An Cire Maguire Cikin Tawagar Ingila Da Za Ta Buga Wasan Neman Gurbi
Published: 14th, March 2025 GMT
Sabon kocin Ingila, Thomas Tuchel ya cire ɗan wasan bayan Ingila Harry Maguire cikin jerin ƴanwasan Ingila da za su buga wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026.
Cikin jerin ƴan wasa 26 da sabon kocin ƙasar Thomas Tuchel ya fitar, ranar Juma’a ya sanar da sunan Marcus Rashford bayan cire shi a wasannin baya.
Haka ma kocin ya saka sunan tsohon ɗan wasan Liverpool da ke taka leda a ƙugiyar Ajax, Jordan Henderson cikin tawagar.
A karon farko mai tsaron ragar Burnley, James Trafford da ɗan wasan bayan Liverpool, Jarell Quansah za su iya samun damar buga wa babbar tawagar Ingila ƙwallo ba a ke cikin tawagar
A ranar Juma’a, 21 da watan Maris ne tawagar Ingila za ta ƙarbi baƙuncin Albania a filin wasa na Wembley, kafin ranar Litinin 24 ga watan na Maris ta kara da ƙasar Latvia a wasannin neman gurbin.
Ga jerin ƴan wasan 26 ga Thomas Tuchel ya fitar domin fafatawa a wasannin.
Masu tsaron raga: Dean Henderson (Crystal Palace), Jordan Pickford (Everton), Aaron Ramsdale (Southampton), James Trafford (Burnley)
Ƴanwasan baya: Dan Burn (Newcastle United), Levi Colwill (Chelsea), Marc Guehi (Crystal Palace), Reece James (Chelsea), Ezri Konsa (Aston Villa), Myles Lewis-Skelly (Arsenal), Tino Livramento (Newcastle United), Jarell Quansah (Liverpool), Kyle Walker (AC Milan, loan from Manchester City)
Ƴan wasan tsakiya: Jude Bellingham (Real Madrid), Eberechi Eze (Crystal Palace), Jordan Henderson (Ajax), Curtis Jones (Liverpool), Cole Palmer (Chelsea), Declan Rice (Arsenal), Morgan Rogers (Aston Villa)
Ƴan wasan gaba: Jarrod Bowen (West Ham United), Phil Foden (Manchester City), Anthony Gordon (Newcastle United), Harry Kane (Bayern Munich), Marcus Rashford (Aston Villa, loan from Manchester United), Dominic Solanke (Tottenham Hotspur)
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Wasanni
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta zargin yin katsalandan a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya musanta zargin katsalandan din Iran a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza.
A yayin da yake amsa tambaya game da ikirarin da shugaban kasar Amurka ya yi na cewa Iran na tsoma baki a shawarwarin tsagaita bude wuta a zirin Gaza, ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da dukkan kasashen duniya tana yin kakkausar suka kan kisan gillar da ake yi a Gaza tare da goyon bayan duk wani tsari da zai kai ga dakatar da aikata laifuka da kuma rage radadin wahalhalun da al’ummar Gaza suke ciki.
Baqa’i ya jaddada cewa; Masu yin shawarwarin Hamas sun fahimci bukatar neman cimma muradun al’ummar Gaza da ake zalunta ta hanyar da ta dace, kuma ba sa bukatar shiga tsakani na bangarori na uku dangane da hakan.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya yi la’akari da katsalandan din Iran a cikin shawarwarin da suka dace da cewa ba shi da tushe balle makama, yana mai jaddada cewa irin wadannan zarge-zarge wani nau’i ne na neman tauyaye hakki da gujewa hakkin da ya rataya a wuyar mutum da kokarin Amurka na gujewa duk wani mugun aiki da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta aikita kan al’ummar Falasdinu, da suka hada da kisan fararen hula 60,000 da ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da mata da kananan yara da kuma killace Zirin Gaza tsawon watanni. Da hana shigar agajin jin kai da kuma kashe fararen hula da ke fama da yunwa da kishirwa a tarkon kisa a wuraren da ake kira cibiyoyin rarraba kayan agaji da wata cibiyar Amurka ta kafa.