An Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Kan Karfafa Rawar Da MDD Ke Takawa A Beijing
Published: 25th, March 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya ce a jiya Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron karawa juna sani na kasa da kasa, mai taken “Karfafa rawar da MDD ke takawa, tare da habaka ra’ayin cudanyar bangarori daban daban” a nan birnin Beijing.
Guo ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na yau da kullum da ya jagoranta a yau Talata, inda ya ce daukacin mahalarta taron na karawa juna sani sun yi imanin cewa, a halin da ake ciki, ya kamata a karfafa ayyukan MDD, da inganta hadin kai da hadin gwiwa, da kuma tinkarar kalubale daban daban da ake fuskanta a duniya.
Dangane da taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar raya kasar Sin na shekarr 2025 da aka gudanar a nan birnin Beijing kwanan baya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, taron shekara-shekarar na bana, ya samu halartar wakilan kasashen wajen sama da 750, kuma kamfanonin da suka halarci taron sun fito ne daga kasashe daban-daban, lamarin da ya nuna cewa, kamfanonin kasashen waje suna da kwarin gwiwar yin kasuwanci da Sin.
Game da rahoto mai taken “Hukumomin leken asiri na Amurka suna sa ido da satar bayanai da suka shafi tashoshin wayar salula na duniya”, wanda kawancen kamfanonin tsaro na Intanet na kasar Sin ya fitar a yau, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin ta nuna matukar damuwa game da munanan ayyukan da Amurka ke yi a yanar gizo da aka bayyana a cikin rahoton, ya kuma bukaci Amurka da ta gaggauta dakatar da hakan. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar da Manufar Sauyin Yanayi
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar wata kungiya mai suna Partnership for Agile Governance and Climate Change (PACE) ta kaddamar da manufofinta na sauyin yanayi a hukumance. Wannan manufa mai mahimmanci ta samar da taswirar dabaru don ragewa, daidaitawa, da tsarin tafiyar da yanayi mai hadewa a duk sassan ci gaba a jihar.
Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da taron wanda aka gudanar a dakin taro na Armani Event Centre dake Kano, Gwamna Abba Yusuf wanda sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Farouk ya wakilta, ya bayyana taron a matsayin wani babban ci gaba a kokarin gwamnatinsa na mayar da jihar Kano a matsayin mai ci gaba a harkokin tafiyar da yanayi da muhalli.
Gwamna Yusuf ya jadadda cewa, manufar tana cike da shirin aiwatar da sauyin yanayi, wanda ke fassara kudirin siyasar gwamnati zuwa tsarin aiwatarwa a aikace.
Ya kuma yi tsokaci kan shirye-shiryen da gwamnati ke yi na samar da makamashi ta hasken rana da ababen more rayuwa.
Gwamnan ya nanata shirin gwamnatin sa na dasa itatuwa miliyan 5 a shekarar 2025 domin rage zaizaiyar kasa, da inganta iskan shaka, da inganta kyawawan birane.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO