An Yi Gargadi Akan Rushewar Kungiyar Agajin Falasdianwa Ta UNRWA
Published: 14th, March 2025 GMT
Shugaban kungiyar agajin Falasdinawa ta “UNRWA’ wacce MDD ta kafa, ya yi gargadin rushewarta da hakan zai hana Falasdinawa na yanzu samun ilimi, haka nan kuma bayar da kayan agaji da bukatun yau da kullum ga mutane miliyan 6 a Falasdinu.
Shugaban kungiyar Agajin Philippe Lazzarini ya fada wa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa; Da akwai hatsari da gaske da kungiyar take fuskanta na rushewa, da hakan zai kara dagula yanayin da al’ummar Falasdinu suke ciki.
Philippe Lazzarini ya kara da cewa; Idan hakan ta faru, to mun sadaukar da falasdinawan da suke rayuwa a wannan lokacin da hana su ilimi.
Tun bayan farmakon Aksa 2023 ne dai HKI da Amurka su ka dauki matakin haramta kungiyar da dakatar da duk wani aiki da ita.
MDD ce dai ta kafa wannan kungiyar domin taimakawa Falasdinawan da kirkirar HKI ya yi sanadiyyar mayar da su ‘yan gudun hijira.
Wasu kasashe da kuma kungiyoyi da dama a duniya sun yi tir da matakin na HKI da kuma Amurka akan wannan kungiya.
Da akwai yaran Falasdinawa 100,000 a cikin Gada kadai da suke karatu a karkashin makarantun kungiyar.
Philippe Lazzarini ya ce, idan aka hana wadannan yaran karatu to mun shuka irin tsattsauran ra’ayi, wanda zai zama babban bala’i.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba
Babban hafsan hafsoshin sojan Iran Manjo janar Musawi ya ce, ko kadan Iran ba ta yarda ko gaskata alkawullan Amurka,balle kuma zancen ‘yan sahayoniya.
Babban hafsan hafsoshin sojan na Iran ya kuma kara da cewa, sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana domin kalubalantar duk wan igigi na abokan gaba.
Manjo janar Musawi ya bayyana hakan ne dai a lokacin da ya yi tattaunawa ta wayar tarho da ministan tsaron kasar Tajikistan Manjo janar Imam Ali Sabir Zadeh.
A nashi gefen, ministan tsaron kasar ta Tajikistan, ya fara da yi wa janar Musawi murnar zabarsa sabon hafsan hafsoshin sojan kasar ta Iran, sannan kuma ya nuna bakin cikinsa akan rashin kwamandojin sojan Iran da su ka yi shahada a sanadiyyar harin ta’addancin HKI.
Manjo janar Imam Ali Sabir Zadeh ya kuma kara da cewa, al’ummar kasar Tajikinstan sun yi bakin ciki, don haka suna isar da ta’aziyyarsu ga al’ummar Iran.
Har ila yau minstan tsaron kasar ta Tajikistan ya yi ishara da tarayya akan harshe da al’ada da kasashen biyu su ka yi, haka nan kuma tarihi.
Haka nan kuma manjo janar Musawi ya yi wa Tajikistan godiya akan yadda ta kasance a tare da Iran a lokacin yakin kwanaki 12, lamarin da ya kara karfin alakar kasashen biyu.