HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Gwamna Abba ziyarar barka da Sallah
Published: 1st, April 2025 GMT
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a fadar gwamnatin jihar.
Sarkin dai ya kai wa gwamnan ziyarar ce kamar yadda aka saba a Hawan Nassarawa da ake gudanarwa bisa al’ada duk shekara.
Sai dai a sakamakon haramcin gudanar da haye-hayen sallah da rundunar ’yan sandan jihar ta yi, Sarkin bai cika duk tsare-tsaren da al’ada ta tanada ba na gudanar da Hawan Sallah.
Aminiya ta ruwaito cewa, Sarkin wanda ya yi ƙoƙarin kawar da idon jama’a, ya bi ta wasu hanyoyin da ba su aka saba bi wajen kai wa gwamna ziyara a yayin gudanar da hawan cikakke.
Haka kuma, Sarkin ya yi amfani da jerin gwanon motoci ƙalilan maimaiko hawa dawakai
Sai dai an tsananta tsaro a duk hanyoyin da Sarkin ya bi tun daga Fadar Sarki ta Gidan Ƙofar har zuwa Gidan Gwamnatin Kano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hawan Nasarawa Jihar Kano Sarki Sanusi II
এছাড়াও পড়ুন:
Miliyoyin Mutane Sun Gudanar Da Bukukuwan “Idin Gadir” A Tehran Da Sauran Garuruwan Iran
A yau Asabar aka gudanar da bikin ranar ” Idin Gadir” a nan birnin Tehran, wanda ya tashi daga dandalin “Inqilab” zuwa dandalin ” Azadi” mai nisan kilo mita 10. Bisa la’akari da halin yake da ake ciki, an bai wa bikin na bana taken: Iran ce, takobin Zulfikar Na Imam Ali.”
Miliyoyin mutane ne dai su ka cika filin bikin na birnin Tehran da mutane su ka fara taruwa tun da tsakar rana, har zuwa bayan faduwar rana. A bisa kirdado kusan mutane miliyan 3 ne su ka taru a nan Tehran.
A cikin sauran birane da garuruwan Iran an yi wannan irin gangamin na raya ranar Idin Gadir wanda yake tattare da girmama shahidan da su ka kwanta dama sanadiyyar hare-haren ta’addancin HKI. Haka nan kuma mahalarta bikin na Gadir sun jinjinawa dakarun kare juyin musulunci na Iran da kuma sojojin kasar akan martanin da su ka mayarwa da HKI a daren jiya Juma’a da kuma a yau Asabar.