2025-10-24@22:47:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2538
«yankin Yammacin Kogin Jordan»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
“Kusan kullum muna cikin tashin hankali a Shinkafi,” in ji shi. Mutumin ya kuma zargi gwamnati daga matakin tarayya har zuwa ƙaramar hukuma da zuba wa matsalar ido. “Hare-haren suna ci gaba a Birnin Yero, Jangeru, Shanawa, da Shinkafi kanta. Ko jiya da safe sun kawo hari sun kama manoma.” A cewarsa, manoma da dama sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron za a sace su. Wasu kuma suna zuwa da dare ne kawai don samun ɗan abin da za su ci. Sai dai, gwamnatin Jihar Zamfara ta ce tana sane da matsalar da jama’ar yankin ke fuskanta, kuma tana ɗaukar matakai don magance ta. Mai magana da yawun gwamna, Mustafa Jafaru Kaura, ya ce: “Gwamnati tana yin duk abin da...
‘Yansanda sun kuma samu kuɗi Naira 92,460 da wasu abubuwan maye kamar giya da sauransu. “Wannan samame sakon gargaɗi ne ga duk masu hannu a fataucin miyagun ƙwayoyi,” in ji SP Adam. “Yaƙinmu da fataucin miyagun ƙwayoyi yana ci gaba, kuma muna kira ga jama’a su riƙa sanar da mu duk wani abin da suka gani na zargi.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara October 15, 2025 Manyan Labarai Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima October 15, 2025 Labarai Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria October 14, 2025
Shugaban Kasar Columbia Ya Soki Donald Trump Akan Bai Wa Isra’ila Makamai Shugaban na kasar Columbia Gustavo Petro ya ce, Bugun kirjin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na bai wa “Isra’ila” makamai tare da cewa ta yi amfani da su da kyau, ba wani abu ne da ya cancanci a yi masa tafi, sunan shi tarayya a aikata laifi. Shugaba Gustavo Petro yana mayar da martani ne akan zancen da shugaban kasar Amurka ya yi a Majalisar “Knesset’ ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya ce; Isra’ilan ta yi amfani da makaman da ya ba ta da kyau. Shugaba Gustavo ya kara da cewa; wadannan makaman na Amurka sun kashe mutane 70,000 sannan kuma sun jikkata wasu 200,000....
“Salon shugabancinsa da amincewa da cancanta sama da son rai ne ya sa kowane mai kishin ci gaba daga ƙarshe yake samun mafaka a APC,” in ji shi. Gwamna Mbah ya bayyana shiga jam’iyyar APC bayan tattaunawa da magoya bayansa, yana mai cewa hakan “sabuwar tafiya ce” ga Jihar Enugu da yankin Kudu maso Gabas wajen samun babban matsayi a siyasar ƙasa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta October 14, 2025 Manyan Labarai Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato October 14, 2025 Siyasa PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai October...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yadda ‘ya’yan jamiyyar PDP ke ficewa suna komawa jam’iyya mai mulki na cigaba da nuna yadda take kara samun koma baya a siyasar Najeriya. Banda haka, rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa na cigaba da yi mata dabaibayi. Shin ko hakan na nufin jam’iyyar ta fara gushewa ne a siyasar Najeriya? NAJERIYA A YAU: Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Yajin Aiki? DAGA LARABA: Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraci Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Sojoji sun kama wata mata da mijinta da suka yi kaurin suna wajen safarar makamai a yankin Saminaka da ke Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna. Dubun ma’auratan ta cika ne a wani shingen binciken inda sojojin Rundunar Operation Fansan Yamma suka gano harsasai 1,207 hannunsu. Kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom ya ce an kama su ne a hanyars ta kai wa ’yan ta’addan da ke addabar yankin Arewa maso Yamma makaman. Ya ce matar mai shekaru 18 mijin masi shekaru 40 suna tsare suna amsa tambayoyi, yana mai jinjina wa sojoji da ’yan banga bisa kwarewar da suka nuna wajen kama miyagun. Kofin Duniya: Da sauran rina a kaba duk da Najeriya ta ci Jamhuriyar Benin 4-0 Na yafe...
Tawagar Super Eagles ta Najeriya sun kara da Cheetahs na Jamhuriyar Benin a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026. Wasan da suka fafata a filin wasa na Godswil Akpabio da ke Jihar da Uyo ya kasance tamkar mai zafin gaske kuma an nuna bajinta. Tun kafin a fara wasan, an samu sauye-sauye hudu daga tawagar da ta doke Lesotho, inda Wilfred Ndidi ya hau matsayin kyaftin, yayin da Moses Simon ke shirin yin buga na 85 a wasannin kasa da kasa. A gaba kuma, an hada Victor Osimhen da Akor Adams domin tayar da kura. Wasan ya fara da sauri — ina minti na uku kacal, Osimhen ya zura kwallo ta farko bayan Chukwueze yi mika...
Dandazon ’yan bindiga sun kai hari a yankin Kankia da ke Jihar Katsina inda suka halaka mutum daya tare da jikkata wasu da dama. Shaidu sun ce ’yan bindiga kimanin 100 a kan babura ne suka kai harin a yankin Kwadawa da ke Gundumar Gashi da ke Karamar Hukumar Kankia, inda ake Ana zargin maharan sun kai harin daukar fansa ne, Maharan da suka kai farmaki a yankin da ke Gabahsin karamar hukumar, sun sace dabbobi da ba a san adadinsu ba, suna masu barazanar halaka duk mutanen yankin. Wakilinmu ya ruwaito cewa a halin yanzu mazauna yankunan Bogga, Taiba Badole, Arahiya, Kwandawa, Rumawa, Gangara da Rugar Bindo da ke gundumar Gachi da kuma Fakuwa/Kafindangi suna yin kaura domin tsira...
Rukaiya Abdullahi mawakiya ce a Masana’antar Kannywood wacce daga bisani kuma ta dawo yin fim duk a masana’antar. A hirarta da Aminiya ta bayyana yadda ta fara aiki a matsayin sakatariya ta ofishin daya daga cikin masu shirya fim. Ga yadda hirar ta kasance: Gabatar da kanki ? Sunana Rukaiya Abdullahi Yaushe kika shigo Masana’antar Kannywood? Na shigo Masana’antar Kannywood a shekarar 2020, amma zan samu kamar shekara 15 ina tare da su sai dai ban fara yin fim ba sai a 2020. Me ya jawo hankalinki kika shigo harkar fim? To da farko dai ba harkar fim na fara da ita ba a Kannywood, na fara da aikin sakatariya ne a wurin ’yan fim, yayan Nasiru Sarkin waka wato...
’Yan Majalisar Tarayya uku daga Jihar Kaduna sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Shugaban Majalisar Wakilai Abbas Tajuddeen ya sanar a ranar Talata cewa masu sauya shekar sun hada da Honorabul Abdulkarim Hussain Mohammed, Aliyu Mustapha Abdullahi da kuma Sadiq Ango Abdullahi. Tajuddeen, wanda shi ma dan asalin Jihar Kaduna ne, ya sanar da cewa, Gwamnan jihar, Uba Sani ya halarci zaman majalisar domin shaida dawowar ’yan majalisar zuwa APC daga PDP. Masu sauya shekar sun bayyana cewa rikin cikin gida da rabuwar kai da suka dabaibaye tsohuwar jam’iyyarsu ta PDP ce ta sa suka yanke shawarar sauya sheka. Shugaban Hukumar Zaɓen Yobe Jihar Yobe ya rasu Faɗa ya ɓarke tsakanin Palasɗinawa da Hamas bayan sulhu da Isra’ila...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa jami’an tsaron JMI suna cikin cikken shiri na kare kasar daga makiya, a duk lokacinda ta sake farma kasar da yaki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baghaei yana fadar haka a jiya litinin a taron yan jaridu da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin. Ya kuma kara da cewa JMI zata saurari shawarorin kawayenta amma kuma tana cikin shirin ko ta kwana idan makiya sun yi kuskure sun fadawa kasar da yaki. Baghaei ya na nuni ne da zantawar firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a makon da ya gabata, inda kuma ya bukaci shugaba...
“Idan mutum ya shiga jarrabawa kuma Allah Ya kawo dama ta afuwa, dole ne ya yi farin ciki. Ni da iyalina da masoyana mun yi murna ƙwarai,” in ji Lawan. “Na gode wa Allah da kuma Shugaba Tinubu saboda ya yi abin da ya kamata a yaba masa.” Ya bayyana cewa rayuwa a gidan yari ta koya masa juriya da fahimtar cewa komai ƙaddara ce. “Tun kafin na bar kotu na sallama komai ga Allah. Na sani cewa duk inda mutum ya samu kansa, akwai darasi a ciki,” in ji shi. Bayan fitowarsa daga gidan yari, Faruk Lawan ya sauya tafiyarsa ta siyasa. Ya ce ya rabu da tafiyar Kwankwasiyya da aka san shi da ita, duk da cewa har...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shekara da shekaru kungiyar malaman jami’oi ASUU ta kwashe ta na gudanar da yajin aiki ba tare da samun biyan bukata ba. Irin wannan yajin aiki da kungiyar malaman ke shiga ya jefa dalibai da malaman da ma harkar ilimi cikin halin ni ‘yasu a Najeriya. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa DAGA LARABA: Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraci Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wasu hanyoyin da kungiyar malaman ASUU za ta iya bi don warware matsalar ta ba tare da dogaro da gwamnatin tarayya ba. Domin sauke shirin, latsa nan
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) ta mayar da martani kan barazanar gwamnatin tarayya ta “ba aiki, ba a biya”, tana mai cewa ba za ta bari a tsoratar da ita da irin wannan gargaɗi ba. Shugaban ASUU, Chris Piwuna, ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today a ranar Litinin. Piwuna ya ce ASUU ta tsaya tsayin daka tare da sauran ƙungiyoyin Malamai kamar CONUA, da NAMDA, da SSANU, da NASU, wajen goyon bayan yajin aikin da ke gudana. Ya zargi Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, da ƙoƙarin rarraba malamai ta hanyar yin alƙawarin biyan wasu ma’aikata albashi. “Ya na ƙoƙarin rarraba kan mu, amma kan mu a haɗe yake. Babu wanda...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baqahea yayi gargadin game da barazanar da ake fuskanta na bazuwar fadan da ake yi a kan iyaka tsakanin kasar Afganistan da kuma kasar Pakistan, a yankin, inda dukkan bangarorin biyu suke musayar wuta a wurare daban daban dake kusa da iyakokin kasashen. Yace babban abin da ke da muhimmanci a wajen mu shi ne batun tsaro da zaman lafiya a kasashen dake makwabtaka da su, kasashen Pakistan da Afghanistan yan uwan mu ne musulmi dake makwabtaka da mu, kuma ya yi amanna cewa duk wani kace-nace tsakanin kasashen biyu to zai iya fantsama zuwa wasu kasashe, Jamhuriyar musulunci ta Iran ta yi kira ga kasashen biyu da su koma teburin tattaunawa, kuma...
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar wa al’ummar jihar a shirye ta ke ta ci gaba da kare mutuncin daidaikun mutane da kungiyoyin da suka sadaukar da kansu domin samar musu da sahihin bayanan sirri da za su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijar. ‘Yan sanda a jihar Neja da ma Nijeriya ƙwararru ne don haka za su ci gaba da aiki da kuma nuna basira da ƙwarewa tare da ƙa’idarta ta sirrin rashin bayyana tushen bayanansu don samun sakamako mafi girma. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Adamu Abdullahi Elleman wanda ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna, ya bayyana cewa a kwanan baya ya halarci wani taron...
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya caccaki matakin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dauka na fara yajin aiki na tsawon makonni biyu, yana mai bayyana matakin a matsayin wanda bai kamata ba kuma bai dace ba ganin irin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na biyan kusan dukkanin bukatun kungiyar. Da yake magana a wani shiri na gidan Talabijin na Channels, ‘The Morning Brief’ a ranar Litinin, Alausa ya bayyana rashin jin dadinsa da matakin da ASUU ta dauka na tsunduma yajin aiki duk da kokarin da gwamnatin ke yi akansu. “A cikin shekaru biyun da suka gabata, babu wani batun yajin aikin ASUU, saboda kokarin da gwamnati ke yi akan biyan duk bukatunsu. “A cikin sa’o’i 24 da...
Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar. Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta. Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako. Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista...
Na farko, hada kai don samar da yanayi mai kyau ga ci gaban mata. Na biyu, a karfafa abubuwan da za su habaka ingancin ayyukan mata cikin hadin kai. Kana na uku, a gina tsarin kare hakkin mata tare. Sai na hudu, a bude sabon babin hadin gwiwa tsakanin mata a duniya. Za a gudanar da taron kolin mata na duniya a yau da gobe Talata a birnin Beijing. Kuma tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, suka yi musafaha da shugabannin tawagogin kasashe, da kungiyoyin duniya da suka halarci taron, tare da daukar hotuna tare da su. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025 Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22 October 12, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025 Manyan Labarai Trump Da Al-Sisi Za Su Jagoranci Taron Zaman Lafiya Dawwamammiya Ta Gaza A Masar October 12, 2025 Manyan Labarai Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor October 12, 2025
Gwamnatin Tarayya, ta gargaɗi Ƙungiyar Malaman Kami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta aiwatar da dokar “babu aiki, babu albashi” idan malaman suka ci gaba da yajin aikin da ka iya zai kawo cikas ga harkokin karatu. A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar da yammacin ranar Lahadi, Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, da Ƙaramar Ministan Ilimi, Suwaiba Sa’id Ahmed, sun ce gwamnati tana da niyyar magance ƙorafe-ƙorafen ASUU ta hanyar tattaunawa cikin lumana. Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja “Gwamnati ta nuna gaskiya, haƙuri da kyakkyawar niyya a tattaunawarta da ƙungiyar,” in ji sanarwar. Ministocin sun bayyana cewa yawancin buƙatun ASUU, kamar ƙarin kuɗin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan October 12, 2025 Daga Birnin Sin Sharhi: Lai Qingde Ba Zai Iya Jirkita Gaskiya Ba October 12, 2025 Daga Birnin Sin Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza October 11, 2025
Wasu jerin shirye-shiryen neman ‘yancin kan Taiwan da hukumomin yankin suka gudanar a baya bayan nan, sun sha suka sosai daga al’ummomin kasa da kasa. Wani nazari da kafar CGTN ta Sin ta gudanar ya nuna cewa adadin mai rinjaye na wadanda suka shiga nazarin, watau kimanin kaso 89.8 sun yi ammana cewa, manufar kasar Sin daya tak ta zama wata matsaya da kasashen duniya suka amince da ita, inda suka soki hukumomin yankin Taiwan bisa shirinsu na neman ‘yanci da takala. Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne cikin harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 13,650 suka bayar da amsa cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sharhi:...
Sai dai duk da cewa Ousmane Dembele na kungiyar kwallon kafa ta PSG ne ya lashe gasar- Yamal ya samu nasarar kyautar gwarzon matashin dan wasa na Ballon d’Or karo na biyu a jere. Lamine Yamal, ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yanwasa mafiya farin jini tsakanin masoya kwallon kafa, musamman ma matasa saboda karancin shekarunsa da kuma yadda yake buga wasa cikin raha. Shekara da shekaru, duniya ta dauka cewa zama fitacce a fagen kwallon kafa na bukatar jajircewa da sadaukarwa. Saboda kafin dan wasa ya iya lashe wannan kyauta sai ya yi aiki tukuru. Sai dai duk da nuna kuruciyarsa, hakan bai hana Yamal cimma burinsa a fagen kwallon kafa ba. A baya ya bayyana...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar. Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi. Asuu ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata. “Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana. RN
A zahiri, zamanin da kasashen yammacin duniya ke ba da umarni ga kasashe masu tasowa ya riga ya wuce. An taba bin tsare-tsaren da kasashen yamma suka tanada, amma ba a samu nasarar da aka sa ran samu ba, wannan sakamako ya sa kasashe masu tasowa daina amincewa da huldar kasa da kasa da kasashen yamma suka tsara. Sai dai, ko wace irin sabuwar dangantakar sassan kasa da kasa muke bukata a zamanin yau? A matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta sha yin kira da a kafa sabon nau’in huldar kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna. Wannan tunani shi ma ya bayyana sarai...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Trump Da Al-Sisi Za Su Jagoranci Taron Zaman Lafiya Dawwamammiya Ta Gaza A Masar October 12, 2025 Manyan Labarai Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor October 12, 2025 Labarai Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa October 12, 2025
Garin Girfa (cinnamon), Garin kaninfari Clove) Yadda za a hada: Za’a samu garin girfa kamar cokali 5 garin kaninfari cokali 7 za a hade waje daya, sai a rika diban rabin karamin cokali ana zubawa a ruwan shayi ana sha sau 2 a rana ayi kamar sati daya. Za a samu waraka da yardar Allah. Ciwon Sanyi Abubuwan bukata: Hulba, Bagaruwa, Man Habbatussauda yadda za a hada: A hada Bagaruwa da Hulba a tafasa su, sai idan ya dan huce sai a zauna a ciki, sannan kuma za a shafa man Habbatussauda a gaban, a sashi kamar yadda za’a yi matsi. In sha Allah za a samu sauki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Adon Gari Ko Kin San… Dalilin...
Irabor ya ce, littafin nasa na ƙoƙarin kawo tarihin “tasirin Boko Haram a Nijeriya ta fannoni daban-daban” da kuma “hakikanin gaskiya a kan Boko Haram, wanda na samo a lokacin ina matsayin kwamandan soji na yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.” Tsohon babban hafsan tsaron ya ce, babban abinda ya fi tayar da hankali a yaki da Boko Haram shi ne yawan rayukan da aka rasa. A cewarsa, “irin rayukan mutanen da aka kashe a rikicin Boko Haram yana da yawa kuma ana iya kwatanta shi da annoba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna October 12, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Yi...
Abubuwan da ake bukata: Semovita (kamar kofi 3-4), Yis (Babban Cokali da rabi, idan kuna so ya tashi sosai), Suga (Babban cokali 2), Gishiri ( rabin cokali), Man gyada ko buta (Babban Cokali 2), Ruwa mai dumi (kusan 1–1½ kofi, gwargwadon yadda Semon ya sha) Yadda za a hada: Za a samu roba sai a zuba Semobita, yis, Sikari da Gishiri a kwano, a juya su da kyau, sannan a zuba ruwa, a zuba ruwan dumi a hankali a cikin hadin, a na gaurayawa har sai ya koma kulli. Sai a zuba man gyada ko Bota a ciki, a ci gaba da murzawa har kullun ya yi laushi ba ya manne ba. Sannan sai a rufe rubar da leda...
Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF) ta tabbatar da cewa ta dauki matakin gaggawa bayan faruwar lamarin inda aka aike da wani jirgin sama daga Legas domin jigilar tawagar zuwa Uyo, sai dai lamarin ya haifar da tsaiko a shirin da tawagar ta ke yi na tunkarar jamhuriyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0 October 9, 2025 Wasanni Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane October 7, 2025 Wasanni Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni October 6, 2025
Daga cikin wadanda shugaban kasar ta Nigeria ya yi wa afuwa da kawai Maryam Sanda ‘yar shekaru 37 wacce aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunta da kashe mijinta da wuka a 2017. Mai Magana da yawun shugaban kasa Bayo Onangua ya saki bayanin afuwar da shugaban kasar ya yi, wacce kuma ta hadad a Faruka Lawan tsohon dan majalisa da aka samu da laifin cin hanci da rashawa a 2021. Sai kuma Ken Saro-wiwa wanda dan fafutuka ne mai rajin kare muhalli a yankin Ogoni da aka zartarwa hukuncin kisa a 1995. Har ila yau afuwar ta shugaba Tunibu ta shafi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa wanda aka zartarwa da hukuncin kisa a 1986 saboda juyin Mulki....
Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa wannan titin ba na yankin Arewa kadai ba ne, ya bayyana shi a matsayin jijiyar ƙasa da ƙasa ne wadda ke haɗa yankuna daban-daban tare da ƙarfafa haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki. Ya kara da cewa titin Abuja- Kaduna da Kano na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Manufar Sabon Fata na (Renewed Hope Agenda), wadda ke nufin sabunta manyan gine-ginen ƙasa da inganta tattalin arziki. Yace “Wannan titi ba hanya ce kawai ba inda yace wata hanya ce ta tattalin arziki wadda ke haɗa mutane, kasuwanni, da dama a fadin Arewacin Nijeriya da ma bayan haka,” A nasa jawabin, Sanata Umahi ya yaba...
Nasarorin da kasar Sin ta samu a cikin gida, sun kafa ginshikin jagorancin duniya, wajen samar da ci gaban harkokin mata, musamman ta hanyar fitar da darussa, ta hanyar kyautata mu’amala tsakamnin bangarorin biyu. Babban misali shi ne yadda ake samun bunkasar dangantakar mata tsakanin kasashen Kenya da Sin, wadda aka inganta yayin ziyarar aiki da shugaban Kenya William Ruto ya kai kasar Sin a watan Afrilun bana. Kasashen biyu sun yi alkawarin zurfafa mu’amalar al’adu, ciki har da mu’amalar mata da matasa bisa tsarin dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Wadannan matakai sun kunshi fannoni kamar su tallafin karatu da horar da sana’o’i, kuma dukkansu sun haifar da babban sakamako. (Safiyah Ma) ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata. Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum. Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta samu nasarar ceto mutum 10 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su tsawon watanni huɗu da suka gabata a Ƙaramar Hukumar Kagarko. A cikin sanarwar da kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka ceto har da yara masu shekaru ɗaya, uku da kuma 13. Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro DSP Mansir, ya ce ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen Kushe Makaranta, inda suka sace mutanen daga gidajensu sannan suka kai su dajin da ke kusa da Rijana. Rundunar, ta ce aikin ceto mutanen ya samu ne ta haɗin gwiwar...
Shugabannin masana’antu sun kuma yi kira ga gwamnati da ta daidaita tattalin arziki, inganta saukin gudanar da harkokin kasuwanci, da aiwatar da shirye-shiryen tallafi ga masana’antu na cikin gida. Bugu da kari, masana sun nuna cewa rikicin kudin waje da rashin daidaito a kimar musayar kudi su ne manyan matsaloli ga kamfanoni masu zaman kansu daga kasashen waje, inda kalubalen samun damar mayar da ribar kamfani zuwa kasashen waje da samun kudin waje ke rage amincewar masu zuba jari sosai kuma yana karfafa su su bar kasar. Binciken da LEADERSHIP Sunday ta gudanar ya nuna cewa yanayin tattalin arzikin Nijeriya ya sha wahala tun daga shekarar 2020, inda wasu kamfanoni suka rufe ayyukansu, ko suka yi kaura, ko...
Baya ga Maryam Sanda, Shugaba Tinubu ya kuma yafe wa wasu mutane da dama, ciki har da Janar Mamman Vatsa, Herbert Macaulay, da Faruku Lawan, wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne daga Jihar Kano. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025
Li ya ce kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jam’iyyar WPK, don ta bayar da jagoranci ga al’ummun kasar Koriya ta Arewa, wajen neman ci gaba bisa halin da kasar take ciki. A sa’i daya kuma, kasar Sin tana fatan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama, kamar aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare da kara musayar manyan jami’ai, da mu’amala kan manyan tsare-tsare, ta yadda za a inganta fahimtar siyasa a tsakanin kasashen biyu, tare da cimma sakamako mai kyau bisa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Koriya ta Arewa. (Mai Fassara: Maryam Yang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ma’aikatar Wajen...
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar wasu sojoji huɗu, bayan ’yan ta’adda sun kai hari yankin Ngamdu na Jihar Borno. Jihar Borno ta daɗe tana fama da hare-haren ta’addanci, musamman daga ƙungiyar Boko Haram. Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno An yi jana’izar sojojin da ’yan bindiga suka kashe a Kebbi Ko da yake wasu mazauna yankin sun ce sojoji 10 ne suka mutu, sai dai mai magana da yawun rundunar Operation Haɗin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, bai tabbatar da hakan ba cikin sanarwar ya fitar a ranar Juma’a. Amma rahotanni sun bayyana cewa sojoji huɗu ne suka mutu, yayin da wasu biyar suka jikkata a yayin harin. A cewar Kanar Sani, ’yan ta’addan sun yi amfani da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 9, 2025
Ya bayyana cewa an riga an hada wadanda aka ceto da iyalansu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike da aikin ceton domin gano wadanda suka aikata laifin da kuma kubutar da sauran wadanda ake tsare da su, idan suna nan. A halin da ake ciki kuma, kwamandan Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba da saurin daukar mataki da hadin kai tsakanin sojoji da ‘yansanda wanda ya kai ga nasarar aikin ceton. Ya sake jaddada kudirin rundunar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Jihar Taraba. Sai dai, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa sojoji da sauran hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar...
Mataimakin shugaban kasar Iran Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, batun kifar da gwamnatin JMI bayan yakin kwanaki 12 ya kuma fita daga abinda makiya zasu iya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar yanakalto mataimakin shugaban kasa na farko yana fadar haka a ranar Alhamis da ta gabata, ya kuma kara da cewa a cikin yakin kwanaki 12 wanda kasashen Amurka da HKI suka dorawa kasar sun so su kifar da gwamnatin JMI a cikin kwanaki 3 zuwa 4 amma suka kasa. Ya ce hatta babban sakataren MDD Antonio Guterres ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da shi dangane daha. Ya kuma tabbatar da cewa makiyan JMI ba zasu iya tumbuke tsarin ba. Yasashen yamma musamman Amurka suna kokarin...
Masu zanga-zanga a nan Iran a jiya jumma’a a manya-manyan garuruwan kasar bayan sallar Jumma’a sun bayyana goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu a Gaza, sannan sun bukaci HKI ta aiwatar da yarjeniyar da ta cimma da kungiyoyi masu gwagwarmaya. Har’ila yau sun bukaci a gaggauta shigo da abinci da magungunacikin zirin Gaza. Tashar talabijin talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga zangar wadanda suka hada da mata da maza, malaman addini, daliban jami’o’i da sauransu suna tattaki daga dandalin inkilab zuwa dandalin azadi. Har’ila yau sun rera wakoki na goyon bayan masu gwagwarmayar, dauke da hotunan shahidai da kuma shuwagabannin kawancen masu gwagwarmaya a yankin. An gudanar da jerin gwanon a cikin manya manyan biranen...
Rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwarta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara October 5, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ October 4, 2025 Tsaro Bayan Sulhu Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina September 22, 2025
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wani Shirin zaman lafiya da ya hada da dakatar da kisan kiyashi a Gaza Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan duk wani mataki ko wani yunkuri da ya hada da kawo karshen yakin kisan kiyashi a Gaza, janyewar sojojin mamayar Isra’ila, shigar da kayan agajin jin kai, sakin fursunonin Falastinawa, da kuma tabbatar da dukkanin hakkokin Falasdinawa. Haka kuma ta kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mai goyon bayan halastacciyar gwagwarmayar al’ummar Falastinu samun tabbatar da ‘yancin kai, ta yi amfani da dukkanin karfinta na diflomasiyya a cikin shekaru biyun da suka gabata, musamman...
Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya
Kasar Venezuela ta yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya tabbatar da cewa Amurka tana yin barazana zaman lafiyar duniya Kasar Venezuela ta yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince cewa; Lallai Amurka tana yin barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, saboda yadda sojojin Amurka suke shisshigi a tekun Caribbean, wannan batu ya zo ne a yayin zaman gaggawa na majalisar a jiya Juma’a. Wakilin dindindin na Venezuela a Majalisar Dinkin Duniya, Samuel Moncada, ya ce: “Suna ba da shawarar ayyuka uku ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya: Na farko, amincewa da barazanar zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa da sojojin Amurka suka haifar a cikin...
Ministar wadda ta je kamfanin domin daukar sabuwar motarta ta alfarma kirar Nord Demir SUB da kamfanin ya hada nataimakin Shugaban jami’ar na sashen kula da ilimi da gudanar da bincike Farfesa Bola Oboh da kuma Shugaban kamfanin Mista Oluwatobi Ajayi ne, suka karbi bakuncinta. A jawabin da ta gabatar a lokacin ziyarar ministar ta bayyana cewa,Duba da yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci wajen fitar da kaya zuwa ketare kamfanin zai iya yin amfani da wannan samar waken fitar da motocinsa zuwa ketare. Ta kara da cewa, Nijeriya na da gurare biyu ne da ake hada motoci da suka hada da, na wannan jami’ar da kuma na EPs, inda ta yi nuni da cewa, karfin da kamfanin ya ke da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata October 10, 2025
“Ta yaya Jonathan zai zama barazana? Mun doke shi a baya lokacin da PDP take kan mulki. “Idan mutum yana ganin cewa PDP ita ce kololuwar jam’iyya a Nijeriya, kuma ya sha kaye a lokacin da yake ganiyarsa, ina ganin sai makiyinsa ne kawai zai tilasta masa ya kara tsayawa takara a zaben 2027,” in ji shi. Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce a yanzu haka Jonathan ya kasance dan siyasa mai daraja, yana mai cewa komawa fagen siyasa na iya rage masa kima da kuma zubar masa da darajar da yake da shi a idon duniya. Ya jaddada cewa Jonathan ya samu damar nuna cewa mulki bai tsole masa ido ba, domin haka ne...
Aƙalla mutum takwas ’yan Ƙungiyar tsaro ta Civilian JTF ko ’yan ƙato da gora aka sanar an kashe a ƙauyen Dan Loto da ke Ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Harin dai na zuwa ne makonni biyu kacal bayan da wasu ’yan bindiga suka kai hari a wani masallaci tare da kashe wasu masallata biyar ciki har da wani Limami a ƙaramar hukumar. ’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali — Likita Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe Dan Loto yana cikin yankin Yandoton Daji, unguwar da ’yan bindigar suka kashe masu ibada biyar a ranar 26 ga Satumba, 2025. Binciken Daily Trust ya nuna cewa, ’yan bindigar sun yi wa ’yan ƙungiyar...
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, a gefen wani taro a kasar Tajakisatan da yake halatta a kasar ya bayyana ce firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya fada masa cewa ya isar da sakonsa ga gwamnatin JMI kan cewa yana son a warware matsalolin da ke tsakaninsa da JMI cikin lumana ba tare da tashin hankali ba. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana shugaba shugaban yana son yazama mai tsaga tsakani a rikicin da JMI take yi da HKI da kuma hukumar maikula da makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA, a dai dai lokacinda yake kiyaye dangantakarsa ta diblomasiyya da kasashen biyu. Putin ya kara da cewa ya sami sakonni daga HKI kan cewa mu fadawa Tehran HKI...
Wani Likitan ƙwaƙwalwa a Asibitin Neuropsychiatric Aro, a Abeokuta, Jihar Ogun, Dokta Emmanuel Abayomi ya ce kimanin mutane miliyan 60 ne ke fama da taɓin hankali a halin yanzu. Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma’a a Abeokuta a wajen wani taron ƙarawa juna sani da Ƙungiyar likitoci ta NAS ƙarƙashin Ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta ƙasa ta shirya domin tunawa da ranar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa ta duniya ta bana. Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna Shirin da Ash Montana Deck tare da haɗin gwiwar Atlantis, Americana 1 da Longhorn Deck suka yi wanda ya ja hankalin ‘yan sanda da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta samu nasarar ceto wasu mutum uku da aka sace, bayan wani samame da ta kai a jihohin Kano da Kaduna. Wannan na daga cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi domin yaƙi da laifuka da tabbatar da tsaron jama’a. ’Yan sanda sun manta hularsu a motar dalibi bayan karɓar ‘cin hancin’ N99,000 NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne tsakanin ranar 7 zuwa 9 ga watan Oktoba, 2025, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori. A cewar Kiyawa, samamen farko ya gudana ne a ranar...
“Akwai da yawa malamai marasa cancanta a cikin aikin. Muna da wadanda ke koyarwa a ajujuwa amma ba su da takardun shaidar koyarwa, musamman a makarantu masu zaman kansu,” in ji ta. Ta bayyana cewa, yayin da wasu mutane ke da sha’awar koyarwa da gaske, rashin horo na hukuma ya hana su shiga aikin koyarwa. Dr. Soyombo ta bayyana cewa TRCN a halin yanzu na da malamai masu rijista kusan miliyan 1.4, tare da shirin kara wannan adadi zuwa miliyan 20 cikin shekaru biyu masu zuwa ta hanyar dijital da saurin rajista. “Mun zamanantar da tsarinmu domin mutane da yawa su sami damar yin rijista,” in ji ta. “Kowane malami yana da bai wa ta musamman...
Wani dalibi mai suna Olawale Ayomide ya zargi wasu ’yan sanda da ke aiki a ofishin Igbeba da ke yankin Ijebu Ode a jihar Ogun da tatsar Naira 99,000 daga hannunsa ba bisa ka’ida ba. Ayomide ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, inda ya ce ɗaya daga cikin ’yan sandan da ake zargi ya manta hular aikinsa a cikin motar bayan sun aikata abin da ake zarginsu da yi. A cewarsa, ’yan sandan sun tsayar da shi ne a lokacin da yake tafiya daga Shagamu zuwa Ijebu-Ode a cikin motar mahaifiyarsa, inda suka zarge shi da tuƙi ba tare da lambar mota ba. Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya ’Yan...
Kazalika, tarihin Dimokiradiyyar kasar ya sha cin karo da kwam gaba kwam baya kusan za a iya cewa, tun bayan dawowar mulkin Demokaradiyya a 1979 da kuma sake dora kasar a wata turbar ta Demokiradiyyar a 1999. Alal misali, jamhuriyya ta hudu ta kasance ta jima sosai, amma kusan babu wasu ayyukan na inganta rayuwar ‘yan kasar da za a bigi Kirji a ce gasu an gani a kasar a zahiri. Idan aka dubi bangaren samar da hasken wutar lantarki kusan za a iya cewa, karni da dama da suka bace, har zuwa yau Nijeriya ta gaza samar da karfin wutar da kuma rabar da ita da ta kai karfin Megawatts 5,000 musamman duba da cewa, wannan adadin...
Yawan mace-mace ta hanyar cutar kwalarar, na faruwa ne duk da biliyoyin Nairori da aka ce gwamnati da abokan huldar kasa da kasa suna kashewa, domin kokarin ganin an dakile ta. Wadannan kudade sun hada da kason kasafin kudi na shekara-shekara, wanda ya kunshi miliyoyin Nairori; akwai dala miliyan 700 da bankin duniya ya bayar domin samar da tsaftataccen ruwa sha, tsaftar muhalli a fadin kasa baki-daya, tallafin dala miliyan 2 daga Majalisar Dinkin Duniya, dubban daruruwan allurar rigakafin cutar kwalara da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka bayar da sauran makamantansu. Alkaluman da aka samu daga cibiyar NCDC, sun nuna cewa a cikin 2020, kasar ta samu rahoton...
Ministan albarkatun mai na Jamhuriyar Nijar Sahabi Oumarou, ya gana da Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Nijar. A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna kan muhimamn batutuwa da suka shafi alakoki da ke tsakanin kasashe biyu da kuma yadda za a kara inganta su. Sannan kuma sun yi musayar ra’ayi kan hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta fuskar cin moriyar juna. Jamhriyar Nijar da Iran suna da kyakkawar alaka ta diflomasiyya, kamar yadda kuma suna yarjeniyoyi da dama da ayyukan hadin gwiwa a fagage daban-daban na diflomasiyya, cinikayya da bunkasa harkoki tattalin arziki da kimiyya da fasaha. Bangarorin biyu sun jaddada wajabcin ci gaba da tuntubar juna domin aiwatar da dukkanin yarjejeniyoyi da aka rattaba hannu a kansu a...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama mutum 26 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kwato makamai da kudade daga hannunsu. Daga cikin abubuwan da aka samu nasarar kwatowar har da bindigogi na gida guda huɗu, makamai masu hatsari da kuma tsabar kuɗi Naira 546,000 da ake zargin wani ɓangare ne na kuɗin fansa. Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC An kama waɗanda ake zargin ne a cikin jerin samame da aka gudanar daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2025, a sassa daban-daban na jihar. Samamen ya haɗa jami’ai daga sashen ’yan sanda na Anchau, Hukumar Kula da Tsaro...
Dare ya jaddada cewa Nijeriya kasa ce mai addinai da dama, wacce aka gina bisa juriya, zaman lafiya, da girmama juna tsakanin mabambantan addinai, al’ummomin da ya ce Tinubu ya shugabanta. Dare ya ambaci maganar Shugaban Kasa inda ya jaddada cewa Nijeriya “kasa ce mai cikakken ‘yanci da girma, wadda aka gina bisa bangaskiya da juriyar jama’arta,” ya kara da cewa “Babu wani addini da ake zalunta, kuma babu wata al’umma da aka ware.” Yana nuna misali da rayuwar Shugaban Kasa a matsayin shaida ta juriya da fahimtar addinai, Dare ya bayyana cewa Shugaba Tinubu, Musulmi ne da yake auren fasto mai bin addinin Kirista. Ya kuma ruwaito Shugaban yana cewa, “Gaba da kiyayya ba su da gurbi...
‘Yan majalisar dai sun amince da naɗin, inda Gwamna Ahmed Usman Ododo ya bayyana Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya. Dangane da kundin tsarin mulkin 1999 (kamar yadda aka gyara), yanzu Shugaba Tinubu zai aika da sunan Amupitan zuwa Majalisar Dattawa don tantancewa. Amupitan, mai shekaru 58, daga Ayetoro Gbede, karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi, Farfesa ne a fannin shari’a a Jami’ar Jos, Filato, kuma tsohon ɗalibin jami’ar ne. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta October 9, 2025 Manyan Labarai Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin October 9, 2025 Siyasa Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso...
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko October 8, 2025 Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025 Daga Birnin Sin Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana October 8, 2025
A yayin yanke hukuncin, kotu ta bayyana cewa: “Na farko (INEC) da na biyu (Farfesa Mahmood Yakubu) an yanke musu hukuncin tura su gidan gyaran hali saboda rashin bin hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Osogbo, Jihar Osun, ta bayar a shari’a mai lamba FHC/OS/CS/194/2024 a ranar 17 ga 5 Fabrairu, 2025.” Kotu ta kuma umarci Sufeton ‘yansanda na ƙasa da ya kama Yakubu tare da tabbatar da fara shari’ar hukuncin raina kotu cikin kwanaki bakwai daga ranar da aka yanke hukuncin. Bugu da ƙari, kotu ta ci tarar INEC da Yakubu Naira 100,000 domin biyan masu shigar da ƙarar saboda raina umarnin kotu. Masu shigar da ƙarar sun haɗa da Action Alliance, Farfesa Julius Adebowale, Injiniya Olowookere Alabi, Barrista...
ShareTweetSendShareMASU ALAKA WasanniBa Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane October 7, 2025WasanniYanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni October 6, 2025WasanniKwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar October 6, 2025
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi, za su fuskanci martani mai tsanani Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) Manjo Janar Mohammad Pakpour ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi a mashigar tekun Farisa, da mashigar Hormuz da tsibirin Iran, za su fuskanci hukunci mai tsauri, nan take, murkushewa, da kuma nadama. A cikin sakon taya murnar zagayowar ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, Manjo Janar Pakpour ya bayyana cewa: “A jajibirin ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, yana mika sakon taya murna ga babban matsayi na kwamandoji da mayakan da suka yi...
Shugaban kasar Ecuador ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi da aka yi Ministan Makamashi na Ecuador, Ines Manzano ya sanar a ranar Talata cewa: An yi yunkurin kashe shugaban kasar Daniel Noboa kuma an kama wasu mutane biyar da ke da hannu a ciki makarkashiyar. Manzano ya ce “Motar Noboa na kewaye da gungun mutane kusan 500 da suke jefanta da duwatsu a lokacin da yake tafiya a cikin ayarin motocin zuwa lardin Cañar, inda aka shirya zai sanar da jerin ayyukan samar da ababen more rayuwa.” Ta kara da cewa: “Daga baya an samu alamun harsashi a motar, amma Noboa bai samu rauni ba a harin.” Hukumomin kasar sun sanar da cewa: Wadanda ake tsare...
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da sabuwar cibiyar taro ta Ahmadu Bello da aka gina a Bauchi, inda ya bayyana ta a matsayin alamar ci gaba a gwamnatin Gwamna Bala Mohammed. Da yake jawabi a wajen taron, Obasanjo ya jaddada muhimmancin dunkulewar duniya, inda ya ce babu wata al’umma da za ta iya rayuwa a ware ba tare da yin hulda mai ma’ana da sauran kasashen duniya ba. Ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed bisa ayyukan raya kasa, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, wanda a cewarsa hakan zai karawa Bauchi damar karbar bakuncin taron kasa da kasa da kuma jawo hankalin masu zuba jari. Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa irin wadannan...
Gwamna AbdulRazaq ya yabawa Shugaba Tinubu yayin da Sojoji suka tura cikakken birgediya domin fatattakar masu garkuwa da mutane daga dazukan Kwara. Hedkwatar sojojin Najeriya ta aika da cikakken birgediya da manyan kayan aiki a sassa daban-daban na Kwara ta Kudu, domin rage matsalolin tsaro a yankin. Wata sanarwa da sakataren yada labarai gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar ta ce Tuni dai sojojin suka yi ta luguden wuta ta cikin kauyukan Oke Ode da Babanla, dukkansu a karamar hukumar Ifelodun. Har ila yau, rundunar ta kara da cewa, aikin ya zarce zuwa Edu da Patigi domin ratsa dazuzzukan da masu garkuwa da mutane suka fara kai hare-hare na matsorata a kan al’ummomi daban-daban tare da yin...
Cristiano Ronaldo ya zama biloniya na farko tsakanin ƴan wasan kwallon kafa a duniya Bloomberg mai sharhi da kididdiga tarin dukiya tsakanin attajiran duniya, ta fayyace tarin kudin da mai shekara 40 dan kwallon tawagar Portugal mai taka leda a Al-Nassr ta Saudiya ke da shi. Ta ce yana da dalar Amurka biliyan daya da miliyan 400 daga kudin da yake samu na albashi da ladan wasa da tallace-tallace da zuba hannun jari. Ya samu albashin sama da dalar Amurka miliyan 550 tsakanin 2002 zuwa 2023 da kwantiragin da ya kai dalar Amurka miliya 18. Lokacin da Ronaldo ya koma Al-Nassr ta Saudiyya a 2022, ya zama wanda ke kan gaba da ake biya albashi mafi tsoka a tarihi. da...
Haka kuma, ya jaddada buƙatar ƙara zuba jari a fannin ilimi, lafiya, da gine-gine don samar da ci gaba mai ɗorewa.Bankin ya ƙara da cewa, idan gwamnati ta ci gaba da aiwatar da waɗannan sauye-sauyen cikin tsari, tattalin arziƙin Nkjeriya zai iya ƙaruwa zuwa kashi 4.4 nan da shekarar 2027.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiTinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas October 8, 2025Manyan LabaraiKwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi October 8, 2025Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025
Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar iran Mohammad Eslami da manyan jami’a daga hukumar rasatom ta hadin guiwar ayyukan makamashin nukiliya sun gana a birnin Tehran kuma sun tattauna kan yadda za su yi aiki tare a bangaren shirin ta na nukiliya na zaman lafiya, Nikolai Spassky ya kawo ziyara iran ne a birnin Tehran tun bayan ziyarar da Eslami ya kai birnin mosko a ranar 24 ga watan satumba, inda bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, na yin aiki tare wajen gina karamar tashar nukiliya iran. Haka zalika bangarorin biyu sun tattauna kan yarjejeniyar da aka kula lokacin da Eslami ya kai ziyara da ya hada da yin aiki tare a cibiyar nukiliyar iran...
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinBabban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025Daga Birnin SinYawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana October 8, 2025Daga Birnin SinAdadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7 October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinAdadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7 October 8, 2025Daga Birnin SinSin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa October 8, 2025Daga Birnin SinSin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare October 8, 2025
Kakakin majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai na kafa tsarin ‘yansandan jihohi a kasar nan domin magance kalubalen tsaro da ake fuskanta.Abbas ya bayyana haka ne a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin dokar hukumar leken asiri da binciken sirri ta shekarar 2024, wanda kwamitin majalisar kan harkokin tsaro da leken asiri ya shirya a harabar majalisar dokokin kasar da ke Abuja ranar Laraba.Kakakin majalisar wanda ya samu wakilcin mamba mai wakiltar mazabar Ilorin ta Yamma/Asa, Honarabul Muktar Shagaya, ya ce, kawo sauye-sauye a fannin tsaro ya zama abinda aka fi mayar da hankali, kuma yanzu dole a tashi daga rubutu kawai zuwa aiwatar da cikakken tsari.Shugaban majalisar ya ce kafa ‘yansandan jihohi ta...
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinSin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa October 8, 2025Daga Birnin SinSin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare October 8, 2025Daga Birnin SinKasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata October 7, 2025
Jaridar Daily Mail ta kasar Burtaniya ta nakalto firay ministan HKI Benyamin Natanyahu yana gargadin Amurka kan abinda ya kira, makamai masu linzami masu keta nahiyoyi wadanda JMI take ginawa barazana ce ga Amurka. Ya ce makaman suna iya isa biranen Amurka daga cikin har gidan Trump da ke ‘Mar-a-Lago’, a bakin ruwa na Palm Beach a jihar Florida. Daily mail ta nakalto Natanyahu yana fadar haka a hirar da ta hada shi da wani dan jirada mai suna Ben Shapiro. Ba tare da bada wata hujja ko dalili ba, Natanyahu ya ci gaba da cewa, makaman wadanda suke iya zuwa wurare masu nisan kilomita 800 zasu kai biranen washington da kuma NewYork har da kuma gidan shugaba Trump dake...
Alkaluman da kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin wato China Railway ya gabatar, sun nuna cewa, ana sa ran jigilar fasinjoji kimanin miliyan 21 da dubu 750, ta jiragen kasa a kasar Sin a yau Laraba. Kana tun daga ranar 29 ga watan Satumban da ya gabata, wato ranar da aka kaddamar da aikin jigilar fasinjojin da suka yi tafiye-tafiye, a lokacin hutun bikin tunawa da kafuwar kasa da na Zhong-Qiu, zuwa jiya Talata, an riga an kwashe fasinjoji fiye da miliyan 160 ta jiragen kasa a kasar Sin.Yau ce ranar karshe a hutun na wannan karo, don haka ake sa ran ganin karuwar zirga-zirgar mutane da suke kokarin komawa gidajensu daga wuraren da suka yi bulaguro. Hakan ne...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum da ake zargin ɗan bindiga ne da ke aiki tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru. Rundunar ta kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai 80 da wasu tarin makamai. Gwamnatin Gombe ta kafa hukumar bunkasa fasahar zamani da tattalin arziƙi Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa wanda aka kama, Adamu Adamu, mai shekaru 30, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Song a Jihar Adamawa. Amma wanda aka kama mazaunin unguwar Jauro Jatau da ke Akko, Jihar Gombe. An kama shi ne ranar 4 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihan bayanai da suka nuna cewa yana tare da wata...
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun tare hanyar Gusau zuwa Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama. Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun tare motoci sannan suka yi awon gava da fasinjojin da ke ciki. Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Wani shaida ya ce ’yan bindigar sun ɗauki lokaci suna sharafinsu kafin daga bisani suka tafi da mutanen da suka kama. Daga cikin waɗanda suka sace akwai Malam Sadis Isa, shugaban Majalisar Malamai ta Ƙaramar Hukumar Gummi, abin da ya jefa al’umma cikin tsoro da damuwa. “Da yammacin ranar Talata, ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ƙaddamar da sabon ginin Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa, wadda aka sanya wa sunan Sir Ahmadu Bello a Jihar Bauchi. An ƙaddamar da cibiyar ne kafin babban taron zuba jari da nufin bunkasa kasuwanci da masana’antu a jihar. Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC A jawabinsa, Obasanjo ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed, bisa irin ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa, waɗanda ke inganta rayuwar jama’a. “Na yi farin ciki da abin da na gani da kuma abin da na ji. Ban zata cewa zan dawo Bauchi cikin ƙanƙanin lokaci don buɗe irin wannan katafaren waje...
“Yanzu muna kammala sabbin sharuɗan aikin da ASUU ta gabatar, kuma za mu bayyana amsar gwamnati nan ba da jimawa ba,” in ji shi.“Shugaba Tinubu yana da niyyar kawo ƙarshen wannan matsala gaba ɗaya.”Ya roƙi ASUU da ta ci gaba da tattaunawa maimakon fara yajin aiki, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na da niyyar gaskiya da jajircewa wajen warware matsalar.LEADERSHIP ta ruwaito cewa ASUU ta fara shirin tursasa wa mambobinta fara yajin aikin gargadi, yayin da wa’adin kwanaki 14 da ta bai wa gwamnati zai ƙare a ranar Lahadi mai zuwa.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Labarai‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato...
Ya buƙaci jama’a suke bambanta “gaskiya da siyasa.”ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa October 7, 2025
Ya gargaɗi masu aikata laifuka da su daina, ko kuma su fuskanci hukunci, inda ya bayyana cewa waɗanda aka kama tuni aka miƙa su kotu.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Labarai‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025LabaraiCika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya October 7, 2025
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ziyarci Banki bayan harin, inda ya yaba da jarumtar mazauna garin tare da alƙawarin bunƙasa tsaro a yankin.Zulum, ya kuma sanar da shirin sake mayar da mazauna ƙauyuka uku; Kumshe, Tarmu’a da Bula Yobe, sannan ya tabbatar da cewa aikin gyaran hanyar Banki ya an fara shi.Ya buƙaci matasa su yi rajistar katin zaɓe, tare da jan hankalin ‘yan kasuwa su haɗa kai da jami’an tsaro domin ɗorewar zaman lafiya.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025LabaraiCika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya October 7, 2025LabaraiSSANU, NASU Za Su Gudanar Da...
Haka kuma ya buƙaci a aiwatar da gyare-gyare don farfaɗo da tattalin arziƙi, inganta ilimi da kiwon lafiya, tare da samar da damammaki ga matasa.Ya ƙara da cewa majalisar za ta sake duba Kundin Tsarin Mulki na 1999 domin bunƙasa dimokuraɗiyya da inganta mulki a Nijeriya.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa October 7, 2025Manyan LabaraiTinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026 October 7, 2025
Uche Nnaji, Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, ya yi murabus daga mukaminsa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata. Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Jerin ministocin da zargin takardun bogi ya tabaibaye su Nnaji na fuskantar zarge-zarge kan sahihancin takardun karatunsa, inda binciken da jaridar Premium Times ta gudanar ya gano cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ta ce ba ta ba shi takardar kammala digiri ba. A cewar jami’ar, tsohon Ministan bai kammala karatunsa a cikinta ba, kuma ba ta taɓa ba shi takardar shaidar kammala ta ba. A cewar jaridar, Simon U. Ortuanya, Shugaban Jami’ar UNN, ya...
Shirye-shiryen sun kammala domin Shugaban Ƙasa ya sanar da sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), bayan da Farfesa Mahmood Yakubu ya kammala wa’adin mulkinsa na shekara goma a ranar Talata. Kafin Yakubu ya sauka daga mukaminsa, rahotanni sun nuna cewa fadar shugaban ƙasa na nazarin mutum uku da ake has ashen za su iya maye gurbinsa: Farfesa Joash Ojo Amupitan, Mai Shari’a Abdullahi Mohammed Liman da Farfesa Lai Olurode. Wata majiya a fadar shugaban ƙasa ta shaida wa Aminiya cewa an kammala nazari, kuma Farfesa Amupitan ne ke kan gaba a jerin waɗanda ake hasashen don maye gurbin tsohon shugaban INEC. Majalisa za ta yi dokar kula da harkar Crypto da POS Ya kamata a karɓe...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci. Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri baya bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takardun Shaida Na Bogi Ga Rayuwar Al’umma DAGA LARABA: Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan zamani da ma irin halin da almajirai suka tsinci kan su a ciki. Domin sauke shirin, latsa nan
Wannan sanarwar ta baya bayan nan da kasar Sin ta yi, ya samu yabo sosai, musammam daga sakatare janar na MDD, yana jaddada cewa, shirin na Sin na da muhimmanci matuka ga tunkarar sauyin yanayi. Su ma kafafen yada labarai na kasa da kasa da manyan jami’an hukumomi da kasashe da dama, sun yaba wa shirin, wanda ya nuna cewa, ana kara ammana da irin rawar da kasar Sin ke takawa a harkokin da suka shafi duniya. Ba alkawari da gabatar da shirin kadai take yi ba, ta kasance mai aiwatar da su a aikace kuma ana ganin nasarorin da take samu a zahiri. Zuwa yanzu, babu wata kasa da ta bayar da gudunmuwa a wannan bangare kamar kasar Sin, kuma...
ShareTweetSendShareMASU ALAKA LabaraiTinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk October 7, 2025Ra'ayi RigaCikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka October 7, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025
Jami’an kare hakkin dan’adam na MDD sun nuna jin dadinsu dangane da hukuncin da kotun duniya ta manyan laifuka ( ICC) ta yanke akan mutum na farko da aka tuhumka akan laifukan Darfur na kasar Sudan. A jiya Litinin ne dai kotun manyan laifuka ta duniya ta yanke hukunci akan Ali Muhammad ali Abd-Al-Rahman wanda ake yi wa lakabi da Ali Khushayb, bisa samunsa da laifi akan laifukan yaki a Darfur shekaru 20 da su ka gabata. Daga cikin laifukan da aka tabbatar da akan Ali Kushayb da akwai bayar da umarnin yi wa mutane da dama kisa, da kashe fursunoni biyu da gatari. Alkalai uku ne su ka yi zaman shari’ar da aka yanke hukuncin tare da samun wanda...
Tinubu, a cikin wata wasika da ya aikewa kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen wanda ya karanta a zaman majalisar a ranar Talata, ya kuma buƙaci majalisar ta amince da batun shirin Sukuk da zai kai kusan dala miliyan $500 a cikin ICM.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Ra'ayi RigaCikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka October 7, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025LabaraiGwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu October 7, 2025
Hukumar kula da yan gudun hijirar a majalisar dinkin duniya ta jinjinawa kasar Iran game da kokarin da tayi wajen kulawa da miliyoyin yan gudun hijira kasar Afghanistan , da suka zauna a kasar na tsawon shekaru, Babban darakta na hukumar ta IOM shi ne yayi wannan bayani ga Mohammad Batgae mtaimakin ministan harkokin cikin gidan kasar iran a birnin janeva a jiya litinin, a wani taro da suka gudanar a bayan babban taron Majalisar dinkin duniya karo na 76 da hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya take gudanarwa. Ana sa bangaren bathaei babban jami’I na kasar Iran ya bayyan yadda jamhuriyar musulunci suka bada kula ta musamman ga dubban yan gudun hijiran kasar ta Afghanistan...
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu
A cewarsa, gyaran yana taimakawa wajen samun bayanai daidai domin tsara ci gaba da kuma rarraba albarkatun ƙasa bisa adalci daga gwamnatin tarayya.“Wannan tsarin yana daidai da yadda ake yi a wasu jihohi, inda ake amfani da bayanan masarautu, yankuna da ƙauyuka wajen tsara ci gaba da rarraba kuɗaɗe,” in ji shi.Gwamnan ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen haɗa kan jama’a da tallafa wa ayyukan ci gaba, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da sabon tsarin cikin gaskiya.Ya yaba wa kwamitin bisa jajircewarsu da yadda suka gudanar da aikin cikin gaskiya da tsari.Tun da farko, shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya bayyana cewa sun karɓi buƙatu 196, wanda 17 don kafa sabbin masarautu, 166 don sabbin yankuna, da...
Ya gode wa Shugaba Bola Tinubu da shugabannin tsaro bisa goyon bayansu wajen yaƙi da rashin tsaro a Kogi.Tags: KogiOdodoTsaroShareTweetSendShare Sadiq Related LabaraiMajalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya 1 hour agoManyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa 2 hours agoManyan LabaraiTinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026 3 hours ago
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya NAHCON da ta rage kuɗin Hajjin bana, inda ya buƙaci hukumar ta fito da sabon kuɗin nan da kwana biyu. Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya bayyana wannan buƙatar a ganawarsa da shugabannin hukumar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja a ranar Litinin. Ya yi kira da a samu ƙarin haɗin kai tsakanin hukumar a matakin ƙasa da takwarorintna na jihohi ciki har da gwamnoni domin a samu sauƙin gudanar da aikin Hajjin na bana. Da yake ganawa da manema labarai bayan taron, mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia ya ce an yi taron ne domin ƙarƙare shirye-shiryen Hajjin na...
Mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Nasarawa sun zabi sabbin jami’anta da za su gudanar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa. Shugaban kwamitin zaben, Mista Samson Osuo, ya sanar da Abubakar Abdullahi na jaridar Daily Trust a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 21 da Danjuma Joseph na National Accord da kuri’u 9 a matsayin shugaban kungiyar. Ya kuma bayyana cewa Mista Chris Nyamtu na gidan rediyon Najeriya ne ya yi nasara da kuri’u 21 yayin da Augustine Kuza na jaridar Pilot na Najeriya ya samu kuri’u 9 a matsayin Sakatare. Mista Abel Daniel na jaridar Guardian a matsayin mataimakin shugaba Awayi Kuje na NAN a matsayin Mataimakin Sakatare, Michael...
Ƙungiyar shugabannin jam’iyyun siyasa (IPAC) ta ce lokaci ya yi da za a cire ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) daga hannun Shugaban ƙasa. Ƙungiyar ta ce kamata ya yi a kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai riƙa yin naɗin shugaban INEC da kwamishinoni da sakatare na hukumar domin tabbatar da gaskiya da cin gashin kai na hukumar. Shugaban ƙungiyar IPAC, Dakta Yusuf Mamman Ɗantalle, ne ya bayyana haka a wani taro da suka yi da kwamitin Majalisar Wakilai da ke nazarin kundin tsarin mulki a Abuja. Ya ce tsarin da ake amfani da shi yanzu na bai wa shugaban ƙasa damar zaɓar shugaban INEC na iya rage amincewar jama’a da hukumar. Jerin...