Tinubu zai sake zama shugaban ƙasa a 2027 — Akpabio
Published: 28th, March 2025 GMT
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu nasarar lashe zaɓe don yin wa’adi na biyu a 2027, duk da ƙoƙarin ’yan adawa na ƙalubalantarsa.
Yayin da yake jawabi a wajen liyafar buɗa-baki da ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC (PGF) ta shirya a Abuja, Akpabio ya nuna ƙwarin gwiwa cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da mulki.
“Za mu dawo a 2027, da sunan Yesu, Amin,” in ji shi.
“Za mu yi wa jam’iyyarmu da Shugaban Ƙasa addu’a. Wa’adin mulkinsa na biyu ya tabbata.”
Liyafar, wacce gwamnonin APC, ’yan majalisa, da ministoci suka halarta, ta zama gangamin siyasa, inda shugabannin jam’iyyar suka jaddada nasarorin Tinubu.
Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce APC za ta ci gaba da mulki: “Yunƙurin ’yan adawa na ƙwace mulki daga hannun Tinubu ba zai yi nasara ba.
“Dole mu yi amfani da ‘wa’azin siyasa’ don nuna ci gaban da muka samu.”
Duk da cewa Tinubu bai sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a karo na biyu ba, shugabannin APC sun fara gangamin mara masa baya ta hanyar taruka da nuna goyon baya, yayin da ’yan adawa ke sukar hakan a matsayin kamfe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nasara wa adi Zaɓe Zaɓe 2027
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki”
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da jijjiga sakamakon sauya sheƙar da ’yan siyasa daga ɓangarori daban-daban suke yi.
A baya-bayan nan tsallakawar da wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa suka yi zuwa Jam’iyyar APC mai mulki ta jawo ɗiga ayar tambaya a kan dalilansu da kuma makomar hamayya a zaɓen 2027.
Hakan dai yana faruwa ne a daidai lokacin da wasu ’yan ƙasar suke kokawa bisa yadda ake gudanar da mulki da kuma yadda wasu manyan ’yan siyasa suke fadi-tashin kafa wata inuwa da suka ce za ta ciro wa talaka kitse a wuta ta hanyar kawar da gwamnatin APC.
NAJERIYA A YAU: Dalilin da zazzaɓin cizon sauro ba ya jin magani DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin ArewaWannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai da nufin gano alƙiblar da siyasar Najeriya take shirin fuskanta.
Domin sauke shirin. Latsa nan