Iran Da Kasahen E3 Zasu Tattauna Batun Shirin Nukliyar Kasar A Sitziland A Gobe Talata
Published: 25th, August 2025 GMT
Za’a gudanar da wani taro tsakanin Iran da kasashen Turai E3 ko Troiko a kasar Switziland a gobe Talata 26 ga watan Augusta da muke ciki.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa tattaunawar Iran tare da kasashen Jamus, Burtaniya da Faransa zata kasance na kan shirin Nukliyar kasar Iran da kuma batun daukewa kasar takunkuman tattalin arzikin da kasashen turai suka dora mata.
Labarin ya kara da cewa mataimakin ministan harkokin wajen kasar Majid Takht Ravanchi ne zai jagoranci tawagra Iran zuwa birnin Geneva don tattaunawar, kuma ana saran tuni sun kasar can don halattan taron.
A ranar jumm’an da ta gabata ne ministan harkokin wajen kasar ta Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa ya zanta ta wayar tarho tare da tokwarorinsa na kasashen Burtaniya, Faransa da Jamus tare da jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na tarayyar turai dangane da taron.
Ya kuma kara da cewa ya fada masu, kan cewa duk wani kokarin da kasashen zasu yi na amfani da ‘shirin Snapback” na shekara ta 2015 wanda kuma ya zo tare da kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2231 zai kara bata dangantaka tsakaninsu da Iran, kuma akwa maida martani mai tsanani.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Bangaladesh Ta Kasa Samun Kudaden Kula da Yan Gudun Hijiran Rohinga August 25, 2025 Jagora: Hadin Kan Al’umma, Jami’ai Da Sojojin Kasa Da Suke Dauke Da Makamai Jan Layi Ne August 25, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Bukatar Gudanar Da Hidima Ga Al’umma Daga Kowane Dan Kasa August 25, 2025 Kwamandan Sojojin Iran Ya Jaddada Aniyar Iran Na Wurga Makiya Cikin Nadama August 25, 2025 Kafofin Watsa Labaran Isra’ila Sun Ce: Ba Za A Iya Hana Sojojin Yemen Kai Hare-Hare Kan Isra’ila Ba August 25, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Kai Hari Kan Kungiyar Red Crecent A Kasar Sudan August 25, 2025 Hamas: Da gangan Netanyahu ya dakatar da tattaunawar zaman lafiya August 25, 2025 Iran: Pezeshkian ya yaba da kalaman Jagora Kan hadin kan al’umma August 25, 2025 Isra’ila ta kai hari kan ababen more rayuwa na fararen hula a Yemen August 25, 2025 Araqchi ya isa Saudiyya don halartar taron gaggawa na OIC a kan Gaza August 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces
Gwamnatin Sudan ta ce: Babu batun sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces na kasar wadanda take daukansu a matsayin ‘yan tawaye
Gwamnatin Sudan ta yi watsi da shawarar sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) da kasashen kasashe masu shiga Tsakani suka gabatar, tana mai jaddada cewa, tana mutunta duk wani kokari da zai taimaka wajen kawo karshen yakin kasar, matukar dai ya mutunta diyaucin kasar da halaltattun hukumomin kasar.
Sa’o’i kadan bayan kaddamar da shirin na bangarori hudu masu shiga tsakani wanda ya hada da Masar, Amurka, Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa, na kiran zaman lafiya a Sudan da kawo karshen yakin, dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan tashar samar da wutar lantarki da ma’ajiyar man fetur da kuma filin jirgin saman Kenana na jihar White Nile da jiragen sama marasa matuka ciki.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira da a ba da sanarwar yin watsi da shirin, inda ta yi nuni da cewa, yaƙin na da nasaba da al’ummar Sudan, kuma za ta tunkare shi, ta kuma yanke shawara da kansa.
Wani mai sharhi kan al’amuran siyasa Youssef Abdel Manan ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Alam cewa: “Kasashen hudu masu siga tsakani ba su da wani hakki, ko na hukuma, ko na dabi’a, ko na siyasa, ko na kasa da kasa, da zai sanya su zama masu kula da al’ummar Sudan.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Kasar Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-Zargen Da Kungiyar G7 Da Kawayenta Suka Yi Kanta September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci