli da miyagun kwayoyi.   Jami’in ‘Yansandan, ya kara da cewa, daga cikin jimillar kararrakin 120, an gurfanar da mutane 97 a gaban kotu, yayin da ake gudanar da bincike kan 22 a halin yanzu.   Bugu da kari, an ceto mutane 47 da aka yi garkuwa da su da kuma mutane 39 da aka yi safarar su amma tuni an hada su da iyalansu.   Jami’in ya kuma nuna wasu kayayyaki da aka kwato a hannun masu laifin da...
    Daga Usman Muhammad Zaria   Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jaddada kudirin gwamnatin sa na ci gaba da bunkasa hanyoyin sufuri a fadin jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kaddamar da wani muhimmin aikin gina hanyoyi a karamar hukumar Mallam Madori. Yayin taron kaddamarwar, Gwamna Namadi ya bayyana cewa aikin yana cikin shirin “Gwamnati da Jama’a” wanda ke karfafa al’umma, rage matsalolin sufuri da kuma karfafa harkokin kasuwanci. Ya ce shirin ya kunshi gina manyan hanyoyi guda shida a sassan jihar, masu tsawon kilomita 179 gaba daya, a kan kudin da ya haura Naira Biliyan 81. Hanyoyin sun hada da Mallam Madori zuwa Gari Uku zuwa Kanya Babba zuwa Malorin Kasim, ta ratsa ta...
    An kuma bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana ƙoƙarin amfani da wannan tattaunawa wajen ƙarfafa dangantaka da Birtaniya, musamman wajen harkokin shari’a, musayar bayanan tsaro, da kula da ‘yan Nijeriya da ke fuskantar matsaloli a ƙasashen waje. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170 November 11, 2025 Manyan Labarai Obasanjo Ya Buƙaci Matasa Su Karɓi Ragamar Shugabanci A Ƙasashen Afrika November 11, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 A Ƙauyen Katsina November 11, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170 November 11, 2025 Manyan Labarai Obasanjo Ya Buƙaci Matasa Su Karɓi Ragamar Shugabanci A Ƙasashen Afrika November 11, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 A Ƙauyen Katsina November 11, 2025
    Wannan faɗa na daga cikin mafi muni a watannin baya-bayan nan, yayin da ƙungiyoyin biyu ke fafatawa kan ikon hanyoyin kamun kifi, da hanyoyin fasa ƙwauri a yankin Tafkin Chadi. Masana harkokin tsaro sun bayyana damuwa cewa ISWAP na iya kai farmakin ramuwar gayya a makonni masu zuwa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Obasanjo Ya Buƙaci Matasa Su Karɓi Ragamar Shugabanci A Ƙasashen Afrika November 11, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 A Ƙauyen Katsina November 11, 2025 Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano November 10, 2025
    ’Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau (ritaya), ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ta ta’azzara a Arewa, inda ’yan bindiga da ’yan ta’adda suka mamaye wasu yankuna suna kafa dokoki tare da karɓar haraji daga hannun jama’a. Janar Dambazau ya yi wannan jawabi ne a taron farko na kan tsaro da aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, mai taken “Barazanar Rayuwa da Tsaron Ƙasa.” Ya ce matsalar tsaro a Arewa ba sabuwa ba ce, domin ta wanzu tsawon sama da shekaru 20. “Ana kashe mutane a masallatai a Katsina, Borno, Zamfara da Kano. Arewa ta sha fama da rikicin manoma da makiyaya, ta’addanci da kuma hare-haren ’yan bindiga. “Mun kai wani matsayi da ’yan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yayin da tattaunawa kan makomar ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ke ci gaba da ɗaukar hankali, batun yadda za a haɗa jami’o’i masu zaman kansu cikin tsarin ƙungiyar ya sake tasowa. Wasu na ganin wannan sabon yunƙuri zai iya zama sabuwar hanyar ƙarfafa hadin kai tsakanin malamai, yayin da wasu ke gargadin cewa hakan na iya kawo tsaiko ga karatun wasu dalibai dake kauracewa jami’oin gwamnati sakamakon yawan yajin aiki da suke tsunduma lokaci zuwa lokaci. NAJERIYA A YAU: Dalilan Yaɗuwar Cututtuka A Irin Wannan Lokaci DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi...
    A wajen taron, tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), ya ce barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya, ya zama gargaɗi ga shugabanni su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro. Obasanjo ya ce, “Ku ne shugabannin yau, domin idan kuka bar gobe a hannun shugabannin yau, za su lalata komai, kuma ba za ku samu gobe mai kyau ba. Ku duba ƙasar Kamaru, shugabanta Paul Biya yana da shekara 92, to me za a ce game da matasan ƙasar?” Tsohon shugaban ya jaddada cewa lokaci ya yi da matasa za su tashi tsaye su jagoranci nahiyar Afrika domin makomarsu ta dogara da abin da suka yi a...
    Usman ya roƙi Gwamnatin Jihar Katsina da hukumomin tsaro su kawo musu ɗauki, domin hare-haren sun lalata noma da tilasta mutane da dama barin gidajensu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano November 10, 2025 Manyan Labarai Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo November 10, 2025 Manyan Labarai Gwamnati Ta Nemi Ƴan Nijeriya Su Ƙwantar Da Hankali Kan Barazanar Trump November 10, 2025
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi gwamnatin tarayyar Nigeria da ta wanke ‘yan Ogoni 9 ta fuskar shari’a, bayan gushewar shekaru 30 da zartar musu da hukuncin kisa. “Ya Ogoni 9 da su ka hada da fitaccen marubuci Ken Saro Wiwa sun kasance masu fafutukar kare muhalli daga gurbata shi da kamfanin man fetur na Shell yake yi. Wannan kiran daga kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ya zo ne a daidai lokacin da ake bude taron kare muhalli na duniya a kasar Brazil. Shugaban kungiyar ta “Amnesty International” a Nigeria, Isa Sunusi ya bayyana cewa; Duk da cewa afuwar da gwamantin ta yi musu ci gaba ne,amma  masu rajin kare muhallin na...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnati Ta Nemi Ƴan Nijeriya Su Ƙwantar Da Hankali Kan Barazanar Trump November 10, 2025 Manyan Labarai Rundunar Sojin Sama Ta Kai Hari Kan ISWAP Da Ƴan Bindiga A Borno, Kwara Da Katsina November 10, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa yanzu babu abin da ya ragewa kasashen yamma banda su amince da Iran a matsayin cibiyar kimiyyar masa’antu ta shirin nukiliya na zaman lafiya. Ministan ta fadi hakan ne a wata ziyara da ya kai hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar,  inda ya bayyana irin namijin kokarin da suke yi wajen kara inganta nukiliyar masana’antu, kuma yace kasarsa ba za ta taba yin watsi da shirin ta na nukiliya domin ayyukan zaman lafiya ba. Haka zalika ya jinjinawa iran game da irin gagarumin ci gaban da suka samu a fasahar nukiliya, inda suka shiga bangare masana’antu da ya yadu zuwa wasu bangarori daban daban. Hukumar kula da makamashin nukiliya...
    ‘Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari a kauyen ‘Yan Kwada da ke cikin garin Farun Ruwa a karamar hukumar Shanono ta jihar Kano, inda suka yi awon gaba da mata biyar, ciki har da masu shayarwa. Mazauna yankin sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kai hari ne a yankin a ranar Lahadi da yamma, inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi sannan suka afka cikin gidaje da dama, sannan suka tafi da matan. Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno “Na samu labarin cewa, an sace mata biyar, wasu daga cikinsu, masu shayarwa ne...
    An cimma wannan nasara ne a wani samame da aka kai tsawon makonni biyu a wasu wuraren da ake zargin ana aikata laifuka a yankin mai arzikin mai, in ji sanarwar.   Rundunar Sojin ta yi alƙawarin ƙara ƙaimi kan tarwatsa duk wata haramtacciyar matata a yankin Neja Delta tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC November 10, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025 Labarai NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna November 9, 2025
    Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar ta Kamaru Chiroma Bakary wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya fitar da wani sakon bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta, da a ciki ya bayyana  mahukuntan kasar da ‘yan daba masu aikata ta’addanci.” Haka nan kuma ya kira yi mahukuntan kasar da su daina abinda ya kira       ” Nuna wariya ta kabilanci.” Har ila yau Chiroma ya fada wa mahukuntan kasar cewa; “Al’ummar Kamaru ba su son su, kuma sun dawo rakiyarsu.” A yayin zaben shugaban kasar da aka gudanar, Chiroma ne ya zo na biyu bayan Paul biya a bisa kididdigar hukumar zaben kasar. An bayyana cewa Biya ya sami kaso 53.66%, yayin da Chiroma ya sami kaso 35.19%. Shi dai...
    Kungiyar ‘yan jarida ta Falasdinawa ta sanar da cewa; sojojin mamayar HKI sun kashe ‘yan jarida 44 da suke a cikin sansanonin ‘yan hijira mabanbanta a yankin Gaza. Sanarwar ta ce, wannan adadin, yana a karkashin jumillar ‘yan jarida 254 da su ka yi shahada a tsawon lokacin yakin da ya fara daga watan Oktoba na 2023, zuwa watan Oktobar wannan shekarar ta 2025. Kwamitin dake kare ‘yancin aikin jaridar dake karkashin kungiyar ‘yan jaridar ta Falasdinawa, ya ce; Kashe ‘yan jarida da HKI take yi wani shiryayyen tsari ne da ya hada kai hare-hare akan sansanon ‘yan hijira da suke a kusa da asibitoci da sauran cibiyoyin da hukumar ‘yan hijirar Falasdinawa ta MDD, Unrwa take kula da su....
    Da yake sanar da sauya sheƙarsa a ranar Litinin ta hanyar shafukansa na sada zumunta da aka tabbatar, Jibrin ya ce magoya bayansa sun yanke shawarar barin jam’iyyar NNPP da kuma kungiyar Kwankwasiyya don shiga APC da kuma yin aiki tuƙuru don marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027.   “A yau, a cikin nuna goyon baya, dubban ‘yan mazaɓarmu a garinmu na Ƙofa, Bebeji, Kano sun yi min maraba sosai. Taron ya tabbatar barinmu jam’iyyar NNPP/Kwankwasiyya, zuwa APC, da kuma goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu a kan mulki,” in ji Jibrin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025...
    ’Yan bindiga sun kai hari a Jihar Kano a daren Lahadi, inda suka yi garkuwa mata biyar ciki har da masu shayarwa. Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne a ƙauyen ’Yan Kwada da ke cikin yankin Faruruwa a Karamar Hukumar Shanono da ke Shiyyar Kano ta Arewa. Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa dandazon maharan sun yi dirar mikiya a garin ne ɗauke da muggan makamai, inda suka yi ta harbe-harbe tare da shiga gidaje suna yin awon gaba da mutane. “Sun zo kamar yadda suka saba, suna harbi a iska suna karya ƙofofi. Sun tafi da mata biyar, ciki har da masu shayarwa,” in ji majiyar. Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma.   Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    A yau Lahadi 9 ga wannan wata, an rufe taron koli na Wuzhen na ayyuka masu nasaba da yanar gizo na duniya na shekarar 2025 mai taken “kirkiro makomar yanar gizo da sadarwa mai bude kofa da hadin gwiwa da tsaro don kafa al’umma mai makomar bai daya a fannin harkoki masu nasaba da yanar gizo”, inda wakilai fiye da 1600 daga kasashe da yankuna fiye da 130 suka halarci taron da tattauna taswirar kirkiro makomar yanar gizo da sadarwa.   Babban sakataren taron Ren Xianliang ya yi bayani a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, an zartas da rahoton aiki na taron yanar gizo na duniya na shekarar 2025 a gun taron koli a...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar kwamitin wasannin Olympics na duniya (IOC) Kirsty Coventry da kuma shugaban kwamitin na karramawa Thomas Bach a Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin. Xi ya nuna cewa, kasar Sin ta kasance mai himma, mai ba da kariya kuma mai yayata ruhin wasannin Olympics. Ya ce, gasar wasanni ta kasa ita ce babban bikin wasanni mafi girma a kasar Sin. Kuma yankunan Guangdong, Hong Kong da Macao ne suka hada hannu wajen shirya gasar wasannin ta kasa karo na 15. Ana kyautata zaton cewa, wannan gasar wasannin ta kasa ba wai kawai za ta bayyana sabbin nasarorin da kasar Sin ta samu a sabon zamani ba ne, har...
    Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran ’yan Najeriya da su haɗa kai don kare ƙasar. Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Oyintiloye, ya ce matsalar tsaro ba a zamanin Tinubu ta samo asali ba, kuma a cewarsa matsalar na shafar addinai daban-daban a ƙasar. “Dole ne mu tsaya tare da Shugaba Tinubu. Wannan ba lokacin rabuwar addini ko...
    Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran ’yan Najeriya da su haɗa kai don kare ƙasar. Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Oyintiloye, ya ce matsalar tsaro ba a zamanin Tinubu ta samo asali ba, kuma a cewarsa matsalar na shafar addinai daban-daban a ƙasar. “Dole ne mu tsaya tare da Shugaba Tinubu. Wannan ba lokacin rabuwar addini ko...
    Daga Usman Mohammed Zaria Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Abba Zari Malamawa a matsayin sabon shugaban kungiyar reshen karamar hukumar Dutse. A jawabinsa yayin kaddamarwar shugaban kungiyar na jihar, Malam Nasiru Idris Sara, ya bukaci sabon shugaban da ya kasance mai gaskiya da rikon amana wajen hulda da ya’yan kungiyar tare da ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki domin cimma nasarar da ake bukata. Malam Nasiru Idris Sara, ya bukaci masu sana’ar dako a karamar hukumar Dutse da su nuna cikakken goyon baya ga sabon shugaban, tare da mutunta ‘yan kasuwa a matsayin su na jigo wajen ciniki da kasuwanci wanda ke bude kofar samu ga ‘yan dako. Ya kuma yi...
    Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani kansila mai suna Nze Ala Kuru Orji yayin da ya fita jefa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe da ke ƙauyen Orumba, a yankin ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu, lokacin zaɓen gwamnan Jihar Anambra da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata. Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya faru ne da ranar Asabar, a akwatin zaɓe na mazabar Ezukaka 1, da misalin ƙarfe ɗaya na rana. Ban taɓa zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa: “Ana tsaka da jefa ƙuri’a sai wasu matasa da ke sanye da abun rufe fuska suka bayyana, suka harbe mutumin...
    ‘Yan sandan Tanzania sun kama Amani Gologowa, mataimakin sakatare janar na jam’iyyar adawa ta Chadema a ranar jiya Asabar, bayan zanga-zangar da ta barke bayan zaben makon da ya gabata. Hukumomi sun sanar da sunayen wasu mutane 9 da ake nema ruwa a jallo dangane da abubuwan da suka faru. Jam’iyyar Chadema da wasu mambobi na kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin dan adam da dama sun yi ikirarin cewa, jami’an tsaro sun kashe mutane sama da 1,000 yayin da suke tarwatsa zanga-zangar, alkaluman da gwamnati ta yi watsi da su a matsayin marasa tushe, amma kuma gwamnatin ba ta bayar da adadin wadanda suka mutu a hukumance ba. ‘Yan sanda sun sanya Gologowa da wasu mutane tara a cikin jerin...
    Tsohon Shugaban Amurka Biden ya yi dirar mikiya kan shugaba Trump cewa; Ba wai kawai yana lalata Fadar White House ba ne  har ma da dukkan al’ummar kasar Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya yi dirar mikiya kan magajinsa Donald Trump, yana mai cewa: Shugaban na yanzu ba wai kawai ya kawo wani abin kunya ga Fadar White House ba ce, har ma ga dimokuradiyyar Amurka. CNN ta ambato Biden yana cewa: A lokacin wani taron Jam’iyyar Democrat a Nebraska a yammacin Juma’a a Omaha: “Biden na cewa, ya san Trump zai kawo wani abin kunya a kasar, amma bai sani ba shin dole ne ya amince cewa akwai wani abin kunya da ya riga ya faru.” Biden yana magana...
    Rahotanni sun nuna cewa dan wasan Taekwando na kasar Iran mai suna Abulfazl zandi ya zamo shi ne na daya a duniya a bangaren maza a ma’aunin kilograme 58, bayan yayi nasarar samun lambar yabo ta zinariya a gasar taekwando ta duniya a kasar China, Hukumar kula da wasan taekwando ta duniya ta fitar da sunayen wadanda suka yi fice a duniya a watan nuwamba, inda ta sanya gasar teakwando ta duniya da aka yi a kasar china , yan wasan kasar Iran da dama maza da mata sun samu gagarumin ci gaba a jerin fannonii daban daban na wasanni. Zandi  ya zo na daya a duniya  da maki 170.80  kuma yana mataki na 4  a bangaren Olympic, A gefe...
    Gasar cin kofin Afirka ta 2025 za a fafata tsakanin kasashe 24 da aka raba rukuni shida dauke da hurhudu kowanne. Da zarar an kammala fafatawar cikin rukunin, duk wadda ta yi ta daya da ta biyu za ta kai wasan zagaye na biyu wato na ‘yan 16 da kuma hudun da suka kare a mataki na uku a rukuni da maki mai yawa. Sai dai zagaye na biyu za a buga ne ziri daya kwalle, duk wadda aka doke sai dai ta tattara kayanta zuwa gida. Gabaki dayan gasar wasanni 52 za a buga, 36 a karawar cikin rukuni da takwas a zagaye na biyu da hudu a kwata fainal da biyu a zagayen daf da karshe da neman...
    Rahotanni sun bayyana cewa a kasar Turkiya an fitar da hukumci kama prime ministan Isra’ila banjamin Natanyaho da wasu jami’an Isra’ila guda 37 da laifin keta hakkin bil adama da kuma yin kisan kare dangi kan alummar Gaza a lokacin yaki, Wannan yana nuna irin mataki mai tsauri na doka da aka dauka kan jami’an Isra’ila a baya bayan nan, kan laifuka yaki da suka tafka kan bil adam a yakin Gaza, da kuma karfafa kasashen duniya daukar matakin da ya dace kan zargin da ake mata na kai hare-haren kan fararen hula. Sabanin tsakanin Ankara da tel aviv ya kara tsananta ne tun bayan da ta fara kai hare-haren kan fararen hula a yankin gaza a shekara ta 2023...
    A bana ne ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, gami da kawo karshen mulkin mallakar kasar Japan a yankin Taiwan da dawo da shi kasar Sin. Kwanan nan ne CMG wato babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin ya wallafa jerin wasu rahotannin talabijin guda biyar dangane da batun dawowar Taiwan kasar Sin. ’Yan jarida ma’aikatan CMG ne suka dauki rahotanni da bidiyo a yankin Taiwan, inda suka yi amfani da kwararan shaidun tarihi, don mayar da martani ga wasu kalaman karya da ke cewa wai “matsayin Taiwan ba shi da tabbas”, tare kuma da bankado markarkashiyar mahukuntan jam’iyyar DPP...
    Bishop Matthew Kukah, na Cocin Katolika da ke Jihar Sakkwato, ya ce barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na kawo wa Najeriya ya farkar da shugabannin ƙasar nan.  Trump, ya zargi Najeriya da cin zarafin Kiristoci tare da barazanar janye tallafin Amurka ko kuma ɗaukar matakin soja domin “ceto Kiristoci” a ƙasar. Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu Sai dai Shugaba Bola Tinubu, ya musanta wannan zargi, inda ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai cikakkiyar dimokuraɗiyya mai mutunta ’yancin yin addini. Da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 60 na ɗan jarida Reuben Abati a Jihar Legas, Kukah, ya ce kalaman...
    Nama ko kaza ko kifi, Man gyada ko gyada da aka nika, Daddawa, Yakuwa (ko kubewa, ko danyen ganyen kuka bisa ga nau’in da ake so), Attaruhu da tattasai, Albasa,Maggi da gishiri, Citta da tafarnuwa (idan ana so)   Yadda ake hadawa: Da farko za a wanke nama, a saka a tukunya, a zuba albasa, daddawa, maggi da gishiri, a dafa har sai ya fara dahuwa. Sannan sai a nika kayan miya, tattasai, attaruhu, da albasa tare (idan ana so, a hada da tafarnuwa da citta). Sai a kaka kayan miya bayan naman ya tafasa, a zuba kayan miya da aka nika a ciki, a barshi ya tafasa sosai. Sannan a zuba man gyada Idan ana da man gyada, a...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025
    Ministan harkokin wajen kasar Ukraine ne ya bayyana cewa da akwai ‘yan asalin kasashen Afirka 1,400 da suke cikin rundunonin Rasha suna tayata yaki. Ministan harkokin wajen kasar ta Ukraine, Adriy Sabiha ya ce; Moscow tana jan hankalin ‘yan Afirka akan su rattaba hannu akan wata yarjejniyar aiki, wacce take daidai da yankewa kansu hukuncin kisa. Har ila yau, ministan harkokin wajen kasar na Ukraine, ya rubuta a shafinsa na X cewa; ‘yan kasashen wajen da ake dauka a cikin sojojin Rasha, ana aike su zuwa inda za a yi saurin kashe su.” Jami’an gwamnatin kasar ta Ukraine sun sha yin kira ga gwamnatocin kasashen Afirka da su hana ‘yan kasarsu yi wa Rasha aikin soja da hakan yake da...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Rahotonni Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025
    Bisa ga imanin da yake da shi ya bayyana cewa “Ba za ka iya samar da zaman lafiya da bama-bamai ba; sai dai ka gina shi da amana,” ya kaddamar da abin da yanzu ake kira ‘Samfurin Zaman Lafiya na Kaduna’.   Tsarin Hadin Gwiwa:r Gwamnatin Kaduna Da ofishin ONSA A tsakiyar wannan sauyi akwai hadin gwiwa mai karfi a tsakanin Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) da Gwamnatin Jihar Kaduna. Tare suka kafa kwamitin fasaha na hadin gwiwa wanda ya kunshi masu ruwa da tsaki, masana halayyar dan’Adam, da shugabannin kananan hukumomi, wannan tawaga ba ta zo da tankoki ko jiragen yaki ba, ta zo da tausayawa, tattaunawa da bayanai. A babban aikinsu na farko, ’yan...
    Tarayyar Afirka ta yi kira da a girmama ‘yancin kai na tarayyar  Najeriya kuma ta yi watsi da barazanar Trump Kwamitin Tarayyar Afirka ya bayyana damuwarsa game da kalaman da Amurka ta yi kwanan nan game da zargin gwamnatin Najeriya da hannu a kisan Kiristoci da kuma nuna alamun yiwuwar shiga tsakani na soja a karkashin hujjar “kare ‘yancin addini.” A cikin wata sanarwa a hukumance, wacce Al Jazeera ta samu kwafinta, Kwamitin ya jaddada jajircewarsa ga ka’idojin ‘yancin kai, rashin tsoma baki, ‘yancin addini, da kuma bin doka, kamar yadda aka tsara a cikin Dokar Tsarin Mulki ta Tarayyar Afirka da sauran kayan aikin da suka shafi hakan. Sanarwar ta tabbatar da cewa: Tarayyar Najeriya kasa ce mai muhimmanci...
    Tun da farko, Daraktan DSS na Jihar Kaduna, Mr. Hakeem Abiola, an shirya taron ne domin nazarin ƙalubalen aiki da kuma karfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro. Ya bayyana cewa hukumar DSS a ƙarƙashin jagorancin Mr. Oluwatosin Adeola Ajayi tana amfani da dabaru biyu – na ƙarfi da na sulhu – domin tabbatar da zaman lafiya. Ya ƙara da cewa ci gaba da tattaunawa da shugabannin addinai da na al’umma kamar JNI da CAN ya taimaka wajen shawo kan rikice-rikice kafin su zama tashin hankali. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah November 7, 2025 Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi...
    “Mutanen duk sun manta da ‘yan garancin da suka yi gaba dayansu suka shiga wani sabon babi. Babban bango da ake ingina da shi ya fadi. Yanzu Kudancin Kaduna na jam’iyyar APC ne.” Ya yi bayanin komawar manyan mutanen biyu zuwa APC wani kokarin ci gaba ne na shi Kakakin majalisar, ya ce SHugaban majalisar ya kara jadddad Sanata Katung da Honorabul. Amos “sun zabi lamarin kawo ci gaba ne. Sun zabi su ci gaba da kasancewa da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne da kuma APC. Wannan ba karamin sauya jam’iyya bane. Jirgizar kasa ce ta siyasa. Wani sabon babi ne ga siyasar Kudancin Kaduna, da kuma gaba dayan Nijeriya.” “’Yan ‘uwana maza da mata wannan sauay shekar wani...
      Bugu da kari, Amurka ta bayyana a fili cewa batun sauyin yanayi shi ne mafi girman yaudara da aka yi a tarihin dan Adam, kuma ta fice daga “Yarjejeniyar Paris” sau biyu, wanda hakan ya yi mummunar illa ga kokarin al’ummun duniya na kyautata yanayin duniya, kana ta zama babban cikas ga hadin gwiwar duniya a fannin magance sauyin yanayi.   Geng Shuang ya kuma bayyana cewa, a kan batun magance sauyin yanayi, abun da al’ummar duniya ke bukata shi ne dunkulewa da hadin gwiwa, ba zargi da dora laifi kan wasu ba. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil November 7, 2025 Daga Birnin Sin...
    Annabi Ibrahim ne ya fara kafa massallaci ya fara tsaida sallah, wadannan salloli na Ikamu da muke yi Annabi Ibrahim ya fara, Annabi Ibrahim ya fara canza a yi layya dabba maimakon dan Adam, saboda darajar da dan Adam yake da ita wajen Allah. Ya kawo tsarin a bar layya da mutane a yi da dabbobi da abubuwa da yawa, sai dai wadannan malamai na wannan lokaci ba su yarda wani ya yi tunanin wani ilmi a waje ba, saboda suna tsoron kar ya yi wani tunani da ya fi nasu, don haka jama’a kar mu ji tsoron wani ilimi, babu wani ilimi da Annabi bai zo da shi ba, amma har yau wanda ba su san ilimin ba suna...
    Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar amincewa da dage takunkumin da ya sanya wa al-Julani Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’a a ranar Alhamis domin amincewa da daftarin kudirin da zai cire takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa Shugaban rikon kwaryar kasar Siriya Abu Muhammad al-Julani da Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Anas Khattab, inda kasashe 14 suka kaɗa ƙuri’a kan amincewar, yayin da kasar China ta kauracewa kada kuri’a. Daftarin kudurin, wanda Amurka ta rubuta kuma ta gabatar, ya yi kira da a dage takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa al-Julani da Khattab. A cewar jami’an diflomasiyyar Majalisar Dinkin Duniya, ofishin jakadancin Amurka ya rarraba daftarin kudurin ga mambobi, kuma an...
    Sudan na fuskantar matsalar jin kai mafi girma a duniya a daidai lokacin da ake kara samun karuwar fada a Darfur da El Fasher Asusun Kula da kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadin cewa: Matsalar karancin abinci mai gina jiki ta kara ta’azzara a Sudan, yana mai tabbatar da cewa matsalar karancin abinci mai gina jiki ta wuce matakin gaggawa a cikin sama da kashi 60 cikin 100 na yankunan. A halin yanzu, shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya jaddada kudurin rundunar sojin kasar na tabbatar da tsaron dukkan iyakokin Sudan da kuma murkushe ‘yan tawayen. Wani sabon gargadin Majalisar Dinkin Duniya ya sanya Sudan a kan gaba wajen fuskantar bala’in...
    Yau 7 ga watan Nuwamba, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Paul Biya murnar yin tazarce a wani sabon wa’adin shugabancin kasar Kamaru. Shugaba Xi ya ce, kasar Sin da Kamaru suna da daddadiyar alaka mai kyau. A cikin ‘yan shekarun nan, amincewar siyasa tsakanin kasashen biyu ta kara zurfafawa, kuma an samu nasarori masu yawa a fannoni daban-daban na hadin gwiwa, tare da mara wa juna goyon baya a kan batutuwan da suka shafi muradunsu da kuma batutuwa masu muhimmanci. A shekara mai zuwa ce za a cika shekaru 55 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da Kamaru, matakin da ya samar musu da sabbin damammaki na ci gaban huldarsu. Xi yana dora muhimmanci sosai kan ci...
    A ranar Juma’ar da ta gabata ne, Trump ya sake mayar da Nijeriya matsayin kasa mai matukar damuwa, sannan ya yi gargadin cewa; “idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bayar da izinin kashe kiristoci, nan take Amurka za ta dakatar da duk wani taimako da take bai wa Nijeriya, sannan kuma mai yiwuwa ta shiga kasar, domin kakkabe ‘yan ta’addan Islama da ke aikata wadannan munanan ayyuka na ta’addanci.” Kazalika, ya kuma umarci Ma’aikatar Yakin Amurka, da ta shirya domin daukar mataki. Pete Hegseth, Sakataren Yakin Amurka, a ranar Asabar ya ce; Ma’aikatar Yaki na shirin daukar mataki. Barazanar Trump dai, ta biyo bayan zargin da wani dan majalisar dokokin Amurka, Ted Cruz, ya yi a shafinsa na D,...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan yace rarrabuwa da sabanin tsakanin musulmi shi ne babban abin da makiya musulunci suke so, kuma yayi gargadin cewa rabe-rabe na cikin gida yana kare manufofin makiya ne da kasashe ma’abota girman kai na duniya. shugaban ya fadawa manya- manyan malaman Ahalus sunna da sauran malaman addini dake Sanandaj a yammacin lardin Kurdistan cewa ta hanyar hadin kai da rikon amana da kuma riko da yan uwantaka na musulunci ne kawai  musulmin duniya za su iya tunkarar makircin Amurka da Israila da ma sauran yan sahayuniya. Har ila yau ya kara da cewa wannan rarrabar ce isra’ila da Amurka da sauran yan sahyuniya na duniya suke so, domin su shagaltar da kasashen musulmi su yi...
    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da sauran ƙasashen duniya “ta hanyar difilomasiyya” game da matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta a yanzu. Kalaman shugaban na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ke barazanar kutsawa Najeriyar domin kai wa ‘yan bindiga hare-hare bayan ya zargin gwamnatin Tinubu da ƙyale su suna “yi wa Kiristoci kisan gilla” Da yake magana yayin zaman majalisar ministocinsa a jiya Alhamis, Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta kawo karshen”ta’addanci”. “Duk da kalubalen irin na siyasa da fargabar da mutanenmu ke ciki, muna ci gaba da tattaunawa da kawayenmu, muna tattaunawa a difilomasiyyance,” “Ina tabbatar muku cewa za mu kawo karshen ta’addanci. Abin da muka saka a...
    Kafar yada labarai ta CGTN da ke karkashin babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ta kaddamar da wasu tashoshi uku a dandalin FAST yau Alhamis 6 ga watan Nuwamba, da ke kunshe da tashar CGTN Global Biz, da ta China Travel, da ta Discovering China. Wadannan tashoshin za su gabatar da shirye-shiryen talabijin zuwa ga masu kallo kusan miliyan 200 a duk fadin duniya, bisa wasu manyan dandalolin FAST guda 15, alamarin da ya shaida babban ci gaban da CMG ya samu a bangaren gabatar da shirye-shirye zuwa sassan kasa da kasa.   Shirin talabijin bisa dandalin FAST, sabon salo ne wanda ya bulla cikin sauri a ’yan shekarun nan a kasuwar shirye-shiryen...
    A sa’i daya kuma, kamfanonin kasashen ketare sun samu tabbacin bunkasar kasar Sin ta hanyar halartar bikin na CIIE. Wasu shugabannin kamfanonin kasashen ketare sun bayyana cewa, kasar Sin na da manyan kasuwanni masu bude kofa, da yanayin zuba jari mai dacewa, tare da manufofi masu karko, wadanda suke janyo hankulansu matuka.   Haka zalika kuma, a matsayin dandalin shigowa da kayayyaki na musamman a duniya, bikin CIIE ya samar da tabbacin cimma moriyar juna ga kasashen duniya. A bana, a karon farko, an kafa dandalolin nune-nunen kayayyaki daga kasashe mafiya fama da talauci, tare da fadada yankunan nune-nunen kayayyakin kasashen Afirka. A halin yanzu, akwai kamfanoni har 163 daga kasashe mafiya fama da talauci da suka halarci baje kolin...
    A yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar gina ingantaccen yankin ciniki cikin ’yanci na tashar ruwa ta Hainan ko FTP a takaice. Shugaba Xi ya bayyana bukatar ne yayin dake sauraron rahoton aiki game gina yankin na FTP a birnin Sanya na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. A cewarsa, gina yankin FTP na Hainan muhimmiyar manufa ce ta kwamitin kolin JKS, wadda aka tsara domin zurfafa cikakkun sauye-sauye, da bude kofa ga waje a sabon zamani. Shugaban na Sin ya kara jaddada bukatar kyautata nazari, da aiwatar da ka’idojin aiki na cikakken zama karo na hudu na kwamitin kolin JKS na 20, tare da kokarin cimma burikan da aka sanya gaba, dangane da bunkasa yankin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Harin Amurka ya bayyana karara kan Venezuela Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Barazanar da ake yi wa Venezuela ba ta dace da al’ummar duniya ba, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance kuma za ta ci gaba da kasancewa cikin hadin kai da gwamnati da al’ummar Caracas. Da yake jawabi a bikin rantsar da ofishin wakilin Ma’aikatar Harkokin Waje a Lardin Hamadan, Araqchi ya bayyana cewa: Wannan ofishin zai taimaka wajen karfafa alakar tattalin arziki, kimiyya, da al’adu ta lardin, da kuma sauƙaƙe hulɗar jakadanci da gudanarwa ga ‘yan ƙasar. Ya lura cewa: Baba’i Ragheb, wani jami’in ma’aikatar da ya ƙware, zai jagoranci sabon...
    Muhimmin fadakarwa daga Sayyid Muqtada al-Sadr kwanaki kafin zaɓen kasar Iraki Malamin Tafarkin Shi’a na Iraki Muqtada al-Sadr ya umurci magoya bayansa a ranar Alhamis da su dakatar da duk wani zaman dirshan da zanga-zanga har zuwa lokacin zaben ‘yan majalisa dokokin kasar mai zuwa. A cikin wata sanarwa, ofishin al-Sadr ya ce ya yi nazari kan ayyukan da suka hada da tarurrukan kabilanci da na matasa da ke goyon bayan shawararsa ta kauracewa zaben kuma ya yi tsokaci, “Daga yanzu har zuwa ranar zabe, babu bukatar wani karin zanga-zanga.” Wannan shawarar ta ci gaba da tsarin al-Sadr na nisantar da kansa daga tsarin zaben tun bayan sanarwarsa a watan Yunin shekara ta 2022 na janye kansa gaba daya daga...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro November 6, 2025 Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu  November 5, 2025 Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025
    Ministan Harkokin Wajen Iran ya yaba da juriyar da kasar ta nuna yayin hare-haren Amurka da Isra’ila, wanda ya tilasta musu rokon a tsagaita wuta ba tare da shiri ba. Da yake jawabi a yammacin ranar Laraba a taron Majalisar Gudanarwa ta Lardin Hamadan, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa abokan gaba sun gaza a dukkan manufofinsu a lokacin yakin na kwanaki 12.   Kalaffafen yakin na kwanaki 12 ya bamu babban darasi inji shi, saboda mun fi karfi da a ranar 13 ga watan Yuni. A karon farko, an yi amfani da makamai masu linzami na Iran a wani rikici na gaske, wanda hakan ya ba da damar gano ƙarfi da rauninsu. A yau, Iran tana...
    Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin ƙasa da ƙasa da shari’a ya jaddada muhimmancin kara karfafa  dangantakar da ke tsakanin Tehran da Riyadh, yana mai cewa ci gaban kyakkyawar alaƙa tsakanin Tehran da Riyadh ba wai kawai yana da amfani ga ɓangarorin biyu ba ne, har ma zai  kara karfafa zaman lafiya a yankin da ma a duniya. Kazem Gharibabadi ya yi wannan furuci ne bayan ziyarar da ya kai Saudiyya da nufin fadada  haɗin gwiwa da haɗin kai tsakanin manyan ƙasashen biyu. Mataimakin ministan harkokin wajen ya jaddada cewa Iran da Saudiyya, waɗanda ke da alaƙa ta tarihi suna da kyakkyawan matsayi don yin hidima ga al’ummarsu da kuma taka domin ci gaban zaman lafiya a yanking abas...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta.   A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta. Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da nasu fahimtar daban kan wannan cuta. NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Shirin Najeriya  A...
      “Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi.   Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na musamman. Ya ce hakan zai rage cunkoso, ya haɗa al’umma, ya kuma farfaɗo da kasuwancin ƙauye da birane.   A fannin lafiya, gwamnati ta ƙaddamar da gina sabon babban asibiti a Nasarawa Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, tare da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya da dama a yankunan karkara, domin sauƙaƙa samun ingantaccen magani.   An kuma sanar da ci gaba da gyaran makarantu a dukkan...
      A gaskiya wannan yanayi ya yi matukar burge ni, kuma sai na zaci ko don saboda ina bako ne, amma yayin da na ga wasu Sinawa suna daukar hotunan bishiyoyin, sai na ce to, babu makawa wannan yanayi ne mai burge kowa da kowa, bako da dan gari kuma ciki har da dattawa. Nan take ni ma na zaro wayata, muka ci gaba da kashe hotuna ni da abokin aikina. Na yi kokarin nuna kawaici a kan yadda yanayin ya shaukantar da ni, amma sai na ga abokin nawa ya fi ni “jazabancewa”, domin shi ya fi ni yawan yin “style” na daukar hoton da kuma yawan hotunan da muka dauka.   Wani abu da na lura da shi...
    Dantsoho ya bayyana cewa, a taron Tashoshin Jiragen Ruwa na Duniya da aka yi a Kobe, Kasar Japan, shugabannin tashoshin jiragen ruwa na Afirka sun yi alƙawarin haɓaka ci gaban Tashoshin yankin ta hanyar tsarin dabaru uku – aiwatar da manufofi, sabunta haɗin gwiwa, da sauƙaƙe ciniki, wanda wannan shi ne abin da NPA ta ƙuduri aniyar aiwatarwa.   Shugaban na PMAWCA ya kuma yaba wa gwamnati da mutanen Jamhuriyar Congo saboda ɗaukar nauyin taron kuma ya yaba wa sakatariyar ƙungiyar bisa jajircewa wurin tabbatar da dandamalin tattaunawar tsakanin yankunan da kuma yadda ake samar da sabbin tsare-tsare a shugabancin kungiyar mai kula da teku. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A...
    Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na gyaran tattalin arziƙi da kuma dawo da amincewa ga tsarin kwangilolin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86 November 5, 2025 Manyan Labarai Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025
    Daga Khadijah Aliyu  An fara shirye-shirye  gudanar da taron shekara-shekara karo na 2 da bikin shigar da sabbin mambobi na Ƙungiyar Masana Harkokin Yada Labarai ta Najeriya (SNB), bayan an kaddamar da Kwamitin Shirya Taron (LOC) a Kano. An tsara gudanar da taron ne daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Nuwamban 2025. Shugaban Ƙungiyar, Farfesa Umaru A. Pate, ya umarci kwamitin da ya gudanar da aikinsa da himma da jajircewa domin tabbatar da nasarar taron, wanda shi ne irinsa na farko da za a yi a Kano. Ya bayyana cewa ana sa ran masana sama da 400 da sabbin mambobi daga ciki da wajen jihar za su halarta. Farfesa Pate ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano kan jajircewarta wurin...
    Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kwara ta ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su ba tare da wata illa ba, a kauyen Igbonla. A cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi, ta fitar, ta ce rundunar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan bindiga sun kutsa cikin wani gida, suna harbi a sama, sannan suka tafi da wasu daga cikin mazauna gidan. Daga nan ne rundunar ’yan sanda tare da ’yan banga da masu farauta suka isa yankin cikin gaggawa, lamarin da ya kai ga ceto sun hada da Fatima Wasiu da Kudus Wasiu da jaririya mai watanni shida, ba tare da jin rauni ba. Sai dai har yanzu ana ci gaba...
    Wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin dan majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Agwara/Borgu a Jihar Neja, Honarabul Jafaru Mohammed Ali. Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a jiya, a kauyen Kubul, kan hanyar Agwara zuwa Babana, a cikin Karamar Hukumar Borgu, yayin da dan majalisar ke hanyarsa ta zuwa ganawa da jama’arsa kan muhimmin shirin ci gaba. Bayan harin, Honarabul Jafaru da tawagarsa sun samu rauni, inda aka garzaya da su asibiti, kuma suna karbar kulawar likitoci a halin yanzu. A halin da ake ciki, jami’an tsaro sun isa yankin domin fatattakar ‘yan bindigar da kuma kare rayukan jama’a. Duk da haka, babu wata sanarwa ta hukuma a hukumance a yanzu game da...
    Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ma’aikatar Ilimi don tabbatar da cewa, daliban jami’a suna ci gaba da karatunsu ba tare da wani cikas ba, yana mai cewa, Gwamnatin Tarayya tana yin duk abin da ya dace don hana Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) tsunduma wani yajin aiki a nan gaba.  Da yake magana da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, a ranar Talata, Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya umarce shi da ya nemo mafita mai ɗorewa ga duk wata matsala da ka iya kawo cikas ga ayyukan ilimi a manyan makarantun kasar nan. Kamar yadda na gaya muku, Shugaban Ƙasa ya umarce mu da cewa, ba ya son ASUU ta sake...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar sama da dala biliyan 9 a duk shekara sakamakon ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, kuma kaso mafi tsoka shi ne fannin zinare. Rahotanni sun ce hakan na karawa ‘yan ta’adda karfi, inda suke amfani da wannan dama wajen tara muggan makamai a yankin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar tsaro. ‘Yan bindigar sun yi ikirarin suna samun kimanin naira miliyan 300 duk mako daga haramtattun wuraren hakar ma’adinai. NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya Shirin Daga Laraba na...
      A halin yanzu, sashen saukar kumbuna da dukkan na’urori da tsare-tsaren da ke aikin tallafa wa saukar kumbo suna ci gaba da shirye-shiryen tarbar ‘yan sama jannatin, kamar yadda Hukumar Kula da Zirga-zirgar Kumbuna ta kasar Sin ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar November 4, 2025 Daga Birnin Sin Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya November 4, 2025 Daga Birnin Sin Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa November 4, 2025
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci game da matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu, inda ta jaddada matsayin Sin na matukar goyon bayan gwamnatin Najeriya, wajen jagorantar al’ummarta zuwa turbar neman ci gaba bisa yanayin da kasar ke ciki. A ’yan kwanakin nan ne shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da sanya Najeriya cikin jerin kasashen da kasarsa ke kara mayar da hankali a kansu, bisa zargin barazanar da ya ce mabiya addinin Kirista na fuskanta a kasar. Trump ya kara da cewa, idan har gwamnatin Najeriyar ta gaza shawo kan kisan Kiristoci, to Amurka za ta hanzarta dakatar da dukkanin tallafin da take baiwa kasar, kana...
    A yau Talata ne firaministan Sin Li Qiang, ya gana da kakakin majalisar wakilan tarayyar Najeriya Tajudeen Abbas, wanda ya isa birnin Shanghai don halartar baje kolin CIIE karo na takwas. Yayin zantawarsu, Li Qiang ya bayyana aniyar kasar Sin ta karfafa salon wanzar da ci gaba bisa manyan tsare-tsare tare da Najeriya, da zage damtse wajen aiwatar da wasu muhimman matakai goma na bunkasa kawance tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, da hada hannu wajen gina shawarar “Zira Daya Da Hanya Daya” mai inganci, da bunkasa matakin hadin gwiwa a sassan gargajiya, da fadada hadin gwiwa a sabbin masana’antu, da kara kyautata gina tattalin arziki da zamantakewar al’ummun sassan biyu. Li Qiang ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen...
    Majalisar Wakilai ta dakatar da zamanta na tsawon mako guda, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan kwangila suka gudanar a ƙofar shiga ginin majalisar dokoki ta ƙasa da ke Abuja, saboda rashin biyan kuɗaɗen ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024. Rahotanni sun ce ’yan kwangilar sun yi dandazo ne a ƙofar shiga majalisar a ranar Talata, domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnati ta gaza biyansu haƙƙoƙinsu duk da cewa sun kammala ayyukan da aka ba su. China ta yi martani kan barazanar Trump ta kai hari Najeriya Kotu ta sahale wa PDP gudanar da babban taronta a Ibadan Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun rufe hanyoyin shiga da fita na majalisar, abin da ya tilasta shugaban majalisar da sauran...
      Yayin da yake gabatar da motocin, Gwamna Zulum ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na samar da tallafin kayayyaki ga jami’an tsaro a kowane lokaci. Ya jaddada cewa, tsaro wani bangare ne na muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.   Zulum ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan kokarin da suke yi na dawo da zaman lafiya a Borno. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya November 4, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike November 4, 2025 Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi  November...
    Ya ƙara da cewa yana cikin farin ciki ganin yadda Gwamna Douye Diri ya fice  daga jam’iyyar, inda ya ce, “Shi da Makinde sun taɓa cewa ba za su bari a lalata PDP ba ko a jawo ta ƙasa, amma ga su yanzu; su ne suka faɗi ƙasa.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi  November 4, 2025 Manyan Labarai Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja  November 4, 2025 Manyan Labarai Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo November 4, 2025
    rahotanni suna nuna cewa mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin  tsaro Malam Nuhu Ribadu ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya da jagororin sassan tattara bayanan sirri kan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump. Trump ya yi zargin cewa ana yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya, inda ya ce yana so gwamnati ta dauki matakin gaggawa ko kuma ya turo sojoji domin su yaki maharan da ya bayyana da ƴanbindiga masu ikirarin jihadi. A sanarwar, ya ce, “na ba sashen yaki umarni su fara shirin daukar mataki. Idan har za mu kai hari, to za mu kai harin ne cikin sauri ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda ƴan ta’addan nan suke kai hari kan kiristoci,” in ji...
    Ya jaddada cewa gwamnati tana tabbatar da tsaron kowa ba tare da bambanci ba. Kalaman Trump sun haifar da ruɗani da cece-ku-ce a tsakanin ‘yan Nijeriya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025 Manyan Labarai Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi November 3, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano November 3, 2025 Manyan Labarai Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso  November 3, 2025 Manyan Labarai Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi November 3, 2025
      Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023, ya fitar da wata sanarwa mai karfi yana gargadin cewa kalaman Trump na iya kara ruruta wutar rikicin addini da kuma kara ta’azzara rashin tsaro a kasar.   A shafinsa na X, tsohon gwamnan ya yi Allah-wadai da matakin Trump na ayyana Nijeriya a matsayin “kasar da ke da matukar damuwa,” wanda kuma ya yi zargin ikirarin “kisan kare dangi ga Kiristoci.”   Kwankwaso, ya yi kira ga Amurka da ta taimaka wa Nijeriya da tallafin fasaha da leƙen asiri maimakon barazana, sannan ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta zurfafa hulɗar diflomasiyya ta hanyar naɗa wakilai na musamman domin tattaunawa.   “Ga ‘yan uwana ‘yan ƙasa,...
    Daga Aliyu Muraki Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa  ta Kasa reshen Jihar Nasarawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya Lafia ta bi umarnin ƙungiyar ta ƙasa wajen shiga yajin aiki na ɗindindin. Wakilinmu wanda ya ziyarci asibitin koyarwar, ya bayar da rahoton cewa likitocin sun bar wuraren aikinsu domin matsin lamba ga gwamnatin tarayya ta biya dukkan hakkokinsu da ke karuwa zuwa biliyoyin naira. A yayin ziyarar, ya ruwaito cewa nas nas da ungozoma ne kawai ke kula da marasa lafiya, musamman a sashen bada kulawar gaggawa,  inda suke ƙoƙarin taimaka wa waɗanda ke cikin mawuyacin hali, yayin da ake tura waɗanda lamuransu ke neman kulawar likitoci zuwa wasu asibitoci domin samun kulawar gaggawa. Haka zalika su ma likitocin ...
      “Wannan yajin aikin yana nan yana gudana, har sai an biya duk buƙatunmu mafi ƙaranci,” in ji shi.   NARD ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a duk faɗin ƙasar a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, bayan abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati na cika jerin “mafi ƙanƙancin buƙatunta.” Wannan matakin dai tuni ya riga ya kawo cikas ga ayyuka a asibitoci mallakar gwamnatin tarayya da na jiha a faɗin ƙasar.   A halin yanzu, Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, a cikin wata sanarwa da Shugaban Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Alaba Balogun ya fitar, ya nace cewa, gwamnati ta saki kuɗaɗe kuma tana ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin...
    Kwankwaso ya kuma buƙaci gwamnatin Tarayya da ta ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da Amurka ta hanyar naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin kare muradun Nijeriya a matakin ƙasa da ƙasa. “Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin wakiltar muradunmu yadda ya kamata a kasashen waje,” in ji shi. A ƙarshe, yayi kira ga ƴan Nijeriya da su zauna cikin haɗin kai da juriya, yana mai cewa lokaci ne da ya kamata a fifita zumunci fiye da rarrabuwar kai. “Yan uwa ƴan Nijeriya, lokaci ne da muke buƙatar haɗin kai fiye da komai. Allah ya taimaki Nijeriya,” in ji Kwankwaso. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba November 2, 2025 Manyan Labarai 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su November 2, 2025 Manyan Labarai Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya November 2, 2025
    A 2022, kasashe shida ne suka daina yanke hukuncin kisa, ko dai gaba daya ko kuma wani bangare. Hudu daga cikinsu; Kazakhstan, Papua New Guinea, Saliyo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun jingine shi kwatakwata. Ekuatorial Guinea da Zambia sun ce za a rika amfani da shi ne kawai kan laifuka mafiya kololuwar muni. A watan Afrilun 2023, majalisar dokokin Malaysia ta kada kuri’ar daina amfani da shi a matsayin tilas kan laifuka 11, ciki har da kisa da kuma ta’addanci. Majalisar dokokin Ghana ma ta kada kuri’ar soke hukuncin kisa a watan Yulin 2023.   Wadanne kasashe ne suka fi yanke hukuncin kisa? Kasashe 20 ne suka zartar da hukunbcin kisa a 2022, idan aka kwatanta da 18 da suka...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 2, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu November 2, 2025 Daga Birnin Sin Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya November 1, 2025
    An ture Mataimakin Gwamna Gefe, Tsarin karba-karba Na Goyon Bayan Kwara ta Arewa. Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak, zai kammala wa’adinsa na biyu a shekarar 2027, amma babu wata alamar cewa mataimakinsa, Mista Kayode Alabi, zai gaje shi. Yanayin siyasa a jihar na nuna cewa yankin Sanatocin Kwara Arewa ne ake sa ran zai samar da gwamna na gaba; Alabi yana daga Kwara Kudu. Kwara ta Arewa ba ta samar da gwamna da tun daga 1999, yayin da Kwara Kudu ta rike kujerar siyasa ta farko a jihar na tsawon shekaru takwas, kuma zuwa 2027 Kwara Tsakiya za ta kasance ta rike kujerar na shekaru 20. Masu nazarin siyasa guda biyu, Comrade Abdul-Rahoof Bello-Labelabe da Comrade AbdulLateef Ishowo, sun bayar...
    A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya. Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, yana mai cewa ma’aikatarsa “na shirye-shiryen ɗaukar mataki” bayan umarnin da Trump ya bayar. Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya  “Muna shirye-shirye don ɗaukar mataki a Nijeriya. Idan gwamnatin Nijeriya ba ta kare Kiristoci ba, za mu kai hari, mu kawar...
    Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku.   Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima November 1, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori November 1, 2025 Manyan Labarai Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da...
    Bug da kari Tinubu ya jinjina wa Shugaban jami’ar, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole (SAN)da ‘yan tawagarsa wajen maida hankalin da suka yi na bunkasa Jami’ar da kumna kudurinta na muradun ci gaban da ake bukata. Shi ma anashi jawabin Shugaban Jami’ar Sarkin Katsina, Alhaji. Abdulmumin Kabir Usman, wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Idah ya wakilta, ya nuna jin dadinsa kan irin kokarin da UNILORIN saboda bunkasar ilimi da kumasamar wuraren koyon kaaratu masu kyau da kuma suka dace. Ya yi ma kallon ayyukan da ak kaddamar a matsayin“ irin abubuwan da ake bukatar gani ke nan”da za su taimakawa lamarin koyarwa, koyo,da kuma bincike, inda ya kara da cewa yadda Jami’ar ta maida hankalinta wajen bunkasa dabarar koyon yin abubuwa...
    Wannan mataki ne awanni kaɗan bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da Anyanwu da wasu mutane uku, lamarin da ya ƙara ta’azzaea rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar PDP. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami November 1, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su November 1, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci November 1, 2025
      Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya November 1, 2025 Daga Birnin Sin Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar November 1, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung  November 1, 2025
    Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya fada wa Shugaban Amurka Donald Trump cewa; a Nigeria ba a lamunta da duk wani rikicin addini. Shugaban na kasar Najeriya ta mayar wa da Tinubu martani ne saboda yadda ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai jawo damuwa ta musamman”, bisa zargin cewa Mabiya addinin kiristanci suna fuskantar barazanar karewa, ya kuma yi alkawalin cewa Amurkan za ta ba su kariya. Donald Trump ya ce; Kiristoci suna fuskantar barazanar karar da su a Nigeria, an kuma kashe dubban kiristoci a kasar.” A yau Asabar, kwana daya daga wancan zancen na Tinibu ne dai shugaban kasar ta Nigeria Bola Ahamd Tinubu mayar da martanin da ya kunshi cewa:  Nageria kasa ce ta Demokradiyya,...
    Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing. Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar. Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin...
      A wannan rana, a gun taron manema labarai da aka gudanar bayan kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, Lee Jae-myung ya ce hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Koriya ta Kudu yana da matukar muhimmanci, ya kuma yi imanin cewa birnin Shenzhen na kasar Sin zai karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC cikin nasara a shekara mai zuwa.(Safiyah Ma) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 1, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka October 31, 2025 Daga Birnin Sin Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu...
    Daga Abdullahi Shettima Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna. Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.” A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi,...
    Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar nuna goyan baya ga wani kudiri da ya jaddada cewa shirin da Morocco ta gabatar kan Yammacin Sahara shi ne mafita ‘’mafi dacewa” ga yankin da ake takaddama a kai.   Kudirin ya nuna goyan bayan kasashe mambobin kwammitin ga shirin na Morocco, tare da bayyana cewa ikon masarautar kan yankin zai iya kasancewa mafita mafi dacewa. Kan hakan ne kwamitin yaya kira ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres da wakilinsa na musamman kan wannan batu, Staffan de Mistura, da su gudanar da tattaunawa “bisa ga” wannan shirin don cimma yarjejeniya da kowa zai aminta da ita. Aljeriya wacce ta ke kaddama da Morocco kan yankin ta kaurace kada...
    Shugaba Samia Suluhu Hassan, wadda ke neman wa’adin ta na farko a hukumance bayan ta gaji marigayi John Pombe Magufuli a 2021, ta tsaya takara ƙarƙashin jam’iyyar CCM mai mulki. Sai dai rashin shigar manyan ‘yan adawa da aka hana tsayawa ko aka daure ya jefa shakku kan ingancin zaɓen da aka gudanar, inda masu zanga-zanga suka yi kira da a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya da zai shirya sahihin zaɓe a gaba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3 November 1, 2025 Manyan Labarai Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa November 1, 2025 Manyan Labarai Jerin Gwarazan...